108
1 MUHIMMAN FATAWOYI AKAN TSARKI, SALLAH DA KUMA AZUMI GUDA 150 DR. JAMILU YUSUF ZAREWA AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA August, 2018

MUHIMMAN FATAWOYI AKAN TSARKI, SALLAH DA KUMA … · Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke

  • Upload
    others

  • View
    2

  • Download
    0

Embed Size (px)

Citation preview

  • 1

    MUHIMMAN FATAWOYI

    AKAN

    TSARKI, SALLAH DA KUMA AZUMI

    GUDA 150

    DR. JAMILU YUSUF ZAREWA AHMADU BELLO UNIVERSITY,

    ZARIA

    August, 2018

  • 2

    بسم اهلل الرحمن الرحيم

    Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah

    su tabbata ga annabi Muhammad manzon tsira da mutanen gidansa da

    sahabbansa.

    Hakika ilimin fiqhun musulunci yana daga cikin ilimomi masu muhimmanci

    wa]anda mutane suke bu}atarsu saboda lamuransu na yau da kullum,

    wannan yasa malamai suka himmatu wajan dawwana wannan ilimin da

    kuma karantar das hi.

    A cikin wannan takardu mun tattaro muhimman FATAWOYI wa]anda suka

    shafi TSARKI, SALLAH da kuma AZUMI daga cikin amsoshin

    tambayoyinmu da muka rubuta a social Media, muna ro}on Allah ya sanya

    albarka a cikinsu ya zamar da su ambato mai kyau gare mu bayan

    rayuwarmu.

    Ina mika godiya ga dalibaina da suke taimakawa wajan tattara wa]annan

    fatawoyi musamman Ashabu Nafi’u da Auwal Balarabe da kuma

    ]an’uwanmu masoyin ilimi da malamai malam Umar Shehu Zaria, da kuma

    Uwar gidana Ummu Huda wacce take hakuri dani saboda amsa wa]annan

    fatawoyi.

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    13-8-2018

  • 3

    BABI NA FARKO

    FATAWOYIN DA SUKA SHAFI TSARKI

  • 4

    1. SIFFAR WANKAN JANABA

    Tambaya:

    Don Allah malam Ina so a siffanta min yadda ake yin wankan janaba,

    saboda ban jima da zama cikakken mutum ba!

    Amsa:

    To ]an’uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda ]aya daga cikin

    abubuwa guda biyu : ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi, ko

    kuma mutum ya sadu da matarsa, duka wa]annan suna wajabta wanka,

    wankan janaba yana da siffofi guda biyu, duk wacce ka ]auka ta yi :

    1. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa manzon

    Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi idan ya zo wankan janaba

    yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun

    hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya debi

    ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa,

    sannan sai ya wanke }afarsa. Bukari da Muslim.

    2. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake siffanta mata

    wankan janaba, inda yake ce mata : "Ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a

    kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka"

    Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 330.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    7-3-2014

    2. IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA

    Tambaya:

    Malam idan ya zama mace ba ta yin haila sai duk bayan wata uku, yaya

    idarta za kasance?

    Amsa:

  • 5

    To malam dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko

    kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk

    shekara take yin haila sau ]aya, saboda Allah ma]aukaki ya rataya idda ne

    da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Ba}ara aya ta : 228

    "Kuma matan aka saka, to za su jira tsawon jinane uku" Don haka duk

    tsawon lokacin da za ta zauna to dole sai ta jira su, kamar yadda ayar take

    nunawa.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    11/3/2014

    3. HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BU{ATA

    A BAN[AKI

    Tambaya:

    Salam, yaya hukuncin mutumin da ya kalli alkibila yayin da yake biyan

    bu}atarsa, amma kuma yana ban]aki ba'a fili yake ba ?

    Amsa:

    To malamai sun yi sa~ani akan wannan hukuncin, Abu-hanifa ya hana

    hakan, Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda

    hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa: "Na hau ]akin Hafsa sai na

    ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana biyan bu}atarsa,

    yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya", kamar yadda Bukari ya

    rawaito a hadisi mai lamba ta : 145.

    Saidai abin da ya fi shi ne : kar mutum ya fuskanci alkibla, ko da a gida ne,

    saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a

    gare shi yake cewa: "Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci al}ibla

    kada kuma ku bata baya" Bukhari a hadisi mai lamba ta : 394 da muslim a

    hadisi lamba ta : 264, tabbas barin kallon al}ibla yayin biyan bu}ata shi ne

    ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sa~anin malamai, don

  • 6

    haka idan mutum zai gina masai a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga

    alkibla. Don neman }arin bayani duba: bi]ayatul-mujtahid 1\115.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    20/3/2014

    4. SHEKARUN DA MATA SUKE FARA YIN HAILA DA KUMA

    SHEKARUN DA SUKE DAINAWA

    Tambaya:

    Malam ban wuce shekaru goma sha]aya ba a duniya, amma na shiga

    ban]aki sai na ga wani jini ya fito min, har ya fara jika }aramin wandona, to

    malam shin wannan jinin haila ne ko kuma na cuta ne ? don na ga kamar

    shekaruna ba su kai na yi jinin haila ba, Allah ya yi maka albaka a rayuwa.

    Amsa:

    To 'yar'uwa yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 amma

    wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan

    shekara 50, wannan ya danganci yanayinta da kuma wurin da take zaune.

    Malamai sun yi sa~ani: shin akwai wata shekara ta musamman da mace take

    fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin da ya sameta kafin wannan

    ko bayan wannan shekarun ba za'a kira shi jinin haila ba? Darimi -Allah ya

    yi masa rahama- ya ce bayan ya am~aci sa~anin da aka yi: (Wannan duk

    kuskure ne a wajena), domin abin lura shi ne samuwar jinin, don haka duk

    lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekara ne ya wajaba a sanya shi

    ya zama haila", abin da Darimi ya fada shi ne daidai saboda Allah da

    manzonsa sun rataya hukunce- hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, ba su

    kuma iyakance wasu shekaru na musamman ba, kamar yadda aya ta :222 a

    suratul ba}ara take nuni zuwa hakan, wannan yake nuna mana iyakance shi

    da lokaci na musamman yana bu}atar dalili na daga litttafin Allah ko daga

    sunnar manzonsa, ba’a kuma samu ba.

  • 7

    Saboda haka jinin da kika gani sunansa jinin haila, saboda kamar yadda

    malamai suka fada duk jinin da ya fito daga gaban mace sunansa jinin haila

    mutukar ba'a samu wani dalili da yake nuna cewa na cuta ne ba . Allah ne

    mafi sani, Don neman }arin bayani duba : Dima’u]]abi’iyya shafi na : 6

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    9-4-2014

    5. HUKUNCIN {ARI KO RAGI A CIKIN AL'ADA

    Tambaya

    Assalamu alaikum, da fatan mallam yana cikin koshi lafiya, don Allah

    malam ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana biyar na saba yi to

    amma wannan karan kwana tara ya yi min, bayan na yi wanka da kwana uku

    sai kuma wani brown din abu tare da jini ka]an yake fito min wanda har

    yanzu bai dena ba, shi ne nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen

    lamarin nawa. Nagode

    Amsa

    Wa alaikum assalam. To malama ana iya samun ragi ko }ari a jinin haila, do

    n haka }arin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka

    ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar

    bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sall

    ah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila,

    to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu A]]iyya ya yi nuni, inda take c

    ewa: "Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila. Bu

    khari 1\426

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    20/04/2014

  • 8

    6. BAMBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI DA KUMA

    WADIYYI

    Tambaya:n

    Don Allah malam ina so a bambance min tsakanin wa]annan ruwaye da

    suke fita, wato maniyyi da maziyyi da kuma wadiyyi ?

    Amsa:

    To ]an’uwa ga abin da ya sawwaka, game da wannan tambayar :

    1. Maniyyi

    Maniyyin namiji: ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa ya yin babbar

    sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin

    da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko

    damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshi kwai.

    Maniyyi mace: ruwa ne tsinkakke, mai fatsi-fatsi, wani lokacin kuma yana

    zuwa fari, wanda yake fitowa ya yin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa

    da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, sannan za ta ji

    tsananin sha'awa da kuma dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama

    da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin

    kamshi kwai, kuma za ta ji sha'awarta ta yanke bayan fitowarsa. hukuncinsa

    shi ne : yana wajabta wanka.

    2. Maziyyi:

    Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin }aramar sha'awa, kamar tunanin

    aure ko kuma tuna wacce kake so ko ta~a ta, haka nan yana fitowa yayin

    wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya sa sha'awa ta tafi, kuma wani

    lokacin ba'a sanin ya fito.

    Malamai suna cewa: Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza, lokacin da

    maziyyi zai fitowa namiji azza}arinsa zai mike, hukuncinsa shi ne a wanke

    farji gaba ]aya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala .

    3. Wadiyyi wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a }arshen fitsari, ko

    kuma }arshen bahaya ga wanda ya jima bai yi ba, yana fitowa ga wa]anda

  • 9

    suke fama da gwauranci ko wa]anda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta

    aure, yana ]aukar duka hukunce-hukuncen fitsari

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    30-11-2014

    7. SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCINSU

    Tambaya :

    Don Allah Malam Ina bu}atar bayani akan ‚kudra‛ da kuma ‚sufrah‛, Allah

    ya saka da Alkhairi.

    Amsa :

    To 'yar'uwa wannan yana daga cikin mas'aloli masu mutukar muhimanci,

    amma ga abin da ya sawwaka game da hakan:

    Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwan ciwo, ya fito

    daga gabanta.

    Kudra kuwa na nufin ‚ruwa ya ringa fitowa daga farjin mace, wanda kalarsa

    ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da ba}i wato kamar ruwa gurbatacce‛.

    Idan ]aya daga cikinsu ya kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana ha]e da

    haila kafin ta sami tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan kuma

    bayan tsarki ne to ba haila ba ne saboda fa]in Ummu-a]iyya mun kasance

    ba ma }irga sufra da kudra bayan tsarki a cikin haila) Abudawud ya rawaito

    shi da sanadi mai inganci, sannan an rawaito daga A’isha RA: (Mata suna

    aiko mata da abin da suke sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra

    (wato ruwan da yake kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi

    gaggawa har sai kun ga farin ruwa ya fito, za mu yi amfani da hadisin

    Ummu-a]iyya bayan an sami tsarki, ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta

    kirga su a cikin haila ba, hadisin A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan

    tana cikin haila ta yadda za ta kirga dasu. Don neman }arin bayani duba:

    Dima'uddabi'iya shafi na: 8

  • 10

    Allah ne mafi sani

    06/12/2014

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    8. SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE?

    Tambaya:

    Salam ]an’uwa kuma malamina ga tambaya naji wata fatawa wacce ba ni da

    ilimi akanta, wai idan mutun ya yi sallah babu alwala wai hukuncinsa sai ya

    sake kalmar shaha]a ta shiga musulunci, menene ingancin wannan

    maganar? Allah ya taimaka Amin.

    Amsa:

    To malam wannan maganar ta shahara a wajan mutane, saidai a wajan

    malamai yin sallah babu alwala ya kasu kashi biyu:

    Idan ya aikata, amma bai halatta hakan ba, ya san ba daidai ba ne, kamar ya

    aikata saboda kasala, wannan kam bai kafirta ba, saidai ya aikata babban

    zunubi. Idan ya aikata yana mai halatta hakan, ko kuma saboda izgilanci ga

    addini, sannan ba jahili ba ne, ba shi kuma da wani ta'awili, tabbas wannan

    aikin kafirci ne, har ma malamai da yawa sun hakaito ijma'i akan kafircin

    wanda ya yi hakan, saboda akwai karyata shari'a a ciki, da kuma

    wulakantata. Don neman karin bayani Duba: Almajmu'u na Nawawy 2\84 da

    minhajussunnah 5\204

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    12\12\2014

    9. TAYI ALWALA DA RUWAN FITSARI, HAR TA YI SALLAH

    BA TA SANI BA

    Tambaya:

    Na kasance lokacin Ina makarantar kwana idan seniona ya aikeni debo ruwa

    kafin na kawo masa ruwan sai nayi fitsari a cikin ruwan, kuma ban san

    adadin mutanen dana yiwa hakan ba, saboda ganin yadda senioyinmu suke

  • 11

    gallaza mana da sunan seniority, ga shi yanzu ban san inda zan gansu ba

    ballantana na nemi afuwar su, me ya kamata na yi kenan a yanzun? nagode,

    Allah ya }ara maka imani da ilmi mai amfani

    Amsa :

    To 'yar'uwa ina ro}on Allah ya kare mu daga irin wannan ]anyan aikin,

    Allah ya sa su kuma shawagabannin ma}arantu su kula da irin wannan cin

    zalin da ake yi a ma}arantun kwana, ina ba}i shawara ki yawaita istigfari,

    mutukar lokacin da kika yi hakan kin balaga, su kam sallarsu da wankansu

    sun inganta, saboda a zance mafi inganci na malamai duk wanda ya yi alwala

    da ruwa mai najasa, bai kuma gano hakan ba, sai bayan lokacin sallar ya fita,

    to ba zai sake sallar ba, haka ma wanda ya yi wankan janaba, saboda addinin

    musulunci addini ne mai sau}i ba ya kama mutum da abin da bai sani ba.

    Allah ne mafi sani . Duba Al'ausad na Ibnul- munzir shafi na 18 .

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    15/2/2015

    10. MUN GAMA SALLAH, ASHE LIMAN YA MANTA BA SHI DA

    TSARKI!

    Tambaya:

    Assalamu alaikum, malam mune muka yi sallah muna karewa liman ya ce ya

    manta bai da tsarki, ya yi fitsari bai yi tsarki ba,. zamu maida wata sallah ne

    ko ta limance kawai babu, ko dukkanmu sallarmu tayi ?

    Amsa:

    To ]an’uwa sallar liman ta ~aci, kuma dole ya sake, amma ku sallarku ta

    inganta, a zancen mafi yawan malamai, saboda dalilai kamar haka :

    1. An rawaito daga Umar- Allah ya yarda da shi cewa: ya ta~a yiwa mutane

    limancin sallar asuba, bayan an gama sallah, sai ya ga maniyyin mafarki a

    jikin tufansa, sai ya sake sallah, amma mamun ba su sake ba.

  • 12

    2. Sayyidina Aliyu yana cewa : "Idan mai janaba ya yiwa mutane limanci,

    zan umarce shi ya yi wanka, ya sake sallah, amma ba zan ce da mamun su

    sake ba .

    3. Abdullahi dan Umar - Allah ya yarda da shi- ya ta~a yiwa mutane sallar

    asuba, sai ya tuna ba shi da alwala, sai ya sake amma mamu ba su sake ba.

    Abin da ya gabata aikin sahabbai ne, aikin sahabi hujja ne, in ba'a samu wani

    sahabin ya saba masa ba. Don neman }arin bayani duba : Almugni 1\419.

    Allah ne mafi sani Dr. Jamilu Zarewa

    27/4/2015

    11. SHIN ZAN IYA YIN TSARKI DA RUWAN ZAMZAM ?

    Tambaya :

    Malam wani ya tambaye ni, shin zai iya yin tsarki da ruwan zamzam,

    saboda ya ji an ce yana }ara karfin mazakuta, to gaskiya malam ban sani ba,

    shi ne na ce bari na tambayi Fukaha'u ?

    Amsa :

    To ]an’uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a

    hadisi cewa : Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir,

    duba Faidhu Alkadeer 3/489.

    Saidai duk da haka ya halatta ayi tsarki da shi a zance mafi inganci, saboda

    ba'a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin }a’idojin

    malamai duk abin da ba'a samu nassin hani akansa ba a cikin mu'amalolin

    mutane to ya halatta, Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo

    daga hannun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ruwan

    zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba . Don neman }arin bayani

    duba : Hashiyatu Ibnu-abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27. Allah ne mafi sani

    Jamilu Zarewa

    18/9/2015.

  • 13

    12. MATAR DA TA GAYYATO JININ HAILA KAFIN LOKACINSA,

    YAYA SALLARTA?

    Tambaya:

    Salam mallam, ina hukunchin macen da in mijinta ya fitine ta da jima'i take

    shan magani don jini yazo mata, Yaya hukuncin jinin yaya kuma maganar

    sallah, ? tunda gayyato jinin ta yi.

    Amsa:

    To 'yar'uwa Allah da manzonsa sun rataya hukunce-hukuncen jinin haila ne

    da samuwarsa, kamar yadda aya ta : 222 a suratul-Bakara take nuni zuwa

    hakan, duk da cewa gayyato shi ta yi saidai zai dauki dukkan Hukunce-

    hukuncen haila, mutukar ya zo da siffofinsa (Ba}I, }arni, kauri).

    Gayyato jini saboda hana miji jin dadi bai dace ba, saboda duk dabarar da za

    ta kai zuwa haramun to ita ma ta zama sa~on Allah, Ya wajaba ga mace ta

    baiwa miji kanta duk lokacin da yake bukata, in ba tana da uzurin da sharia

    ta yarda da shi ba, don haka bai kamata mace ta hana mijinta saduwa da ita

    ba ta hanyar dabara. Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    31/10/2015

    13. BANA IYA RI{E ALWALA, YAYA SALLATA ?

    Tambaya:

    Salamun Alaikum, Malam barka da yau, Malam ina fama da matsalar basir

    wadda har takai wasu lokutan ban iya ri}e alwala, ko da kuwa na shiga bayi,

    in nayi alwala sai ta karye kafin a gama sallah, kuma ko na sake wata hakan

    zai sake faruwa, to malam yaya zanyi?

    Amsa:

    To ]an’uwa ina ro}on Allah ya yaye maka wannan musibar, Mutukar a mafi

    yawan lokutan rayuwarka kana fama da tusa, to abin da yake kanka shi ne:

  • 14

    i. Ka rinka yin alwala yayin kowacce sallah, duk abin da ya fito bayan

    haka, ba zai hana ingancin sallarka ba, Allah ba ya ]orawa rai abin da

    ba za ta iya ba.

    ii. Idan a wasu lokutan take fitowa, ta yadda hakan ba ya maimaituwa a

    rabin rayuwarka, ko mafi yawanta, to ya wajaba ka yi alwala duk

    lokacin da ta fito.

    iii. Duk cutar da Allah ya saukar tana da magani, don haka zai yi kyau ka

    nemi Magani iya ba}in ko}arinka a wajan masana.

    Don neman }arin bayani duba : Alfawakihuddawany na Annafraawy 1\340.

    Allah ne mafi safi.

    Dr. Jamilu zarewa

    26/11/2015.

    14. ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM?

    Tambaya:

    Salam Malam, Allah ya }arama ]aukaka da imani. ga tambayata: Shin

    mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana haila matukar yasa Condom?

    Amsa:

    To ]an’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya

    Condom, saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin

    haila a aya ta 222 a suratul Ba}ara da }azanta, sannan ya rataya halaccin

    saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma

    yın wanka.

    Ba namiji ne ka]ai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai

    haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna

    cewa: ba za'a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condom.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    28/11/2015

  • 15

    15. JINI YA BARKE MIN, SABODA AN YI MIN WANKIN CIKI ?

    Tambaya :

    Assalamu alaikum, Dan Allah inada tambaya macen da tayi bari aka mata

    wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata ya kuma baiyana jinin ciwo

    ne, shin za ta dinga wanka ne lokacin da za tayi kowace sallah? ko kuwa

    tsarki kawai za ta yi lokacin sallah?

    Amsa:

    To ]an’uwa za ta yi tsarki kuma ta yi alwala ya yın kowacce sallah, saboda

    hukuncinsu ]aya da mai istihâlâ, kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah

    su tabbata a gare shi ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish a hadisin Ibnu

    Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayin kowacce sallah, lokacin da

    ya tabbatar tana yın jinin cuta. Don neman }arin bayani duba: Risala Fi

    Dima'u Addabi'iyya: 45.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    28/11/2015

    16. ZAN IYA SHAN MAGANIN TSAYAR DA HAILA SABODA

    AIKIN HAJJI?

    Tambaya:

    Ya halatta mace ta tsayar da jinin haila saboda hajji??

    Amsa:

    To 'yar'uwa ya halatta, mutukar likita ya tabbatar miki ba zai cutar da ke ba,

    saidai tsayawa a dabi'ar da Allah ya halicce ki akai shi ya fi kyau, saboda

    shan magunguna irin wa]annan yana birkita kwanakin al'ada, kamar yadda

    bincike ya tabbatar.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    21/12/2015

    17. NA YI WANKAN JANABA, SAI MANIYYI YA SAKE ZUBO MINI?

    Tambaya:

  • 16

    Assalamu Alaikum tambayata ita ce: idan mace ta sadu da mijinta tayi

    wanka bayan sun gama tana zaune sai ta ji maniyyi ya zubo mata shin zata

    }ara yin wani wanka ko kuma wanda tayi ya isa ?

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, To idan sabuwar Sha'awace tazo mata, ta zubar da

    maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma idan saboda saduwar da suka yi ne

    a baya, zata wanke wurinne, ta sake alwala, amma babu bu}atar sake wanka,

    wanda ta yi na farko ya isa. Duba Bi]ayatu Almujtahid 1/48 da Insaf 1/232.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    2/1/2016

    18. AL'ADATA TA RI}ICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI

    Tambaya:

    Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya, don Allah a taimaka

    min da amsa don ko}arin gyarawa akan lokaci.

    Malam matsala gareni, duk haihuwa ta sai anyi min tiyata, sai likita ya bani

    shawarar tsarin iyali don in huta, sai daga nan al'adata ta ri}ice, sai yazo yau

    ba zan sake ganin shi ba sai bayan kwana biyar sai yazo min da yawa, to ni

    dai wanka na nake yi na cigaba da ibadata, to malam ibadata tayi ko da

    gyara?

    Sai kuma da watan Ramadan ya zo min da na kai iya kwankin da yake min

    wato kwana biyar sai nayi wanka na cigaba da azumina kuma jinin yana

    zuwa bai ]auke ba, don sai da yamin wajen kwana goma sannan ya ]auke

    nayi wanka, to shine akace min sai na rama wannan kwanaki goman, to

    malam yaya azumin nawa?.

    Amsa:

    To 'yar'uwa Allah ma]aukakin sarki a cikin al}ur’ani ya rataya hukuncin

    jinin haila ne da samuwarsa, don haka mutukar kin ga jinin haila da

    siffofinsa (Ba}i, }arni, kauri) to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa

  • 17

    lokacin da zai ]auke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo

    miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake

    zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah da azumi ba.

    Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa

    "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a

    lokacin da }ur'ani yake sauka kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai

    lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali suna birkita al'ada,

    wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba likita ne ya tabbatar da lalurar shan

    ba, ko kuma aka gane maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa.

    Allah ne mafi sa ni

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    22/1/2016

    19. SHIN MAZIYYI YANA KARYA ALWALA?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum wa rahmatullah malam ina yi maka fatan alkhairi,

    tambayata anan ita ce mutum ne yayi alwala yayi komai sai da yaje

    masallaci tayar da sallah sai maziyyi ya fito masa shin malam mutum za

    sallame sallar ne ko zai }arasa ta kuma yaya hukuncin sallar tasa idan ya

    }arasa Allah ya }arawa malam lafiya da wadatar zuciya na gode

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, ya wajaba ka yanke sallah, ka saké Alwala, an rawaito

    daga Aliyu RA yace: "Na kasance mutum mai yawan maziyyi sai na umarci

    Mikdad ya tambayar min Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

    sai ya ce maşa: Idan ya fito ka sake alwala, ka wanke azza}arinka, kamar

    yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 266" Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    9/2/2016

  • 18

    20. INA YIN HAILA DUK SATI, MENENE HUKUNCIN ALLAH ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum Malam tambaya nake, mace ce sati-sati take ganin

    al'adarta, tun lokacin da tayi fama da ri}icewar al'ada, daga baya zubar jini

    har na kusan wata ]aya, ta je asibiti sun yi bincike da hotona lokuta dabam

    dabam ba'a gane komai ba, amma sun ba ta magani da allura domin

    ]aukewar jinin, Tun daga lokacin da jinin ya ]auke sai jinin al'ada ya rinka

    zuwa mata sati-sati, Asibiti suka ce yanzu kam sai dai ayi Addu'a. tambaya

    malam Shin zata bar sallah duk sati saboda ganin jinin ko menene shawara?

    Nagode

    Amsa:

    To 'yar'uwa Allah ma]aukakin sarki, ya rataya hukuncin jinin haila ne da

    samuwarsa a aya ta: 222 a suratul Ba}ara, don haka mutukar kin ga jinin

    haila da siffofinsa (Ba}i, }arni, kauri) to ya wajaba ki bar sallah da azumi,

    har zuwa lokacin da zai ]auke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama ya

    zubo miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukkanta, to a lokacin ne

    yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah da azumi ba.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    28/2/2016

    21. BA TA HAILA SAI DUK SHEKARA, YAYA IDDARTA?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum malam ina da tanbaya: mace ce aka saketa saki uku

    amma ba ta yi jini ba sai bayan shekara ]aya, yaya iddarta za ta zama

    kenan?

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi shekara uku

    kafin ta kammala, saboda Allah ya rataye iddar matar da aka saka ba ta

    yanke kauna daga haila ba da jini uku, kamar yadda aya ta : 228 a suratul

    Ba}ara ta tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani

  • 19

    Dr. Jamilu Zarewa

    4/3/2016

    22. JININ BARI, BA YA HANA SALLAH !

    Tambaya:

    Assalamu alaikum wa rahmatullahi Malam, Ciki ne Na wata ]aya sai nake

    zubar da jini, har ance nayi bedrest shi ne nace yaya matsayin sallah ta? zan

    cigaba da yi ne ko zan bar ta har sai nayi wanka?

    Amsa:

    Malama ya wajaba ki yı sallah, saboda jinin da kike gani jinin barı ne, Jinin

    barin cikin da bai kai wata hudu ba, ba ya ]aukar hukuncin jinin haihuwa,

    saboda ba'a busawa ]an tayin rai ba a lokacin, wannan ya sa ba zai hana

    sallah ba. Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    5/3/2016

    23. ZAN IYA WANKAN JANABA, BA TARE DA ALWALA BA?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum tambayata anan shine: Menene hukuncin yin wankan

    janaba ba tare da yin alwala ba?

    Amsa:

    Ya halatta ayı wankan janaba ba tare da alwala ba, kamar yadda ya zo a

    hadisin Ummu-salama, Saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a

    gare shi ya siffanta mata wankan janaba da cewa: "Ya ishe ki, ki zuba ruwa

    sau uku akan kı sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in kika yi haka, kin

    tsarkaka" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma Albani ya inganta shi a

    hadisi mai lamba ta: 251.

    A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya nuna wankan ya yi da

    waccar sifar da kika tambaya.

  • 20

    Saidai sifar da tazo da alwala a hadisin Nana A'isha ita ce mafi cika, kamar

    yadda malamai suka bayyana. Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    6/3/2016

    24. MACE, ZA TA IYA YIN FITSARI A TSAYE ! ! !

    Tambaya:

    Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah malam

    menene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko namiji a Musulunci?

    Amsa:

    Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da Bukhari ya

    rawaito cewa: "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya je

    jujin wasu mutane sai ya yı fitsari a tsaye" kamar yadda Bukhari ya rawaito

    a hadisi na 222, tare da cewa duk hukuncin da ya zo dağa Annabi tsira da

    amincin Allah su tabbata a gare shi yana ha]a mace da namiji, in ba'a samu

    abin da ya ke~ance shi ba.

    Tabbas fitsarin mace a tsaye zai jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda

    yanayin halittar da Allah ya yı mata, kuma yana daga cikin }a’idojin sharia

    gabatar da wajibi akan abin da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga

    mace, saidai zai kai ga }unci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba ta

    ingantuwa saida ita.

    Duk hadisan da suka zo cewa Annabi ya hana yin fitsari a tsaye ba su

    inganta ba, sai hadisin Nana A'isha wanda Hakim ya inganta, in da take

    cewa : "Duk wanda ya ce muku Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a

    gare shi ya yi fitsari a tsaye kar ku gaskata shi" kamar yadda Nasa'i ya

    rawaito a hadisi mai lamba ta: 29, Malamai suna cewa : za'a ]au maganarta

    akan tana bada labari ne akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu

    wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da ba koyaushe take zama tare da

    shi ba, yana daga cikin }a’idoji a wajan malaman Usulul-fiqhi : Duk wanda

    ya tabbatar da abu za'a gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda

  • 21

    wanda ya tabbatar yana da }arin ilimi na musamman wanda ya buya ga

    wanda ya kore. Don neman }arin bayani duba : Sharhu Assuyudy ala

    Sunani Annasa'I 1\26. Allah ne mafi sani.

    Dr Jamilu Zarewa

    8/3/2016

    25. BABU HADISI INGANTACCE AKAN YAWAN KWANAKIN HAILA !

    Tambaya:

    Na karanta amsar da malam ya bada wadda ban fahimce ta~a, game da

    tambayar da aka yi mishi, ta zuwan jini duk sati tare da cewa ta je asibiti

    amma sun ce saidai ta yi hakuri, in na fahimci tambayar: hukuncin matar da

    take da irin wannan lalura shi ne : za ta bar sallah a duk lokacin da jini ya zo

    mata in lokacin yin al'adarta ne ko da ya cigaba har fiye da kwanakin da take

    yi mutukar bai wuce kwana (15) ba, Amma in ya wuce haka za ta yi wanka

    tayi sallah don haila ba ta wuce kwana(15).

    Amsa:

    Abin da abokina ya fada shi ne fatawar Malikiyya da Shafi'iyya, saidai babu

    ko hadisi ]aya da ya tabbata akan cewa : jinin haila ba ya wuce kwana sha

    biyar, duk hadisan da suka zo akan haka ba su inganta ba, daga ciki akwai

    hadisin da aka rawaito cewa: "An tambayi Annabi tsira da amincin Allah su

    tabbata a gare shi game da tawayar addinin mace, sai ya ce: "[aya daga

    cikinsu zata zauna rabin rayuwarta ba ta sallah" Ibnul Jauzy ya raunana shi a

    littafinsa Attahkik 1\263 haka Annawawy shi ma ya ce: hadisin }arya ne,

    kamar yadda ya zo a Al-Majmu''u 2\405, Ibnu Abdulha]y shi ma ya raunana

    shi a cikin Tankihu attahkiki1\414, Baihaki a cikin Ma'arifatu assunan wal-

    athar 2\145 yana cewa: ‚Na nemi hadisin da sanadi a littattafan hadisi amma

    ban ta~a ganinsa ba‛,

  • 22

    Haka nan Hanafiyya sun tafi akan cewa: Jinin haila ba ya wuce kwana

    goma, saidai duk hadisan da suka kafa hujja da su babu ingantacce a ciki,

    Duba Al-ilal Al-mutanahiyah na Ibnu Al-jauzy 2\382.

    Zance mafi inganci shi ne haila ba ta da wasu kwanaki na musamman,

    kamar yadda sheik Ibnu Uthaimin ya tabbatar da haka a littafinsa na

    Dima’u]]abi’iyya, tun da Allah da manzonsa sun rataya hukunce-

    hukuncenta ne da samuwarta, don haka duk inda aka samu jinin haila da

    sifofinsa (ba}i, }arni, kauri) hukuncinta yana tabbata, saidai idan ya kasance

    mafi yawan rayuwa ko dukkanta, a lokacin ne zai zama jinin cuta.

    Allah ne mafi sani.

    Dr Jamilu Zarewa

    11\3\2016

    26. WANDA YAKE CIWON IDO, ALWALA ZA TA FADI A KANSA?

    Tambaya:

    Assalaamualaikum Ina da tambaya: Idan mutum aka yi masa aiki a ido ance

    kar ruwa ya ta~a, to idan zai yi sallah taimama zai yi ko zai iya yin alwala ba

    tare da sa ruwa a wajen ba? Allah ya saka da alkhairi

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, zai yi alwala cikakkiya, sai ya tsallake wurin da yake

    da ciwon, saboda }a’idar: الميسور ال يسقط بالمعسور Duk ibadar da za'a iya yin

    wani bangarenta, to dukanta ba ya saraya, saboda rashin iya aikata wani

    bangarenta, sai fa idan bangaren nata shari'a ba ta bu}atarsa, kamar mai

    olsar da zai iya yin azumi zuwa azahar ya sare, Allah ne mafi sani

    Dr Jamilu Zarewa.

    19/03/2016

    27. INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA ?

    Tambaya:

  • 23

    Salam, Dr. macece mijinta ba shi da lafiyar kwanciyar aure tsawon lokaci,

    sai ya zama tana yawan fitar da maniyyi ko ba tayi wani dogon tunani na

    sha'awa ba, ya matsayin ibadarta yake?

    Amsa:

    To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba,

    ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, katange

    ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya

    tabbatar.

    Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da sau}in

    sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya

    wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa,

    Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.

    Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin ha]ari, mata nawa

    ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin?

    Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta

    hanyar jin dadi.

    Allah ne mafi sani.

    Dr Jamilu Zarewa.

    21/03/2016

    28. ZA MU IYA WANKA DA RUWAN ZAM-ZAM ? Tambaya:

    Assalamu Alaikum, malam, Don Allah menene hukucin yin tsarki da ruwan

    zamzam, ko wanka da shi. Nagode.

    Amsa:

    To ]an’uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a

    hadisi cewa : Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir,

    duba Faidhu Al}adeer 3/489.

    Saidai duk da haka ya halatta ayi wanka da tsarki da shi a zance mafi

    inganci, saboda ba'a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga

    cikin }a’idojin malamai duk abin da ba'a samu nassin hani akansa ba a cikin

  • 24

    mu'amalolin mutane, to ya halatta, sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya

    bubbugo daga hannun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,

    ruwan zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba. Don neman }arin

    bayani duba: Hashiyatu Ibnu- abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.

    Dr Jamilu Yusuf Zarewa

    13/04/2016

    29. INA CIKIN SALLAH, SAI NA TUNA AKWAI NAJASA A HULATA?

    Tambaya:

    Asalamu alaikum, Mallam mutun ne yana tsakiyar sallah ya kai raka'a ta

    biyu sai ya tuna kamar akwai najasa a hularsa, amma bai tabbatar ba sai ya

    cire hular, ya cigaba da sallah, toh ya sallarsa take?

    Amsa:

    Wa alaikumus salaam, wanda ya tuna da najasa a hularsa, zai iya hanzari ya

    cire ta ya yar, in har ya yi haka sallarsa ta yi, saboda abin da aka rawaito

    cewa: Annabi sallallahu alaihi wasallama wani lokaci yana sallah, sai ya cire

    takalminsa, daga baya sai yake bawa sahabbansa labari cewa: Jibrilu ne ya

    ce maşa akwai najasa a jiki, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma

    Nawawy ya inganta shi a Al-muhazzab 3\132, hadisin sai ya nuna ingancin

    sallar wanda ya yı haka, tun da ba'a rawaito Annabi sallallahu alaihi wa

    sallama, ya sako sallarsa daga farko ba.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    13/6/2016.

    30. DUK MINTI BIYU SAI NA YI TUSA, YAYA SALLATA ?

    Tambaya: Salamun alaikum Malam wai akwai sallah ga wanda in yana

    sallah yake fitar da tusa koda ace yayi kashi kafin yayi sallar, amma in har

    yazo sallah sai ta fito koda ace zaiyi alwala sama da 10?

    Amsa:

  • 25

    Wa alaikum assalam, akwai sallah akan shi, ba za ta ta~a faduwa ba akansa,

    ya wajaba a gare shi ya yi alwala yayin kowacce sallah, dağa nan duk abin

    da ya fito yana sallah ba zai cutar da shi ba, tun da in aka ce ya sake alwala

    yayin fitowar kowacce tusa ba zai iya ba, zai kuma shiga cikin wahala,

    Sharia ba ta ]orawa rai sai abin da za ta iya, kamar yadda ayoyi da hadisai

    da yawa suka tabbatar da haka.

    Babu takurawa da }unci a cikin addinin musulunci kamar yadda ayar

    }arshe a suratul Hajji ta tabbatar da hakan. Don neman }arin bayani duba:

    Alfawakihuddawany na Annafraawy 1/340.

    Amma idan tusar ba'a mafi yawan lokuta take fitowa ba, ya wajaba ya sake

    alwala duk sanda ta fito, saboda sallah ba ta ingantuwa saida alwala.

    Kula da wasuwasi abu ne mai muhimmancin gaske, saboda da yawa Shai]an

    ne yake busa a duburar dan'adam amma ba tusa ba ce, wanda ya ji haka, to

    kar ya fita daga sallarsa, har sai ya ji iska ko }ara ta fita, kamar yadda

    hadisin Bukhari ya tabbatar da hakan.

    Dr Jamilu Yusuf Zarewa

    24/04/2016

    31. INA SO NA SAN SIFFOFIN JININ HAILA?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah tambaya

    gare ni kan wani ruwa da yake fitomin amma kuma ba jini ba ne, ina ganinsa

    kasa-kasa babu wari ko qarni tare da shi ina ganinsa idan nayi azumi ko nayi

    aiki sosai, sai marata ta yi ciwo shine yake fitomin, yaya Azumina da sallah

    ta take shin zan cigaba da yinsu? sannan yana fitomin wajan qarfe 3 na rana.

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, mutukar ba jini bane, kuma ba ba}i ba ne, ba shi da

    karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi kyau ki je wajan likita don ya

  • 26

    duba lafiyarki, saboda abin da kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da

    ya rasa ]aya daga cikin siffofinsa. Allah ne mafi sani

    Dr Jamilu Yusuf Zarewa

    7 Ramadan, 1437H (12/06/2016).

    32. ALAMOMIN [AUKEWAR JININ HAILA!

    Tambaya:

    Assalamu alaikum. Allah ya }arawa Mallam Basira. Malam tambaya ta akan

    jinin haila ne: Malam an ce alamar da ake gane }arshen haila shi ne idan

    jinin ya canza kala zuwa ruwan kasa, Na ga alamar hakan sai na yi wankan

    tsarki bayan haka sai kuma ya cigaba da zuba na kwana biyu Malam tsarkin

    nawa yayi? yaya matsayin sallah da azumina? Nagode.

    Amsa:

    To 'yar'uwa abin da na sani daga malaman fiqhu shi ne: Ana gane ]aukewar

    jinin haila ne ta hanyoyi guda biyu:

    1- {e}asar-kasanki, Ta yadda mace za ta ga gabanta ya bushe ko

    kuma tsumma ko always din da ta tare jinin da shi.

    2- Fitowar farin ruwa bayan ]aukar lokaci ana haila.

    Idan jininki ya koma ruwan kasa kafin ki ga ]aya daga cikin wa]annan

    alamomi guda biyu, to ba ki gama haila ba, kuma ba za ki ]auki hukuncin

    masu tsarki ba, don haka azuminki da sallarki ba su yi ba. Idan kika ga ruwa

    mai kama da kasa bayan ]aukewar jinin haila, to ba zai cutar da tsarkin da

    kika samu ba, kamar yadda hadisin Bukhari daga Ummu A]]iiya ya

    tabbatar da hakan. Don neman }arin bayani duba: AdDima’u]]abi’iyya

    shafi na: 14.

    Allah ne mafi sani.

    Dr Jamilu zarewa.

    10/7/2016

  • 27

    33. HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI?

    Tambaya:

    Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya, mace ce bayan mijinta ya sadu

    da ita, kafin ta yi wanka sai jini ya zo mata ya za ta yi wanka, shin gaba dai

    za ta yi niyya ko kuma wannan na biyun za tayi?

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta yi wanka ]aya

    kawai.

    Saboda yana daga cikin }a’idojin sharia idan ibadoji guda biyu suka ha]u,

    kuma manufarsu ta zama guda ]aya, sannan za'a iya ha]a su a lokaci guda,

    to sai ]aya ta shiga cikin ]ayar, wannan yasa mai janabar da jinin haila ya

    same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da wankan }arshe, saboda sau}in

    musulunci da kuma ]aukewa jama'a abin da zai }untata musu, kamar yadda

    aya ta }arshe a suratul Hajj ta tabbatar da hakan. Allah ne mafi Sani.

    Dr Jamilu Zarewa

    11/09/2016

    34. YAUSHE AKE YIWA YARO KACIYA?

    Tambaya

    Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa yaro kaciya shekara

    nawa ya kamata ayi masa?

    Amsa

    Wa alaikumus salam, To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya

    kayyade wani lokaci da za'a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa :

    babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da za ta iya

    ma}alewa a al'aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da

    balagarsa, saboda idan ya balaga shari'a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba

    zai cika ba, in ba'a yi masa kaciyar ba, daga cikin }a'aidojin malamai shi ne

    duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma

    mustahabbi ne ayi masa, tun yana ]an-}arami, saidai wasu malaman sun

  • 28

    karhanta yin kaciya ranar 7 ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da

    yahudawa a cikin hakan. Don neman }arin bayani duba Fathul-bary 10/349.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    30/09/2016

    35. SHARU[AN KARBAR IBADA! Tambaya:

    Assalamu alaikum, Dr. don Allah ina son a gayamin sharu]an karbar ibada

    wanda mutum yakeyi.

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, sharudan karbar ibada guda biyu ne, tsarkake niyya ga

    Allah, da kuma biyayya ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare

    shi a siffar ibadar da kuma yanayinta ko adadinta.

    Duk ibadar da ba ta cika wa]annan sharu]an ba, ba za'a amshe ta ba.

    Allah ne mafi sani

    Dr Jamilu Zarewa

    18/10/2016

    36. MIJINA YA SADU DA NI, KAFIN NA YI WANKAN HAILA?

    Tambaya:

    Assalamu alaykum, Malam inada tambaya, malam menene hukuncin mace

    ta}are haila ba tayi wanka ba mijin ta ya sadu da ita?

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne: ta jira sai ta yi

    wanka kafin su sadu, kamar yadda suka fahimta a suratul Bakara ayata 222,

    amma Abu-hanifa yana ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar

    da yankewar jinin haila kawai. Riko da mazhabar farko shi ne ya fi saboda

    Allah ya kira haila da kazanta. Babu wata kaffara ga wanda ya sadu da

    matarsa kafin ta yi wanka bayan yankewar jinin haila. Allah ne mafi sani:

    Dr Jamilu Zarewa

    2/11/2016

    37. INA SO NA MUSULUNTA, AMMA INA CIKIN JININ HAILA?

  • 29

    Tambaya:

    Assalamu Alaikum, Allah yasa malam yana nan lafiya Ameen, tambayata ita

    ce: idan mace za ta musulunta tana cikin jinin haila ya zata yi wajen wankan

    shiga musulinci ta bari sai tayi tsarki ko yaya?

    Amsa :

    Wa alaikum assalam, ta musulunta kawai, domin ai wankan ba dole ba ne a

    mafi ingancin zance, saboda hadisin da ya tabbata cewa: (Musulunci yana

    rushe abin da ya gabace shi).

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    08/12/2016

    38. MAI HAILA ZA TA IYA TA|A IZU GOMA?

    Tambaya:

    Assalamu Alaikum, Malam. Wai gaskiya ne mace mai haila za ta iya ri}e

    Al}ur’ani izu gima?

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, Abin da yafi zama daidai shi ne: kar mai haila ta ta~a

    ko da wani bangare ne na Al}ur’ani, saboda hadisin Amru Bn Hazm wanda

    wasu malaman hadisin suka inganta inda Annabi Tsira da amincin Allah su

    tabbata a gare shi yake cewa: (Kar Wanda ya ta~a Al}ur’ani sai mai tsarki),

    kamar Albani a Sahihi wa dha'ifil Jami'i hadisi mai lamba ta: 13738.

    Amma ya halatta ta karanta ta hanyar kallo, saboda duk hadisan da suka

    hana mai haila karatun Al}ur’ani ba su inganta ba.

    Allah ne mafi sani

    Dr Jamilu Zarewa

    4/01/2017

    39. HAILA TA ZO MATA SAURA MINTI 3 RANA TA FADI?*

    Tambaya: Assalamu alaikum, Malam tambayata ita ce mata ce ta yi azumi

    har saura minti (3) a kira rmagariba sai jinin hailarta ya zo, to tambayata a

  • 30

    nan ita ce, wannan azuminta na wannan ranar yana nan ko za ta biya bayan

    sallah?. Allah Ya }arawa Malamanmu basira.

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, in har jinin hailar ya fito a wancan lokacin da ka

    ambata,, to azumin ta ya karye, saboda azumi yana kammala ne bayan

    faduwar rana,, ita kuma na ta ya warware kafin lokacin,, wannan yasa za ta

    rama bayan sallah.

    Allah ne mafi sani.

    Dr Jamilu Yusuf Zarewa

    01/06/2017.

    40. NA GA WANDONA A JIKE DA MANIYYI BAYAN NA

    KAMMALA SALLAR LA'ASAR ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum malam na tashi da janaba nayi salar asuba da azahar da

    kuma la’asar, duk nayi sallah sai bayan naje wanka da yamma naga wando

    na da alamun manniyi shin ya ingancin sallolina na baya ? Nagode

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, mutukar ka tabbatar a baccin asuba maniyyin ya fito,

    to ya wajaba ka sake asuba da azahar da la'asar din, In har ka yi wani baccin

    bayan azahar to za ka danganta janabar ne zuwa ga baccin }arshe da ka yi, ta

    yadda sallar da kayi bayan baccin }arshe ita za ka sake, kamar yadda Imamu

    Malik ya rawaito a Muwadda daga Sayyady Umar. Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    13/11/2017

    41. SHA{{A BA TA GUSAR DA ABIN DA YAKE NA HA{{IKA

    Tambaya:

    Assalamu alaikum Malam Dan Allah mafita nake nema na kasance cikin

    matsanancin kokonto, a sallah da alwala, na dade inayi nayi shekaru kuma

    ina addu’a Allah ya yayemin saboda na damu matuka, to yanzu abin yana

    neman yayi yawa idan nayi sallah sai in ta kokonto bayan kuma nasan tabbas

  • 31

    nayi, amma zuciya sai ta rinjaya akan in sake sai in yi raka'’o’i da yawa a

    sallah, to haka ma idan na yi alwala sai inji kamar ta karye.

    Malam Don Allah a taimakamin yadda zan yi in daina abin yana damuna

    matuka musamman yanzu da yake }ara yawa. kuma nadage wajen yin

    azkhar, ataimaka min malam.

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, Ki yawaita Istigfari, saboda yawan zunubai yana jawo

    matsaloli. Sannan ki dinga amfani da abin da ya rinjaya a zuciyarki, kar ki

    rinka waigawa zuwa waswasin Shai]an, mutukar ba ki samu abin da ya goge

    ya}ininki ba.

    Ibnu Uthaimin a cikin littafinsa Manzumatul Kawa'idul Fiqhiyya wal-

    usuliyya ya fadi wurare uku da ba'a waigawa zuwa kokwanto, daga ciki

    akwai: Idan kokwanto ya yawaita.

    Yana daga cikin }a’idojin sharia wa]anda malamai suka cimma daidaito

    akansu: "Sha}}a ba ta gusar da abin da yake tabbas, tun da kina da tabbaci

    akan aikinki, me yasa za ki waiga zuwa ga kokwanto?

    Yawan sake ibada saboda kokwanto yana jawowa mutum ya tsani ibadar,

    tare da cewa Allah bai wajabta masa hakan ba, Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    16/11/2017

    42. MANUFOFIN ALWALA DA TSARKI

    Tambaya:

    Malam ina son bayani akan manufar da tasa ake yin alwala ??

    Amsa:

    Addinin musulunci addini ne na tsafta, yana umarni da tsaftar ciki da ta

    waje, wannan yasa ya yi umarni da alwala yayin kowacce sallah, da kuma

    tsarki idan mutum ya shiga ban]aki ko kuma janaba ta same shi, kamar

    yadda ya yi umarni da rage gashin baki da kuma yanke farce. Ilimin zamani

    ya zo ya tabbatar da muhimmancin alwala da wankan janabar da musulunci

  • 32

    ya yi umarni da su, domin littattafan likitanci sun tabbatar da cewa: "Fatar

    dan'adam tana tara wasu kwayoyin cututtuka, musamman wurare masu

    danshi kamar hammata, gashi, kuma alwala da wanka suna tafiyar da mafi

    yawan wa]annan kwayoyi, saboda alwala tana tsarkake gabobin da suke

    bude, wanka kuma yana tsarkake dukkan jiki", ga wasu daga cikin

    hikimomin da suka sa aka shar'anta tsarki, da kuma alwala a musulunci :

    1. Neman yardar Allah ma]aukaki, domin duk lokacin da mutum ya yi

    alwala ko yayi tsarki to yana tabbatar da umarnin Allah ne.

    2. Tunkude kwayoyin cuta, wa]anda za su iya samun mutum idan bai yi

    tsarki ba.

    3. Tabbatar da lafiyar gabobi.

    4. Tsarkaka daga zunubai da kuma samun lada mai yawa kamar yadda aya

    ta (6) a Suratul Ma'ida ta yi bayanin haka.

    5. Sabawa rai, da abubuwa ma]aukaka.

    Don neman }arin bayani duba: Makasidush Sharia na Jamilu Zarewa Shafi

    na: 221. Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    21/1/2018

    43. SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA ?

    Tambaya: Malam shin mace mai ciki za ta iya ganin haila?

    Amsa: Yawanci idan mace ta ]au ciki jini yakan daina zuwa mata, Imamu

    Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da yankewar jini) Idan

    mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya kasance kafin haihuwa da kwana biyu

    ko uku kuma a tare da shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne,

    idan kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa da

    haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba biki ba ne, saidai

    shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma

    jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba? Anan

    malamai sun yi sa~ani:

  • 33

    Abin da yake daidai shi ne jinin haila ne in dai ya zo a yadda ta saba yin

    jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana ]aukarsa a jinin

    haila, in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma

    babu wani dalili a al}ur’ani ko a sunna da zai hana shi ya zama haila.

    Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i, kuma Baihaki ya hakaito hakan

    daga cikin maganganun Ahmad.

    Don haka yana tabbata ga mai ciki mai haila abin da yake tabbata ga mai

    haila mara ciki sai a gurare guda biyu :

    1. Saki- Ya haramta a saki matar da idda ta wajaba a gare ta idan tana haila,

    amma mai ciki ya halatta a sake ta a cikin haila, saboda sakin matar da bata

    da ciki ya sabawa fa]in Allah ( Kuma ku sake su a farkon iddarsu) Suratud

    Dalak aya ta 1, wato a farkon tsarkin da bai take ta a cikinsa ba. amma sakin

    mace mai ciki tana haila sakin ta ne ga iddarta, wannan ya ha]a da tana cikin

    haila ko tana cikin tsarki, saboda iddarta tana kasancewa ne da haife wannan

    ciki, don haka bai haramta a sake ta ba, bayan an yi jima’i da ita.

    2. mace mai ciki idan ta yi haila ba za ta yi idda da ita ba, saboda iddar ta

    tana kasancewa ne da haife cikinta, wannan ya ha]a da tana haila ko ba ta yi,

    saboda fa]in Allah ma]aukaki ( Iddar mata masu ciki tana kasancewa ne

    idan su ka haife cikinsu). Suratu]-]alak aya ta 4.

    Don neman }arin bayani duba : Dima’u]]abi’iyya shafi na 11.

    Dr. Jamilu Zarewa

    4/2/2018

    44. HUKUNCIN SAKIN MAI HAILA

    Tambaya:

    Malam mun samu ri}ici da matata ko ya halatta na sake tana haila??

    Amsa:

    Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fa]in Allah "Ya kai

    Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a farkon iddarsu) Suratu A]]alak

    aya ta farko, wato a farkon tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba.

  • 34

    Ana nufin a halin da za su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya

    faruwa sai idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin tsarkin da bai take ta ba,

    domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci idda ba, saboda hailar da

    ya sake ta a ciki ba za’a kirga da ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da

    tsarki bayan ya sadu da ita, domin bai sani ba shin ta ]auki ciki ta yadda

    iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta ]auka ba ta yadda za ta yi

    idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai sakin ya haramta.

    Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa : Ibn umar ya saki matarsa tana

    haila, sai Umar ya bawa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

    labari, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi fushi, sai

    ya ce "Ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya ri}e ta har ta yi tsarki

    sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so ya ri}e ta ko kuma ya

    sake ta kafin ya sadu da ita, wannan ita ce iddar da Allah ya umarta a saki

    mata a ita".

    Ana togace gurare guda hudu wa]anda sakin mace mai haila yake hallata :

    A. idan sakin ya kasance kafin ya ka]aita da ita ko kafin ya sadu da ita, to

    anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda anan ba ta da idda, sakinta ba

    zai zama sa~awa fa]in Allah ma]aukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba.

    B. idan ta yi hailar ne tana da ciki.

    C. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL'I) to anan babu laifi ya

    sake ta tana haila.

    D. Idan yaki saduwa da matarsa kuma aka yi watanni hudu bai dawo ba.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    21/2/2018

    45. NAGA BUSASHSHEN MANIYYI A JIKIN RIGATA ?

    Tambaya:

    Malam akwai wata rigata dana jima ban sanya ba, yanzu na ]auko sai na

    ga maniyyiyi busashshe a jiki, yaya zan yi da shi ?

    Amsa:

  • 35

    Wa alaikum assalam abin da yake kanka shi ne ka kankare shi, kamar

    yadda nana Aisha take yi da maniyyin manzon Allah tsira da amincin

    Allah su tabbata a gare shi idan ya bushe a jikin rigar shi.

    Allah ne ma fi sani.

    Dr.Jamil Yusuf Zarewa

    13/08/2018

  • 36

    BABI NA BIYU

    FATAWOYIN DA

    SUKA SHAFI

    SALLAH

  • 37

    46. HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI [AYA

    Tambaya:

    Malam tambaya: yanzu za ka ga dan }aramin gari, amma sai ka ga sama da

    masallacin juma'a ]aya a cikinsa, shin hakan ya halatta ?

    Amsa:

    To malam babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai

    sun yi ijtiha]i a cikin mas'alar zuwa maganganu guda uku, maganar da ta fi

    inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da masallacin juma'a guda ]aya

    a gari ]aya, mutukar akwai bu}atar hakan, kamar ya zama masallacin farkon

    ba zai ishi mutane ba, ko kuma za'a samu wata fitina idan aka ha]u wuri

    ]aya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala,

    wajan isowa zuwa gare shi.

    idan babu bu}ata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda ]aya a gari ]aya,

    saboda daga cikin hikimomin shar'anta juma'a akwai samun ha]in-kan

    musulmai, da kuma nisha]antar da juna, da samun lada mai yawa, hakan

    kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda ]aya, wannan ita

    ce maganar Ibnu Taimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu

    manyan maluma Allah ya yi musu rahama .

    Allah ne ma fi sani.

    Dr.Jamil Yusuf Zarewa

    4/06/2013

    47. HUKUNCIN LADANCI A SALLAH

    Tambaya:

    Malam meye hukuncin ladanci a sallah, haram ne ko in aka yi ba laifi?

    Amsa:

    To ]an’uwa mutukar liman yana daga murya, to yin ladanci bidi'a ne kamar

    yadda wasu malaman suka fada, amma idan liman yana da lalura ko rashin

    lafiya ko kuma masallacin yana da girma ta yadda dukkan mamu ba za su ji

    muryarsa ba, to ya halatta, saboda a lokacin da Annabi tsira da amincin

  • 38

    Allah su tabbata a gare shi ya yi rashin lafiya, sayyidina Abubakar ya

    kasance yana ]aga murya da kabbara saboda ba'a jin na Annabi tsira da

    amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito

    Allah ne mafi sani .

    Dr. Jamilu Zarewa

    9/1/2014

    48. HUKUNCIN SALLAH A MASALLATAN DA SUKA KAUCEWA AL{IBILA

    Tambaya:

    Ina da fatawa, wanda ya san masallatan gari sun kaucewa al-}ibla, ya zai yi?

    yayi magana abin bai gyaru ba, zai iya kauracewa masallatan garin ne, ko zai

    rika sallah haka dai?

    Amsa :

    Yana da mutukar muhimmancin gaske, ya yi zurfin bincike kafin ya yi

    da'awar cewa masallatan garinsu sun kaucewa alqibla, saboda daga cikin

    }a'idojin shari'a : duk abin da ya tabbata da ya}ini, to ba za'a rusa shi ba,

    saida ya}ini, don haka kar mutum ya kauracewa masallatan unguwarsu

    saboda kawai tunanin sun kaucewa al}ibla, ba tare da dalili kwakwkwara ba,

    wanda zai gamsar.

    Fuskantar alkibila sharadi ne a sallah, amma sallar jam'i kuwa malamai sun

    yi sabani akan hukuncinta, Malikiyya sun ta fi cewa : sunna ne, wasu kuma

    sun tafi cewa wajibi ce, don haka mutukar ya tabbatar cewa sun kaucewa

    alkibla kuma babu yadda zai yi ya gyara musu, babu kuma wani masallaci

    da yake akan daidai to tabbas zai iya yin sallarsa a gida, domin sharadi shi

    ne gaba da sunna da wajibi, amma in zai samu wadanda za su yi sallah tare

    daga baya to wannan shi Ne daidai, saboda hadisan da suke nuna wajabcin

    sallar jam'i suna da karfi. Allah ne ma fi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    10-1-2014

  • 39

    49. YAUSHE NE LOKACIN SALLAR WALAHA ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum. Malam daidai wanni lokaci ne ya dace a bisa kiyasin

    lokaci ayi sallar walaha?

    Amsa:

    Wa alaikum assalam, to malam lokacin sallar walaha yana farawa ne idan

    rana ta fara ]agawa, kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a

    gare shi yake cewa a cikin hadisin Muslim mai lamaba ta :748 "Sallar

    walaha lokacin da 'ya'yan rakuma suka fara jin zafi" sannan lokacin yana

    karewa dab da zawalin rana, da minti sha biyar ko kusa da haka.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamil Yusuf Zarewa

    25/02/2014

    50. HUKUNCIN CANZA WURI BAYAN SALLAR FARILLA KAFIN

    SALLAR NAFILA

    Tambaya:

    Menene asali ko dalili idan mutum ya idar da sallah zai yi nafila sai naga ya

    dan matsa baya ko gaba daga inda yayi sallarsa, akwai hadisi ne akan haka?

    Amsa:

    To ]an’uwa Akwai hadisin da yake nuna haka, saidai wasu malaman hadisin

    sun raunana shi kamar Bukhari a sahihinsa, a hadisi mai lamba : 848, amma

    Albani ya inganta shi saboda yawan hanyoyinsa, a cikin littafin Sahihu

    sunani abi-dawud 3/178.

    Malamai suna cewa : ana so ayi hakan saboda gurare da yawa su yi ma

    mutum shaida, Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri, saboda abin

    da aka rawaito daga Aliyu - Allahya }ara masa yarda- yana cewa : "Yana

    daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar nafila" wannan yasa

  • 40

    Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya yi sallar farilla,

    don kar a zaci sallar ba ta kare ba . Fathul-bary 2\335

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamil Yusuf Zarewa

    15/3/2014

    51. HUKUNCIN BIN SALLAR JAM'I DAGA LASIFIKA

    Tambaya:

    Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da i}ama ta

    lasipika, ko ya halatta in bi sallar jam'i daga lasifika ?

    Amsa:

    To 'yar'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu :

    1- Idan ya zama ]akinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya

    halatta, saboda nana A'isha ta bi sallar kisfewa rana daga ]akinta a zamanin

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya

    rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 184, sannan Abdurrazak ya rawaito

    cewa : takan bi ragowar salloli daga ]akinta" kamar yadda ya zo a littafinsa

    na Musannaf a hadisi mai lamba ta : 4883, saboda ]akinta a jikin masallacin

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake.

    2. Idan ya zama ]akin ba ya ha]e da masallacin, to zance mafi inganci shi

    ne: bai halatta ki bi ba, saboda a zamanin Annabi tsira da amincin Allah su

    tabbata a gare shi sahabbai suna ha]uwa ne a wuri ]aya ne idan za su yi

    sallar jam'i, ba sa rarrabuwa, wannan sai yake nuna cewa, hakan shi ne siffar

    sallar jama'i, sannan jera sawu a sallah wani yana bin wani dole ne a sallar

    jam'i. Don neman }arin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al

    mushaikih shafi na : 50.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamil Yusuf Zarewa

    28/4/2014

  • 41

    52. INA SO NA YI TSAYUWAR DARE! Tambaya:

    Malam ina sha'awar yin tsayuwar dare saboda ]imbin falalar da ta kunsa,

    saidai a lokuta da yawa, na kan so na tashi, amma sai na kasa, ko malam zai

    taimaka min da shawarwari akan abin da zai taimake ni wajan yin wannan

    babban aikin, Allah ya }arawa malam ]aukaka, amin.

    Amsa :

    To ]an’uwa ina fatan Allah ya datar da mu gaba ]aya zuwa wannan ibada

    mai girma, akwai abubuwa da malamai suka yi bayanin cewa, suna

    taimakawa wajan samun damar tsayuwar dare, ga wasu daga ciki :

    1. Baccin rana : Hasanul Basary ya wuce wasu mutane a kasuwa da rana, sai

    ya ce wa]annan ba za su yi bacci ba, sai aka ce masa E, sai ya ce ina ganin

    darensu ba zai yi kyau ba" .ma'ana ba za su iya tsayuwar dare ba .

    2. Yin bacci da wuri : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya

    karhanta bacci kafin sallar isha da kuma yin hira bayanta, kamar yadda ya zo

    a hadisin Muslim mai lamba ta : 647, kuma dalilin da ya sa ya karhanta yin

    hira bayanta saboda hakan zai iya hana mutum tsayuwar dare.

    3. Aikata ladubban bacci yayin kwanciya, ta yadda zai karanta abin da ya zo

    a cikin sunna na ladubban bacci.

    4. Umartar wani ya tashe shi kamar matarsa ko wanda suke tare.

    5. Rashin cika ciki da abinci.

    6. Nisantar yin aiki mai wahala da rana.

    7. Nisantar abin da zai kawo maka fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage

    burirri}a da tunanin abin da ya wuce.

    8. Nisantar zunubai, Fudhail bn Iyadh yana cewa : "Idan ka ga ba ka iya

    tsayuwar dare, to ka tabbatar zunubai ne suka dabaibaye ka. In har ka kiyaye

    wa]annan, in Allah ya so za ka dinga tashi.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamil Yusuf Zarewa

    25/11/2014

  • 42

    53. NA JONA SALLATA DA TA MAMU, BAYAN AN GAMA JAM'I,

    SHIN TA INGANTA ?

    Tambaya:

    Salam malam, Shin ya halatta abi wanda bai samu cikakken jam'i ba sallah?

    Misali,na zo masallaci na tarar da jam'i na sallar asr saura raka'a 2, da aka

    idar na mike tsaye don }arasa raka'a 2 da ta rage min, sai ga ma}ararre ya

    sake ha]a jam'i da ni. Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? A amsa min tare

    da hujjoji.

    Amsa:

    To ]an’uwa malamai sun yi sa~ani akan wannan mas'alar zuwa zantuka

    guda biyu :

    Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan haramcin hakan, saboda

    ba'a samu magabata suna yi ba, sannan kuma shi masabuki ba liman ba ne,

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma ya yi umarni da

    bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa sallah ta ki karewa, tun da

    wanda ya bi masabuki shi ma in ya gama yana ramako wani zai iya zuwa ya

    bi shi, don haka sai ya haramta, Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma

    Mawahibul-jalil4\489.

    Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi ingancin zancensu, sun tafi

    akan halaccin hakan, saboda hadisin Ibnu Abbas lokacin da ya ga Annabi

    yana sallah da daddare sai ya bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a

    hadisi mai lamba ta :666, ta yadda a cikin hadisin za mu fahimci cewa ya

    halatta mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa bai yi niyyar

    hakan ba tun daga farko, tun da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a

    gare shi bai hana Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa ba su fara

    da shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya rabu da liman to yana

    ]aukar hukuncin mai sallah shi ka]ai ne, don haka sai ya halatta a bi shi.

    Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.

  • 43

    Zancen da ya fi inganci shi ne zance na biyu saboda abin da ya gabata da

    kuma hadisan da suke nuna falalar sallar jam'i.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamil Yusuf Zarewa

    7/12/2014

    54. HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA!

    Tambaya :

    Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da yake da janaba ya kira

    sallah?

    Amsa:

    To ]an’uwa wasu daga cikin malamai suna cewa tsarki ba shara]i ba ne

    yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce wanda ya nuna hakan,

    don haka ya halatta ga mai janaba, da mai }aramin kari su yi kiran sallah,

    saidai abin da ya fi shi ne yin cikakken tsarki kafin kiran sallah, saboda fa]in

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi " Ina kin na am~aci Allah

    alhali ba ni da tsarki", kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai

    lamba ta :16, kuma Albani ya inganta shi a Sahihu-sunani Abi-dawud 1\16.

    Don neman }arin bayani duba : Fathul-bary 3\113 da Majmu'u fataawaa wa

    makaalatin mutanawwi'a 10/338.

    Dr. Jamilu Zarewa

    7/12/2014

    55. SHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'A ! !

    Tambaya:

    Malam menene hukuncin shafa hannu a fuska bayan gama addu'a?

    Amsa:

    To dan'uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: "Annabi

    tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi idan ya ]aga hannayansa ya yi

    addu'a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa" Attirmizi: (3386).

    Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da

  • 44

    rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi sa~ani game da ingancin shi,

    Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda

    ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta : (1345).

    Akwai wadanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su

    masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra'ayin

    Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu'ul fataawaa 22\509,

    haka Albani a Silsila Sahiha 2\146.

    Malaman Fiqhu sun yi sa~ani game da shafar fuska bayan addu'a, wasu sun

    tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu- hajar

    ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a ]aya daga cikin fatawoyinsa, akwai

    kuma wadanda suka tafi akan cewa ba za'a ayi ba, saboda rashin ingancin

    hadisan da suka zo akan haka. Abin da na fahimta a wannan mas'alar shi ne

    ba za'a aibanta wanda ya shafa fuskarsa ba bayan addu'a, tunda yana da

    magabata . Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    11-2-2015

    56. DAGA INA SAHU YAKE FARAWA ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum malam ya gida ya kuma aiki, malam don Allah ina da

    tambaya: sahun sallah ta dama za'a fara ne ko ta hagu.?

    Amsa :

    To ]an’uwa sahun da yake bin liman zai fara ne daga bayan liman ma'ana a

    sanya liman a tsakiya, saboda fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata

    a gare shi "Masu hankali daga cikinku, su bi bayana" kamar yadda Muslim ya

    rawaito a hadisi mai lamba ta : 116.

    sannan da fa]in Anas RA lokacin da yake bada labarin ziyarar da Annabi

    tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kai gidansu : " Sai muka tsaya

  • 45

    ni da marayan a bayansa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai

    lamba ta :694, daga nan kuma sai a cigaba da cika shi ta bangaren dama.

    Haka nan ake so sahu na biyu shi ma ya kasance, ya fara daga tsakiya ya tafi

    zuwa dama, saboda fa]in Bara'u dan Azib (RA) "Mun kasance idan muka yi

    sahu a bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mu kan so

    mu kasance a damansa, ya fuskanto mu da fuskarsa " Muslim a hadisi mai

    lamba ta : 709.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    21\2\2015

    57. DAGA HANNU SAMA LOKACIN AL{UNUT ! ! !

    Tambaya:

    Assalamu Alaikum Malam Jamilu, akwai hujja akan daga hannaye lokacin

    yin al}unut a sallah, musamman al}unut ta lokacin masifa ? nagode

    Amsa:

    To ]an’uwa, zance mafi inganci shi ne mustahabbancin ]aga hannu yayin

    al}unutu, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ]aga

    hannu a sallar asuba lokacin da ya yi addu'a ga wa]anda suka kashe mutum

    saba'in makaranta, kamar yadda [abrani ya rawaito a Mu'ujamussagir a

    hadisi mai lamba ta : 111, kuma Albani ya inganta shi a Irwa'ul-galil 2\181.

    Sannan an rawaito hakan daga Umar da Usman da Ibnu Mas'ud, da Abu-

    hurairah . Don neman }arin bayani duba Attalkis na Ibnu Hajar 2\40

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    27/1/2015

    58. BACCIN BAYAN SALLAR ASUBA!

    Tambaya:

    Assalamu alaikum, malam ina da wata tambaya shin menene hukuncin y

    in bacci bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!

  • 46

    Amsa:

    Wa alaikum assalam.To malam babu wani hadisi mai inganci wanda ya hana

    bacci bayan sallar asuba, sai dai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka, wa

    nnan yasa Annabi tsira da amincin allah su tabbata a gare shi idan ya yi salla

    r asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Alla

    h ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta: 67

    0.

    Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Allah

    ka sanyawa al'umata albarka a cikin jijjifinta" Tirmizi a hadisi mai lamba ta:

    1212, kuma ya kyautata shi.

    Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai albarka, wanda bai dace da bacci ba,

    wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi tsira da amincin Allah su tabbata

    a gare shi. yake so ya aika, yakan aikata ne a farkon yini saboda albarkar lok

    acin. Wasu daga cikin magabata, sun karhanta yin baccin bayan sallar asuba,

    Urwatu dan Zubair yana cewa : "Idan aka ce min wane yana baccin safe na k

    an guje shi' kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a

    Musannaf dinsa 5\222. Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko kosuwanci a

    irin wannan lokacin.

    Allah ne mafi sani.

    DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

    30/01/2015

    59. LIMANCIN KURMA!

    Tambaya:

    Assalamu alaikum, malam menene hukuncin bin kurma wanda ba ya ji

    sallah?

    Amsa:

    To ]an’uwa limancin kurma bai inganta ba, harma wasu malaman sun

    hakaito ijma'i akan haka, saboda kurma ba zai iya tsayar da wasu daga cikin

    rukunan sallah ba, kamar kabbarar harama da karatun fatiha da sallama, don

    haka binsa sallah zai jawo sallar wa]anda suke binsa ta zama ba ta cika ba.

  • 47

    Saidai wasu malaman sun tafi akan cewa, ya halatta ya yiwa kurame irinsa

    limanci. Don neman }arin bayani duba : Sharhul-kabir na Abdurrahman dan

    khudaamah 2\38. Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    15/2/2015

    60. SHIN MAI SALLAR FARILLA ZAI IYA BIN MAI SALLAR NAFILA?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum, malam maye hukuncin mai yin sallar farilla ya bi me

    nafila?, Malam Allah ya }ara lafiya, ya ja kwana.

    Amsa:

    To ]an’uwa malamai sun yi sa~ani akan wannan mas'alar, saidai zance mafi

    inganci shi ne hallacin hakan, saboda Mu'az dan Jabal (RA) ya kasance yana

    yin sallar Isha tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

    sannan ya je wajan mutanensa ya jagorance su sallar isha, kamar yadda

    Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 711.

    Malamai suna cewa : ]aya daga cikin sallolin Mu'az a nan nafila ce, tun da

    ba'a yin sallar Isha guda biyu, don haka ko dai ya zama wacce ya yi da

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ita ce nafila, sai ya zama

    ya yi koyi da mai farilla, ko kuma wacce ya yi da mutannansa ita ce nafila,

    don haka sai ya zama mutanansa suna farilla, shi kuma yana nafila, a

    kowanne ]aya daga cikin biyu, zai zama akwai inda mai nafila ya yi koyi da

    mai farilla. Kasancewar an yi abin a zamanin Annabi tsira da amincin Allah

    su tabbata a gare shi bai yi inkari ba, dalili ne da yake nuna ingancin hakan,

    tun da ba ya yin shiru idan ya ga kuskure.

    Don neman }arin bayani duba : Almajmu'u na Nawawy 4\169.

    Dr. Jamilu Zarewa

    17/2/2015

  • 48

    61. JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKE!

    Tambaya:

    Assalamu Alaiykum, Malam matata ta haihu sati biyu kenan, to Malam

    yanzu takan wuni Jini bai zo ba, sai da daddare in ta kwanta sai Jinin ya zo,

    to shin Malam za ta iya yin wanka da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i ?

    kokuma yaya za ta yi? Nagode Allah Ya }ara illimi mai albarka.

    Amsa:

    To ]an’uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to yana ]aukar

    hukuncin jinin bi}i ne, haka ma tsarki yana ]aukar hukunce-hukuncen tsarki,

    ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ba ta ga jini ba, Saidai idan yana

    yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta ha]a sallolin da ba

    ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a

    ciki, kuma Allah yana cewa : "Bai sanya muku }unci a cikin addini ba"

    Suratul Hajj: 78. Allah ne mafi sani .

    Don neman }arin bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214.

    Dr. Jamilu Zarewa

    22/2/015

    62. JINI YA ZO MIN, BAYAN CIKINA YA KAI WATA BIYU !

    Tambaya:

    Assalamu alaikum, malam ya kokari, tambayace gare ni, na yi wata biyu ban

    ga al'ada ba, sai yanzu ta rinka zuwa tana ]aukewa, na zo asibiti sun ce juna

    biyu ne, to in yazo min da safe shikenan sai ya ]auke sai kuma gobe da safe,

    sai in ya ]auke inyi wanka in cigaba da sallah, malam ko ya halatta hakan ?

    Amsa:

    To yar'uwa wannan jinin da kika gani mutukar yana kama da jinin hailar da

    kaki saba gani, to zai hana sallah, kuma zai ]auki dukkan hukunce-hukuncen

    jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana ]aukarsa a jinin haila,

    in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu

    wani dalili a al}ur’ani ko a sunna da zai hana shi ya zama haila.

  • 49

    A zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila, don haka duk yinin da ki ga

    jini to yana ]aukar hukuncin jinin haila ne, haka ma tsarki yana ]aukar

    hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ki yi wanka duk yinin da ba ki ga jini

    ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to kina iya jinkirta wankan, sai

    ki ha]a sallolin da ba ki ga jini ba a lokutansu kamar azahar da la’asar ko

    magrib da isha, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki,

    kuma Allah yana cewa : "Bai sanya muku }unci a cikin addini ba" Suratu

    Hajj 78. Don neman }arin bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214

    da Dima’u]]abi’iyya shafi na 11

    Dr. Jamilu Zarewa

    26/2/2015

    63. HUKUNCIN ADDU'A TSAKANIN HUDUBAR JUMA'A TA FARKO

    DA TA BIYU!

    Tambaya:

    Assalamu alaikum malam ya gida ya kuma ]awainiya da fatan kowa lafiya

    Allah yasa haka ameen, tambayata akan hallaccin addu'a da akeyi tsakanin

    hudubar farko da ta }arshe, Allah ya saka da alkhairi.

    Amsa:

    To ]an’uwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "

    A ranar juma'a akwai wani lokaci da babu wanda zai dace da shi, ya ro}i

    Allah a lokacin, face sai ya amsa masa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a

    hadisi mai lamba ta: 893.

    Malamai sun yi sa~ani game da wannan lokacin zuwa wajan zantututuka

    arba'in, kamar yadda Ibnu Hajar ya hakaito a Fathul-bary, 2\419, daga cikin

    wa]annan maganganun akwai cewa : tsakanin hudubobin juma'a guda biyu

    ne lokacin yake fadowa, don haka wasu malaman suke ganin mustahabbancin

    yin addu'a tsakanin hudubobi biyu, saboda musulmi zai iya dacewa da

    wancan lokacin mai falala. Allah ne mafi sani.

  • 50

    Jamilu Zarewa

    2/3/2015

    64. MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya }ara basira, malam wata mata

    ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba,

    ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da

    ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana

    jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam

    za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da

    shi? , na gode Allah ya }arawa malam basira da hazaka .

    Amsa:

    To 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki,

    saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada a hadisin da

    Muslim ya rawaito mai lamba ta : 81. Ga shi kuma aya : 10 a suratul

    Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba

    da zamanku akwai matsala a addinan ce.

    Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Ba}ara aya ta : 222,

    Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda

    hadisin Bukhari mai lamba ta : 616 ya tabbatar da hakan, Saidai zunubin

    barin sallah shi ka]ai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai

    shi kotu, alkali ya raba ku. Don neman }arin bayani duba Al-minhajj na

    Nawawy 2\69.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    6/3/2015

  • 51

    65. BUDURWATA BA TA HAILA, FALALACE KO MATSALA CE ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum dan Allah malam a taimaka min, matar da zan aura a

    yanzu haka auren bai fi wata biyu ba, shekararta 20 amma ba ta ta~a jinin

    haila ba, to malam wannan matsalace ko kuma falalace? sannan kuma za ta

    iya haihuwa? malam a taimakamin don Allah.

    Amsa:

    To ]an’uwa tabbas haila tana daga cikin alamomin da suke nuna cewa mace

    za ta iya ]aukar ciki, kamar yadda wasu malaman tafsirin suka fada, wannan

    ya sa lokacin da za'a yiwa matar annabi Ibrahim bushara da haihuwa sai da ta

    yi haila, saboda kasancewarta tsohuwa, kamar yadda wasu malaman tafsirin

    suka fassara ayar suratu Hud, don haka haila kuma alama ce ta haihuwa, duk

    matar da ba ta yin haila da wuya ta haihu.

    Akan iya samun wasu matan 'yan kadan wa]anda suke iya haihuwa ko da ba

    su ta~a yin haila ba, saboda Allah mai iko ne akan komai.

    Abin da nake ba ka shawara shi ne ku je wajan likitoci, don su gwada ta, in

    har suka tabbatar ba za ta iya haihuwa ba, kana iya hakura da auranta, saboda

    haihuwa ginshiki ne, daga cikin ginshikan da suke sa ayi aure.

    Rashin yin haila ba falala ba ce, saboda hadisi ya tabbatar da cewa: "Haila

    jini ne da Allah ya hukuntawa dukkan 'ya'yan nana Hauwa'u da jikokinta"

    kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba : 290.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    11\3\2015

    66. YADDA AKE YIN SALLAH A JIRGIN SAMA DA MOTAR HAYA

    Tambaya:

    Asallamu alaikum, Gafarta Mallam ya halatta yin sallar Farilla a cikin

    Mota/jirgin Sama da na Ruwa? domin wasu lokutan Mutum ya kan yi tafiya

    mai nisa zuwa jahohin kudu, ga lokacin Sallah ya yi ba sa Tsayawa domin

  • 52

    ayi Sallah, saboda ma fi akasarin fasinjojin Ba Musulmai ba ne, kai har

    direban ma ba Musulmi bane.

    Amsa:

    To ]an’uwa ya halatta ka yi sallah a jirgi ko mota, idan ya zama ba za ka

    sauka ba, sai bayan lokacinta ya fita, saboda fa]in Allah ma]aukaki "Kuma

    Allah ya wajabtawa muminai sallah a cikin lokuta kayyadaddu" Suratunnisa'i

    aya ta:103.

    Amma mutukar za ka iya riskar lokacinta bayan ka sauka, to ka jinkirta ta

    daga farkon lokacinta shi ya fi, saboda ka samu damar cika ruku'u da sujjada

    yadda ya kamata, hakanan idan tana daga cikin sallolin da matafiyi zai iya

    ha]a ta da 'yar'uwarta, kamar azahar da la'asar, ko magriba da Isha, saboda za

    ka iya jinkirta ta farkon, ka yi ta ha]e da ta }arshen.

    Duk sallar da ka ji tsoron fitar lokacinta za ka iya yinta a jirgi ko mota

    gwargwadon yadda ka samu iko, don haka ya halatta ka yi nuni da ruku'u ko

    sujjada lokacin da kake sallah a mota, idan kuma jirgi ne mutukar ka samu

    damar yi a tsaye ba za ka zauna ba, sannan ka yi kokari a duka wajan

    fuskantar alkibla, sai in ya ta'azzara. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata

    a gare shi ya halatta yin sallah a jirgin ruwa kamar yadda Albani ya inganta

    hadisin a Sahihul-jami'i a hadisi mai lamba ta : 3777, wannan sai ya nuna

    halaccin yi a mota da jirgin sama, saboda dukkansu ababen hawa ne.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    11\3\2015

    67. MACE ZA TA IYA YIN LIMANCI?

    Tambaya:

    Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace ta yiwa mata yan'uwanta

    limanci, toh in ramadan ya zo na kan tara mata na musu, da yake duk

    anguwar na dan fi su karatu, toh kusan anguwar ba malamin sunna ko ]aya

  • 53

    sai 'yan bidi'a, shi ne suke nema na ba su aya ko hadisi akan hakan, malam a

    taimakamin don Allah ?

    Amsa:

    To 'yar'uwa ina ro}on Allah ya jikan malam Ja'afar, mu kuma ya kyautata

    namu }arshen, ya halatta mace ta yiwa 'yan'uwanta mata limanci, saboda abin

    da aka rawaito cewa : Nana A'isha da Ummu Salama –Allah ya }ara musu

    yarda- sun yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin

    Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan nan Shafi'i a Musnad dinsa da

    sanadi mai kyau, Almajmu'u (4/187).

    Haka nan an rawaito cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare

    shi ya sanyawa Ummu-waraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yiwa matan

    gidansu limanci, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta :

    491, kuma Albani ya kyautata shi.

    Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yiwa matan unguwarku limanci, tun da

    kin fi su karatu, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. yana

    cewa: "Wanda ya fi iya karatun al}ur’ani shi ne zai yi limanci" Muslim 1078.

    Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a tsakiyarsu in suna da yawa, in

    kuma ita ka]aice sai ta tsaya a damarki. Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    13\3\2015

    68. MATATA TANA NAKU[A, GA SHI KUMA AN TADA SALLAR

    JAM'I ! -

    Tambaya:

    Wani ne a office ana kiran shi a waya, matarshi na matsanancin hali na

    na}uda, ana bu}atarsa, ikon Allah kuma gashi an tada i}ama za'a yi sallah sai

    wasu suka ce ya tafi wurin mara lafiya. wasu kuma suka ce ya tsaya ya gama

    sallar, to me ya kamata ya yi ?

    Amsa:

  • 54

    To ]an’uwa abin da yake daidai anan Shi ne : ya tafi wajan matarsa, saboda

    idan ha}}in Allah da na bayi suka ci karo akan gabatar da na bayi, saboda shi

    Allah mawadaci ne, Sannan za ta iya hallaka idan ka bar ta ba ka je ba, sallar

    jam'i kuma akwai sa~ani akan wajabcinta, ga shi kuma za ka iya gamawa ka

    dawo kafin lokacinta ya fita, yana daga cikin }a’idojin sharia, duk abin da

    ake bu}atarsa yanzu-yanzu akan gabatar da shi akan wanda za'a iya

    jinkirtawa, ko da bai kai shi daraja ba.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    22/3/2015

    69. ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI'A NE ?

    Tambaya:

    Assalamu Alaikum. tambaya. Allah ya gafartawa Malam, Na kasance ina

    amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a

    kowanne lokaci. Ina matsayin haka a sharia?

    Amsa:

    To ]an’uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi hakan ba zai sa ya zama

    bidi'a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai

    zaman kanta, yana amfani da shi ne don ya kiyaye adadin zikirinsa.

    Yin amfani da 'yan yatsu shi ne ya fi, saboda hadisi ya yi nuni cewa: za'a ba

    su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma

    Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba: 3486, don haka za su yi maka

    shaidar abin da ka yi na alkairi, sa~anin carbi.

    Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalinsa yana

    wani wajen, sa~anin idan da hannu yake yi, jan carbi yakan iya sanya wasu

    su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne,

    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana yin tasbihi da

    hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lamba:

  • 55

    1286, wanda Albani ya inganta, saidai wasu malaman suna cewa in ya yi da

    hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi.

    Saidai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan

    carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi'a, ga shi kuma

    ba'a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.

    Don neman }arin bayani duba : Majmu'ul fataawa 22\187 da Lika'ul maftuh

    na Ibnu-uthaimin 3\30. Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Zarewa

    24\3\2015

    70. NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KO ZAN IYA YIN

    ADDU'AR BUDE SALLAH?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum inada tambaya Malam, shin idan an fara sallah ka zo za ka

    bi liman, za ka karanta addu'ar da ake yi ne bayan kabbarar harama?

    Amsa:

    To ]an’uwa abin da malamai suka fada shi ne: mutukar ya riski liman a

    mike, to zai yi addu'ar bude sallah, sannan ya karanta fatiha, ko da kuwa a

    raka'a ta biyu ne, saidai idan ya riski liman a ruku'u, to zai shiga tare da shi,

    kuma addu'ar bude sallah za ta fadi, saboda wurin yinta ya wuce .

    Raka'ar da ka fara samu tare da liman, ita ce raka'ar farko a wajenka, wannan

    ya sa za ka yi addu'ar bu]e sallah, ko da kuwa shi liman a raka'a ta uku yake

    ko ta hudu, wannan shi ne zance mafi inganci, idan ka riski liman a tsaye

    amma abin da ya rage ya yi ruku'u, ba zai isa ka karanta addu'ar bu]e sallah

    ba, sannan ka karanta Fatiha, to za ka karanta fatiha, ka bar karanta addu'ar

    bude sallah, saboda addu'ar bude sallah sunna ce, karanta fatiha ga mamu

    kuma wajibi ne a wajan wasu malaman.

    Don neman }arin bayani duba Al-majmu'u na Nawawy 3/276 da kuma

    Majmu'ul fataawa 30/150.

    Allah ne mafi sani .

  • 56

    D. Jamilu Zarewa

    11/4/2015

    71. SHIN ABAYA TANA DAUKAR HUKUNCIN HIJAB ?

    Tambaya:

    Assalamu alaikum, malam don Allah tambaya nake da ita kamar haka:

    Abaya da mata suke sanyawa tana iya ]aukar hukuncin Hijabi ne, domin

    zaka ga ko harami za ka gan su da irin wannan shigar, kuma nayi kokarin

    leka wasu littafai masu alaka da hijab ban iya kaiwa ga magana akan hakan

    ba, malam ko akwai maganganun malamai akai? Allah ya saka maka da

    alkhairi.

    Amsa:

    To dan'uwa, abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne : ta sanya tufar da

    za ta suturce jikinta, in ban da fuska da tafin hannu a wajan wasu malaman,

    wasu malaman kuma suna ganin fuska al'aura ce, don haka ita ma ya wajaba

    a rufe ta, tun a nan kyawun mace yake, kayan da za ta sa su zama masu

    kauri, ba ya halatta ta yi ado in ba a cikin gidan mijinta ba, ko tare da

    muharramanta.

    Suturar mace musulma ba'a so ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba'a

    so su zama kayan da za su ja hankali, ko wadanda aka fesa musu turare.

    Mutukar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata, ba ta matse shi

    ba, za ta dauki matsayin hijabin da Allah da manzonsa, suka yi umarni. Don

    neman karin bayani duba : Majmu'ul-fataawa 22\110 da Hijabul-

    mar'atulmuslima shafi na : 54 zuwa 67. Allah ne mafi sani .

    Dr. Jamilu Zarewa

    15\4\2015

  • 57

    72. LAULAYIN CIKI YASA INA WAIWAYE A SALLAH, YAYA

    SALLATA ? !

    Tambaya:

    Assalamu alaikum malam, Don Allah macece take fama da yawan zubar da

    yawu a bakinta sa