Upload
others
View
0
Download
0
Embed Size (px)
Citation preview
Da sunan Allah mai rahama mai jin qai
Yin qoqari don samun sanayya da alaqa da ababn koyi na
daga kyawawan abubuwa, dangane da haka ne ma Imam
Rida (AS) ke cewa: aikin dukkan masu son mu da gaskiya
shine taimakon shia'ar mu. Tun a da can zuwa yanzu
akwai alamu masu yawa da kan iya bayyana mana
matsayi da girman kowanne xaya cikin ma'asumai (AS) a
rubuce da tarihance. Abinda shia kan iya yi – musamman
Iraniyawan cikin su – yana kasancewa ne duk shekara
makarantun Addini kan yaxa wata sabuwar koyarwa da
kan tafi da zamani.
A wannan littafi zamu bayyana muku abubuwan da muka
gada sannan kan dadai da mu musamman a wannan
zamanin daga Imam Ridha (AS).
Cibiyar wayar da kai da ake kran da Darul Hadis ce ke
kokarin kawo mana sakonni da ilimin da ya shafi binciken
yau da kullum – daga cikin wani xan abu- wanda mafi
yawancin sa an yada shi ne da yare farisanci wanda ya
shafi Imami na takwas (AS) don (amfanuwa da sunnoni
masu salo-salon, tare da yaxawa a matakan litattafai
qanana da mujalladai, ba tare da tauye saqon da ya qunsa
na ilimi ba, ba kuma tare da samun matsalar bugawa ba
ka rashin cikar adadin da ake buqata ba). wannan ne yasa
a duk faxin qasa shekara ta 2931 Hijri Shamsi, aka tsara
wannan aiki don wayar da kai kan dukkan hadisan da
suka fito daga Imami na takwas (AS), aka zartar da
shawarar samar da gungun mutane don yaxa abubuwan da
muka gada daga wannan Imami na takwas wato Imam
Ridha (AS).
Waxannan abubuwan da muka gada sun fito ne daga
wurare ko mavuvvuga daban da ban za kuma a yaxa su da
yanayoyi biyar [amfanuwa daga ingangantun
mavuvvugogi], [citratattun maganganu masu
mauhimmancin gaske], [amfana daga quararrun
mavuvvugai], [salo kala-kala] da [yadda da yin amfani da
salo mabambanta) daga muhimman ilimomi gamammu da
suka rage waxanda muka gada.
Gamayyar litattafai shida ne da suka haxa da:
2. Littafin [wata na kawas], na Mahdi Gulam Ali,
Tarihin rayuwar Imam (AS) daga rayuwar sa zuwa
shihadar sa, wanda aka rubuta shicikin taqaitattun
haruffa, wanda ya haxa vangarori 55 (cikin
taqaitattun shekarunsa masu albarka).
1. Littafin (Minawi Nigahi to) wanda ya tattaro
qananan Qissoshin da suka haxo tarihin rayuwar
Imam Ridha (AS) da mafi kyawun darussa masu
qayatarwa.
9. Littafin {Dar huduri Darya) na Hassan Ali Zadeh,
wanda ke da vangarori biyu [suka tattaro waqoqin da
suka yabi Imam Ridha (AS) cikin hikima daga
Hakim Sinayi Har suna nan (tun kimanin shekaru
dubu aka rubuta waqoqin] da [qananan waqoqin,
masu baitoci xaixai da mai baituka huxu-huxu].
4. Littafin [Inja Asiman, nazdiktar Ast], na Mustafa Pur
Najati, wanda ya kwatanta tare da kawo ziyarori
Imam Ridha (AS) da ke nuni zuwa ga rayuwar sa
(AS) ba kai tsaye ba gaban.
5. Littafin [Masihye Xus] Hamid Ahmadi Jalfa'yi,
zavavvun karamomin Imami na Takwas Imam Ridha
(AS) guda Arba'in.
6. Littafin [Barguzideh Kitab Shinasi Imam ridha (AS)]
na Hadi Rabbani, sannan rubutun da aka ciro shi
daga mavuvuugar da ta haxo da na sauran Imamai
Sha biyu (AS) tare da sanin kevantaccen rubutu.
Godiya ga marubutan Arjamad waxanda suka nemo
waxannan rubututtuka masu cike da amfanarwa da ke
qara mana kyautata zaton samun amfana ga masu neman
ilimi da makaranta.
Gabatarwa
Ya Allah ka yi salati ga Imam Ali Xan Musa Arridha:
Shakhsiyyar Imam Ali Ridha (AS) na daga cikin
muhimmiyar matsaya kuma mafi girma wajen dukkan
Iraniyawa wajen girmamata a matsayin addini da
mazhaba, a 'yan shekarun da suka gabata sai Iraniyawa
suka dauki niyyar yaxa koyar da abubuwan da 'ya'yan
Annabin Allah (SAW) suka bar mana ta wannan salon.
Da shigowar fararen matafiyan da suka keto daga
wuri zuwa wani sabida yanayi da neman kyautata rayuwa
da aminci, sai ya zama haske ya fantsama da motsawar
su, tun daga waxannan ranakun Xus da Sana Abad suna
zama masu alfahari, har zuwa yau ya zama kowanne ba
Iraniye ke amfanuwa da wannan ni'ima.
Wannan yanayi ya kyautata da zuwan baqo
Don kuwa dukkan baqikun san su
Ni kaina na so ace nima na zamo cikin waxanda
suka gan ku
Lungunan Kurasan ma kun san su
Don haka ne ma samuwar wannan hasken na Manzo
(SAW), sai aka buxe littafin Imamanci, sannan duk wani
fasali cikin wannan littafin na shiryarwa zuwa ga nuna
qoqarin Ahlulbait (AS) da yadda duniya ta zalunci hujjar
Allah (SW), fasali na takwas a littafin Imamanci kawai,
tunda sauran fasalolin na daban masu muhimmanci,
waxanda ke siffanta matsayi da girman wakilin Manzo
(SAW) na takwas.
Duk shekara ana samar da gomomin rubutattun
falaloli da matsayin Alayen Manzon Allah (SAW), da
haka ne zamu iya cewa mafi muhimmancin abun da kan
iya jawo buri zuwa ga yaxa koyarwa da tarihin Ahlulbait
(AS), wannan littafin mai suna [wata na takwas] nada
abubuwa huxu.
Rubutawa ko yaxa tarihin rayuwar Imami na takwas
Imam Ridha (AS) daga rubutattun mavuvvugogi
ingantattu.
Bayani da karantar da muhimmain saqo na ilimin ta
sassauqar hanya.
Maganganu masu tsada cikin haruffa 'yan kaxan
cikin kowanne vangare "da aka tattauna cikin littafin".
Tsara tarihin rayuwar Imam (AS) daga haihuwar sa
zuwa shihadar sa cikin vangarori 55.
Babban abin farin ciki da ke sanya fata na gari da
ake ganin za a samu nasara wajen yaxa maganganun da
koyarwar alayen Muhammad (SAW) sannan ya janyo
mutane zuwa yardar su (AS).
Yardar Ridha yardar Allah ce.
Domin idan Ridha ya yarda Allah ya yarda.
Mahdi Gulam Ali
Mash'had, labrarin masallacin Jami'u
Goharshad.
11- Zulqida = 62-Shahrivar 1936
WATA MATA DAGA HABASHA
An kama wani jirgin ruwa na matafiya a arewacin
Africa, matafiyan daga arewacin na Africa sun kama
hanyar su zasu wuce zuwa Habasha, sun taho daga nisan
duniya, tun daga Africa ta yamma sannan su tsallako ta
cikin Saudiyya suna son zuwa Hijaz cikin qasar Kuwait.
Bayan wasu kwanaki suna tafiya sun isa Madina
cikin Saudiyya sun tsaya don su huta na tsawon lokaci
sabida wahalar da ke tattare da su musamman mata, sai
daya daga cikin tsofaffin 'yan kasuwa ya zo tare da
sarakuna goma zuwa kasuwar Madina domin siyaen bayi.
Imam Musa xan Ja'afar (AS) ya tambayi Hisham,
xaya cikin yaran sa dake tare da shi cewa: ba wani xan
kasuwa da yazo daga Maroko (Morocco) zuwa nan
Madina ne? Da yake Hisham baqone a kasuwa sai ya
bada amsar da ta sava haqiqa.
Da yake Imam na jiran wani da zaizo daga can
Marokon ne sai yake cewa, dole a samu wanda ya zo daga
can, xan kasuwan da yake baqo mai alamun tafiya
(tafiyayye) kuma mutumin Maroko! Zo muje kasuwar
tare.
Lokacin da suka isa kasuwa, suka xan yi binciken na
xan qanqanin lokaci, sai kuwa suka gano xan kasuwa
mutumin Maroko, suka nemi ya nuna musu bayi. Imam
(AS) na son siyen bawa sabida yiwa mahaifiyar sa mai
albarka da girma hidindimu, mai suna Banu Hamideh
Musfa, sai ya zamana ba'a samu mai irin halayyar da suke
so ba sai wata daban, Imam ya ce: bana buqatar wannan,
ai kana da wata baiwar, ina take?
Mutumin bai wani muhimmantar da tambayar da
Imam ya yi masa ba sai ya ce: bani da wata! Wannan
kawai nake da su/ita, Imam (AS) yaji haushin qaryar da
wannan xan kasuwa ya yi masa, sai ya ce masa: na san
kana da wata baiwar ka faxamin inda ka ajiye ta ba, tana
ina?
Sai wannan xan kasuwar cikin sanyin gwiwa yace:
ina rantse maka da Allah xayar da nake da ita bata da
lafiya ne (ba buqatar na saida maka da ita a haka)!!
Imam dai yace gaba da karfafa maganarsa na neman
shi wannan mara lafiyar yake so ba wata ba, ya fuskanci
xan kasuwar nan ya ce: to mai zai hana na ganta, sai mai
siyarwar (xan kasuwar) ya nemi Imam ya tafi zuwa wani
xan lokaci sai ya dawo kasuwar kafin ya kawo baiwar.
Washe garin wannan ranar sai Imam yace da
Hisham kaje kasuwa wajen wannan xan kasuwar na jiya
ka tambayomin kuxin baiwar da mukayi magana da shi,
duk qimar kuxin da ya sa mata duk tsadar ta zan siyeta.
Lokacin da Hisham yaje wajen wannan xan kasuwar
sai xan kasuwar ke tambayar sa kan cewar: shin wannan
mutumin da suke tare da shi jiya wanene?
Da yake Hisham baya son baiwa wannan xan
kasuwar dogowa kuma cikakkiyar amsa sai yace: wani
mutum ne daga qabilar Bani Hashim, xan kasuwar da
yazo daga Marokon yace: na san rabe-raben sadat na bani
Hashim amman inason sanin shin shi wannan mutumin
daga wane vangare na bani Hashim ya fito? Hisham ya ci
gaba da voye masa labarin ya bashi amsar cewa: kawai
dai xaya daga cikin manyan Banu Hashim ne.
Xan kasuwa ya ce: a haqiqanin gaskiya dai sunan
wannan baiwar [Tuktam] daga wani waje mai nisan gaske
a Maroko na siyawa kaina ita, kuma mace ce sananniya
cikin Ahlulkitabi lokacin da na gan ta, ya ce: wannan
baiwar bata dace da kai da ire-iren ka ba, dole ta zama
tare da mafi ingancin mutane a bayan qasa, domin idan ta
zama tare da irin wannan mutumin (mafi ingancin
mutanen) bayan wani xan lokaci qanqani zata haifi xa
wanda zai gagari dukkan wani xa a gabasci da yammacin
duniya ta yadda duk wanda yazo gaban sa dole ya rusuna.
Hisham yace da wannan xan kasuwar: wanda zai
siyeta na daga cikin mafiya ingancin mutane kuma in
Allah ya yarda abun da ka faxa shine zai faru tunda
wannan Ahlul kitabi na da wannan sifa, kaidai ka zura ido
zaka gani.
Uwa da Uba
[Tuktum] ta shiga gida Imami na Shida, wato wajen
matarsa Bani Hamideh Musaffa, matar Imam Sadiq (AS)
babar Imam Musa Al-Kazim (AS) wacce na daga cikin
maxaukaka kuma sanannun cikin Ajamawa wajen tsarki
kan sauran mata, sai ta kalle ta, Taga cewa wannan
baiwar Allah na da matuqar Kamewa sannan tana
mutuqar taimakawa matan gidan wajen ayuukan tare da
hidimta musu.
Ta vangaren addini da girmama sauran mata na tare
da Tuktam da take yi ya sa ta zama itace mafi girma da
daraja cikin matan, idan tazo kusa da Tuktam bata iya
zama sabida girmamawa sannan Take kiranta da Suna
Hamida, wannan ne yasa sannan dukkan matan gidan
suma suka yi shawarr cewa su dinga kiranta Uwar gidan
tasu da Hamida, sai ya zama daga wannan lokacin sai
sunanta ya zama Hamida.
A wannan lokacin ne Hamida, ta ga Manzo (SAW)
cikin mafarki yana bata umarni cewa: Ke Hamida ki
baiwa xan ki Musa Najma, akwai xanta da zai zo duniya
zai zama mafi darajar mutane a bayan qasa.
Sai Hamida ta yiwa xan ta Musa (AS) maganar
auren Najma ta yi masa bayani cewa: ya xa na: wannan
'yar itace tafi dacewa da kai domin banga wata yariya
kamar ta ba, sannan bani da kokwanto kan abunda nake
gaya maka, Allah (SW) na son tsarkake mana wannan
tsatso ne ba wani abu ba, ka kyautata mata2.
2 Uyunu Akhbarur ridha (AS) Littafi na 2 shafi na 24 hadisi na 1 da shafi na 21 hadisi
na 9.
Haihuwa
Yaushene Najma ta samu juna biyu? Masu ruwaya
dangane da samun cikin sa na cewa ta ce: lokacin da aka
samu cikin dana Ali, ban ji nauyin da masu ciki suke ji
ba, duk sanda na kwanta barci san na dinga jin Tasbihi da
hamdala da hailala daga cikina, sannan wannan karatun
na bani nutsuwa amman idan na tashi daga bacci, bana jin
muryar.
Lokacin da cikin ya isa haihuwa, a ranar Lahadi, sha
xaya ga watan Zulqida shekara ta 241 bayan hijira a
Madina na haife shi, Tarihin haihuwar sa da watan
Shamsiyya daidai da Goma ga watan Deiy shekara ta 299
hijira shamsiyya.
Farkon wanda ya fara yiwa Najma barkar haihuwar
wannan xa shine Musa Xan Ja'afar (AS), yake gayawa
matarsa cewa: madalla da wannan babbar kyauta da
girmamawa ta Ubangiji, wannan girmamawar Ubangiji ce
gareki.
Nan take Imam Musa (AS) ya dauki wannan yaro
cikin cikin farin zanin goyo daga wajen babar sa, sannan
ya yi masa kiran salla a kunnen dama ya yi masa iaqama a
kunnen hagu ya nemi a kawo masa ruwa, ya yiwa yaron
amfani da shi, sannan ya dawo da shi wajen mahaifiyar ya
ce: karve shi ki sani cewa hujjar Allah ne a kan qasa.
Wannan jariri na Najma, yayi saurin girma qwarai
da gaske, yana shan nono sosai, bayan haihuwar Najma ta
kasance koda yaushe cikin ganawa da Allah da zikirori,
tana cewa sabida kulawa ta musamman ga xana Ali xan
Musa Arridha (AS) nono bayan sallar mustahabbi bana
iya samun daman kammala zikirori na1.
1 Al-kafy, littafi na xaya, shafi na 416, Uyunu Akhbarur ridha (AS) Littafi na 2 shafi
na 24 da na 21 da na 12 hadisi na 1..Al-irshad, shafi na 924. Tajil walid, shafi na 41.
Hai'atu wa nujumu islami, littafi na 1, shafi na 912.
Suna da shuhura (xaukaka)
Imam Musa xan Ja'afar (AS) ya sanyawa xan sa
suna Ali sannan ya sanya masa laqabi da Ridha, sannan
koda yaushe yana son ganin yana magana da wannan xan
nas, sannan idan yana magana da shi da suna Ridha yake
kiran sa, wani lokacin idan xan sa na kusa da shi yana
kiransa AbulHassan.
Bayan wannan ne – shihadar Imam Ridha (AS) –ya
rayu tsakanin waxanda suka sava da mahaifin sa, sannan
Ma'amun ya kira Imam Ali Ridha (AS) da suna cewa
shine ya dace da zama shugaban dukkan musulmai, Imam
Jawad (AS) dangane da wannan maganar na cewa: ina
rantsuwa da Allah qarya suke, abinda ke bakin su ya sava
da abinda ke cikin zuciyar su, Allah mai girma da
xaukaka da suna Ridha ya kira shi, don haka ne ma sabida
neman yardar Allah – mai girma da xaukaka – a
samaniyar sa, sannan ga manzon sa da Ayimma bayan
qasa sune hujjoji kuma yardaddu.9
9 Uyunu Akhbarur ridha (AS) Littafi na 2 shafi na 29 hadisi na 2 da shafi na 24 hadisi
na 1. Kashful Gumma, littafi na 9 shafi na 16.
Siffofinsa da ya kevanta da su
Imam (AS) ba gajere bane sannan ba dogo bane,
wato yana da matsakaicin tsayi, fuskar Imam (AS) ta xan
yi kusa da yanayin duhu-duhu saidai ba duhun ne da shi
ba, za mu iya cewa yana da xan cakuxen baqi a tattare da
shi, lokacin sanyi a kan tabarma da makamantan ta yake
zama, lokacin sanyi kuma yana zama kan abunda aka yi
shi da auduga.
Kayansa masu kaushi ne sannan masu tauri ne,
amman duk sanda zai gana da mutane yana gyatta kansa
da kaya mafi kyawun da yake da shi.
Yana sanya manyan kaya yayin haduwa da mutane.
Tare da sanya turare na shafawa jiki da na kaya, sannan
yana tanadar turare mai tsada.
Kwarjinin sa da haibar sa sun kai matsayin da –
masoya da maqiya – duk mutane na gurfana masa, duk
wanda ko waxanda suka gan shi, suna matuqar girmama
shi, duk sanda ya zauna tare da mutane yana musu
zantuka masu albarka kyawawa, sabida kwarjinin da yake
da shi ba wanda ke iya yi masa magana da qarfi.4
4 Al-kafy, littafi na 6, shafi na 522, da littafi na 2, shafi na 521 hadisi na 9, Uyunu
Akhbarur ridha (AS) Littafi na 1 shafi na 211 hadisi na 2 da shafi na 296. Rayuwar
Imam Ridha (AS) littafi na 2, shafi na 11.
Rayuwar Imam tare da mahaifin sa
Imam Ali xan Musa Ariidha (AS) tun ma kafin ya
isa zuwa ga Imamanci tsakanin 'ya'yayen Imam Musa xan
Ja'afar na daban ne, Imam Sadiq (AS) tun shekaru kafin
haihuwar jikansa yake gayawa xan sa Imam Kazim (AS)
busharar xan da zai haifa, da wannan ne ma Imam Ali
Ridha (AS) tun daga yarinta ya zama qarqashin kulawar
ta musamman daga wajen Mahaifin sa.
Ko yaushe Imam Kazim (AS) yana gayawa sauran
'ya'yansa cewa duk wani abu na ilimi ko neman sani su
dinga tambayar dan uwansu, yana ce musu: wannan xan
uwan naku Ali Ridha (AS) masanin cikin Alayen Manzo
(SAW) ne, ku dinga tambayar sa duk wata tambaya ta
ilimi, kuma duk abinda ya gaya muku ku yarda da shi
sannan ku yi aiki da shi; na ji da babana Ja'afar xan
Muhammad (AS) yana cewa: malami cikin alayen
Muhammad (SAW) na tsatson ka, na so ace (kai ina ma
dai) zan haxu da shi na gan shi, sunan su daya da
Shugaban Muminai Ali (AS).5
5 Alamul wari, littafi na 2, shafi na 55.
Yan uwan sa maza da mata
Imam Kazim (AS) na matuqar qaunar dukkan
'ya'yan sa. Yana da kimanin 'ya'ya 91. Wannan ne ya sa
Imam Ridha (AS) yake da 'yan uwa maza da mata birjik,
waxanda suka fito daga iyaye mata daban-daban.
Sunayen 'yan uwan Imam Ridha (AS) maza – su sha
takwas – waxanda suka haxa:
Ibrahim, Abbas, Qasim, Hamza, Isma'il, Ja'afar,
Harun, Hassan, Ahmad, Muhammad, Sulaiman,
Abdullah, Is'haq, Ubaidullah, Zaid, Hassan, Fadl da
Hussain.
Sunayen 'yan uwan Imam Ridha (AS) mata – suma
sha takwas ne – waxanda suka haxa:
Fatima qarama, Fatima Babba, Ruqayya, Hakima,
Ummu Abiha, Ruqayya Qarama, Ummu Ja'afar, Lubaba,
Zainab, Khadija, Alliyyah, A-mina, Hassana, Bariha,
Ai'sha, Ummu Salma, Maimunah da Ummu Kulsum.
Cikin dukkanin 'ya'yan Imam Musa (AS), Babban
xansa, Imam Ali Ridha (AS) ne wanda yafi kowannen su
matsayi da iko da ilimi da falala.6
5 Al'irshad littafi na 2, shafi na 244.
Nagartattun 'yan uwan sa
Ahmad xan Musa – wanda cikin Iran aka sani kuma
ya shahara da Shahcirag –, tsakanin dukkan 'yan uwan
Imam Ridha (AS) yafi kowannen su matsayi da
mutumtaka, mutum ne mai matuqar martaba, baban sa
Imam Kazim (AS) na matuqar qaunar sa, sannan bayan
Imam ridha yana gabatar da shi kan dukkanin sauran
'ya'yan sa haka nan ma sauran 'ya'yan suna matuqar
girmama shi.
Ahmad xan Musa wanda tsakanin shekara ta 122
zuwa ta 129AH lokacin da yake son zuwa ganin xan
uwan sa ya nufin Kurasan a Khan Zaniyan, kusa da Shiraz
kan hanyar sa Abdullahil Ma'amun (sarkin abbasiyawa
dan Harunar Rzashid) yasa aka tsare shi a hanya ya
shahadantar da shi.
Isma'il xan Musa, xaya daga cikin 'yan uwan Imam
Ridha (AS) na cewa: duk lokacin da muka fito waje tare
da baban mu tare da xan uwan mu Ahmad, yaram baban
mu sun fi alaqantuwa da Ahmad sosai, shi kansa baban
namu baya rabuwa dashi koda na xan qanqanin lokaci,
koda yaushe yana kule da shi.
Ana cewa: Ahmad, bayi dubu ya 'yanta zuwa ga
Allah (ya sanar da bayi dubu Allahn su).
[Muhammad xan Musa] shima xaya ne cikin 'yan
uwan Imam Rida (AS) da yake mutum ne mai xaukaka
kuma mai kyawawan ayyuka, dangane da shi ana cewa
wasu lokutan ma'abocin tsarki da salla ne sannan dukkan
daren sa yana qarar da shi cikin tsarki da yin salla, ko
yaushe baya rabuwa da alwala, sannan ruwan alwalar sa
koda yaushe baya nesa da shi.yana sallatar dukkan rabin
daren sa, sannan ya yi baccin na wani xan lokaci sannan
ya qara tashi ya yi alwala ya yi salla, wannan ne ya sa
baccin sa ya zama kaxan sosai sannan koda yaushe yana
shagaltuwa da ibadu.
Xaya daga cikin na dab da shi na cewa: duk sanda
na ga Muhammad sai na tuna faxin allah maxaukakin
sarki cewa: «»1 w ato «»1
7 Suratuz Zariyat, Aya ta 81. 1 Al-irshad littafi na 2, shafi na 245, Jogirafin tarihin tafiyar Imam Ridha (AS) shafi na 18.
Mafi darajar 'yar uwa Imam (AS)
Fatima babba, wacce ta fi shahara da Fatima
Ma'asuma (AS), zamu iya cewa ita mafi darajar 'yar uwa
mace da Imami na takwas yake da ita cikin dukkan 'yan
uwan sa mata, an haifi wannan baiwar Allah a farkon
watan Zul'qi'ida shekara ta 219AH, sannan Imam Ridha
(AS) ya tafi Khurasan, a shekara ta 122 Fatima (AS) ta
bar Madina zuwa sabida haduwa da xan uwan ta, a kan
hanyarta zuwa wajen sa a Saweh ta kamu da rashin lafiya,
daga nan ne ta nemi a kawota Qum, lokacin da mutanen
Qum suka san zuwan ta suka tattaru suka tarbota Musa
xan Khazraj ya yi alfaharin saukarta, bayan kwanaki sha
shida zuwa sha Takwas ne, sabida tsananin rashin lafiyar
da ya tsananta mata tana 'yar shekaru ishirin da takwas ta
bar duniya, tun daga wannan lokacin ne mutanen garin
Qum suka gina muhallin daaka binne ta (AS), bayan ta
akwai jikar Imam Jawad ('yar Zainab 'yar Imam Jawad
(AS)) wacce aka binne ta a Gumbad (arewacin Iran kusa
da bodar Turkmanistan).
Imam Ridha da Imam Jawad (AS) suna cewa: Allah
ya riga ya sanya ladan wanda ya ziyarce ta Aljanna, wani
lokaci Sa'ad, xaya cikin masana da yake a Qum, ya je
wajen Imam Jawad (AS) a Khurasan, Imam Jawad (AS)
yake ce masa: kusa da ku akwai qabarin dangin mu, Sa'ad
ya bada amsa cewa: e, qabarin 'yar uwar ku Fatima 'yar
Musa xan Ja'afar ne, Imam ya jaddada masa ya ce: duk
wanda yake wajen ta ya ziyarce ta xan al'janna ne, a nan
ne ya baiwa Sa'ad labari dangane da ziyarar 'yar uwar su
wanda har yanzun nan yana nan kuma masu ziyarar
fatima Ma'asuma (AS) suna zuwa har yanzu. Shekaru
kafin haihuwar Imam Musa (AS) Imam Ja'afar (AS) yayi
maganar haramin Fatima Ma'asuma (AS) yake cewa: ba
da daxewa ba daga cikin 'ya'ya na xa a binne jikata a
wannan garin (Qum) mai suna Fatima, al-janna
sakamakon wanda ko wacce ya/ta ziyarce ta.3
9 Kamiluz ziyarat shafi na 824 hadisi na 8 da na 2, biharul anwar littafi na 57 shafi na 289 hadisi na 49 da littafi na 99 shafi na 255, hadisi na 5, da shafi na 257 hadisi na 5.
Matar sa (AS)
Sunan matar Imam (AS) kafin ya aureta [Dareh]
amman bayan ya aure ta sai ya canza mata suna yake
kiranta da [Khizuran]. Tana da dangantaka da mariyatul
Qibxiyya matar Manzo (SAW). Sauran sunayen ta sun
haxa da [Sabikah Nubiyah], [Raihana] ana mata al-kunya
da [Ummu Muhsin]. Abar al-fahari babar Imam Jawad
(AS) mai suna Khizuran ce, asalinta 'yar Sudan ce.22
80 Al-kafi, littafi na xaya, shafi na 492. A'a lamul wari shafi na 824. Manaqibi Ibni Shahr Ashub, littafi na 4, shafi na 879.
'ya 'yan sa (AS)
Imam Ridha (AS) xa xaya tal Namiji yake da shi,
wannan nazarin cikin marubuta tarihi xan da suke
kawowa a matsayin xan sa (AS) namiji shine Imam Jawad
(AS). Saidai wasu daga cikin su sun kawo wasu maza
cewa Ima (AS) ya riqe su ne a gidan sa ya kula da
tarbiyyar su.
Babar Imam Jawad (AS) Khizuran ce. Lokacin da ta
samu ciki, Imam Ridha (AS) ya yi mata bushara da cewa
xan da zata haifa na daga cikin hujjojin Allah a bayan
qasa don haka ta bashi kulawa ta musamman, ta wani
vangaren kuma Hakima babba cikin yayyen sa mata ta so
idan an haife shi ta kula da Babar sa Khizuran ta zauna
tare da ita.
Anan nan kwatsam 22 ga watan Rajab Ranar
Juma'a shekarar 235 hijira Qamariyya cikin Madina aka
haife shi, farin ciki da annashuwa suka cika mahaifinsa,
ya xauki yaron daga hannun mahaifiyar sa ya yi masa
kiran sallah a kunnen sa na dama iqama kuma a kunnen sa
na hagu sannan ya sanya shi cikin zanin haihuwa, wannan
xan da aka haifarwa Imam (AS) na kama da Musa da Isa
(AS) yake gayawa shi'arsa cewa haqiqa Allah (SW) ya
qaddara bani wanda zai gaje ni, ya gaji iyalen Dawud ...
Imami na takwas ya sanyawa wannan xan nasa suna
Muhammad sannan yake masa al-kunya da Abu Ja'afar.
Imam Muhammad xan Ali wanda akewa laqabi da
Jawad (AS) baban sa ya yi shihada lokacin da bai wuce
shekaru takwas ba, ya xauki nauyin Imamanci a
waxannan qananan shekarun nasa masu albarka. Wannan
ne yasa ya zama Imami mafi qarancin shekaru da ya zama
Imami cikin tarihin ahlulbait (AS) wanda ya savawa
abunda aka saba gani, duk da haka shi'a sun karvi
Imamancin sa a waxannan shekarun bisa Ikhlasi ba tare
da wani ko wasu ya/sun sava kan Imamancin sa ba.
wannan karva da kowa ya yiwa Imamancin sa ya sanya
dun qoqarin da Imam Ridha (AS) na wayarwa da sanin
ma'anar Imama ya zama wani yanayi da ya qara fito da
abun ga kowa da kowa har ma ake cewa.
Shekarun Imam Jawad basu wuce 15 a ranar
qarshen Zul qi'ida shekara ta 112HS a bagdad aka
shahadantar da shi.22
88 Al-kafi, littafi na xaya, shafi na 492.al-irshad littafi na 2 shafi na 278. A'a lamul wari shafi na 824. Manaqibi Ibni Shahr Ashub, littafi na 4, shafi na 879. Biharul Anwar, littafi na 82, shafi na 808. Hayatul Imam Jawad (AS) shafi na 58-55.
Tare da al-Qurani
Imam Ridha (AS) da ya kasance ran Al-qur'ani,
koda yaushe yana nishaxantuwa da shi, dukkan zantuka
da hirarrkin Imam Qur'ani ne, masoya da maqiyan sa suna
da imanin cewa Imam (AS) qur'ani ne da yake da gangar
jiki, Ibrahim xan Abbas Suli (wanda ya bar duniya a
shekara ta 141AH), yana daga cikin masana kuma manya
cikin ahlussunna, ya yi wa Imam hidima ta wani lokaci,
yana cewa: Ma'amun yaso wai da Tambayoyi kala-kala
daban-daban ya jarraba Imam Ridha (AS), sai ya zama
dukkan tambayoyin da ya yi Imam (AS) da qur'ani ya
amsa masa su, dukkan amsoshi magangani da huxubobi
da bada misalai dukkan su Imam Ridha (AS) da qur'ani
yake yin su.
Kullum bayan gama salla da addu'o'in asuba yana
shagaltuwa ne da karanta qur'ani har ma yana cewa: ya
kamata ya ace duk bayan sallar asuba mafi qaranci mutum
ya karanta aya 52 ta qur'ani.
Haka nan ma da daddare ma lokacin da mutum zai
kwanta, ya kamata ya karanta al-qur'ani sannan lokacin da
yake karanta qur'anin ya zama a duk wani waje da aka
ambaci al'janna ko azaba ya yi kuka, ya nemi Allah ya
sanya shi a al'janna ya nemi tsarin Allah daga wutar
jahannama, ya kasance duk bayan darare uku yake sauke
qur'ani.
Lokacin da Imam ya yi wa Khaza'i kyautar kaya ya
ce masa: Ka kula da wannan rigar sosai, dare dubu sannan
a kowanne daga waxannan dararen dubu an yi raka'a dubu
da ita sannan an sauke qur'ani da ita sau dubu duk da ita
na karanta.
Daga maganganun shiriya da Imam ya karantawa
wani daga yaran sa mai suna Nazir xan Ahmad xan
Muhammad bazanti magana dangane da hadafi ya ce
masa: ba komai bane sai cikakken littafin Allah (SW).21
82 Littafin malla yahduruhul Faqih littafi na 8 shafi na 505, uyunu akbarur Ridha (AS) littafi na 2 shafi na 810, hadisi na 4 da na 5. Al-amali na sheikh Saduq, shafi na 751 hadisi na 80288458. Al-amali na sheikh Xusi, shafi na 859, hadisi na 749. Basairud darajat, littafi na 8, shafi na 245, hadisi na 1.
Imam (AS) da addu'a
Wani vangare da zamu iya kalla sosai cikin rayuwar
Imam Ridha (AS) shine, yin addu'a. Imam (As) ya
kasance mai matuqar yin yana matuqar shagaltuwa da yi
addu'a da harshen sa mai albarka.akwai gomomin addu'o'i
masu matuqar kyau da ya bar mana. Kai Imam ba wai
kawai yana addu'a bane yana ma kaxaitar da wasu tare da
sanya su yin addu'a yana cewa:
Maganar da yake maimaitawa yaransa da yawa
itace, itace: an bar muku makamin annabawa, wani ke
tambaya cewa: mene takobin annabawan da aka bar
mana? Imam (AS) yace masa: addu'a.
Ima yake cewa salati xaya cikin dawwamammun
addu'o'i ne harma yana cewa: duk wanda ba zai iya yin
komai na neman gafara ba (wato ya rasa kalar istigfarin
da zai yi), ya yi wa Muhammad da Iyalan gidan sa salati,
domin cewa salati yana shafe zunubai.
Wani daga cikin 'yan shia ya nemi Imam (AS) ya yi
masa assu'a, sai ya ce masa: [shin kana tunanin bana
muku addu'a ne? Ai lokacin da nake ganin ayyukan ku ina
muku addu'a, ina rantsuwa da Allah cewa: akullum da
daddare ana nuna min ayyukan ku ina gani.
Imam (AS) ya ci gaba da cewa: shin baka karanta
faxin Allah (SW) ba cewa [ka gaya musu (ya
Muhammad) cewa: ku yi aiki, Allahda manzon sa da
muminai na ganin ayyukan ku] ka sani cewa abun da ake
nufi da uminai a wannan lokacin shine Ali xan Abi Xalib
(AS) ne, a yau kuma Imamin zamanin ka ne.29
88 Al'kafi, litafi na xaya shafi na 289 hadisi na 4 da shafi na 41 hadisi na 5. Amali, na Saduq, shafi na 888, hadisi na 828.
Ibadar sa ta dare da rana
Raja'a xan Dahhak, yaron Ma'amun ne da ya sanya
shi ya taho da Imam Ridha (AS) daga Madina zuwa
Khurasan. Ya rubuta bayani mai yawan gaske, da ya
tsamo magana kan ibadun Imam (AS):
Ma'amun ya bani umarnin cewa na kula tare da
sanya idanu ga wannan malamin sannan kada mu biyo da
shi ta hanyar Qum, mu biyo da shi ta hanyar Basra,
Ahwaz da faris, kuma dare da rana kada mu rabu da shi
ko mu yi nisa da shi mu kula da shi tare da bashi kariya
sosai har sai mun iso da shi zuwa wajen Ma'amun, na
zamo koda yaushe tare da shi bana rabuwa da shi tun daga
Madina har zuwa har zuwa Marwa, ina rantsuwa ga Allah
ban tava ganin wani mutum mai tsoron Allah da ambaton
Allah kamar sa ba, gaba xayan lokutan sa na tafiya ne
wajen tuna Allah (SW) duk sanda yake sallah yana
tsawaita sujjada da tasbihi uku da salati, tun duhun asuba
idan ya yi sujjada yana tasbihohi da da salati har sai rana
ta xago, bayan nan sai ya yi wa mutane huxuba da wa'azi
zuwa zawali (xagowar rana2 sannan ya sake alwala, ya
koma wajen da yake salla ya yi raka'o'i shida (sallolin
masu raka'o'i biyu guda uku) a raka'ar farko bayan fatiha
sai ya karanta suratul Ma'un, raka'a ta biyu kuma bayan
ya karanta ta sai ya karanta suratul ikhlas, a sauran
raka'o'i huxun ma yana karanta suratul ikhlasin, yana
sallamewa bayan kowacce raka'a biyu, haka nan cikin
kowacce raka'a ta biyu bayan ya karanta fatiha akwai
kalar qunutin da yake karantawa, sai ya yi kiran salla da
iaqama, sannan ya sallaci azzahar xin sa, tunda sallar
azzahar ce, tana da sallar azzahar ce yana karanta tasbihai
huxu, bayan ya tafi sujjada ya yi sujjadar godiya bayan
nan sai kaji kalamr "alhamdulillah!!" daga bakin sa,
bayan ya xgo kansa daga sujjadar godiya, sai ya miqe
sannan ya qara sallatar wata sallar raka'a shida, cikin
kowacce raka'abayan hamdala da surtul ikhlas sannan
yana sallama qarshen kowacce raka'a biyu, cikin kowacce
salla bayan ruku'u yana qunut, bayan ya gama sai ya yi
iqamar wata sallar, bayan ya gama sallar sai ya yi iqamar
sallar la'asar, bayan ya idar sai ya zauna yayi ta yin tasbihi
sau huxu har sai sanda Allah ya so zai gama, bayan ya
gama sai ya yi sujjada ya yi godiya ga Allah, idan kuma
lokacin faxuwar rana ya yi wato lokacin magriba, sai ya
yi alwala, ya yi sallar magriba da kiran salla xaya iqama
xaya, da qunut xaya a raka'a ta biyu kafin tafiyar ruku'u
bayan gama karatun sura, yana sallamewa sai ya ci gaba
da zaman da ya saba yi bayan salla ya yi wannan tasbihin,
bayan ya gama sai ya yi sujjadar godiya, ya xago kansa ba
tare da ya yiwa kowa magana ba, sannan ya yi raka'a
huxu nafilolin bayan magriba, cikin kowacce raka'a ta
biyu yana yin al'qunuti bayan kammala karatun sura, yana
karanta suratul majd a raka'a ta farko suratul ikhlas a
raka'a ta biyu tare da yin dukkan tasbihai, da wasu
karatuttuka, sannan ya yi buxa baki, sannan ya xan huta
har zuwa xayan ukun dare, sannan ya tashi ya fara sallar
ishsha ya sallace ta cikin raka'o'i huxu, bayan karatun sura
a raka'a ta biyu yana yin al'qunuti, bayan ya sallame yana
zama a inda ya yi sallar ya yi ta yin tasbihi kamar yadda
muka ambata a baya (cikin sallar magriba), bayan gama
addu'o'in bayan salla sai ya yi sujjadar godiya, ya xago ya
tafi shimfixar sa ta bacci, a daidai lokacin da sulusin dare
(xaya bisa uku) na biyu ya yi, a na qarshen sai ya tashi
daga bacci sabida sallar dare.24
84 Uyunu akbarur Ridha (AS) littafi na 2, shafi na 810, fassarar Mustafid da Gaffari.
Halayen Imam Ridha (AS)
[Ibrahim xan Abbas Suly] babban mawaqi ne
sannan marubuci a zamanin imami na takwas yake ya xan
yiwa Imam (AS2 hidima na xan wani lokaci, ya kawo
wani tarihi na halayen Imam (AS) mutane sun karvi
wannan ruwayar daga gareshi yake cewa:
Ban taba ji ko gani Abul Hassan (AS) yana kirawa
wani jafa'i ko mummunan fata cikin zantukan sa ba, ban
kuma tava ganin ya katse mai magana ba, yana haqurine
har sai mai maganar ya gama maganar sa, sai ya ga idan
ya dace ya yi magana sai yayi idan kuma ba sai ya yi
magana ba sai ya yi shiru, ban tava ganin ya takurawa
wani kan yin wani aiki ba, sannan in har yana da damar
yin aiki yana yi da kansa, baya miqe qafafuwan sa gaban
kowa, baya dorawa abokan zaman sa nauyin komai, ban
tava ganin ya faxawa masu yi masa hidima baqar magana
ko zagi ba, ban tava ganin ya zubar da miyau a gaban
wani ba.
Ban tava ganin yana qyaqayata dariya ba, yana dai
yin murmushi da sunan dariya; baya kevancewa shi kaxai
yayin cin abinci, yana kiran yaransa da masu yi masa
hidima zuwa cin abinci, har masu gadin gida da masu
kiwon dabbobi sun san cewa kaxan yake bacci, mafi
yawan daren sa yana qarar da shi da ibadu, tun daga
faxuwar rana har zuwa gefin asuba, yana yana yawan yin
azumi, azumi uku cikin kowanne wata bai tava wuce shi
ba, yana cewa: wannan muhimmancin sa kamar kamar
azumin da ake yi ne duk shekara, yana yawan bada
sadaka a voye sannan yana matuqar kyautatawa mutane,
mafiya yawan sadaqar da yake yi yana yin ta cikin duhun
dare neduk wanda ya vata ko ya kasa fahimtar wani abu
yana taimaka masa daidai damar da yake da ita, baya
qyale shi.25
85 Uyunu akbarur ridha (AS), littafi na 2, shafi na 814, hadisi na 7, ku duba. Uyunu akbarur ridha (AS), littafi na 2, shafi na 871, babi na 44 (babin halayen girma na Imam Ridha (AS) da yadda yake ibada)
Ciyarwar da yake yi koda yaushe
Imam Kazim (AS) na da matuqar kyauta kamar
girgije, haka ma xansa Imam Ridha (AS) ya gaje shi
wajen irin wannan yawan kyauta.
Haka wani ani malamin sunna zamanin Imam Ridha
(AS) ya faxa dangane da shi (AS) cewa: yana da matuqar
sadaqa da kyautatawa koda yaushe yana cikin infaqi
sannan kowa cikin mutane ya san shi da cewa yafi yin
infaqin voye, kuma mafiya yawan waxannan sadaqoqin
da yake bayarwa da kansa yake bi cikin dare yana baiwa
mabuqata, kuma duk wanda ya zo da maganar cewa
kamar shi ya gani cikin dare yana kyautuka, yana kore
maganar.
Safwani xan Yahaya na daga manyan masana cikin
shia, yana cewa: wata rana ina gidan Imam Ridha (AS),
sai wani cikin yaran sa ya shigo, Imam ya tambaye shi
cea: yau wani infaqi ka yi?
Ya bada akasin amsar da ya kamata ya baya, Imam
ya ce masa: yanzu ta yaya zamu iya baiwa Allah wani abu
(daga dukiyoyin mu) kenan? Ka yi infaqi, koda kuwa na
dirhami xaya ne.
Wata rana a Khurasan, sai ga labari ya bayyana
cewa, mutane na zuwa daga newa don ganin xan sa, sai ya
rubuta wasiqa da sunan xan sa Imam Jawad (AS) cewa:
ya xa na, naji ana cewa mutane na kai komo zuwa wajen
ka sannan da kaxan kaxan, wannan kuma rowar su ce,
bana son a yi amfani da kai don fakewa bayan wani aikin
alheri (akwai waxaanda zasu iya yaudara da shi), ina son
ya zama kada wani ya qara fice da shige wajen ka, ina son
ko yaushe ya zama kai ke zuwa wajen mutane, sannan
duk sanda kake son fita wajen wurin mutane, dole zinare
da azurfar su zama tare da kai, sannan duk wanda ya
kawo maka matsala yana neman xauki ka biya masa
buqatar sa, kowaye da baffofin ka ya nemi buqatar qasa
da dinare hamsin kada ka bashi komai, amman idan ya
wuce haka ka yi masa, idan daga baffofin ka mata ne
kuma kada ka bada qasa da dinare ishirin da biyar kada ka
bayar, amman idan ya haura haka ka bayar, ina son Allah
ya sanya ka a matsayin mafi kusa da shi, ka yi imfaqi, ka
baiwa talaka da mai buqatar da bashi da komai.26
85 Al-kafi littafi na 4, shafi na 48 hadisi na 5, da shafi na 44 hadisi na 9. Uyunu akbarur ridha (AS), littafi na 2, shafi na 814, hadisi na 7.
Kukan sa (AS) dangane da Imam Hussain (AS)
Tuna Imam Hussain (AS) da matuqar qaunar Turba
Hussainiyya wani abu ne sananne da aka san Imami na
takwas da shi lokacin rayuwar sa, yana matuqar
muhimmantar da duk wani abu da ya shafi Imam Hussain
(AS), duk goma ga watan muharram ya zama wani lokaci
da shia ke haduwa a yi zaman jimamin suhagan Shahidai
(AS). Imam Ridha (AS) ya ce: baba na ya kasance duk
lokacin da Muharram ya kama, baya dariya koda yaushe
fuskarsa na cikin damuwa,har sai waxannan kwanaki
goman na farko sun wuce.
Idan goma ga wata kuma ta yi, wannan ranar a
wajen sa rana ce ta juyayi da baqin ciki da kuka ce har
yana cewa: a rana irin ta yau ce Hussain (AS) a baki
tafkin Allah da aka hana shi amfana da shi, aka kashe shi.
Rayyan xan Shabib xaya cikin yaran Imam Ridha
(AS) dake Qum, ya kawo ruwayoyi daga Imam Ridha
dangane da Ashura da muharram, Imam (AS) yana ce
masa:
Ya xan Shabib! Idan zaka yi wa wani abu kuka, ka
yiwa Hussain xan ali (AS) kuka, an cire masa kansa a tare
da shi akwai mutane goma sha takwas dun an kashe su,
nagartattun da a lokacin babu kamar su a bayan qasa.
Ya xan Shabib! Idan ka yi kuka ga Hussaini (AS)
hawayen ka ya kwarara, Allah zai yafe maka zunubanka
qananan su da manyan su, kaxan xin su da masu yawansu.
Ya xan Shabib! Idan wani na son jin abunda zai
haxa shi da Allah mai girma da xaukaka sannan ya yafe
masa zunuban sa, ya ziyarci Hussani (AS).
Ya xan Shabib! Idan kana son ka gan mu ka ji daxi
tare da mu Ahlulbai cikin Al'janna maxaukakiya, ka taya
mu jimami, ka zama mai jimami, sannan ka zama mai
farin ciki da farin cikin mu, ka ratayu da wilayar mu.21
87 unuyu akhbaruru Ridha (AS) littafi na 8, shafi na 299, hadisi na 57. Amali na sheikh Saduq, shafi na 890, hadisi na 899.
Busharar sa (AS) game da bayyanar Imamuz
Zaman (AF)
dole ne sai a hankali- a hankali shi'a zasu iya
fahimtar gaiba a wancen lokacin, voyuwar wani Imam
daga cikin Imamai sannan da yadda zai bayyana , da
yadda lamarin zai zama voyayye ga mutane lokacin gaiba.
Wasu ranakun Imam (AS) ya kan yi tafiya wurare don
nunawaq mutane addini da sanar da su Imamai sabida ba
cikin sauqi Imamai ke shiryar da mutane ba, a wannan
yanayin ne Imami na takwas (AS) ke yin amfani da wasu
'yan damammaki da yake da su zuwa wurare daban-daban
sabida sanar da mutane Imamanci da Imamai wasu
lokutan ma har yana musu bisharar haihuwar Imam
Mahdi (AF) ya qara musu da bayanin siffofin sa ga wasu
daga ciikin shi'ar sa. Yana sanar da mutane abubuwa da
yawa dangane da zamanin gaiba, Da'abal Khaza'i, xaya
daga cikin mawaqan shi'a a wannan zamanin wanda
wajen Imam (AS) ya karvi walayar Ahlulbait (AS), ya tafi
Khurasan ya yabi Ahlulbait (AS). Sunan xaya daga
mawaqan [madarisi ayat] ne, ya yi baituka biyu gamre da
Imam Mahdi (AF) da baitoci 'yan kaxan masu daxi yana
cewa.
Fitowar Imam (Imam Mahdi (AF)) babu makawa
sai ta afku (ya fito).
Zai tsaya qyam da sunan Allah da yardar sa.
Ya fayyace mana tsakanin gaskiya da qarya.
Ya qara mana ni'ima kan ni'ima (ta hanyar kawar
mana da quncin rowa)21.
Bayan Imam (AS) ya ji waxannan baitoci, sai ya
kama kuka mai ttsanani, bayan wani xan lokaci ya xago
kansa sama ya ce da Da'abal: ya kai Khaza'i! Rai mai
tsarki ne ya hau kan harshen ka waxannan baitukan suka
fito. Shin kasan wannan Imam xin wane shi da kuma
zamanin da zai bayyana ya tashin?
Da'abal ya bada amsa: ban sani ba ya shugaba na, na
ji ne daga gareka kana faxar cewa wannan Imamin zai
tashi ya cika duniya da adalci ya tsarkake ta bayan ta cika
da zalunci da danniya.
Imam (AS) ya ce: ya Da'abal! Wannan Imamin za a
haife shi ta hanyar xana Muhammad, bayan sa san xan sa
Ali, bayan sa sai xan sa Hassan, shin Hassan xin shine zai
haifi wannan Imamin hujjar Allah a bayan qasa, wanda a
lokacin gaibar sa za a samu masu jiran bayyanar sa haka
nan daidai bayyanar sa zai shugabanci duniya baki xaya,
kowa sai ya rusuna masa zai shugabanci kowa, koda zai
rage saura kwana xaya duniya ta tashi Allah zai jinkirta
wannan ranar har sai ya bayyana ya cika duniya da adalci,
kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya, amman
lokacin da zai zo yaushe ne? bayar da wannan amsar
daidai yake da bada labarin lokacin tashin al-qiyama.23
81 Fassara: ba wanda ya san ldaidai lokacin bayyanar sa, sannan yana bayyana albarka zata game kowa da kowa kowanne mai haqqi zai samu daidai haqqin sa, zai sakawa mai mummunan aiki da mummunan aikin sa, haka mai kyakkyawan aiki da kyakkyawan sakamako zai saka masa. 89 (wannan abun na fassara ta sama lamba ta 81) na cikin Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 555 hadisi na 85, mai ruwaya D'abal xan Ali Khaza'i.
Alaqar sa da Gadir (idin gadir)
Ya xauki gadir a matsayin babban idi muhimmi
cikin shianci, cikin qoqarin da Imami na takwas ke yi
shine: duk ranar goma sha takwas ga zulhijja Imam na
zama tare da masu yi masa hidimar gida suna jiran sauran
shia, su kuma shi'ar su kan zo cikin farin ciki su halarci
mazaunin. Wasu lokutan ma wasu daga cikin 'yan shi'an
na gayyatar Imam zuwa wajen shan ruwa (buxa Baki).
A duk anar gadir Imam na yin bayanai masu yawa
da suka afku a wannan ranar, a qarshen zaman kuma yana
bada kyaututtuka kala-kala kamar kayan sawa, abinci,
zobba, takalma ... ga waxanda suka halarci zaman sannan
yana haxawa da mutanen gidan sa.
Imam (AS) cikin wasu jalasosi da ya yi tare da
Ahmad xan Muhammad biznaxy, ya ke labarta masa wani
makusancin sa da ya rayu a Iraqi, ya ce masa: ya xan abi
Nasr! Ranar gadir, a ko'ina kake, ku zama kusa da Sarkin
Muminai, domin Allah (SW) a wannan rana ne, Allah na
gafarta zunuban shekara xaya tare da 'yanta duk wanda ya
yi ziyarci Amirulmuminin (AS) mace ko namiji daga
wuta sannan zai samu kaso ninki biyun wanda ya halarci
daren lailatul Qadr, duk wanda ya ciyar da dirhami xaya a
wannan rana, daidai yake da ladan ciyar da dinare dubu a
sauran ranaku, dun haka ne ma a wannan rana ka
kyautatawa 'yan uwa da abokan arziqin ka, ka farantawa
maza da mata a wannan ranar.12
20 Tahzibul Ahkam, littafi na 5, shafi na 24, hadisi na 55. Misbahul mutahajjid shafi na 752.
Munafunci (abu ne marar kyau) abun hani
Bayan kammala aikin hajji da wasu 'yan Shia suka
yi, sai suka yanke shawarar zuwa Makka, a wannan
lokacin kuma Imam ya shagaltu da mutane da ke zuwa
wajen sa masu yawa kuma a'kai-a'kai, cikin waxannan
ranakun ne sai waxannan masu ziyarar da suka gama
aikin hajji suka qaraso wajen Imam (AS) a mazaunin sa,
sannan a qarshen wannan tattaunawar, bayan gama
tattaunawar sa kenan, sai waxannan mutanen suka nemi
sanar da Imam kan su da nuna masa cewa su masoyan sa
ne na haqiqa, sai ya dakatar da su.
Wani mutum daga Khurasan a matsayin shugaban
matafiyan da suka zo daga Khurasan ya nemi mutane da
su baiwa Imam Kumusi, Imam bai ji daxin wannan
munafuncin nasa ba cikin vacin rai ya ce: wannan meye
haka? Kuna tsarkake mu tsarkake a harsunan ku amman
kuma – wannan gaskiyar da Allah ya sanya mana ita –
kuna tauye mana ita, ku sani ba zamu baku dama ba, ba
zamu baku dama ba, ba xayan ku da zamu yafewa.12
28 Al'kafi, littafi na 8, shafi na541, hadisi na 25.
Ilimin ubangiji
A qarni na biyu shekarun musulunci qamara ana
ganin Madina a matsayin xaya daga cikin jiga-jigan
garuruwan musulunci, a lokacin samartakar Imam Ridha
(AS) sbayan mahaifin sa ya amsa kiran ubangiji, ya
shagltu da koyarwa, xalibai daga vangarorin duniya sun
zama xaliban sa, daga China ne Khurman ne da sauran
nisan duniya sun sha ilimi sosai.
Malik xan Anas (wanda ya bar duniya a shekara ta
213HQ), shugaban xayan mazhabobin sunna, ya halicci
makarantar Imam (AS) shi da sauran wasu manya-manya
cikin sunna, a wannan lokacin kuma Imam Ridha (AS)
yana cikin shekarun samartaka wanda a lokacin bai cika
shekaru talatin ba yake irin waxannan gagaruman ayyuka
na qyanqyashe xaliban ilimi. Wannan babban qoqari mai
qimar gaske da Imam (AS) ya bayar wa malamai da
makarantun sunnan ya bada mamakin gaske ta vangarori
da dama. Zahabi babba cikin jigogin Malaman sunna ne,
dangane da wannan akarantarwar da Imam (AS) ya yi, ya
rubuta cewa: Shi (Ali xan Musa) ya kasance na farko
wajen bada gudunmowa, har ma ga Malik xan Anas ya
bayar da fatawa, yana shekarun samarta.
Sunan sa ya shahara a Madina cikin masallacin
Manzo (SAW) wajen koyar da karatu malamai.
Muhammad xan Amru Waqdi ya bayyana (wanda
ya bar duniya a shekara ta 121HQ), shima na xaya cikin
malaman ahlus sunna yana cewa ba wanda zai iya bada
wannan gudunmaowa ta ban mamaki a irin waxannan
shekaru na samartaka shima ya rubuta cewa: Shi (Ali xan
Musa) ya bada fatawa a shekaru ashirin da wani abu cikin
masallacin Manzo (SAW) a Madina!
Sannanen abu ne cewa ya bayar da wannan
karatuttuka ne bayan wasu 'yan shekaru da wafatin baban
sa Imam Musaal Kazim (AS) (bayan shekara ta 219HQ)
kenan.11
22 Al-muntazam, littafi na 80, Shafi na 889, hadisi lamba ta 8884. Siyar a'alamun nubala'a, littafi na 9, shafi na 811, lamba ta 825.
Sanin yarurruka
Imam Ridha (AS) ya san dukkanin yarukan zamanin
da yake ciki, Aba Sulat Haruwi, ya zauna tare da Imam
(AS) a Khurasan, yana cewa: duk inda Imam (AS) ya
haxu da mutum zia magana da shi, yana masa magana ne
da yaren sa (Imam naiwa kowa magana da yaren da ya fi
iyawa), ina rantuwa da Allah, mafi fasaha kuma mafi
daxin zance ne cikin kowanne yare idan yana yi, wata
rana ta tambaye shi: ina mamakin yadda nake ganin idan
yana magana da kowannen yare yadda yake sarrafa
kalmomi da salon magana, ya akayi ya iya wannan?
Imamn (AS) ya ce: Aba Sulat!! Ni hujjar Allah ne a bayan
qasa, Allah baya hana hujjarsa sanin dukkan abinda ke
tattare da bayin sa, shin baka ji Shugaban muminai Ali
(AS) na cewa ba: mu ne aka baiwa (babin zance = faslal
khixab) shin faslal khixab shine sanin dukkanin yaren da
ke bayan qasa.
Nawa ne cikin xaliban Imam (AS) da suke daga
Roma da Saqalabi (wuri ne tsakanin Bulgeria da
Istambul) waxanda da yaren su Imam ke magana da su:
Imam (AS) da yaren Farisanci da Sindi ma duk ya yi
huxubobi.
Bayan yarukan mutane ma Imam ya san yarurruka
daban-daban na waxanda ba mutane ba, har zancen
dabbobi ma yana ganewa, Sulaiman Alawi sau da yawa
ya faxi faxar cewa: Muna zaune a gefen lambu, sai ga
wani gyado (tsunstu qarami yello mai kamar benu) ya zo
kusa da Imam Ridha (AS) ya zauna Daura da shi, yana ta
in kalar kukan sa yana cewa, cik cik cik.
Sai Imam (AS) ya kallo ne ya ce min: ka san abinda
wanna gyadon yake cewa? Na ce: Ya san Allah da
Manzon sa da iyalan Manzon sa.
Imam ya ce: cewa yake [ga wani maciji can a gida
na zai cinye min 'ya'ya na]. Xauki wannan itacen ka bishi
zuwa gidan nasa ka kashe macijin.
Na xauki itace na shiga wajen na ga maciji ya shiga
gidan tsuntsun, na kashe shi.19
28 Uyun ahbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 227 da na 221, hadisi na 8,2 da na 8. Basairud darajat, shafi na 845, hadisi na 89.
Zantuttukan da ya bayar na ilimi a matsayin hadisai
Ta wajen hadisan Imam Ridha (AS), shia sun
amfana da ilmomin daban-daban masu yawa. Ba mamaki
nawawi ma ya rawaici wannan ruwayar da take cewa:
[duk wanda ya kiyaye hadisai 42 yake amfanar al'umma
ta da su, Allah zai tashe shi ranar qiyama matsayin
malami]
Wannan ne ma ya haifar da hadisan da nawawi ya yi
guda 42.
Idan muka lura da ajujuwan koyar da hadisai na
ahlus sunna da gungun mutanen da suka karkatar da
maganganunsa a wannan lokacin, Imam Ridha (AS) yana
gargaxin shia da cewar in har zasu xauki ko karvi hadisi
su kula sosai sabida kada su xauki ko su samu cakuxa
shubuha da gaskiya cikin addini kamar yadda ake samu
kuma aka samu cikin ahlus sunna, domin juyawan wauta
ce da son rai, don haka ne Imam (AS2 ke tsanantawa
xalibansa kula wajen xaukar hadisai. Aba Salt Harawi
yana cewa: duk wanda ke kula da lamurranmu mu
Ahlulbait Allah ya yi masa rahama ya kula da shi.
Aba Salt ya kasance mai son kare rayuwa da
lamurran Imam da wilaya, yana yawan jin wannan daga
Imam (Imam na bayyana shi da) cewa: ya san ilimomin
mu, kuma yana sanar da mutane su, da mutane za su san
kyawawan maganganun mu, da sun bi mu.
Wannan maganar na kallafawa shia koyon hadisan
Imamai (AS), har ma Aba Salt na cewa: wannan shine
haqiqanin abunda ya cancanci mu yiwa Annabin Allah.
Sannan Kuma Imam (AS) na yin wani abu, shine
cewar wasu lokutan sau da yawa yana kawo hadisi daga
kakannin sa (AS) tare da son shia da masu ruwayar 'yan
shia sun ji, da yawansu kuma sun zama malamai masu
naqalto hadisai, wannan ne ma ya sa, ya kan shirya
majalisi ga Aba salt da sauran yaransa hadisan Manzo
(SAW), wasu malamai wasu kuma yaran sa, yana ce
musu idan hadisi ya danganci fiqihu, basira ko neman
qarin bayanin ilimi ku nemi sanin ma'anar sa, amman idan
baku samu ba ku rawaito shi yadda yake, da ace kada ku
raywaito shi gara koda dubun hadisan da baku san
ma'anar su ba ku kawo.14
24 Ma'anil akhbar 210. Uyun ahbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 87. Akhabri Isfahan, littafi na 2, shafi na 881.
Zaman bayar da hadisi
Imam Ridha (AS) ya yi zama-zama kala-kala a
wurare daban-daban, kamar: Nazir, Madina, Makka, Kufa
da Khurasan. Wasu lokutan cikin waxannan zama-zaman
yana karantar da hasidan da suka zo daga Kakannin sa
(AS) ne da na Manzo (SAW) wasu lokutan kuma yana
karantar da abubuwan da suka kevanci al'amuran
musulmi. Maudu'in wasu zama-zaman da yake fiqihu ne,
wani lokacin tafsiri wani lokacin wa'azantarwa ta gaba
xaya, na tsamar da mutane daga jirkicewar da aka yi cikin
karantarwar addini, tare da bayyana haqiqanin koyarwar
shi'anci, masu rubututtuka kan abubuwa da yawa na
wannan zamanin suna zuwa inda Imam (AS) ya ke don
rubuta bayanan ilimi cikin shauqi.
Muhammad xan Isa, xaya daga cikin yaran Imami
na takwas (AS). Ya rubuta rubututtuka da yawa cikin
waxanna zama-zaman da Imam (AS) ke gudanarwa, yana
bada labari yana mai cewa: ni da Yunus xan
Abdurrahman mai yi wa Imam (AS) hidima mun isa
wajen Imam, ya yin da muka isa kusa da qofar sa (AS)
mun tarar da gungun mutane sun haxu suna neman izinin
shiga wajen Imam (AS).
Lokacin da suke neman wannan izinin da kafin
zuwan su da bayan sa wasu mutane na shige da fice,
lokacin da muka yi sallama Imam (AS2 ya bamu damar
zama, sai Yunus xan Abdurrahman ya ce: ya shugaba na!
Ka bani izini na tambayi wani abu?
Sannan Yunus ya fara yin tambayoyi masu yawa.
Wasu lokutan Imam (AS) na buqatar shia su dinga
zuwa gidan sa ko su haxu a wani waje don su saurari
huxubobin sa.
Haxuwar mutane da yawa wajen Imam (AS) a
Madina cikin jalasosin sa na Madina sun yi rubutu sosai, a
Khurasan kuma ba raguwa suka yi ba sun nunnunka
yawan na Madinan ne. lokaci xaya mutane masu wucewa
wasu na cewa adadin waxannan mutanen ya kai 262
mutane shia daga garurawa daban-daban suka halarta.
Wasu lokutan kuma wasu daga xalibai ne ke
koyarwa tare da kawo maganar Imam (AS), su tattaro
bayanan sa ko hadisan Manzo (SAW) da ya kawo su
sanya shi cikin litattafai. Don buga misali bari mu kawo
muku abinda Ahmad xan Amir Xa'i a shekara ta 234 HS a
Madina, ya kaho hadisan Manzo (SAW) masu yawan
gaske cikin zama xaya, bayan wannan zaman ne sai ya
sanyawa waxannan hadisan suna [sahifatur Ridha (AS)]
ya yaxa ta wace har yanzu cikin nasara littafin na nan.15
25 Al'kafi, littafi na 4, shafi na 28. Tahzibul ahkam, littafi na 5, shafi na 24, hadisi na 9.Qurbul asnad, shafi na 200. Ihtijaj, littafi na 2, shafi na 480, Al-mujtani'i, shafi na 22.
Kyawawan hadisai (silsilar zahab)
A wannan zamanin ana lissafa Nishabur cikin
manya-manyan buranen da masana hadisan ahlus sunna
shahararru suka yi dandazo, akwai masana da masu
hadisai sosai, kamar irin su Is'haq xan Rahwiya, malamin
Buhari (marubucin mafi muhimmancin littafin hadisi mafi
girma wajen ahlus sunna), shima a wannan zamanin yana
nan.
Mafiya yawan mutanen wannan garin ahlus sunna
ne a wancen lokacin, amman a tare da su da gefunan su
akwai shia da ke rayuwa tare da su.
Cikin tafiyoyin masu nisa da Imam (AS) ya yi, ya
xauki lokaci mai tsayin gaske cikin Nishabur, sannan ya
yi jalasosi masu yawa sabida yanayin da ya samu kansa
cikin Nisabur xin, mafi muhimmanci zaman karatu da
Imam (AS) ya yi shine na neman manyan masanan cikin
ahlus sunna su halarta (ya shirya musu).
Wani cikin waxanda suka halarci wannan zaman ya
yi rubutu kan hakan yana cewa:
Lokacin da Imam Ridha (AS) ya shiga Nishabur ya
karvi wani waje da zai zauna wanda aka gina da takardu
masu zinare da Nuqre.
A wannan lokacin ne mutane a yawa cikin manyan
mahaddata hadisi da masana suna nemi Imam (AS) tare
da haxa shi da Allah a wuri mafi yawan mutane (tsakkiyar
kasuwa) suka roqe shi cewa: don girman iyayen ka masu
tsarki, don girman fuskarka mai albarka ka gaya mana
hadisan da iyayen ka suka bar maka, ka naqalto mana!
A wannan lokacin ne Imam (AS) ya tsayar da
tawagar sa ya basu hadisai tare da haxuwa da sauran
musulmai ya amfanar da su daga kalmomin bakin sa mai
albarka, mutane na tashi tsaye daga wuraren zaman su,
suna miqewa tsaye don girmama shi.
A lokacin wannan huxuba ne, gungun wasu mjtane
suna kuka shave-shave sabida farin cikin da ya lulluve
su... wasu kuma sun shagala da rubuta zantukan sa masu
al'barka, wasu kuma sun xaga kawunan su gaban sa suna
kuka.
Har zuwa kusa azzahar sabida yawan mutane wajen
taro ya kasa samun shiru, mutane kawai kuka suke sabida
soyayya ga xan annabin su, sai daidai wannan lokacin
qarar kuka ta tsaya.
Sai a wannan lokacin ana samu shiru a ko'ina,
malamai da mafifita na shela cewa: ya mutane! Ku
saurara ku ji, kada ku cutar da xan Manzo.
A wannan wajen akwai kimanin mutane dubu
ashirin da huxu riqe da alkalumma a hannun su, suna jiran
Imam (AS) ya fara magana su dinga rubutawa.
A wannan wajen Imam Ridha (AS) ke cewa: Naji
daga babana Musa xan Ja'afar, shima ya ji daga baba na
Ja'afar xan Muhammad, shima ya ji daga baba na Hussain
xan Ali shima ya ji daga baba na Ali shugaban muminai,
shima ya ji daga xan'uwa sa xan ammin sa Muhammad
manzon Allah (SAW) yana cewa: naji daga Jibril na
cewa: ya ji daga Allah mai girma da xaukaka na cewa:
Kalmar [la'ilaha ilallah]- na nufin imani da qudurcewa
da kaxaita Allah- ta kevanta da ni kaxai, duk wanda ya
shiga cikin wannan kalma, azba ta zata sauqaqa gareshi.
Xaya cikin masana na faxar haka yana cewa:
wannan hadisi da irin wannan sanadin aka karantawa
wani sarki, ya bada umarnin a rubuta wannan hadisi da
zinare, sannan ya yi wasiyya da cewa: idan ya mutu a
binne shi da ita matsayin likkafani da shi a binne shi da
shi. Haka ma wani cikin malamai ya faxa cewa: koda
marar hankali aka karantawa ruwaya irin wannan mai irin
wannan salon zance mai kyau ya karanta ta, ya samu
hankali ba abun mamaki bane. Duba sanadi irin na
wannan ruwaya mai tsarkin sanadi daga Imam (AS).16
25 Biharul anwar littafi na 49, shafi na 825, hadisi na 8 wanda aka ciro daga kashful gumma daga tarihin Nishabur.
Tattaunawar sa (munazarori ko ku ce Debate xin sa)
Bayan shekaru xari biyu bayan aiko Manzo (SAW)
sun wuce, a wannan tsayin lokaci duniyar musulmai ta
cika da sanin abubuwa masu yawa waxanda suka savawa
musulunci, shinge na tsakanin qasashe da ta wani
vangaren da kuma zuwan wasu mutane malamai daga
wani waje zuwa wani na daga 'yan kasuwa masu addini
da mazhabobi daban-daban na cikin garuruwan
musulunci, ta yadda shbuhohi daban-daban zuwa
koyarwar musulunci, a gefe guda kuma ga koyarwar
Ahlulbait (AS) ta vangaren wilayar Imam Ridha (AS) na
qalubalantar su, cikin kowanne zamani da lokaci ana
samun sababbin shubuhohi masu matuqar qarfin gaske.
Ga vangaren masu fassara na halifofin abbasiyawa da 'yan
bambaxen su da suke rubututtuka da yarurrukan da ba
larabci ba da kuma fassara larabci zuwa wani yare da
akasin haka, wannan lamurran ya sanya shubuhohi na
yawo ko ina tsakanin malaman shia da waxanda ba su ba,
don haka ne kan mas'alolin da suka shafi addini.
Da yawan waxannan bahasosi da Imam (AS) ya yi
suna zuwa mana a matsayin muqabaloli (munazarori)
tsakanin Imam (AS) d amalamai masana da na wasu
mazhabobo da malaman addinai daban-daban, mafiya
yawan maunazarorin Imam (AS) yana yin su ne kan
mas'alolin tauhidi sannan imamanci. cikin jalasosin
munazarar Imam (AS), akwai wasu jalasosi biyu waxanda
ska fi sauran shahara da aka yi musu suna da nuskhat,
wanda ya yi bahasi mai tsayi da Ma'amun dangane da
Manzo (SAW) da ismar sa. Jalasar nan ta fara da kalmomi
kamar haka: Ya xan Manzon Allah! shin kana da ra'ayin
cewa dukkan annabawan Allah ma'asumai ne? lokacin da
Imam ya bashi amsar cewa haka ne, sai ya qara tamnayar
Imam (AS) cewa: tunda haka ne, meye ma'anar wannan
ayar mai girma: [Adam ya savawa ubangijin sa wannan
ne ya sa shi wahala].11
Inda wannan zaman ya qayata shine inda gaba
xayan tambayoyin sa Imam (AS) da qur'anin ya dinga
amsa masa su (yana bashi amsa). Wannan munazarar da
ta gudana tsakanin mutane biyu kuma mai tsayi a qarshen
ta sai da Ma'amun ya kasa voye mamakin sa kan irin
yadda Imam ke amsa masa tambayoyin sa cikin sauqi, a
nan ne ma yake cewa: Ya Baba Hassan! Na rantse da
Allah ingantaccen ilimi na wajen Iyalan gidan Manzo
(SAW), babu wanda ya isa ya samu wannan ilimin
matuqar ba daga wannan gida ya fito ba, Allah ya saka
maka da mafificin ladan sa, har ma a wannan zaman
Ma'amun na gayawa Imam (AS) cewa: [na shaida kai xan
Manzon Allah (SAW) ne na haqiqa].
Jalasa ta biyun itace jalasar Imam (AS) da ya yi
munazara da manyan masana na addinai daban-daban a
fadar Ma'amun a gaban sa, wannan zaman ya yi matuqar
tsayin gaske sosai wanda ya haxa 'yan addinai daban-
daban daga vanagarorin Nasara (jasliq), yahudawa (ra'asi
jalut), sabiyawa (masu bautar tauraro), Zartush, Rumawa
da masu kalam na Buda. Imam (AS) na musu hukunci ne
da litattafan su na Attaura da Injila sannan ya nuna musu
abubuwa da yawa ya yi musu bahasi a nan take ya basu
amsa gamsasshiya.11
27 Suratu Xaha, aya ta 828. 21 Attauhid shaf na 448-487, uyunu akhbarur Ridha (AS), littafi na 8, shafi na 854, da littafi na 2 shafi na 200.
Hadisan Imam Ridha (AS)
A zamanin Imamancin Imam Ridha (AS) ta
vangarori da dama cikin musulmai sun karvi hadisan
Manzo (SAW), haka nan ma shia sun rawaici ruwayoyin
Manzo (SAW) tare da rubuta su sannan sun xauki hakan
da matuqar muhimmanci a zamanin Imam (AS). A
wannan lokacin ne shia suka samu damar rubuta litattafan
hadisai da yawan gaske. Imam (AS) ya yi amfani da
wannan damar da ya samu cikin rayuwar sa sosan gaske
inda ya yaxa hadisai masu yawa cikin musulmai, wasu
lokutan Imam (AS) ta hanyar zantuttukan sa yake isar da
saqonni wani lokacin kuma da sunan amsar tambaya sai
ya rubuta xan littafi mai kamar wasiqa, ya aikawa shiar sa
wani lokacin kuma yana musu rubutu don karar da su
ilimi. Ya kasance mai baiwa shia ilimi ta hanyar huxubobi
masu ban mamaki dangane da Iyalan gidan Manzo
(SAW) ko zantuttukan addini masu rikitarwa da sauqaqa
don tabbatar da su kan gaskiya da haskaka musu gaskiya
da nuna musu vata, Imam (AS) ya kasance yana cewa:
[duk masu wuce gona da iri kan matsayin mu cikin
qagaggun abubuwa, to wannan yana qasqantar da girman
Allah (SW) ne ta hanyar wuce gona da iri]. Don haka
duka wata ruwayar da ba'a fahimce ta ba ku maidawa mai
ita kayar sa.
Buqatuwar mutane da 'yan shia baki xaya
musamman samun rikicewa da samun qagaggun
ruwayoyi ya sanya Imam Ridha (AS) ya nemi sabunta
bayanai kan tauhidi da mas'alolin Imamanci, har yana
cewa: zuwan Imam cikin hukuma zai taimaka wajen yaxa
ingantattun ruwayoyi da suka shafi addini sannan zai yi
tasirin gaske sosai, kusan rabin ruwayoyin da suka rage
dukkan su daga Imami na takwas (AS) ne daga
maudu'o'in da suka ilimin kalam da aqida.
Cikin nasarar da aka samu an samu kimanin
ruwayoyi 1522 daga Imam Ridha (AS) cikin abubuwan
da suka wanzu a hannun mutane zuwa yau waxanda suka
haxa da tafsiri, fiqihi, aqida da halaye.13
29 Ihtijaj, littafi na 2, shafi na 484. Musnadi Imam Ridha (AS) asari Azizullahi Axardy wanda ya tara ruwayoyi daga Imam Ridha (AS).
Yaran da yake da su masana
Wani qoqari da Imam Ridha (AS) ya yi bayan
waxancen qoqari kala kalan da ya yi shine samar da
manyan masana malamai qwararru. Mafiya yawan yaran
da ya qyanqyashe manyan masana fiqihu ne da hadisai,
cikin manyan litattafai, ya samar da manyan masana sama
da xari uku.
Sannan kuma xaliban na Imam (AS) na da matuqar
kaifin basira ta yadda dukkan abunda suka fahimta ya
zauna kenan, sun rawaito addu'o'i da yawa daga Imam
(AS), sannan da yawansu su kan zauna tare da Imam a
wuraren tafiye-tafiye majalisosi da huxubobi kai har ma a
ibadun su da suka haxa da xawafi a filin hajji, da yadda
ake aikin hajji, yaya ake salla, haka nan ma salon yadda
ake ziyara a Najaf mai tsarki duk sun kawo mana
ruwayoyi.
Wasu daga cikin masu ruwayoyi daga Imam wato
yaran sa sun haxa da:
Ahmad xan Muhammad xan abi Nasr Buznaxi,
Muhammad xan sinan, Fadl xan Shazan, Muhammad xan
Isma'ila xan Bazi'i, Hassan xan Ali washa'a, Hassan xan
Ali xan Fadhal Taimi, Safwan xan Yahya, Yunusa xa
Abdurrahman, Sulaiman xan Ja'afar xan Ibrahim Ja'afari,
Ahmad xan Amiru xa'i, Muhammad xan Fudhail Sirfi da
Mu'umar xan Khalad.
Mafi muhimmancin siffa da waxannan masu rawaito
hadisi daga shia a zamanin Imam (AS) shine suna iya
tattara hadisai su mai da su matsayin littafi, ana cewa
cikin lokaci qanqani Imam Ridha (AS) ya samar da masu
rauwaya birjik a wurare irin su Khurasan, da wasu jama'a
daga Shia waxanda suka zamo masu matuqar buqatar da
ruwaya daga Iraq da Hijaz har zuwa Khurasan waxanda
ake jin hadisai daga wajen su. Don buga misali zamu iya
kawo muku wasu daga cikin su kamar haka: Hassan xan
Jahm xan Bukair xan A'in, Hassan xan Ali washa, Khalf
xan Hammad Asadi, Rayyan xan Salt Ash'ari Qummi,
Da'abal xan Khaza'i, Mu'umar xa Khallad, Muhammad
xan Sinan da ...92
80 Al kafi littafi na 8, shafi na 820, da littafi na 4, shafi na 529, kamiluz ziyarat, Hadisi na 48. Uyunu Akhbarur ridha (AS), littafi na 2, shafi na 81-85 da shafi na 818 hadisi na 5, Rijalul Barqi, shafi na 827 zuwa na 880. Rijalux Xusi, shafi na 858-810.
Bazanxi, Abun qaunar Imam (AS)
Ba mai ja kan cewa Abu Ja'afar Ahmad xan
Muhammad abi Nasr, wanda aka fi sani da Bazanxi na
daga cikin mafi girma da inganci cikin gbaki xayan yaran
Imam (AS), wanda har zuwa shekara ta 112AH yana nan
da ran sa, abun alfaharin Imamai Ma'asumai uku a
rayuwar sa, wato Imam Kazim, Imam Ridha xa Imam
Jawad (AS) wasu lokutan yana rawaito ruwayar Imam
(AS) da suna [sahibur Ridha].
Ya rawaici ruwayoyi masu yawan gaske daga
Imami na takwas waxanda ya rubuta su, shi mutum ne
mai yawan sani sannan malamin hadisi ne kuma
mawallafi ne kan abubuwan da suke magana kan
Ahlulbait (AS).
Shi wannan bawan Allah ya rayu ne kusa da Kufa
wani yanki da ake kira da Qadisiyyeh. A lokacin mafiya
yawan masu rayuwa a kufa Iraniyawa ne, Barnaxi ba
Iraniye ne. Imam (AS) [akwai yiuywar lokacin da yake
kan hanyarsa zuwa Khurasan ne) ya zauna a Qadisiyyeh
na wani xan lokaci, a wannan lokacin Barnaxi ya yi waje
don rubutu, hakan ne ya san Imam (AS) ke yi masa
kyaututtuka don rubuta zancen Allah.
Mafi muhimmancin aikin da wannan bawan Allah
ya tsaya qyam a kai shine shiga gaban duk wani kuskuren
da aka zo da shi addini don juya karantarwar Imamanci.
Shi kansa a farkon Imamancin Imami na takwas ya xan yi
kokwanto, amman lokacin da ya tabbatar da gaskiyar
hakan, sai ya miqa wuya tare da sallamawa dukkanin ta.
Ahmad xan Muhammad Barnaxi yana cewa ya je
Madina wata rana, farkon dare sai wani yaron Imam ya zo
mazaunin su yana cewa: Imam na son ganin ku.
Barnaxi ya yi matuqar alfahari da murna ganin cewa
zai baqunci Imam cikin wannan daren, a qarshe-qarshen
daren Imam (AS) ya ce: ina tunanin yanzu baza ka iya
dawowa Madina ba, yau ka zauna tare da mu, da asuba da
yardar Allah mai girma da xaukaka sai ka kama hanyar ka
ta komawa. A nan take Imam (AS) ya kiran bawan sa ya
ce mata: sanyawa wannan baqon gadon da nake kwanciya
ya kwanta, ni zan kwanta a qasan nan wajen, sannan ka sa
masa filo na da abin jingina ta.
Barnaxi ya kalli irin wannan kyautatawa da Imam
ya yi masa yake labarta cewa:
A ran sa yake gaya kansa cewa: wannan mutumi
mai matuqar xaukaka ne ke sanya ni a muhallin sa?!
Allah na tare da wannan mutumi da duk matsayin da yake
da shi yake haka, ban tava yiwa wani irin wannan
kyauatar ba, Imam ya bani shimfixar sa na yi amfani da
ita, bargon sa da matashin sa duk ya bani na amfana cikin
wannan dare, ba xaya cikin yaran sa da ya taba yi min
wannan.
Na zauna ina ta saqe-saqe a raina yana gefe na sai
ya fuskance ni ya ce:
Ya Ahmad! Shugaban muminai Ali (AS) ya baqunci
Sa'asa'a ya ce masa wannan saukar da na yi maka sabida
ina alfahari da kai na yi maka, ba alfaharin ka bane nawa
ne, ka barni na girmama ka Allah ma ya girmama ka.92
88 Uyunu akhbarur Ridha (AS) (fassara) littafi na 2, shafi na 584 hadisi na 89. Wasailush Shia, littafi na 2, shafi na 888.
Yunus xan Abdurrahman, Malami masani
Sau uku yana cewa: Zan nunnuka maka Al'janna,
babu wani da Imam ya gayawa irin wannan maganar sai
shi. Irin wannan ne ya sa hatta cikin 'yan shia wasu na
qiyayya da shi. Imam Ridha (AS) ya yio matuqar nutsuwa
da Yunus xan Abdurrahman. Yunus ya rubuta llitattafai
masu yawan gaske [littsfin syyukan rana da dare] xaya ne
cikin litattafan sa wanda ya tattaro addu'o'i da ayyuka
masu yawa. Kusan kowanne gidan 'yan shia akwai
wannan littafin. Imam Hassan Askari (AS) – shekaru
kaxan bayan wafatin Yunus – ya yi wa wannan littafin
duba tun daga farkon sa har zuwa qarshen sa ya ga yadda
littafin ya qunshi ilimummuka ya yiwa Yunus addu'a
matuqar gaske ya ce: Ya Ubangiji a madadin kowanne
xaixaikun haruffan wannan littafi ranar lahira ka sanyawa
Yunusa haske da yardar ka.
Shi ba kawai ta vangaren ilimi ya yiwa addini aiki
ba, har ma ta ayyukan zahiri ya yi matuqar qoqari, wanda
mutumin Iraqi ne, sau 54 cikin shekaru 54 yana zuwa
hajji da Umara. Imam Ridha (AS) ma daga Khrasan ya
tava aika masa kyauta ya bashi umarni cewa, ka yi hajji
xaya da niyyar Imam (ka yi min aikin hajji nima), ya
kasance mai matuqar biyayya ga wilayar Ahlulbait (AS).
Yana matuqar takawa gullatun shia burki haka nan ba
yana shan gaban masu jirkita koyarwar addini, haka nan
yana tsayawa gaban maqiya Imam Ridha (AS). Ya tava
inkarin wilayar Imami na takwas amman da ya haxu da
gaskiya ya gaen ta sai ya zama ya yi dace da taqawa da
cikakkiyar biyayyar Allah sai ya zama xaya daga cikin
manya-manyan yaran Imam Ridha (AS) sannan ya zama
xaya tal mafi ilimi da ganewa na yaran Imam (AS), a
wannan zamanin ya yi suna da Salmanul Farisi.
Ja'afar xan Isa shima na cikin yaran Imam (AS),
yana cewa: mun kasance tare da Yunus a gidan Imam, sai
aka bada labarin cewa ga wasu gungun shia daga Basra
suna son a basu izini zasu ga Imam (AS). Imam (AS) ya
ce da Yunus, ka zauna a bayan labule cikin xakin nan
kada ka fito har sai na neme ka.
Mutanen Basra suka qaraso, suka faxi maganganu
marasa daxi dangane da Yusun, Imam ya sunkiyar da
kansa qasa baice komai ba, suka faxi dukkan abunda suke
son faxa na vatanci ga Yunus suka tafi, a sannan sai Imam
(AS) ya yiwa Yunus magana: fito daga xakin, sai ga
hawaye ya jiqe fuskar Yunus jagaf, yana kuka ya ce da
Imam: ya shugaba na, ina matuqar kare wannan mazhabi
iyakar qarfi na, amman shiar ku na min irin wannan halin.
Imam Ridha (AS) ya ce: ya Yunus! Idan Imam ya
yarda da kai, kada zuciyarka ta karaya kan irin waxannan
zantuttukan, ya Yunus! Kada ka danganta kyawun aikin
ka da sai mutane sun fahimce ka sam kada ka dinga
lissafa su.
Yunus xan Abdurrahman a rayuwar sa ya zaman
Xalibin Imam Kazim (AS) da Imam Ridha (AS) sannan
ya yaxa koyarwar Ahlulbait (AS), sannan ya bar duniya a
shekara ta 121AH.91
82 Rijalul Kasshy, shafi na 414, Rijalun Najashi shafi na 447, lamba ta 8201, Tahzibul Ahkam, littafi na 1, shafi na 40, hadisi na 828.
Aba salt, yaron qarshe daga cikin yaran Imam (AS)
Abdusslam xan Salih, wanada aka fi sani da Aba
Salt Haruwi, ya shahara a matsayin yaron Imam (AS),
asalin sa mutumin Iran ne, amman an haife shi a Madina.
Abun lura cikin rayuwar wannan bawan Allah shine cewa
ana lissafa shi cikin gagga-gaggan malamai, Imam (AS)
na shiga Khurasan sai Allah ya yi masa luxufi (Aba Salt)
da karvar shianci.
Ya zauna tare da Imami na takwas a Khurasan,
mutane da yawa masu daraja da wasun su suna zama tare
da shi, sabida haka ne ma ya sanya shi karatun hadisi mai
yawa a hauzozin Ahlussunna, haka ma ya yi karatu wajen
Imam Ridha (AS) tun kafin ma ya zama Shia, inda daga
nan ne wajen Imam (AS) din ya fahimci shianci ya ga
gaskiya, kafin ya zama shia ya rubuta ruwayoyi masu
yawa kan wilayar Ahlulbait (AS), Ma'amun ma na
matuqar girmama shi, ba mamaki sabida wannan ne ma
ya sa shi kaxai ya baiwa dama ya zo tare da shi a qarshen
rayuwar Imam sanda ya bashi guba, da shi ya fara haxuwa
bayan ya fito daga wajen Ma'amun.
Aba Salt Haruwi ya rubuta abubuwa masu yawa
dangane da tarihin Imam Ridha (AS) har ma yana cewa:
Wata rana muna zaune a majlisin Ma'amun, Imam
na magana dangane da wata ruwaya daga Manzo (SAW)
da ta zo tana mai cewa: [ya Ali xan Abi xalib, kaine mai
raba wuta da al'janna ranar al'qiyama]. Ma'amun bai gane
zurfin wannan ruwayar ba, sai ya fuskanto Imam (AS) ya
na cewa: menene dalilin da ya sanya Ali (AS) ya zama
mai raba wuta da al'janna ranar al'qiyama?
Imam Ridha (AS) ya ce: ya Ma'amun! Shin baka ji
wannan ruwayar daga baffan ka Abdullahi xan Abbas ya
rawaito daga Manzo (SAW) ba yana cewa : [son Ali
imani ne, qin sa kuma kafirci ne ba?] ba?
Ma;amun ya ce: haka ne wannan ruwayar na ji ta
daga kaka na.
Imam ya ce: don haka al'janna ta muminai ce wuta
kuma ta kafirai ce, wannan ne ya bada natija kan cewa Ali
(AS) na raba wuta da Al'janna, wanda ya cika da son sa
zai shiga al'janna wanda kuma ya cika da qin sa zai shiga
wuta, wannan ya tabbatar maka da hujja.
Mamaki ya kama Ma'amun ya ce: Kada Allah ya
nuna min rayuwa ba tare da kai ba, yadda kake magajin
kakan ka Manzo (SAW), kakan ka Annabin Allah.
Bayan gama wannan zaman sai Imam (AS) ya koma
gida, lokacin da ya isa gida, sai ya zo wajen sa: ya ce
masa: baba ta da baba na fansa ne gare ka ya xan Manzon
Allah! dubi irin yadda ka amsa min wannan tambayar
tawa cikin sauqi sannan a bayyane!
Imam ya ce: ya Aba Salt! Waccen amsar da na
bayan Allah ne ya yi min ilhamar ta, da gaske ne na ji
wannan ruwayar daga iyaye na da Kakanni na cewa
Manzo (SAW) ya cewa Shugaban Muminai Ali (AS)
cewa: [ya Ali, kaine mai raba wuta da al'janna ranar
al'qiyama, wuta zata dinga cewa wannan nawa ne wannan
naka ne].99
Aba Salt ya kasance tare da Imam (AS) har zuwa
lokacin shahadar sa. Shine ya fi kowa kawo cikakke kuma
tabbataccen bayanin yadda Imam (AS) ya yi shahada, ya
88 Uyunu akhbarur Ridha (AS) shafi na 15, Hadisi na 80.
yi rubutu kan wafatin Imam, bayan maganar wafatin
Imam ya kawo wasu abubuwan da suka shafi Imam (AS)
a wani littafin daban.94
84 Rijalun Najashi, shafi na 245 da A'alamul wardi, littafi na 2, shafi na 78.
Ciratuwar Imamanci
Hisham xan hakam da Aliyyu xan Yaqxin,
waxannan biyun na daga mafi girman yaran Imam Kazim
(AS). Wasu yaran na Imam (AS) suna cikin manya-
manyan masana masu tsoron Allah muminai. Wata rana a
zamanin Imam Kazim (AS) Hisham da Aliyyu bin
Yaqxin suna zaune tsakanin shia a Bagdad, sai Aliyyu
xan Yaqxin ya buxe baki yana cewa: ina kusa da bawan
Allah (imami na bakwai) a zaune sai ga xan sa Ridha ya
shigo, sai Imam ya ce da ni: ya Ali xan Yaqxin! Wannan
shine Ali, shugaban 'ya'ya na ne. ina masa al'kunya da
Abul Hassan, ka gayawa sahabbai na, ban gane abunda
Imam (AS) ya ke nufi ba, Hisham ya ji maganar da Imam
(AS) ya yi min: sai ya xora hannun sa kan goshin sa ya
ce: haba kai kuwa Aliyyu xan Yaqxin! Me kae son kace?
Ali xan Yaqxin ya ce: ina rantse maka da Allah,
wannan abun da na faxa a wajen ka naji shi. Hisham ya
ce: ka san me maganar nan ke nufi kuwa? Lamarin
Imama zai koma hannun sa bayan mahaifinsa ne.
Hassan Kashani shima xaya ne daga cikin mawaqan
qarni na takwas, cikin waqar sa yayi nuni da irin wannan
maganar cewa:
Baban shi na masa al'kuna da Abul Hassan
Ta ko'ina ka dube shi zaka ga Hassan ne
Al'kunyar da koya ya san shi da ita kowacce rana
Al'kunyar sa ta zame masa tamkar sunan sa.
Dawud Raqqi shima yana cewa: na ce da Imam
Kazim (AS), ya shugaba na! Na tsufa, ka tsamar da ni
daga halaka, waye Imami a bayan ka? Imam (AS) ya nuna
xan sa Abul Hassan (Imam Ridha (AS)) ya ce: baya na
wannan ne majivincin lamarin ku.
Sanda Imam (AS) na kurkuku a Basra ya tura
wasiqa zuwa Madina a rubuce yana sanar da mutane
cewa: baya na Abul Hassan ne wasiyyi na.
Dawud xan Ruzbi ma na cewa: na kawo khumusin
dukiya ta wajen Imam Kazim (AS), sai ya karvi wasu
daga ciki ya bar min wasu. Na ce masa: ya naga wani abu
ka xauka daga ciki (ba duka ba)? sai ya ce min: ragowar
ka baiwa Imamin zamanin ka (majivincin lamarin ka), ka
dinga bashi. Bayan wani lokaci sai labarin wafatin Imam
(AS) ya zo min. Ba a xauki wani lokaci ba sai na gane
cewa Imam Ali xan Musa Ridha (AS) shine wannan
imamin na zamani na bayan a baya na kasa gane cewa
shine Imamin zamanin nawa.95
85 Al'kafy, littafi na 8, shafi na 888-884, hadisi na 8,8,9,da na 88. Tarihin Muhammad (SAW), shafi na 840.
Shekaru ishirin na Imamanci
Ranar juma'a ishirin da biyar ga watan Rahab
shekara ta 219AH ne Imam Kazim (AS) yana shekara ta
hamsin da biyar ya amsa kiran Ubangijin sa, Labik na
cewa: wannan wafatin na sa ya faru ne qarqashin umarnin
Harun cikin kurkuku ta hannun sandy xan Shak ta hanyar
guba ya shahadantar da Imam (AS), sannan aka binne shi
a maqabartar Bagdad a Rakh.
A wannan shekarar xan sa Imam Ridha (AS) na da
shekaru 95 sannan kuma shine babban xan Imam Kazim
(AS) imami na bakwai – ya karvi wannan ragama ta
imamanci ya zaun kan kujerar mahaifin sa. Imam Ridha
(AS) bayan wafatin mahaifin sa ya xauki wannan lamari
na Imamanci mai nauyin gaske don cika umarnin
Ubangiji ya dinga shiryar da mutane har zuwa shekara ta
129AH aka shahadantar da shi a Xus, sannan imamar ta
ciratu daga kansa.
Imami na takwas, a shekara ishirin yana kan
Imamanci, shekaru sha takwas da rabi a Madina sannan
akwai kimanin shekaru biyu da rabi ya zauna a
Khurasan.96
85 Al'kafi, littafi na 8, shafi na 475. Tahzibul ahkam, littafi na 5, shafi na 18. Al'irshad, littafi na 2, shafi na 247. Uyun akbarur Ridha (AS), littafi na 8, shafi na 899, hadisi na 4.
Tsayawar sa (AS) qyam don hana karkatar da addini
(inhirafi)
A shekarun qarshe na rayuwar Imami na bakwai
(AS) ya garar da ita ne cikib gidan kaso Prison, don haka
haxuwar sa da shia ya yi wuya, sannan kuma shia a voye
suke baba wani waje da zaka samu cewa mafiya yawan su
shia ne a wajen kai suna voye shiancin su ne ma, don
haka sai ya zamanto cewa haxuwar Imam (AS) da 'yan
shia ya zama wani abu marar yiyuwa.a wannan lokacin ne
Imam Kazim (AS) sabida samarwa shia mafita sai ya
samar da wakilai waxanda sune 'yan aike tsakanin sa da
mutane, suna kai komo da tambayoyin mutane wajen sa,
da wasiqi da dukkan tambayoyi da ilimantarwar shia suna
yin su ne ta wasixar mutanen tsakkiyar, mafiya yawan
wakilan Imam (AS) mutane ne masu addini masana ne
sosai, ya basu damar sarrafawa da ajiye dubunnan dinarai.
Duk da cewa a irin wannan yanayin Imam Musa
(AS) ya rayu duk da haka sai da Harun ya sanya shi a
gidan Kaso daga qarshe ya shahadantar da shi, ya nemi
shawarar mutane da yawa wakilan kuxaxe da dukiya don
ya shahadantar da Imami na bakwai, a wannan shekarar
ya bayar da kuxaxe da yawa don mutane su zama tare da
shi, sannan da yawa daga cikin wakilai sun canja, ta
hanyar bada cin hanci da rashawa ga yaran Imami na
bakwai.
An samu mutane da yawa masu cewa wai Imam
Kazim ya shiga gaiba ne wacce daga baya zai bayyana zai
kuvutar da mutane daga hannun azzalumai, kamar abun
na nufin cewa shine qarshen Imamai (AS) mai ceton
al'umma, don haka ne ma kai tsaye zai tabbata Imam
Ridha (AS) ba Imami bane, malamai da masana daga
cikin makusanta kuma yaran Imam Kazim (AS) wakilai
na gari yara na musamman ga Imam Kazim (AS) – irin su
Safwan da Yahya xan Yunus xan Abdurrahman – sun
tsaya qyam kan waxannan jirkice-jirkicen na qarya don
kare addini. Amman abin ban haushi shine tarin jahilai da
marasa cikakkiyar wayewa saida suka rinjayi jumillar
waxannan mutanen kan jihadin su.
Ana ta yaxa shubuhohi da sauye-sauye ta vangarori
daban-daban, wannan ne ya sa lokacin Imam Ridha (AS)
ya yi huxubobi masu yawa da suka shafi Imamanci.
Imam Ridha (AS) ma ya tsaya qyam kan waxannan
qarairayi da aka dinga yin su game da labarin Imami na
bakwai, sannan ya amsa waxannan shubuhohi ta hanyoyin
Ilimi. Haka nan ma masana cikin yaran Imam sun
bayyana gaskiya ga mutane don warware waxannan
shubahohi. Shekaru da yawa ana rubuta hadisai da
ruwayoyi.91
87 Qurbul isnad 200.
Manyan masu canja ma'anar addini
Wata fitina ta kunno kai cikin yaran Imam Kazim
(AS). sune wadanda ke zuwa daga garuruwa daban-daban
da sunan masu karvar Khumusi daga Imami na bakwai.
Mutane uku masu sojan gona da ke cikin su sune:
Aliyyu xan Abi Hamza Baxa'ini, Zayad xan Marwan
Qandi, da Usman xan Isa Rawa'si.
Daga vangaren hukuma kuma, ana tuhumar Imam
Musa (AS) da cewa garuruwan musulmai na aika masa
kuxaxe don ya haxa sojojin da zasu qaulbalanci
gwamnatin Abbasiyawa. Sabida wannan ne ma aka
tsanantawa Imam (AS) da 'yan leqen asiri na tattalin
arziki daga vangaren hukuma. Haka tarihin Imamai (AS)
ya zama ta vangaren dukiya ta yadda dole suke rarraba
aikin karva da sarrafa kuxaxen khumusi a hannun
talakawa. Sai abun ya zama kodai ba kai tsaye Imami ke
karvar kuxi ba ko kuma ya sanya wani karva da tara su
har ma wani lokacin da sarrafa su, amman a lokacin
Imamancin Imam Ridha (AS) lamurran kuxaxe gaba xaya
ya koma hannun sa, saida wasu mutane uku waxanda
suka qi maida wannan dukiya ga Imam Ridha (AS),
wajen Abi Hamza Baxa'ani akwai dinare dubu talatin,
wajen Ziyad xan Marwan Qindi akwai Dinare dubu
saba'in, wajen Usman xan Isa akwai Dinare dubu talatin
da kaniz shida.
Son duniya da kwaxayin matsayi ne ya sanya
waxannan mutane ukun basu maida dukiyar hannun xan
Imam Kazim (AS) kuma wakilin sa ba.
Lokacin da Imam Ridha (AS) ya rubutawa Usman
wasiqa zuwa Misra, ya nemi ya dawo/kawo da wannan
dukiyar, cikin amsar da ya baiwa Imam (AS) har akwai
cewa: mahaifin ka ai bai mutu ba, duk wanda ya ce ya
mutu ya yi qarya.
Da wannan jita-jitar ya ke yaudarar mutane ya tara
dukiya mai tarin yawa.91
81 Uyunu akhbaruru Ridha (AS), littafi na 8, shafi na 888. Al'gaiba na xusi, shafi na 47.
Masu mulkin zamanin Imam (AS); mulkin Harun
Lokacin Imamancin Imami na takwas (AS), ya yi
daidai da lokacin mulkin [Harunaar Rashid], yana da
'ya'yan sa biyu [Amin] da [Ma'amun]. Zamu iya cewa
Harun da Ma'amun ne mafi shara cikin halifofin
Abbasiyawa sanannu.
Da taimakon shuwagabannin vangarori daban-daban
ya samu nasarar cinye Makka sannan ya xora kansa kan
garuruwan musulmi da qarfin mulki, yana sanya dukkan
qarfin sa don ganin bayan duk wanda ya sava masa, ya
haxa hukuma mai qarfin gaske wacce cikin abinda ta sa
gaba har da takurawa gungun masu aqidar da suka sava
masa, kamar Alawiyyawa da ya sanya musu karan tsana
mai qarfin gaske, sanna ya shiga gaban dukkan wasu
manyan wannan mazhabi da motsin su na yau da gobe,
kamar Imam Kazim (AS) shima ya samu takunkumi mai
tsanani, a wannan hukumar ne aka takurawa Imam har da
shiga gidan kaso kala-kala wanda a qarshe har sai da aka
shihadantar da Imami na bakwai, abun ban mamaki ya
faru a wannan lokacin, cewar wani yaron Imami na
takwas (AS), mai suna Muhammad xan Sinan, ya yi
magana kan shaksiyyaer Harun da alqalamin sa ya
bayyana haqiqanin yadda suka tarwatsa mu sabida takura.
Yana cewa: ba komai kan takobin Harun sai jini.
Waxannan wahalhalu bayan shihadar Imam Kazim
(AS) ma wahalhalun sun ci gaba, saidai qalu balen da ke
gaban Imam Ridha (AS) lokacin Harun sam basu hana shi
abunda ya ke so ba kai ya ci gaba ma da faxawa mutane
kada su damu yana cewa: Harun ba zai iya yi min komai
ba, wannan ya sanyawa shia nutsuwa kan rayuwar Imam
Ridha (AS), da wannan magana ne Imam Ridha (AS) ya
sanya shia nutsuwa da cewar Harun ba zai iya cutar da shi
ba.93
89 Al-kafi, littafi na 1, shafi na 257 da 251. Uyunu akhbarur Ridha (AS), littafi na 8, shafi na 89.
Faxan neman mulki bayan mutuwar Harun
A shekara ta 239AH Harun ya mutu, ya bar duniya
yana riqe da yanki mai girma da qarfin gaske, amman
wajen ayyana halifan sa ya gagara (bai ayyana ba),
wannan ne ya sa wajen gadon wannan ya sa aka kasa
halifancin nasa ga 'ya'yan sa uku (Amin, Ma'amun da
Mu'utaman) amman wani cikin yaran Harun ya bada
shaida cewar ya yi wasiyya cewa wanda zai gaje shi a
bayan sa shine qaramin cikin 'ya'yan sa maza marar
tajribar su wato Muhammad Amin bayan sa sai Ma'amun
bayan sa sai Mu'utaman. Wannan ne ya sa assasa yaqi da
husuma tsakanin su na tsawon shekaru bakwai wanda aka
sheqar da jini mai yawan gaske, a qarshe dai cikin shekara
ta 231AH sojojin Ma'amun suka kashe Amin ya mamaye
yankin sa, bayan kashe Amin sai tsarin Abbasiyawa baki
xaya ya koma hannun Ma'amun ya ci gaba.42
40 Tarihin Ya'aqubi, littafi na 2, shafi na 480. Tarihil khlafa'a, shafi na 824. Al'kamil fit tarikh, littafi na 5, shaf na 291.
Halifancin Ma'amun
Ma'amun shi kaxai saida ya yi shekaru talatin a kan
mulki bayan kashe xan uwan sa da sunan Halifan
abbasiyawa na bakwai wanda ya gaji karagar mulkin
baban sa. An kashe Amin ne a shekara ta 235AH sabida
yaqin da ya afku tsakanin sa da xan uwan sa, inda wannan
ya sa ya maye gurbin sa da cire shi da ya yi, aka xakko
kan sa daga Khurasan har zuwa Bagdad.
Cikin nayani mai zurfi ta hanyar ruwayoyi daban-
daban ya bayyana cewa, tsanantawar da Imam Ridha (AS)
ya samu a mulkin Harun da lokacin da ake faxa tsakanin
Amin da Ma'amun yana aiki tuquru na kare mazhabin sa
daga masu canja koyarwar sa da sauran qananan maqiya,
dalilin da ya sa Imam Ridha ya qara samun sararawa
shine cewa: maqiya sun shagala da kawukan su don haka
sun kau da kai daga takurawa shia.
Masu bincike da tahlil kan tarihi, sun bayyana
halayyar Ma'amun sama da na kowanne halifan
Abbasiyawa sabida mutum ne, mai wayon gaske, mai
basira, jarumi kuma wayayyen gaske ne. sannan duk da
haka mutum ne mai son zama a tattauna mas'alolin yau da
gobe sannan yana da matuqar son wasanni, babban
abunda Ma'amun ya fi so a rayuwar sa shine caca, kixe-
kixe da shan giya.
A shekara ta 122AH Ma'amun ya kira Imam Ridha
(AS) zuwa Khurasan, a cikin watan azumin wannan
shekarar ya sanya shi majivincin lamurran mutane, ya
sanya mutane su yi masa bai'a, har zuwa qarshen rayuwar
sa (AS) – kenan kimanin shekaru biyu da watanni biyar –
ya zauna a Khurasan.42
48 Tarikhul khulafa'a, shafi na 805. Tarihin xan Khldun, littafi na 8, shafi na 880. Raywar Imam Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 242 zuwa na 244.
Tsayuwar sa da wahalhalun da ya sha (AS)
Hukumar da bata gama tsayawa qyam da qafarta ba
ta Ma'amun bayan gama yaqunquna da ya gudana
tsakanin su da kashe Amin, sannan a gefe guda akwai
gungun mutanen da basu yarda da gwamnatim ba sabida
wasu dalilai na siyasa.
A wannan lokacin ya zamanto aminci a yankin
musulmai ya ragu sosai, sannan ga wasu Alawiyyawa da
suka tsaya suna qalubalantar gwamnatin, sai ya yi niyyar
xaukar wani salo na [kira zuwa ga Imam Ridha (AS) daga
alayen Muhammad (SAW) – wato janyo hankalin masu
turjiya waxanda ke iqirarin son Manzo(SAW)] wannan
abu ya sanya hukumar Abbasiyawa cikin haxarin gaske.
Zamu yi muku bayanin hakan cikin isharori kamar haka:
A shekara ta 231 an samu turjiya daga wata babban
runduna, ikin zulhijjar wannan shekarar Hassan xan
Harsh ya xaga tuna da suna [Arridha daga Alayen
Muhammad (SAW)] a vangaren Misra, da gefen Nail inda
ya tara runduna mai yawan gaske.
A dai wannan shekara ne Halb da gefen ta aka samu
wasu qarqashin [Nasr xan Shisu Aqili]. A wannan
shekarar ana samu wasu masu turjiyar suma inda aka
gwbza da sunan yaqin [Maidan] wanda aka kashe
kimanin mutane dubu ishirin.
Shekara ta 233AH Abu Saraya daga Kufa ya
shelanta kansa matsayin shugaba a hukumar Ma'amun. A
tare da shi akwai Muhammad xan Ibrahim Xan Isma'il
Hasani (wanda ya shara da Ibni Xaba-xaba) cikin wannan
tsyawar sun samu nasara sun kafa daula ta wani xan
lokaci a Kufa. Haka nan ma Abus Sirara shima ya samu
dama na kama garuru kamar Makka, Basra, Yemen, Fars,
Ahwaz da Mada'in. Manyan masu faxa a ji a nan yankin
Alawiyyawa ne – mutane uku cikin su ma 'yan uwan
Imam Ridha (AS) ne: Abbas xab Muhammad xan Isa xan
Ja'afar, Hussain xan Hassan Afxas, Ibrahim xan Musa xan
Ja'afar (AS), Isma'il xan Musa xan Ja'afar (AS), Zaidu xan
Musa xan Ja'afar (AS), Muhammad xan Sulaiman xan
Dawud xan Hassan xan Hassan (AS). Abbasiyawa sun
kashe da yawa daga cikin su lokacin tsayawar Abus
Siraya wanda bai kai shekara xaya ba, wanda ya kai
kimanin mutane xari biyu wannan mutanen da aka kashe
bai yi kyau ba.
A shekara ya 122AH xan Imam Sadiq (AS),
Muhammad xan Ja'afar Dibaj a Makka tare da wasu
gungun mutane da suka yi masa bai'a shima ya tashi, Isal
Jalludi wanda yake sojan sa ne ya gan shi, ya bashi
wasiqar amana, na neman hukuma daga wajen Ma'amun.
A sha biyar ga Zulqidar wannan shekarar, Zaidu xan
Musa ma ya miqe inda ya cinnawa wasu gidajen
Abbasiyawa wuta hakan ne ya sa kowa ya san shi da
Zaidu mai wuta.41
42 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 8, shafi na 224, Hadisi na 1. Tarikhul umam wal mamluk, na Xabari, littafi na 1, shafi na 544. Al'kamil fittarikh, littafi na 5, shafi na 800 zuwa 805. Maqatilux xalibin, shafi na 855. Rayuwar Imam Ridha (AS). Qarshi, littafi na 2, shafi na 212.
Kirawo shi zuwa Madina (AS)
Halifan da bai kama qasa ba, ya ar'aika da wasiqu
masu yawa ga Imam (AS) zuwa Madina, Imam (AS) na
bada amsar rashin yadda kan zuwan sa Khurasan, wannan
ne ya sa Halifa Ma'amun ya aiko manyan nakusa da shi
daga yaran sa su biyu da ake kira Raja'a xan abi Dahhak
da Yasir wanda yake mai hidima ga hukumar Abbasiyawa
tare da rundunar sojoji masu yawa don tafiya tare da
Imam (AS) daga Madina zuwa Khurasan, aka basu
umarni su girmama Imam (AS) matuqar girmamawa da
bashi kariya sannan su zama koda yaushe tare da shi,
sannan kada su sake su takura shi kan yin wani abu yayin
tafiyar, su bar shi cikin walwalar da yake so.
Tunda daman Ma'amun na buqatar hukumar sa ta
tsaya da qafafun ta sannan yana son tafiyar sa ta ta xore
ba tare da wani abu ya shiga gaban ta ba, Imam Ridha
(AS) ya gane dukkan abubuwan da Ma'amun ke buqata,
haka nan mutanen Madina da dangin Imam (AS) suma
sun gane dalilin Ma'amun na neman lallai sai Imam (AS)
ya je kusa da shi Khurasan ya zauna, har suke yake cewa:
Imam (AS) ya jejje qabarin manzo (SAW) ya dinga kai
komo na bankwana har sai da mutane suka ji qarar kukan
sa da gane baqin cikin sa na bankwana, su da wasu
mutanen Madina suka gane cewa wannan tafiyar ba
kamar wacce ya sake yi bace, Imam (AS) yake cewa: ina
bankwana da garin Kaka na zan fita daga cikin sa, haka
nan ma zan fita zuwa duniya ta haqiqa, sannan za a binne
ni kusa da Harun, a Khurasan ma ya faxawa wani yaron
sa Hassan xan Wassha cewa: lokacin da na nufi fitowa
daga Madina duk dangi na sun mi nuni sannan suka dinga
magana dangane da ni cewa suna ta yi min kuka, wanda
har saida na ji kukan, sannan na raba musu dinare dubu
goma sha biyu na gaya musu cewa wannan tafiyar da zan
yi ba zan dawo ba.49
48 Uyunu akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 281 hadisi na 21. Alkhara'ij wal Jara'ih, shafi na 207, hadisi na 859.
Daga Madina zuwa Marwa
Bisa umarnin da Ma'amun ya bayar na cewar idan
za'a taho da Imam (AS) daga Madina a biyo da shi ta
hanyar Basra, Ahwaz, da Fars, sannan ya qara bayyanawa
qarar cewa kada a biyo da shi ta garuruwan Shia, kamar
Kufa, da Qum.
Sabida abubuwan da suka faru a xan shekarun da
suka gabata na wannan lokacin, don haka sai hanyar
Imam Ridha (AS) ta kasance kamar haka: Nuqreh
(Ma'adani Nuqreh), Nabaj, Basra, Ahwaz, Bahban,
Shiraz< Isxakhr, Abrqu, Dahshir, Yazd, Khazaniq, Rabax
ta gaban Badum, Nishabur, Dahsurkh, Kuhisangtarash
(Kuhsangi), Xus, Nugan, Sarkhas sannan Marwa.
Rubututtuka da yawa na tarihi dangane da yadda tafiyar
Imam (AS) ta kasance na nan a tanade.44
44 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 818, Hadisi na 5. Sannan akwai map R.K wanda ya nuna tafiyar Imam (AS) a jogirafance daga Madina zuwa Marwa.
Zaman sa waliyyul ahd
Waliyyul ahad, na nufin zama shugaba kuma
majivincin lamarin mutane bayan mutuwar Halifa.
Wannnan matsayin wanda shine mafi girman matsayi
bayan halifa ya bada shi ne don kawai ya zama mutane
mafi kusa da Imam (AS) sun dafa masa, cikin xan tarihin
Imami na takwas muna karantawa cewa, a shekarun
qarshen rayuwar sa Ma'amun ya naxa shi matsayin
waliyyul ahd din sa, ba wani cikin Ma'asumai da aka tava
sanya shi a wannan matsayin. Wannan zai haskaka mana
a fili cewa ana son amfani da qimar Imam Ridha (AS) ne
don cimma manufa, tunda a nomal yanayi babu yadda za
a yi mutum Azzalumi kamar Harun ya karva tare da
amncewa da wannan lamari.
Tun bayan kashe xan uwansa Amin da ya yi, ya yi
alqawarin sai ya san yadda ya yi ya gyara siyaysar sa ta
gida. Kada ya gaza yin abun da mahaifin sa ya yi. Mafi
girman matsalar da Ma'amun yake fuskanta shine
tsayawar Alawiyyawa, da wasu Iraniyawa da waxanda
basu yadda da mulkin sa ba, wannan ya sanya dole
Ma'amun don ya gayara siyasar sa yana buqatar ya kira
Imam Ridha (AS) ya naxa shi matsayin Magajin sa kawai
domin itace mafita mafi kyau.
Dalilin da ya sa Imam (AS) ya karvi waliyyul ahd
Tunda cewa Imam Ridha (AS) ya shiga Marwa,
Ma'amun ya yi qoqarin sanya Imam (AS) a kan gadon
mulkin sa cikin jalasosi masu yawa da suka gudana amma
kakaf ba inda Imam (AS) ya karvi wannan tayi, duk na
gefen Ma'amun sun yi matuqar shan mamaki, kowa ya
san wannnan abu da Ma'amun yake yi ba a san ta da
sunan hanyar gyara ba, Fadl xan Sahl, wazirin sa Ba
Iraniye kuma masanin siyasar Ma'amun, ya yi matuqar
jayayya da Ma'amun kan wannan abu da ya ke yi yana ce
masa: har yanzu banga halifanci mafi faxuwa a qasa
kwasha-kwasha kamar naka ba, a zama na qarshe, bayan
halifa ya baiwa Imam (AS) karagar mulki yana juyo masa
da ita na cewa baya so, a wannan zaman ma'amun ya
cewa Imam (AS): ina ganin ka fi dacewa ka karvi wannan
kujerar, ka yadda na zama farkon wanda zan yi maka
bai'a, sai a nan Imam (AS) bashi amsa ta qarshe yake ce
masa: idan wannan halifancin ya dace da kai (allah ne ya
baka shi), bai kamata ka cire shi daga wajen ka ka baiwa
wanin ka ba, idan kuma bata dace da kai ba (ba kai Allah
ya sanyawa ita ba qwata ka yi), ba yadda za a yi ka mayar
da ita ga wani sai da dalilin kana son wanin ka ya
girmama ka, wannan maganar, na tabbatar da cewa
hukumar Ma'amun ta qwace ce, rashin cancantar hukumar
Ma'amun, dole ya haqura da wannan tayi ba yar hukma a
hannun sa tunda Ima bai karva ba.
Bayan wasu kwanaki da wannan tattaunawar
Ma'amun ya rasa yadda zai yi da Imam don ya karvi
hukuma, a qarshe sai ya sanya Imam waliyyul Ahd,
wannan naxi da ya yi wa Imam ya savawa burin abun da
Imam (AS) ke so, dalilin Imam na hakan ya na cewa: na
samu labari daga Kaka na cewar, za a kashe ni ne ta
hanyar guba, za a zalunce si a shahadantar da ni, a daidai
lokacin da mala'ikun sama zasu yi min kuka, sannan za a
binne ni a kusa da Harunar Rashid.
Lokacin da Ma'amun ya ji wannan maganar daga
Imam (AS) sai ya fashe da kuka ya tambayi cewa: ya xan
Annabin Allah! wa zai kashe ka? Ina raye, wa yake da
wannan qarfin ran da zai maka wannan mugun aikin?!
Imam (AS) ya ce: idan na ga dama zan iya faxar
wanda zai kashe ni zan iya bayyana kowane.
Halifa, a qarshe Imam (AS) ya ga ana masa gargaxi
da kisa, sannan ya gane cewa kaxai hanyar kuvuta shine
ya haqura ya karvi wannan muqamin, tunda ko ya karvi
muqamin ko kuma ya mutu.
Imam Ridha (AS) dole ya karva don gudun kada ya
jefa kansa cikin halaka, saidai ya sanya sharaxin cewa ba
zai tava shiga lamarn gudanar da hukuma ba.
Ma'amun ya karvi hakan. A wannan lokacin ne duk
inda waliyyul ahd zai kasance, a tare da shi akwai kyauta
da yake rarrabawa mutane. Ma'amun ya sanya an yi kuxi
da sunan Imam Ridha (AS), duk wanda ya yi godiya idan
Imam (AS) ya yi masa kyauta, yana bashi abunda zai ishe
shi na shekara, ya bada umarni ga dukkan mutane da su
cire baqaqen kayan da Abbasiyawa su sanya korayen
kaya (sabida koraye ne kayan gidan Manzo (SAW)).45
45 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 289, Hadisi na 8, da shafi na 847, hadisi na 81..
Yi wa Imam (AS) bai'a
Kamar yadda tarihi ya bayyana, mutanen Khurasan
da masu godewa hukuma da [Imam Ali xan Musa Ridha
(AS)] ranar asabar biyar ga watan ramadan shekara ta
122AH46 mutane suka yiwa Imam (AS) bai'a da sunan
waliyyul ahad na hukumar Abbasiyawa.
Ma'amun ya baiwa xansa Abbas ya fara yiwa Imam
(AS) bai'a ya zama na farkon yin bai'a kafin koya ya fara
yi masa.
Sannan sarakuna da sauran mutane suka biyo bayan
Abbas suka yi bai'a, a zaman bai'ar ne, tsakanin halifa da
Imam suka yi wani zama tsakanin su, sannan mawaqa da
masu kirari suka dinga yabon Imam (AS) da halifa.
Halifa ya xebe tsammanin cewa Imam (AS) zai
karvi wannan waliyyul ahd xin, ya sanya aka yi
gagarumin biki a garuruwan musulmai, ya bada haqqoqin
shekara xaya baki xaya sannan baqaqen kayan
abbasiyawa ya sa kowa ya cire ya sa kore, sannan ya bada
umarni cewa dukkan kuxaden zinare da na tagulla
(Dirhami da Dinar) a sanya sunan Imam Ridha (AS) a
jikin su. Wasu daga waxannan qwandalayen a gidan ajiye
kayan tarihi da ke Berlin [mai lamba 2132] da England a
garin London [da lamba 113].
Bayan kwana biyu bayan gama zaman bai'a, sai
halifa da kansa ya bada Umarni cewa a taru a yi takardar
yarjejeniya tare da sa hannu kan shedar naxa waliyyul ahd
(mai jiran gado), bayan yaxa wannan labarin cikin
garuruwan musulunci, sannan masu huxubar juma'a su
45 Tarihin shamsi, bai'ar Imam Ridha (AS), 80 farvardin, shekara ta 895 HS (hai'at wa nujumi islami, littafi na 2, shafi na 825).
dinga yiwa mai jiran gado addu'a kan membarorin su, a
hankali sai ga wannan labarin ya baiwa kowa mamaki,
masoya da maqiya duk baki xaya.41
47 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 245, hayatu Imam Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 807, wanda ya rubuta, ya rubuta siaffar yadda kuxin da aka yi da suna Imam Ridha (AS) jikin tsabar da ke cikin gidan ajiye kayan tarihi.
Dalilin bada muqamin mai jiran gado
Tambayar da ya kamata mu yi a nan shine mai ya sa
Ma'amun ya dage sai ya bada wannan muqamin ga wanda
ba suka sava da shi. Amsar wannan a fili take kowa zai
iya cewa siyasa ce ta sanya shi yin hakan ba wani abu ba
kamar yadda muke gani sannan da wasu dalilai masu
goyawa hakan baya.
Wasu daga cikin dalilan sune cewar ma'amun na son
wasu cikin shia su karkato zuwa gare shi, don haka ya
kamata ya shugabantar da Imam Ridha (AS) tare da
girmama shi.
Wasu kuma sun yi imani da cewa Ma'amun na cikin
yanayi mafi wahala da tsoro yadda ya san cewa zai iya
yiyuwa sojojin Amin su juya masa baya daga qarshe sai
ya zamo lamarin halifanci ya bar gidan Abbasiyawa ya
koma asalin sa ga Alayen Muhammad (SAW).
Gungun jama'a dangane da wannan lamari su na
cewa, halifa ya samu nasarar lafar da rigimar cikin gida
don haka bari ya fuskanci rigimar waje da siyasa sabida
wahalar da ya sha na yaqin cikin gida don haka yaqi bai
kamace shi ba, don haka bari ya xaga tutar cewa shi ya
yarda da alayen Muhammad don haka sai ya samu
sararawa.
An kai ga kallon cewa asalin abunda ya ja Ma'amun
na bada halifanci wanda daga qarshe ya bada waliyyul
ahd, ba komai ya sa haka ba sai don neman wanzuwar
daular Abbasiyya. Saidai sanin Imam Ridha (AS) da
cewar wannan maganar ta Ma'amun ba tabbatacciya bace
kamar yadda rubutu ba zai tava tabbata kan ruwa ba.
Sabida Harun na mutuwa sai ga shi ya kaiwa
gwamnatin Amin hari ya kashe shi sabida son mulki,
wannan na nuna maganar bada mulki yaudara ce, wannan
ne ya sa kowa ya gane Ma'amun ya rasa wasu da yawa
daga masu hankali da suka goya masa baya, waxanda da
yawan su Iraniyawa ne a wannan lokacin Abbasiyawa sun
sanya Iraniyawa a gefe sabida suna ganin kamar sun san
inda suka dosa. A wannan lokacin ne sabida neman
karvuwar Abbasiyawa da neman karvuwa da kafuwar
halifanci ya ci tura ta wani vangare, rauni ya bayyana
cikin halifancin Abbasiyawa a Bagdad inda mafi yawan
masu faxa a ji sun sha gaban Abbasiyawa.
Baiwa Imam (AS) shugaba mai jiran gado na daular
abbasiyawa sabida sun fahimtar cewa daidai lokacin
daular abbasiya na dab da iya samun matsala da rushewa,
wanda zai zama Ma'amun na barin karaga ba wani xan
Abbasiyawa da zai qara mulki, sai mulki ya dawo hannun
banu Hashim, don haka idan Abbasiyawa na son su ci
gaba da tasiri cikin hukuma dole Ma'amun ya nemi
mafaka kada su rasa gaba xaya.
Wannan ne kuma abinda zai faru ga Halifan da zai
zo bayan sa, don haka sai ya yi kokarin ya gyara lamarin
hukumar sa.
Sabida haka ne ya sanya Imam mao jiran gado na
wani xan lokaci wanda tun ba'a je ko'ina ba ya yi
shawarar sanyawa Imam guba a abinci ya shahadantar da
shi.
Rashin aiki tare da hukuma
Ma'amun ya fara da buqatar a karvi shugaban ci
sannan ya qare da bayar da mai jiran gado, duk da cewa
duk maganganu biyun Imam (AS) ya fahimci me ye
hadafin sa. Ma'amun da baida komai sai qoqarin tabbatar
da wilayar sa sabida son karvuwa wajen mutane sannan ta
sanadin jan Imam (AS) ya sanya shi mai jiran gado zai
sauqaqa masa hakan, sai ya tilasta Imam (AS) da karvar
mai jiran gado ko mutuwa, cikin tambayar da Imam (AS)
ya yi kan hakan ya ce: Allah ya hane ni da na kai kaina ga
mahallaka, da ace an bani zavi kan na xauka tsakanin
zavuka biyu (halifanci ko jiran gado), ba wanda zan karva
a ciki, ba zan canja tsari ba, sannan ba zan jirkita tsarin
magabata na ba kawai abinda zan yi shine shawara da
fuskantarwa daga nesa.
Waxannan sharuxxan, haka ya yi bayanin wannan
da cewa na rintse ido daga dukkan zavuvvuka na
hukuma, ta dole ba yadda na iya saida na karvi wannan
mai jiran gado.
Bayan Imam (AS) ya karvi mai jiran gado rana
tsaka yana cikin gida a zaune sai wannan abun mamaki ya
faru. Kamar yadda sau da yawa Ma'amun na neman
taimakon Imam (AS) duk da cewa Imam (AS) ya sanya
masa sharuxxa kafin karvar muqamin Jiran gado, kan
cewa ba zai shiga cikin gudanarwar hukuma ba, sabida ya
nunawa mutane yadda ya kamata halifanci ya kasance
yake tambayar sa yana ce masa: [na karvi wannan
muqami ne bisa sharuxxa kan cewa ba zan cire ko na naxa
wani muqami ba, sannan ba zan sa a yi ko na hana a yi ba
ta yadda koda Allah ya tambaye ni kan dukkan wani
kuskure ko kan siyar da duniya ta zan kuvuta].
Haka nan dai bayan Fadl xan Sahl shima ya bar
duniya, Ma'amun yake cewa Imam (AS): ya Ali xan
Musa, yanzune kake buqatar kasantuwa kusa da ni sosan
gaske, ya kamata ka taimaka min wajen gudanar da
lamarin hukuma, Imam (AS) ya bashi amsa yana cewa:
zaka iya yin halifancin ka kamar yadda ya dace, zamu
zama masu taimaka maka da addu'a a koyaushe.
Cikin amsar da halifa ya bayar lokacin sallar idi
shima Imam saida ya sanya masa sharaxi, saidai an
takurawa Imam (AS) da ya dinga yiwa mutane sallar
juma'a a madadin halifa, wannan lamari ba qaramin
takurawa ya zama ga Imam (AS) ba. Yasir Hadimin sa
yana cewa: duk sati idan Imam (AS) zai dawo daga
masallaci, yana roqar Allah mutuwar sa, irin wannan
addu'a Imam yake yawan yi yana cewa: Ya Mahaliccin
bayi! Idan har idan na bar duniya wannan takura zata rabu
da ni, ka gaggauta sadani da mutuwa.41
41 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 889, Hadisi na 8, da shafi na 85, hadisi na 84, da babi na 20, hadisi na 25 da hadisi na 29.
Mawaqa a Khurasan
A rubuce yake cikin qa'idoji cewar duk wanda ya
zama mai jiran gado ko ya hau halifanci manyan mawaqa
zasu dinga masa waqoqi kala-kala. Wannan al'ada a haka
aka santa a tarihin magabata na wannan yanki, da yawan
mawaqa shahararru na wannan zamanin sun waqe Imam
(AS), kamar su: Nazir Ibrahim xan Abbas suli, Da'abal
xan Ali Khaza'i, Zainu xan Ali Khaza'i, Abu Nawas sun
zo Khurasan, sun yabi Ahlulbait (AS) da waqoqi na kirki
waxanda suka ja hankalin kowa, Da'abal da yae shi shia
ne, ya yi wa Imam Ridha (AS) da Ahlulbait (AS) waqa da
[kamar yadda ayoyi suka faxe su] wacce ta shahara da
madarisi ayat, waxannan waqoqin suna koyar da adabi, a
waxannan ranakin da Imam (AS) ya shigo Khurasan
waqoqin sa sun yi matuqar yaxuwa.
Za a iya cewa: waqoqin Abu Nawas a shekarn (246-
231AH) suna daga mafi girma mafi kyawun adabi da aka
yi a zamanin Imami na takwas (AS).
Wasu na cewa Abu Nawas na daga cikin makwafin
mawaqan da suka zo kafin muslunci, a zaman waqe mai
jiran gado bai samu halarta ba, bayan ranar ne Ma;amun
ya yi wa Abu Nawas magana ya ce: kai ne babban
mawaqin wannan lokacin wanda bani da kamar sa, mai
yasa baka zo wajen waqe mai jiran gado na ba ka waqe
Ali Xan Musa (AS) ba? a nan take Abi Nawas ya tsara
waxannan baituka biyun:
Ka sani cewa ban qi yabon xan Musa ba.
Da mutanen da suke tare da shi.
Ina faxar cewa ba zan bar yabon Imami ba.
Wanda Jibrilu ke wa baban sa hidima.
Ma'amun ya yi matuqar mamakin wannan waqar
sosai, ya baiwa Abu Nawas kimanin abinda ya baiwa
mawaqan da suka tattaru a ranar kyauta.
Bayan wasu 'yan kwanaki sai Abu Nawas ya haxu
da Imam Ridha (AS) ya gaya masa na yi maka wasu
baitoci, zan so ka saurara ka ji, Imam Yace: karanta; sai
ya jero baitoci kamar haka:
Masu tsarki tufafin ku sun tsarkaka
Sallah na inganta ne yayin da aka ambace ku.
Wanda ba alawi ba ku gaya masa
Bashi da wani alfahar a qarshen zamani.
Lokacin da Allah zai kuvutar da halittu zai dakatar
da shi
Ya xaukaka ku ya tsarkake ku ya ku waxannan
mutane.
Kune mafiya xaukaka kuma wajen ku akwai
Ilimin littafi da abunda surori ke qunshe da shi.
Imam (AS) ya ji daxin wannan waqar sosan gaske
yace masa: banji wata waqa da tafi wannan ma'ana ba
kafin yanzu, nan take ya yi wa yaron sa magana ya
tambayr shi cewa: nawa muke da shi kuxi yanzu? Sai ya
bada amsa cewa: dinare xari uku ne, Imam ya ce: baiwa
Abu Nuwas dukkan kuxaxe na, sannan ya ce: saidai kuxin
kaxan ne.
Daga nan sai Imam (AS) ya ci gaba da tafiya zuwa
inda ya nufa.43
49 R.K, Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 828, Hadisi na 80. Al'a'alam, littafi na 2, shafi na 225.
Sallar idi
Halifa ne da kansa yake sallar idi, amman bayan
Imam (AS) ya karvi halifanci bisa takurawar da Ma'amun
ya yi masa, sai ya nemi Imam (AS) ya yi wa mutane sallar
idi. Imam (AS) ya qi karva. Duk da haka halifa ya
takurawa Imam (AS), da ya takura sosai sai Imam (AS)
ya bashi amsa da tambaya cewa: ya Amir! Ka qyale ni da
yin wannan aikin, duk da cewa ina son yin sa, amman
idan ka dage kan sai na yi sallar idin, zan yi wa mutane
salla irin wacce Manzo (SAW) da Sugaban muminai
Imam Ali (AS) ke yi wa mutane.
Ma'amun ya karvi wannan sharaxin a haka. Sai
labari ya baza ko'ina cewa Imam Ridha (AS) zaiwa
mutane salla a Marwa. Da asubar ranar salla, Imam ya
shirya ya yi wanka ya tafi wurin salla, ya sany baqin
rawani sannan ya yafa hirami wani a wuyan sa ya sakko
qirjin sa ya nufi wajen salla, idon sawun sa a buxe, ya
shiga wajen salla, yaran sa da na kusa da shi suka tsaya a
wajen jira suna jiran tafiya wajen salla, Imam (AS) ya
fuskanto su ya ce: ku yi shiga irin yadda na yi baki xayan
ku.
Nan fa wasu mutane suka fusata suka fito waje,
Imam ya fara tafiya da buxaxxiyar qafarsa yana mai xaga
kansa sama ya ce [Allahu akbar] sau huxu.
Imam (AS) ya ci gaba da kabbara baki xayan
yaran sa kuma suna faxa tare da shi. Lokacin da Imam
ya fito daga wajen da suke da murya mai qarfi ya yi
wannan tashibin yana cewa: Allahu akbar Allahu
akbar, Allahu akbarAla ma haza na, Allahu akbar
ala ma razaqtana min bahimatul an'am,
walhamdulillahi ala ma abla'ana.
Imam ya xan tsaya kaxan fuskanci mutane bayan
isar sa wajen salla, sai qarar kuka kake ji mutane na ta
kuka, suka miqe tsaye sabida girmama shi ya yi
kabbarori huxu, ji kake ko ina na amsa muryar Imam
(AS), sama, qasa, qofa da katanga na amsa muryar
Imam (AS), labari ya jewa Ma'amun: lokacin qasan sa
akwai Fadl xan Sahl a gefen sa, ya cewa halifa: ya
Amir! Idan har irin haka Ali xan Musa zai dinga jan
mutane salla, zai xebe maka dukkan magoya baya
hakan kuma zai haifar da fitina, abinda ya fi kawai
shine ka karvi wannan daga hannun sa kawai.
Duk da haka Imam (AS) ba qarasa daidai inda
zai salla ba, sai Ma'amun ya tashi daga kujerar sa ya
nemi a gayawa Imam (AS) ya dawo, da labari ya same
shi sai ya dawo, ya nemi a bashi takalman sa ya sa ya
dawo gida, wannan ne ya hana mutane su yi sallar Idi
ta wannan ranar a bayan Imam Ridha (AS).52
50 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 850, Hadisi na 28.
Varewar siyasar wasa
A haqiqa da ta tabbata ga Ma'amun cewa ba zai
iya cimma hadafin sa da yake zato ba kawai don
mayar da Imam (AS) mai jiran gado, yana nema ya
bar vangaren banu Abbas sannan a gefe xaya ba zai
iya karkata zuwa ga vangaren Banu Hashim da
alawiyyawa ba. Khurasan yanki ne da ke gabascin
duniyar muslmai, a wannan lokacin ba zai yiyu ta
zama cibiyar hukumar musulmai ba, don haka dole ya
mayar da cibiyar mulki ta koma Bagdad, a gefe guda
kuma ya samu cikas da matsaloli, dole abunda ya fi
masa shine ya zai yi yanzu ya sauke tasirin Imam
Ridha (AS)?
Sai zavi uku ya rage masa: kodai ya tafi da Imam
(AS) zuwa Bagdad, na biyu ko kuma Imam (AS) ya
zauna a Madina na uku ko kuma ya zauna Khurasan
ya ci gaba da rayuwar sa.
Sai ya lissafa cewa idan Imam (AS) ya zauna a
Madina ko Khurasan zai zama an samu wani vangare
na mabiya da sojoji mabiya mai jiran gado kenan – zai
zama mai jiran gado xaya ne – wannan kuma babban
haxari ne ga hukuma. Wannan kuma zai bada kafar
nan gaba halifanci ya iya komawa wajen alawiyyawa
sannan shia su samu babbar mafaka.
Ta vangare xaya kuma halifa bashi da damar
komawa Bagdad sabida matsalar siyasa, dole ya zama
Imam (AS) na tare da shi in har zai koma, wannan
lamarin ya jaza masa damuwa na ganin shiga tsaka
mai wuya da ya yi, don haka dole ya zavi abun da
shine mafi nasara gare shi ko menene kuwa.
Ga Abbasiyawa 'yan vangarancin da ke Bagdad,
waxanda sam baza su yarda/jure a bada jiran gado ga
wani xa daga bani Hashim ba, koda kuwa da sunan
kujerar Abbasiyawa ce, sannan kuma a zuciyar
Ma'amun bashi da nufin Imam (AS) ya gaje shi, wani
mai magana ya nuna yi hasashe kan cewa, abun ya yi
kiki kaka dole Ma'amun ya ga hanya xaya da zai bi ya
sha shine ya kashe Imam (AS).
Bayan wafatin Imam (AS) kenan sai Ma'amun ya
rubuta wasiqa zuwa ga Abbasiyawa da mutanen
Bagdad yana musu magana wacce ke nuna
shu'umancin sa:
[wasiqar Ma'amun zuwa ga Abbasiyawa, yaran
sa da mutanen Bagdad, ina sanar muku da mutuwar
Ali xan Musa, wanda na so muku da ku yi biyayya
gare shi a baya na, sai gashi maqiya ...].
Akwai wani rahoto da ke hannun Ma'amun shi
kuma ya na cewa Ma'amun ya tabbatar da Ali xan
Musa a matsayin mai jiran gadon sa ya nemi mutane
da su yi masa uzuri (tunda babu shi yanzu), xaya daga
marubutan zamanin da mai suna xan Khaldun cikin
bayanin abunda wannan wasiqar ta qunsa shine:
Ma'amun ya nufi wajen Hassan xan Sahl da mutanen
Bagdad da yaran sa, maimakon Imam zai sanya xan sa
ya zama mai jiran gadon sa, sai gashi ya shelanta cewa
ya bar duniya, don haka sai ya komar da ita ga xan
nasa.52
58 Tarihin xabari, littafi na 1. Waqio'in da suka faru a 208AH. Tarihin xan Khaldun, littafi na 8 shafi na 250.
Kurkukun sarkhas
Cikin kwanakin da Imam (AS) yake cikin
kurasan, sabida zaman sa cikin gwamnati, ya zauna
cikin wani gida a Sarikhas, ba wanda ya san yaushe
wannan wajen ya zama kurkuku sannan da wane dalili
ta zama a nan, shin dalilin mahaifinsa ya zo nan ne ya
zo ko kuma daman tana kan hanyar sa ta zuwa Marwa
tunda daga Nishabur ya yi niyyar zuwa Sarkhas,
sannan kuma wannan garin kan hanyar matafiyan
hukuma ne masu kai komone zuwa Bagdad.
Wanda kawai Imam ya haxu da shi cikin
kurkukun shine Aba Salt Haruwi, yake cewa: lokacin
da na je gidan da Imam (AS) yake zaune a Sarkhas,
sai na ga hannuwansa da qafafuwan sa cikin sarqa, sai
na roqi masu gadi kan cewa zan gan shi, suka qi ban
xama, lokacin da suka ga na takura sai na shiga, sai
suka ce: ba zai yiyu ka shiga ba kawai don ku yi
magana sabida Imam (AS) dare da rana yana sallah
raka'a dubu nafila, kawai awannin farkon rana kamar
daidai zawali da kuma dab da magriba yake da su,
amman a wannan lokutan baya zuwa ko'ina, koda
yaushe yana shagalltuwa da iziri da munajati.
Aba Slat ya yi matuqar shan mamaki dangane da
irin wannan Ibada da Imam ya ke yi, sai ya nemi
gandirobobin gidan kason da su bashi dama lokacin da
Imam baya salla su samu damar ganawa, ya dage sai
suka ayyana masa lokacin da zai zo don ya yiwa Imam
(AS) hidimar, sai ya ci sa'a ya samu sa'a Imam (AS)
na zaune a wajen da ya saba yin salla yana xan
tunani....51
52 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 818, Hadisi na 5.
Faxuwar rana
Aba Salt, sananne ne kan soyayyar Imam Ridha
(AS), ya kasance yana tare da Imam tun shekarun
farkon rayuwar sa, ya rubuta abubuwan da suna faru
dangane da wafatin Imam (AS) a wani littafi da ake
kira [wafatu Ridha]. Yana cewa: Imam Ridha (AS) ya
gaya min cewa: ya Aba Salt! Gobe zan je wajen
wancen shu'umin, idan ka ga na fito kaina babu komai
(ba rawani a kai), ka yi min magana amsa, amman
idan na fito kamar yadda kaina yake kaina a suturce,
kada ka yi min magana.
... lokacin asuba ta yi, sai ya sanya kayan sa, ya
zauna daidai inda yake ibada yana xan jira, a daidai
wannan lokacin da yake xan jira kwatsam sai ga xan
Aiken Ma'amun ya shigo, ya ce: shugaban ka na kiran
ka. Imam (AS) ya sanya takalmin sa, ya yafa hiramin
sa ya sanya turare, ya fara tafiya ina bin sa a baya har
saida ya shiga wajen Ma'amun, a gefen Ma'amun
akwai ruwan xan itacen da ake kira angur da na kayan
marmari, an xan sha wani kaso daga ciki, an rage wani
kaxan a ciki, yana ganin shigowar Imam (AS) sai ya
miqe tsaye da sunan girmamawa ya rungume Imam
(AS) ya sumbace shi Imam ya zauna a gefen sa,
wannan ragowar lemon angur xin da ke gefe ya xakko
ya baiwa Imam ya ce: ya xan Manzon Allah! ban tava
ganin angur mai kyan wannan ba a rayuwa ta. Imam
(AS) ya ce masa: kai wannan wane irin angur ne mai
kyau haka da yake daga al'janna, Ma'amun ya ce xan
sha ka ji: ina neman afuwa ba sai na sha ba, Ma'amun
ya ce: dole ka sha fa, sabida me bazaka sha ba? ba
mamaki kana min wata mummunar fassara ne shi ya
hana ka ci, sai ya xauki angur xin ya kawo kusa da
shi, bayan yan sakanni sai Imam ya xan xauki wasu ya
ci, ya sanya guda uku a bakin sa, kawai sai ya yar da
wanda ya rage a bakin sa ya tafi. Ma'amun ya
tambaya: ina zaka tafi? Ya ce: ka san inda ka aika ni,
ya lulluve kan sa da abaya ya fito.
Anba Salt ya ce: ban yi masa maganar komai ba
har saida ya shiga gida, ya ce: ku kulle qofofi, kada ku
baiwa kowa dama ya shigo, aka rufe qofofi, Imam
(AS) ya kwanta kan gadon da yake bacci, ban daxe
cikin gidan ba ina cike da damuwa da baqin ciki ina
tsaye kawai sai ido na ya cika da haske sai na ga ashe
wani saurayi ne ya zo, mai kyan kallo mai kwantacce
kuma kyakkyawan gashin kai, wanda ban tava ganin
mai kama da Imam Ridha (AS) kamar sa ba, ina ganin
sa ban yi komai sai na tambaye shi: ranka ya daxe,
dukkan qofifi a rufe suke, ta ina ka shigo? Ya ce:
yanzu haka daga Madina aka kawo ni nan wajen, a
yadda qofofin suke a rufe ka shigo. Na tambaya:
wanene kai? Ya ce: ni hujjar Allah ne a kan ka ya Aba
Salt, nine Muhammad xan Ali, sannan ya tafi wajen
baban shi ya nufi xakin da mahaifin na sa ke ciki ya ce
min mu shiga tare. Idanun sa na kallon mahaifin sa
Ridha (AS), wuf ya rungume baban sa ya sanya
hannun sa a wuyan baban sa, ya sumbaci goshin sa, ya
kwantar da shi kan shimfixa, yana cikin kwantar da
mahaifin nashi yana sumbatar sa, sai ya gaya masa
wata magana a hankali wacce ban fahimci mai ya ce
masa ba, ina ganin levven Imam Ridha (AS) farare qal
har sun fi dusar qanqara haske ... bayan wani xan
lokacin sai Imam (AS) ya bar duniya.
A qarshe dai, Imam Ali xan Musa ar Rdha (AS)
ya bar duniya yana shekara 55, a ranar juma'a qarsehn
watan safar 129AH ta dalilin guba a Xus aka
shihadantar da shi. An yi jana'izar sa (AS) a gidan
Hamid xan Qahxaba Xa'iy a qauyen Sana,bad – qauye
daga cikin qauyukan Nuqan a yankin Xus – ana binne
shi a can.59
58 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 8, shafi na 89, Hadisi na 89, da Littafi na 2, Shafi na 245. Al'irshad, shafi na 804.
Saqo zuwa ga shiawa
Sayyid Abdulaziz Hasani, daga tsatson Imam
Hassan al-mujtaba (AS) yake, yana daga cikin yaran
Imam (AS), mafiya yawancin ruwayoyin da ya kawo a
rayuwar sa daga Imasm Ali Al'hadi (AS) da mahaifin
sa ne, yana saurayi ya hidimtawa Imam Ridha (AS).
Imam (AS) ya bashi wasu saqonni ya roqe shi cewa ya
isarwa da Shia wannan saqon, saqon shine:
Ya Abdulazim! Ka isarwa da abokaina sallama
ta, ka gaya musu kada su baiwa shexan dama a
rayuwar su, su yi riqo da faxin gaskiya da riqon
amana. Ka yi musu wasiyya cewa su kawar da duk
wani abu da zai vata musu lokaci cikin rayuwar su (su
guji aikin banza).
Su ringa ziyartar junan su, wannan zai qara musu
alaqa tsakanin juna, kada su rarraba a tsakanin su; ina
maka ransuwa duk wanda ya sava da wannan zan yi
fushi da shi, zan roqar masa Allah ya haxa shi da
azaba mai tsanani tun a nan duniya da lahira, sannan
za a tashe shi cikin masu riya.
Ka gaya musu cewa Allah, yana jin qan masu
kyautata aiki daga cikin su, zai azabtar da waxanda ke
munana aiki a cikin su, duk wanda ya sake ya
munanawa 'yan uwan sa ko ya yi tarayya da wani don
cutyar da wasu ya sani cewa ni ya cutar koda kuwa
niyyar mummuna ya samu wani ya yi, duk wannan ya
yi wannan ya sani cewa Allah ba zai yafe masa ba har
sai lokacin da ya tuba ya daina wannan aikin amman
idan bai tuba ba, zaia cire masa Imani daga zuciyar sa
sannan a cire shi daga cikin wilayar mu, ba zai samu
rabon komai daga wilayar mu ba, ina neman tsarin
Allah da samun afkuwar wannan cikin shiar mu.54
54 Al'ikhtisas 247.
Falalar ziyarar sa da lokacin ziyarar
Ruwayoyi rubutattu masu yawan gaske daga
Manzo (SAW) da Ma'asumai (AS) game da ladan
ziyarar Imam Ridha (AS), masu ruwaya na kiran
wannan ruwayar da ruwayar Imami baqon Khurasan.
Idan muka kalli tarin ruwayoyin da suka zo suna
magana kan ladan ziyarar Ma'asumai (AS), zamu gane
cewa mafiya yawan ruwayoyin na kwaxaitarwa kan
ziyarar su (AS), daga ruwayoyin ziyarar Imam
Hussain (AS), wacce ta haxa da ziyarar Imam Ridha
(AS). Wannan ruwaya ta bayyana cewa idan mai
ziyara ya ziyarci haramin Ridha (AS) sannan ya san
haqqin Imam xin sannan ya yi biyayya ga Imam xin,
Allah zai bashi lada mai tarin yawa sabida wannan
zaiyarar (sama da ladan ziyarori).
Wasu ladan na nufin: yafe laifuffuka na baya da
na gaba, ladan shahidan Badar, ladan hajji miliyan
xaya, shiga al'janna, biyan buqatu, sanna zai samu
alherai uku a ranar qiyama:
Lokacin da za a bada littafi a daga ko a hagu,
lokacin hawa siraxi da lokacin auna ayyuka.
Wani mutum ya tambayi Imam Jawad (AS) cewa
ya yi aikin hajjin sa na wajibi, sannan yana son sake
yin na biyu, shin zai je hajji ne ko kuma ya je ziyarar
Imam Ridha (AS)?
Imam Jawad ya bashi amsa cewa: ya fi cancanta
ka je Khurasan ka isar min da gaisuwa wajen Baba na
Abul Hassan, sannan ka yi ziyara sannan zai fi kyau
ka yi wannan ziyarar cikin Rajab ... .
A wata ruwayar daban Imam Jawadya ce da
Ayyub xan Nuhu: duk wanda ya je ziyara kabarin
mahaifi na, Allah zai yafe masa zunubansa sababbi da
tsofaffi, sannan ranar al'qiyama, membarin waxanda
suka ziyarci baba na na daura da na Manzo (SAW)
sannan za a tsame su daga shiga cikin hisabi.
Lokacin da Ayyub xan Nuh ya ji wannan magana
ta Imami na tara (AS), shekara mai zuwa bayan kufa
sai ya tafi Khurasan, ya ziyarci Imam Ridha (AS),
wani cikin shia ya gan shi, bayan ya ji wannan ruwaya
daga bakin sa, ya tambaye shi ya ce: Ayyub! Sabida
me ka zo nan? Ayyub ya bada amsa cewa: na zo nan
ne na hau membari!
Ya ce: mafi muhimmanci kuma mafi dacewar
lokacin ziyarar Imam Ridha (AS) wajan Rajab ne,
ishirn da uk Zulqida da ishirin da biyar Zulqida (ranar
naxe qasa) ce.55
55 Kamiluz ziyarat, shafi na 208-201. Mafatuhul jinan, vangaren ayyukan watanni.
Mai aminar da Barewa
Shahid Saduq (912AH) xaya daga manyan
malaman shia cikin qarni na huxu. Ya rubuta littafi da
ya kevanci Imami na takwas Imam Ridha (AS) da
sunan [uyunu akhbarur Ridha (AS)] wanda yake da
adadi litattafai biyu. Vangaren qarshe na wannan
littafin ya yi magana ne kawai kan karamomi da
mu'ujizozin da suka bayyana dangane da Imam (AS)
bayan shahadar sa ta vangaren qabarin sa mai tsarki,
cikin wannan vangaren ya kawo abubuwa sha uku da
ya yi bayanin su kamar haka:
Hakim Razi shima shia ne da ya ke kula da
haram xin Imam Ridha (AS), Mizban da Abu Mansur
xan Abdurrazaq – yana cikin manya-manyan Xus.
Abu Mansur ya naqalto daga Hakin Razi cewa:
ka saurara da kyau ka ji! Zan gaya maka wani matsayi
na wannan wajen ziyarar, a shekaru na na yarinta ban
san komai ba, ina baiwa masu ziyarar wannan haramin
taimakon da zan iya na rage musu wahala, ina qulle
musu kayan su na ziyara, na kai musu dukuyar su inda
suke so, wani lokacin ina tafiya farauta, wata rana na
haxu da wata barewa a Mash'had, na shuna mata karen
farauta ta, ya bita da gudu wanda ya tilasta mata har
saida ta shiga filin Haram, sai barewar ta tsaya karen
ma ya tsaya a daura da ita basa motsin komai, duk
yadda na kora karen baya iya motsawa zuwa wajen ta,
sai barewar ta tafi zuwa wani vangare na gefen
haramin don vuya, karen ya tsaya bai bita ya shiga ba.
Sai da kaina na shiga wajen barewar, banga
barewar ba, Abu Nasr Qari na zaune a wajen ya ga
duk abunda ke faruwa, sai na tambaye shi: barewar da
ta shiga nan yanzu-yanzu ina ta tafi ne haka? Ya ce:
barewa! Ban ganta ba, ga alamun barewa amman babu
ita. Sai na shiga haram wajen Imam (AS) na tuba, na
kuma yi alqawarin cewa ba zan qara cutar da duk
wanda ya shigo ziyara haram ba ko wanene har
qarshen rayuwa ta kai zan ma kyautata masa ne
maimakon munanawa, daga wannan lokacin duk
sanda wata matsala ta taso min, ina zuwa nan ne na yi
ziyara, sanna na roqi Allah buqatu na, kuma duk sanda
na yi haka Allah na biya min buqatu na. Yanzu haka
sau biyu a Mash'ahd ina roqon Allah sanda aka
kwantar da wani yaro a Mash'had yana tashi da yardar
Allah, a tabbace yake har yanzu ana samun biyan
buqata a wajen matuqar an roqi Allah buqatar a
wannan wajen.56
55 Uyunu Akhbarur Ridha (AS), littafi na 2, shafi na 215, Hadisi na 88.
Ladubban ziyara
Mustahabbi ne lokacin ziyarar qabarin Imam
Ridha (AS) a Mash'had, kafin a fito daga gida a yi
wanka a sanya kaya mafi kyau. Ana son wanda ya fito
daga gida zuwa Haram tun daga fitowar sa kada bakin
sa ya shagala da ambaton Allah cikin jin daxi da
nishaxantuwa, ya dinga qananan taku yana cewa:
Allahu akbar, la'ilaha ilallah, subhanallahi wal
hamdu lillahi, daga cikin qananan ziyarorin sa (AS)
da suka zo daga xansa Imam Jawad (AS), akwai
kevantaccen salati, wanda ake son shima lokacin da
aka kusanto qabarin Imam (AS) a dinga karanta shi
kamar haka:
[ya Allah ka yi salati ga Imam Ali xan Musa
Ridha (AS), imami mai taqawa (tsoron Allah) da
gudun duniya (zuhudu) kuma hujjar ka kan dukkan
wanda ke bayan qasa da wanda ke cikin qabar, mai
gaskiya shahidi, slati mai yawa cikakke tsarkakke mai
saduwa mai maimaituwa mai bin juna kamar yadda ka
fifita wanda ya yi salati ga waliyyan ka!51
57 Kamiluz ziyarat, shafi na 809, hadisi na 8 da na 2.
Inda aka cirato wannan littafi
2. Ihtijaj, na Ahmad xan Ali xan Abi Xalib
Xabrisi, waxanda suka buqa, mabugar
Nu'uman Najafi, 2366M
1. Akhbaru Isfahan, Hafiz abu Nu'aim Isfahani
(wanda ya mutu shekara ta 492AH), Baril –
London, 2394M.
9. Al'ikhtisas na Shekhul Mufid (wanda ya mutu
shekara ta 429AH), Tahqiqin: Ali akbar
Gaffari, cibiyar yaxa musulunci ta Qum, bugu
na huxu 2424AH.
4. Al'irshad fi ma'arifatu Huajullah alal Ibad, Abu
Abdullahi Muhammad xan Nu'uman Akbari
Bagdadi wanda aka fi sani da Shekhul Mufid
(wanda ya mutu shekara ta 429AH) tahqiqi da
yaxawa, cibiyar yaxa musulunci ta qum, bugu
na xaya 2429AH.
5. A'alamul wara bi a'a lamul huda, Fadl xan
Hassan Xabrisi, cibiyar Ahlulbait (AS),
2421AH Qum.
6. Al'amali na Abu Jafar Muhammad xan Ali Xan
Hussain Xan Babuya, Qummi wanda aka fi
sani da Sheikh Saduq (wanda ya mutu shekara
ta 912AH), tahqiqi da yaxawa: Cibiyar Bi'isa,
Qum, bugun Farko 2421AH.
1. Amali na shekh Xusi, Abu Ja'afar Muhammad
xan Hassan wanda aka fi sani da Xusi (wanda
ya mutu shekara ta 462AH), Tahqiq: cibiyar
Bi'isa, darus saqafa, Qum, bugun farko
2424AH.
1. Biharul Anwar wanda ya cika da ruwayoyin
Imamai (AS), na Muhammad Baqir Majlisi
(wanda ya mutu shekara ta 2222AH), tahqiqi,
cibiyar Wafa, Beirut, bugu na biyu, 2429AH.
3. Basairu darajat, Abu Ja'afar Muhammad xan
hassan Saffa, Qummi (wanda ya mutu shekara
ta 132AH), labirarin Ayatullahi Mar'ashin
Najafi, Qum, bugu na farko 2424AH.
22. Tarihin xabari, tarihul umam wal muluk,
Muhammad xan Hariri Xabari, Beirut, cibiyar
ilimi, 2429AH.
22. Tarikhul kulafa'a, Abdurrahmanus Suyuxi,
tahqiqi Abdullahi Mas'ud, Dimashq, Darul
qalamul arabi, 2422AH.
21. Tarikhu mawalid (wanda aka buqa a Nafisa),
Xabrisi (wanda ya mutu shekara ta 541AH),
labirarin Ayatullahi Mar'ashin Najafi, Qum,
bugu na farko 2426AH.
29. Tarikhu Ya'aqubi, Ahmad xan Ya'aqub, cibiyar
yada al'adun Ahlulbait (AS)-Qum.
24. Tarihin ibni Khaldun (wanda ya mutu shekara
ta 121AH), Daru ihya'u turasul Arabi, Beirut,
Lebanon.
25. Tahzibul Ahkam fi shahril Muqanna'ah, Abu
Ja'afar Muhammad Hassan Wanda aka sani da
Shiekh Xusi (wanda ya mutu shekara ta
462AH), darut ta'arif, Beirut-Lebanon.
26. Attauhid, Abu Ja'afar xan Muhammad xan Ali
xan Hussain xan Babuyah qummi wanda aka fi
sani da Sheikh Saduq (wanda ya mutu shekara
ta 912AH), 2931HQ, Tehran, Maktabin sa.
21. Hayatu Imam Ridha (AS), Baqir Sharif
al'qarshi, wanda ya yaxa Sa'ad xan Jabir, Qum.
21. Hayatu Imam Jawad (AS), Baqir Sharif
al'qarshi, wanda ya yaxa Sa'ad xan Jabir, Qum.
23. Al'khara'ij wal jara'ih, Saeed xan Habatullah
Rawandi (shugaban addini a rawandi) (wanda
ya mutu shekara ta 519AH), tahqiq da yaxawa,
Mu'assasar Imam Kahdi (AF), Qum, 2423AH,
bugun farko.
12. Al'Khisal na Abu Jafar Muhammad xan Ali
Xan Hussain Xan Babuya, Qummi wanda aka
fi sani da Sheikh Saduq (wanda ya mutu
shekara ta 912AH), tahqiqi da yaxawa: cibiyar
yaxa musulunci, Qum, bugu na huxu 2424AH.
12. Rijalul Barqi, Ahmad xan Muhammad Barqi,
tahqiqi Jawad Qiyumi, yaxawar Qiyum,
2423AH.
11. Rijalux xusi, Abu Ja'afar Muhammad Hassan
Wanda aka sani da Shiekh Xusi (wanda ya
mutu shekara ta 462AH), tahqiqi Jawad
Qiyumi, cibiyar yaxa musulunci, Qum, bugu na
xaya 2425AH.
19. Rijalul Kisshi (ikhtara ma'arifatur rijal), Abu
Ja'afar Muhammad Hassan Wanda aka sani da
Shiekh Xusi (wanda ya mutu shekara ta
462AH), tahqiq Mahdi Raja'i, cibiyar Ahlulbait
(AS) qum Bugu na xaya 2424AH.
14. Rijalun najashi (fihrs asma'a musannadash
shia), Ahmad xan Ali Najashi (wanda ya mutu
shekara ta 452AH), darul adwa'a – Beirut,
bugu na farko 2421AH.
15. Siyar a'alamun Nubala'a, Muhammad Ahmad
Zahabi, tahqiq Shu'aibul Arnuwax, baitul
afkarud duwaliyya, Beirut.
16. Uyunu akhbarur Ridha (AS), Abu Jafar
Muhammad xan Ali Xan Hussain Xan Babuya,
Qummi wanda aka fi sani da Sheikh Saduq
(wanda ya mutu shekara ta 912AH),
manshuratul a'alami, Tehran.
11. Uyunu akhbarur Ridha (AS), (mai fassara) Abu
Jafar Muhammad xan Ali Xan Hussain Xan
Babuya, Qummi wanda aka fi sani da Sheikh
Saduq (wanda ya mutu shekara ta 912AH),
fassarar, Gaffari dea Mustafid, yaxawa saduq,
Tehran.
11. Al'gaiba, Abu Ja'afar Muhammad Hassan
Wanda aka sani da Shiekh Xusi (wanda ya
mutu shekara ta 462AH), 2915HS, Qum,
maktabatu basiri.
13. Qurbul Isnad, Abudllahi xan Ja'afar Himiri
Qummi (wanda ya mutu shekara ta 924AH),
tahqiq da yaxawa, mu'assasar raya alamun
Ahlulbait (AS), Qum, bugu na farko 2429AH.
92. Al'kafi, Abu Ja'afar Siqatul Islam, Muhammad
xan Ya'aqub Kulaini (wanda ya mutu shekara
ta 913AH), tahqiqi, Ali akbar Gaffari, darul
kutubul Islamiyya, Tehran.
92. Kamaluz ziyarat, Ja'afar xan muhammad xad
kuluye (wanda ya mutu shekara ta 961AH),
tahaqiqi, Jawad Qayyumi, yaxawar faqaha,
Qim, bugu na farko, 2421AH.
91. Kashful gumma fi ma'arifattul Ayimma (AS)
Aliyyu xan Musa arbali, tahaqiqi Hashimur
Rasulul mah'lati 2422AH darul kitabul islami.
99. Alkamil fit tarikh, Aliyyu xan Abul Karami
wanda aka fi sani da Xan Asir, Daru Sadir,
Beirut 2915HQ daidai da 2365AH
94. Littafin Malla yahdhuruhul faqih, Abu Jafar
Muhammad xan Ali Xan Hussain Xan Babuya,
Qummi wanda aka fi sani da Sheikh Saduq
(wanda ya mutu shekara ta 912AH), tahqiqi,
Ali Akbar gaffari, muassasar yada musulunci,
Qum, bugu na biyu.
95. Al'mujtaba minar du'a'ul mujtaba, sayyid
Radiyyud din Ali xan Musa xan Xawus
664AH, tahqiqin safaud din al'basri.
96. Alkamil fittarikh, Ali xan Abi Karam, wanda
aka fi sani da xan asir, Daru sadir, Beirut
Lebanon 2915AH = 2365HS.
91. Musnadul Imamur Ridha (AS), Azizullahu
Axardi, yaxawar kungardeh Imam Ridha (AS),
garin Ridhawi, 2426AH, Mash'had.
91. Misbahul mutahajjid, Abu Ja'afar Muhammad
Hassan Wanda aka sani da Shiekh Xusi (wanda
ya mutu shekara ta 462AH), tahqiqin ali asgar
mirwarid, muassasar fiqihun shia, Beirut,
Lebanon.
93. Ma'anil akhbar, Sheikh Saduq, Abu Jafar
Muhammad xan Ali Xan Hussain Xan Babuya,
Qummi wanda aka fi sani da Sheikh Saduq
(wanda ya mutu shekara ta 912AH), tahqiqi,
Ali Akbar gaffari, yaxawa jami'atul mudarrisin
hauzar ilimi ta Qum, 2962HS.
42. Maqatilux xalibin, Aliyyu xan Hussain, abul
faraj Isfahani, tahqiqin Ahmad sugar, Qum,
sharifur radhi, 2424AH.
42. Manaqibu a'li abi Xalib (manaqin na ibn Shahr
Ashub), Rashiduddin Muhammad xan Ali xan
Shar Ashub, Mazandarani (wanda ya mutu
shekara ta 511AH), mabugar ilmiyya, Qum.
41. Al'muntazim fi tarihil muluk wal umam,
Abdurrahman xan Ali wanda aka fi sani da
Jauzi wanda ya mutu shekara ta 531AH, darul
kutubul ilmiyya, Beirut, Lebanon.
49. Wasa'ilush shia, ila tahsili masa'ilush shari'a,
Muhammad xan Hassan wanda aka fi sani da
sheikh Harr Amili, wanda ya mutu shekara ta
2224AH, mu'assasar Ahlulbait (AS) li ihya'it
turas 2299-2224AH, Qum.