80
Hasken Karatu Littafi don Makarantun Firamare na 2 Adamu A. Kiyawa Tijjani S. Almajir Halima A. Îangambo Sani L. Abdurrahman Hausa prel 2.indd 1 5/13/14 5:00 PM

Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 2.pdf · Wasan Tarbiyya Mai Naso 57 Darussan Cikin Wasan 61 Tamboyoyi 61 Jagora 62 16 Tatsuniya 63

  • Upload
    others

  • View
    109

  • Download
    43

Embed Size (px)

Citation preview

i

Hasken KaratuLittafi don Makarantun Firamare na 2

Adamu A. KiyawaTijjani S. AlmajirHalima A. ÎangamboSani L. Abdurrahman

Hausa prel 2.indd 1 5/13/14 5:00 PM

ii

Learn Africa PlcFelix Iwerebon House52 Obå Åkrån ÅvenueP.M.B. 21036Ikejå, Lågos StåteTel. (01) 7403967, 4393111Fåx (01) 4964370E-måil: [email protected]: www.learnafricaplc.com

Åreå offices ånd brånchesÅbujå, Ajegunle, Åkure, Benin, Enugu, Ibådån, Ilorin, Jos, Kåno, Onitsha, Owerri, Port-Harcourt, Zåriå ånd representåtives throughout Nigeriå

Åll rights reserved. No pårt of this publicåtion måy be reproduced, stored in å retrievål system, or trånsmitted in åny form or by åny meåns, electronic, mechånicål, photocopying or otherwise, without the prior permission of Learn Africå Plc.

© Learn Africa Plc 2014First published 2014

ISBN 978 978 925 100 1

Illustråtions by Franklin Oyekusibe

Hausa prel 2.indd 2 5/13/14 5:00 PM

iii

Babi Shafi1 Karatu da Rubutu 1 Ha∂aKalma 1 KalmomiMasuGa∫aBiyu 2

KalmomiMasuGa∫aUku 2 KalmomiMasuGa∫aHu∂u 3 Tambayoyi 3

2 Almara I 6 LabarinSarkinZafidaSarkinBau∂iya 6 Tambayoyi 7 Labarin Wani Mariri 7 Tambayoyi 9 Jagora 9

3 Ta∂i 10 Tambayoyi 11 Jagora 11

4 Kacici-kacici 12 Ma’anar Kacici-kacici 12 Tambayoyi 14 Jagora 15

Abubuwan da ke Ciki

Hausa prel 2.indd 3 5/13/14 5:00 PM

iv

5 Tausayi 16 Tausaya wa Gajiyayyu 16 Tausaya wa Dabbobi da Tsuntsaye 17 Tambayoyi 18 Jagora 18

6 Sunayen Abubuwa 19 Sunayen Gargajiya 19 Sunayen Yanka 19 Sunayen Tsuntsaye 20 Tambayoyi 20 Jagora 21

7 Kalmomin Aiki 22 Kalmomin Aiki 22 Aikata Aikin Kalma 22 Tantance Kalmomin Aiki 23 Tambayoyi 24 Jagora 25

8 Tsaftar Muhalli 26 Mene ne Muhalli? 26 Tsaftace Muhalli 26 Misalan Tsaftar Muhalli 26 Tambayoyi 32

9 Karatu da Rubutu 33 KarantaWa∂annanJumloli 33 Rubuta Wadannan Jumloli 34 Jagora 36

Hausa prel 2.indd 4 5/13/14 5:00 PM

v

10 WasanninMotsaJiki 37 Wasan Burum-burum 37 In Gero Ya Nuna 38 Jagora 39 Wasannin Yara 39 Wasannin Yara Maza 40 Jemage 41 Wasannin Yara Mata 42 Ayye Yaraye 43 Jagora 44

11 Gaisuwar na Gaba 45 Gaisuwar na Gaba 45 Jagora 46

12 Almara II 47 Kura da Akuya da Ciyawa 47 Tambayoyi 48 Malami da Karuwa da Sarkin Baka 48 Tambayoyi 49

13 KarinMaganadaMaganganunAzanci 50 Ma’anar Karin Magana 50 Ma’anar Azanci 50 Misalan Karin Magana 50 Kakkarya Harshe 51 Misalan Kakkarya Harshe 51 Jagora 53

14 idaya 54 idaya 54

Hausa prel 2.indd 5 5/13/14 5:00 PM

vi

Tambayoyi 55 Jagora 56

15 WasanKwaikwayo 57 Ma’anar Wasan Kwaikwayo 57 Misalan Wasan Kwaikwayo 57 Wasan Tarbiyya Mai Naso 57 Darussan Cikin Wasan 61 Tamboyoyi 61 Jagora 62

16 Tatsuniya 63 ‘Yar Bora da ‘Yar Mowa 63 Darussan da ke Cikin Tatsuniyar 67 Tambayoyi 68 Jagora 68

17 Kulawa da Iyali 69 Tambayoyi 70 Jagora 70

18 Karikitan Cikin Gida 71 Karikitan Tsakar Gida 71 Karikitan Îaki 72 Tambayoyi 72 Jagora 72

Hausa prel 2.indd 6 5/13/14 5:00 PM

vii

Gabatarwa

An rubuta jerin wannan littatafi guda shida mai suna Hasken Karatudonakoyawa∂alibai

namakarantunfiramaredagashekarata∂ayazuwatashida.Anrubutadarussanda

zaakoyartabinsabuwarmanhajarHausawaddaHukumarBincikedaHa∫akaIlimita

Nijeriya(NERDC)tashirya.Darussandakecikinwa∂annanlitattafaisunshafifannonin

nahawudaadabidaal’adunHausawa.Anyiamfanidahanyoyisau˚a˚awajentaimakon

koyardawa∂annanlitattafaicikinsau˚i.Wa∂annanhanyoyisunha∂ada:

1 Akwai shiryayyun tambayoyi, masu sa a karanta darasi, a fahimce shi sosai kafin

bayar da amsoshin.

2 Akwaizanenhotuna,daalamominrubutu,adukwurindayakamata,don˚ara

armasa karatu da ilimantarwa, musamman don gane abubuwan, da ake bayani

sosai.

3 Akwai jagora a karshen kowane babi, don baiwa malami haske game da yadda

zaigudanardakoyarwa,dakuma˚arinhaskecikinwasulitattafan.

Anafatanidan∂alibiyagamawa∂annanlitattafaigudashida,tozaisamicikakkiyar

shimfi∂atafahimtarfanninHausa.Donhaka,muhimmiyarmanufarwannanlittafi,ita

cesamarwamalamaiabubuwandazasukoyarcikinsau˚i,sukuma∂alibaisuga

darussan da ake koya masu a zahiri. Allah ya taimake mu, amin.

Hausa prel 2.indd 7 5/13/14 5:00 PM

viii

Hausa prel 2.indd 8 5/13/14 5:00 PM

1

Babi na 1

Karatu da Rubutu

Ha∂a KalmaAna iya samar da kalmomi a Hausa ta hanyar ha∂a ba˚a˚e da wasula. A littafi na ∂aya, an nuna mana yadda ake samar da gajerun kalmomi masu ga∫a ∂aya. Bari mu ˚ara kawo wasu misalan da aka ba mu a can baya.

c + i = ci

b + a = ba

k + a + n = kan

m + a + i = mai

k + a + u = kau

A wannan darasi, za mu koyi yadda ake samar da kalmomi masu ga∫a biyu da uku da ma fiye.

Hausa Pry 2.indd 1 5/13/14 5:00 PM

2

1. Kalmomi Masu Ga∫a Biyu: Akan samar da kalmomi masu ga∫a biyu ta hanyoyi kamar haka:

ka + re = kare

ma + ge = mage

bi + yar = biyar

gi + da = gida

mi + yau = miyau

2. Kalmomi Masu Ga∫a Uku: Akan samar da kalmomi masu ga∫a uku kamar haka:

ga + fi + ya = gafiya

ku + je + ra = kujera

ta + kar + da = takarda

far + tan + ya = fartanya

ma + la + mai = malamai

Hausa Pry 2.indd 2 5/13/14 5:00 PM

3

3. Kalmomi Masu Ga∫a Hu∂u: Akan samar da kalmomi masu ga∫a hu∂u kamar haka:

ma + ka + ran + ta = makaranta

tat + ta + ba + ra = tattabara

ma + ka + ma + shi = makamashi

al + ˚a + la + mi = al˚alami

ba + la + ra + be = balarabe

Tambayoyi: Cike Gurbi 1

1. h + + u = hau

a) o b) e c) a d) u

+ a + n = can

a) e b) n c) m d) c

k + a + = kai

a) i b) n c) a d) u

Hausa Pry 2.indd 3 5/13/14 5:00 PM

4

2. ∂a + = ∂aki

a) ku b) na c) ki d) sa

han + ya =

a) kanya b) manya c) hanya d) yanka

shi + = shida

a) da b) ga c) ka d) shago

3. + ka + = shinkafa

a) tan b) shin c) shan d) san sa + bu + lu =

a) sakata b) sabara c) sabulu d) sukari

ma + + ra = madara a) sa b) ka c) ha d) da

Hausa Pry 2.indd 4 5/13/14 5:00 PM

5

Tambayoyi: Cike Gurbi 2

1. ka + = a) li b) re c) lo d) du 2. + je + ra = a) ki b) la c) si d) ku

3. + + ya = a) gar + tan b) ja + ta c) far + tan d) far + gan 4. + ka + ma + shi = a) ma b) al c) ta d) ga

5. ba + la + + be = a) ya b) ta c) ra d) sa

Hausa Pry 2.indd 5 5/13/14 5:00 PM

6

Babi na 2

Almara I

Labarin Sarkin Zafi da Sarkin Bau∂iyaWata rana tafiya ta kama Sarkin Zafi da Sarkin Bau∂iya zuwa wani gari. Suna cikin tafiya sai hadari ya ha∂o. Sai Sarkin Zafi ya ce da Sarkin Bau∂iya, ‘Ina dabara?’

Hausa Pry 2.indd 6 5/13/14 5:00 PM

7

Sarkin Bau∂iya ya ce, ‘Kowa tasa ta fisshe shi’. Kafin ruwa ya sauko, sai Sarkin Zafi ya yi sauri ya zaro lauje, ya yanki ciyawa, ya tufka ta, ya gina bukka, ya shige ciki. Sarkin Bau∂iya yana kallonsa, har ruwa ya sauko. Sarkin Zafi ya ce, ‘To yau na ga ta bau∂iyar taka.’ Sarkin Bau∂iya ya shiga yin bau∂iyar tasa tsakanin ∂igo da ∂igon ruwa, har aka yi ruwa aka ∂auke ko ∂igo ∂aya bai sauka a kansa ba. Bayan da aka ∂auke ruwa, sai Sarkin Zafi ya fito bakin bukkarsa. Bai ankara ba sai santsi ya kwashe shi, ya yi sama. Sarkin Bau∂iya ya ce, ‘To yau ina zafin naka da ake fa∂a?’Kafin Sarkin Zafi ya kai ˚asa, sai ya yi farat, ya zaro lauje, ya yanki kaba, ya sa˚a tabarma, ya shimfi∂a ta, ya fa∂a a kai.

Tambayoyi Za∫i kalmar da ta dace a cike wa∂annan gurabu. 1. Suna cikin tafiya sai ______ ya ha∂o. a) ruwa b) hadari c) iska d) zafi2. To yau na ga ta ______ taka. a) baudiyar b) dabarar c) gaggawar d) wayon3. Sarkin zafi ya fito bakin _________. a) ∂akinsa b) shagansa c) bukkarsa d) ajinsa

Labarin Wani MaririWani mariri, ya tafi shan ruwa a tafki. Sai ya ga inuwarsa a cikin

Hausa Pry 2.indd 7 5/13/14 5:00 PM

8

ruwa, ya ce, ‘Ashe haka nake da kyau! Ban yi tsammani duk dajin nan akwai mai ˚aho kamata ba. Ga tsawo, ga kyau, ga tsini. Amma kash! Kafafuna sun yi min ka∂an. Da sun yi kyawun ˚ahona, da ba haka ba’. Bai sani ba, mafarauta sun fito da karnukansu. Da jin motsi sai ya ∂aga kai, yana sauraro. Sai suka hango ˚ahonsa, suka sakar masa karnuka. Mariri ya zura a guje, karnuka suna biye da shi.

Nan da nan ˚afafun da ya raina suka yi masa rana, ya bar karnuka baya nesa, ya shiga cikin kurmi. ahon da yake yabo, ya sar˚afe cikin duhun kurmi. Ya yi, ya yi, ya fita ya kasa, har karnuka suka zo suka kama shi. Masu farauta suka zo suka buge suka yanka.

Hausa Pry 2.indd 8 5/13/14 5:00 PM

9

TambayoyiCike guraben da aka bada da kalmomin da suke biye. 1. Mariri ya tafi shan ruwa a ____________.2. Ga tsawo ga kyau ga _______________.3. Mafarauta sun fito da _______________.4. Kafafun da ya __________ suka yi masa rana.5. Ya shiga cikin ______. a) kurmi b) karnu kansu c) raina d) tafki e) tsini

Jagora

Malami tare da ∂alibai, su fito da darussan da ke cikin wa∂annan labarai na sama, da kuma na wasu labaran da za a kawo a cikin aji.

Hausa Pry 2.indd 9 5/13/14 5:00 PM

10

Babi na 3

Ta∂i

Samir, Sassan jiki suna da suna? Ee, kowanne yana da sunansa.Wanne da wanne ne a fuska? Akwai idanu da hanci da baki.Idanunka guda nawa ne? Idanuna guda biyu ne.Ina suke? Ga ∂aya a dama, ∂aya kuma a hagu. Bakinka ma guda biyu ne? A’a, kunne ne guda biyu.Baki ∂aya ne ke nan? Ee, sai dai le∫∫a guda biyu.

Hausa Pry 2.indd 10 5/13/14 5:00 PM

11

Hussaina, hannuwanki nawa ne? Hannuwana guda biyu ne.afafuwa fa? afafuwa ma guda biyu ne.Da me kike tafiya? Da ˚afata nake tafiya.Wa∂anne ne sauran sassan jiki? Akwai ciki da baya da goshi

da sauransu.

Tambayoyi1. Kawuna nawa mutum yake da su?2. Kawo sassa uku a jikin kan mutum?3. Yatsu nawa ne a hannun mutum?4. Shin ana amfani da ˚afa wajen ∂aukar abu?5. Wane sashen jiki ake amfani da shi wajen jin magana?

Jagora

Malami ya samar da zanen hoton sassan jikin mutum, sannan ya sa yara su bayyana kowane sashe da amfaninsa. Malami ya sa yara su bayyana sassan jikinsu ta hanyar nunawa.

Hausa Pry 2.indd 11 5/13/14 5:00 PM

12

Babi na 4

Kacici-kacici

Ma’anar Kacici-kaciciKacici-kacici tambayoyi ne na wasa ̊ wa˚walwa. Ana yin tunani don ba da amsar da ta dace kai tsaye. Kacici-kacici wasa ne da yara suka fi yi musamman da dare a lokacin yin tatsuniya ko a dandali. Wata rana da yamma, Samir da Samira sun je gidan su Hassan da Hussaina domin wasa. Sai Hassan ya ce su yi wasan kacici-kacici. Sai Samir ya fara, sauran kuma suna

Hausa Pry 2.indd 12 5/13/14 5:00 PM

13

amsawa kamar haka: Samir : ulin ˚ulifita.Hassan : Gauta.Samir : Shirim ba ci ba.Hussaina : Baba.Samir : Ta˚anda ba ta ˚ashi ba.Hassan: Kanwa.Samir : Baba na ∂aka gemu na waje.Samira: Haya˚i.Samir : Abu filili, abu falala, abu maliya malik.Hussaina: Wal˚iya.Samir : Yadda ∂illin yakan yi ∂illin, haka ma ∂illin yakan yi ∂illin.Samira : Yadda kaza takan yi ˚wan nan, haka ma ˚wan nan

yakan yi kaza.Samir : Shanuna dubu-dubu turkensu ∂aya.Hassan : Tsintsiya.Samir: Makaranta a dokar daji.Hussaina : Mm, na ba ka gari.Samira : Gidan tururuwa.Samir : Kututture uku gagara ∂auri.Hassan : wai.Samir: Gaya ∂aya dama duniya.Hussaina: Farin wata.

Hausa Pry 2.indd 13 5/13/14 5:00 PM

14

TambayoyiKawo amsoshin wa∂annan kacici-kacici ta hanyar za∫ar amsoshin da aka bayar a ˚asa.

1. Tambaya : Gwanda lili da liyo. Amsa : …………………................................... 2. Tambaya : Kurkucif kucif. Amsa : ………………......................................3. Tambaya : Faifaina ∂inkin Marido. Amsa : ………………………............................4. Tambaya : Kullum ana ba ka, ba ka godiya. Amsa : ………………………........................….5. Tambaya : Samarin gidanmu masu fararen kai. Amsa : …………………...............................….6. Tambaya : Îan baka a bayan shuri. Amsa : …………………...............................….7. Tambaya : Abu ∂il ya saukar da mai gari daga kan doki. Amsa : ………………………..........................…8. Tambaya : Abu ziriri, abu zarara, abu tufkar Allah. Amsa : ………………………....................…….9. Tambaya : Far tuwon faifai. Amsa : ……………………...............................10. Tambaya : Abu ∂il ya sa mai gari kuka. Amsa : ……………………...........................…..

Hausa Pry 2.indd 14 5/13/14 5:00 PM

15

Amsoshi:Tatsuniya, Barkono, Zuma, Ciki, Gashi, Kwanciyar kare, Ta∫are, Gwanda noma da awo, Fitsari, Sartse.

JagoraMalami ya sa ∂alibai su kawo wasu kacici-kacici da suka sani, daban da wa∂anda aka kawo, tare da bayar da amsoshinsu da kansu. Malami ya fa∂a wa ∂alabai ma’anar kalmomin da ˚ila ba su san su ba, kamar: gauta da baba da shuri, da turke da faifai, da kututture, da baka da sauransu.

Hausa Pry 2.indd 15 5/13/14 5:00 PM

16

Babi na 5

Tausayi

Tausayi shi ne nuna kulawa ga wani mutum ko wata halitta. Taimako wata hanya ce ta tallafawa a lokacin bu˚ata. Tausayi yana sa mu taimaka wa mutum ko wata halitta idan sun shiga wani hali maras da∂i.

Tausaya wa GajiyayyuGajiyayyu su ne wa∂anda suke kasa yin wani abu da kansu sai an taimaka masu. Misali: yara, da tsofaffi, da guragu, da makafi, da marasa lafiya da sauransu. Ana taimaka wa gajiyayyu ta hanyoyi da dama kamar haka:1. Wajen tsallaka titi.2. Kar∫ar kaya daga hannun tsofaffi a kai masu.3. Taimaka wa wani, ya ∂auki kaya a kansa ko ya sauke.4. Dubiyar maras lafiya.5. Taimakawa a wajen ha∂ari, kamar na mota ko gobara da

sauransu.6. Hana cin-zali.

Hausa Pry 2.indd 16 5/13/14 5:00 PM

17

Tausaya wa Dabbobi da TsuntsayeDabbobi da tsuntaye halittu ne na Allah. Suna da rai kamar mutane. Idan an cutar da su ba sa jin da∂i. Idan an ji tausayi ko an taimaka masu suna jin da∂i. Allah Ya hana a cutar da su. Ya yi umurnin a kyautata masu. Za a iya tausaya wa dabbobi da tsuntsaye ta hanyoyi kamar haka:1. Ku∫utar da su daga wahala, kamar tarko idan ya kama su.2. Hana dukansu.3. Ba su abinci da ruwa a kan lokaci.

Hausa Pry 2.indd 17 5/13/14 5:00 PM

18

4. Kula da lafiyarsu.5. Hana yi masu duk wani nau’i na azaba. 6. Hana lalata she˚ar tsuntsu.

Tambayoyi1. Me ake nufi da tausayi?2. Me ake nufi da taimako?3. Su wa ya kamata a tausayawa?4. Cin-zali yana da kyau?5. Me ake yi wa wanda ya yi ha∂arin mota ko gobara?

Jagora

Malami ya nemi ∂alibai su kawo wasu hanyoyi, na tausayi da taimaka wa gajiyayyu da dabbobi da tsuntsaye.

Hausa Pry 2.indd 18 5/13/14 5:00 PM

19

Babi na 6

Sunayen Abubuwa

A littafi na ∂aya, an nuna suna da kalma wadda ake yin amfani da ita wajen kira ko ambaton wani abu. Sunaye kashi-kashi ne. Akwai sunayen mutane da na dabbobi da tsuntsaye da sauransu. Akwai sunaye mutane tun na gargajiya da na yanka.

Sunayen GargajiyaWa∂annan sunaye ne da Hausawa suke amfani da su tun kafin ha∂uwarsu da wasu al’umma. Misali:

1. Barau2. Korau3. Cindo4. Talle5. Ta-rana

6. Ci-tumu7. Ajuji8. Ranau9. Damina10. Tambaya

Sunayen YankaWa∂annan sunaye ne da Hausawa suka samu bayan zuwan addinin Musulunci. Misali:1. Musa2. Salisu

Hausa Pry 2.indd 19 5/13/14 5:00 PM

20

3. Zainab4. Fatima5. Yusufu6. Adamu

7. Halima8. Aisha9. Ibrahim10. Abubakar

Sunayen TsuntsayeTsuntsaye ma kowanne da sunansa. Daga ciki akwai:1. Tattabara2. Balbela3. Kaza4. Carki5. Gado 6. Aku7. Beni8. Hankaka9. Shaho10. Ungulu

TambayoyiA. Amsa wadannan tambayoyi.

1. Shin ana amfani da suna wajen kira?2. Ware sunayen gargajiya a nan. (Musa, Cindo, Ali, Barau)3. Gado da aku sunayen ……… ne. (yanka/tsuntsaye)4. Zuwan Musulunci ne ya kawo sunayen……… . (gargajiya/

yanka)5. Ware tsuntsayen gida a nan. (carki, kaza, balbela,

tattabara)

Aku Ungulu Kaza

Hausa Pry 2.indd 20 5/13/14 5:00 PM

21

Jagora

Malami ya kawo hotunan tsuntsayen gida da na dawa, don nuna wa yara. Malami ya yi ˚o˚arin yi wa yara bayanin sunayen gargajiya da na yanka.

B. Ja layi tsakanin sunan tsuntsu da hotonsa kamar yadda yake a misali.

1. Tattabara

2. Hankaka

3. Shaho

4. Jimina

5. Îawisu

Hausa Pry 2.indd 21 5/13/14 5:00 PM

22

Babi na 7

Kalmomin Aiki

Kalmomin AikiA littafi na ∂aya, an yi bayani game da kalmomin aiki. Inda aka nuna cewa kalmomin aiki, suna ̊ unshe da aikin da ya faru a cikin jimla. A nan za a ˚ara kawo misalan kalmomin aiki, don nuna aikin da kuma tantance shi a cikin jimla. Misali:

1. Dur˚usa2. Tsuguna3. Du˚a4. Rubuta5. Sayi6. Hura7. Karanta8. Duba

9. Tura10. Mi˚a11. Kar∫a12. Li˚a13. Harba14. Yanka15. Auna

Aikata Aikin KalmaA nan za a yi ˚o˚arin misalta aikin kalma a aikace, kamar yadda yake a littafi na ∂aya, ta hanyar nuna yadda aikin yake bayyana a cikin jimla. Misali:

Hausa Pry 2.indd 22 5/13/14 5:00 PM

23

Tantance Kalmomin AikiA nan za a yi ˚o˚arin tantance kalmomin aiki ne, ta hanyar nuna muhallin aikata wani aiki sa∫anin wani daban. Misali:1. Ana harba kibiya.2. Ba a hura wuta da hanci.

Hussaina ta mi˚a wa Samir littafi.

Ya harba kibiya.

Hausa Pry 2.indd 23 5/13/14 5:00 PM

24

B. Ja layi tsakanin kalmar aiki da hoto kamar yadda yake a misali.

1. Karanta

Wa∂annan kalmomi da aka tisa a cikin jimla ta ∂aya da ta biyu, duka kalmomin aiki ne. Sun bambanta dangane da yanayin da aka aiwatar da aikin a cikin jimlar.3. Samir ya tsuguna. 4. Hassan ya dur˚usa.

A jimla ta uku da ta hu∂u an nuna kalmomin aiki guda biyu domin tantance irin ayyukan da jimlolin suka nuna sun faru, wato tsuguna da kuma dur˚usa.

TambayoyiA. Amsa wa∂annan tambayoyi.

1. Kalmomin aiki suna nuna abin da aka yi?2. Wa∂anne ne kalmomin aiki a nan? a) Dur˚usa b) fensir c) hura d) taga3. Malami ya ............ darasi a allo. (rubuta/ yanka)4. Yaro ya ........littafi. (sayi/ harba)5. Wane ne ya yi harbi?

Hausa Pry 2.indd 24 5/13/14 5:00 PM

25

Jagora

Malami ya umarci ∂alibai su aiwatar da kalmomin aikin, da aka nuna a cikin misalan jimlolin da suka gabata. Malami ya sa ∂alibai su tantance kalmomin aiki, a cikin jimla da kuma a aikace.

1.

2. Tura

3. Harba

4. Du˚a

5. Hura

Hausa Pry 2.indd 25 5/13/14 5:00 PM

26

Babi na 8

Tsaftar Muhalli

Mene ne Muhalli?Muhalli shi ne wurin zama ko kwana ko wurin aiki. Gida muhalli ne. Makaranta muhalli ce. Shago ma muhalli ne.

Tsaftace MuhalliDole ne mu ri˚a kula da muhallinmu muna tsaftace shi don kare lafiyarmu. Muna tsaftace muhallinmu ta hanyoyi da dama.

Misalan Tsaftar MuhalliMuna iya tsaftace muhallinmu ta hanyoyi kamar haka;1. Shara a-kai-a-kai: Tilas ne mu ri˚a share muhimman wurare

kamar: a) Îakin kwananmu. b) Tsakar gida. c) Azuzuwanmu. d) Harabar makaranta. e) Ban-∂akuna. f) Shaguna, da ofisoshi, da ˚ofar gida, da kuma kan

hanyoyinmu.

Hausa Pry 2.indd 26 5/13/14 5:00 PM

27

2. Nome Ciyayi: Ciyayi suna iya tara ˚wari, da sauran abubuwa masu cutarwa kamar sauro, da kunama, da maciji da sauransu. Yana da kyau koyaushe a ri˚a nome ciyayi ko a sare su, a ri˚a tara su ana ˚onewa. Kada a ri˚a bari ciyawa tana taruwa har ta yi duhu.

Hausa Pry 2.indd 27 5/13/14 5:00 PM

28

3. Kawar da Shara Daga Muhalli: Tara shara na iya kawo cutattuka, saboda gur∫ata muhalli da iskar da ake sha˚a. wari irin su ̊ udaje, za su iya ∂ebo ̊ wayoyin cuta daga shara, su ya∂a mana su, ta hanyar abin da muke ci ko muke sha. Haka nan sauro, yana iya ∫uya a cikin tarin shara, daga nan ya saka mana cutar zazza∫in cizon sauro. Don haka, yana da kyau da muhimmanci, a ri˚a kwashe shara ana zubar da ita nesa da muhalli.

4. one Juji: Juji ma wani wuri ne, da yake tara ˚azanta da ˚wayoyin cutattuka, da kuma ˚wari masu cutar da ∂an’adam. Sa’ilin nan juji wuri ne na taruwar aljanu. Don haka kada a ri˚a barin juji yana taruwa da yawa. Taruwar juji yana tare kan hanya, ya toshe hanyoyin ruwa, ya ri˚a kawo wari da cunkoso a muhalli. Yana da kyau a ri˚a ˚one juji a-kai-a-kai, ana kwashe shi ana kai wa gona don a yi taki da shi.

Hausa Pry 2.indd 28 5/13/14 5:00 PM

29

5. Share Turken Dabbobi: Turken dabbobi wuri ne da ake ∂aure dabba. Ita kanta dabba tana jin da∂i, idan ana share turkenta a koyaushe. Turken dabbobi yana tara ̊ azanta,

da ru∫a∫∫en abincinsu da kashinsu, da fitsarinsu ko zubewar ruwa. Turken dabbobi yana kawo wari a cikin gida, sannan yana tara ˚udaje, musamman da damana. Idan ana so a ji da∂i a muhallin da ake da turken dabbobi a kusa, tilas ne a ri˚a yawan share shi ana gyara shi.

6. Yasar Kwatami: Kwatami wuri ne da ruwa ke bi. Wani lokaci ruwa yana biyo wa ta kwatami, tare da datti ko ˚azanta iri-iri. Cikewa ko toshewar kwatami tana hana ruwa gudu har ya yi ambaliya, musamman da damina. Ita kuwa ambaliyar ruwa tana iya kawo rushewar gidaje, ko lalacewar su, ko zaizayar ˚asa. Shi ma kwatami yana tara sauro. Don haka yashe kwatami yana da kyau. Mutanen unguwa ne suke taruwa, suna yashe kwatami don jin da∂in zama a muhallinsu.

Hausa Pry 2.indd 29 5/13/14 5:01 PM

30

7. Tsaftace Rariya: Rariya hanya ce ta fitowar ruwa, daga cikin gida zuwa kwatami. Ruwan da yake biyowa ta rariya mai ˚azanta ne. Yana ∂auke da fitsari, da ruwan wanke-wanke, da ruwan wanka, da sauransu. wayoyin cuta da sauro suna taruwa a cikin rariya. Ita ma rariya tana yin wari idan ba a gyara ta ba, har ta dami mutane a muhallinsu. Ledoji, da takardu, da guntun sabulu, ko soso sukan toshe rariya. Don haka yana da kyau a kula da tsaftar rariya.

8. Gyara Wurin Wanka da Wanki da Wanke-wanke: Wurin wanka, da wurin wanki, da wurin yin wanke-wanke dukkansu suna bu˚atar a ri˚a tsaftace su. Wurare ne da ake yawan yin amfani da ruwa. Shi kuwa ruwa idan ya ha∂u da ˚azanta ko aka bar shi yana taruwa, zai iya tara ˚wayoyin cuta ko sauro. Don haka, idan ana so a zauna cikin ˚oshin lafiya dole a ri˚a yawan gyara wa∂annan wurare. Wannan kuma shi zai sa a ji da∂in zama a muhalli.

Hausa Pry 2.indd 30 5/13/14 5:01 PM

31

9. Tsaftace Makewayi: Makewayi, ko bayi, ko ban∂aki shi ne wurin da ake shiga, ko ake zagawa domin a yi fitsari ko bayan-gida. Wuri ne da yake tara ˚azanta da ˚wayoyin cuta da ˚wari irin su kyankyaso. Ga shi kuma ana yawan shigar su a koyaushe. Rashin tsaftace su yana iya sa duk sa’ilin da za a fito daga ciki a fito da ˚wayoyin cuta da za su iya saka rashin lafiya. Ana amfani da wasu daga cikin wa∂annan abubuwa don tsaftace makewayi;

a) Ruwa mai tsafta. b) Garin sabulu. c) Tsintsiya. d) Maganin kawar da wari. e) Maganin kashe ˚wayoyin cuta.

Hausa Pry 2.indd 31 5/13/14 5:01 PM

32

Tambayoyi1. Mene ne muhalli?2. Kawo ire-iren muhalli guda uku.3. Kawo hanyoyi guda biyar na tsaftace muhalli.4. Fa∂i muhimman wurare guda biyar da ya kamata mu ri˚a

sharewa?5. Wa∂anne irin abubuwa ne masu cutarwa suke ∫uya a cikin

ciyayi?6. Shin yana da kyau mu ri˚a zubar da shara kusa da muhalli?7. Ya dace a ri˚a barin juji yana taruwa da yawa?8. Me da me turken dabbobi yake tarawa?9. Me yake kawo ambaliyar ruwa da lalacewa ko rushewar

gidaje?10. Kawo abubuwa uku da ake yin amfani da su wajen tsaftace

makewayi.

Hausa Pry 2.indd 32 5/13/14 5:01 PM

33

Babi na 9

Karatu da Rubutu

Karanta Wa∂annan Jumloli:Ga Samir.Ga zomo.Samir yana son zomo.Zomo yana son karas.Samir yana bai wa zomo karas.Zomo yana cin karas.

Hausa Pry 2.indd 33 5/13/14 5:01 PM

34

Rubuta jumlolin da ke sama a wa∂annan layuka na ˚asa:_____________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________

Karanta Wa∂annan Jumloli:Wannan tsoho ne.Tsoho ya ri˚e sanda.Zai tsallaka titi.Mota ta taho.Tsoho ya tsaya.Rubuta jumlolin da ke sama a wa∂annan layuka na ˚asa:

Hausa Pry 2.indd 34 5/13/14 5:01 PM

35

_____________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________

Karanta Wa∂annan Jumloli:Ga Baba.Ga akuya.Baba yana jan akuya.Baba zai yanka akuya.Yau za mu ci nama da yawa.

Hausa Pry 2.indd 35 5/13/14 5:01 PM

36

Rubuta jumlolin da ke sama a wa∂annan layuka na ˚asa:____________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________

Jagora

Malami ya samar da wasu gajerun jumloli sau˚a˚a ∂alibai su iya karanta su da rubuta su.

Hausa Pry 2.indd 36 5/13/14 5:01 PM

37

Babi na 10

Wasannin Motsa JikiWasan Burum-burumWannan wasa ne na yara maza. Wasa ne da yara suke ∫oye wa juna. Ana rufe wa yaro ∂aya ido ko ya rufe da kansa, sauran yara su nemi wuware su ∫oye masa. Shi kuma sai ya yi ta nemansu, ta hanyar lalube har ya yi sa’ar kama ∂ayansu. Wanda aka kamo, shi ne na gaba da za a rufe wa ido, shi kuma ya nemo saura. Kafin a fara wasan ana yin wa˚a don a sami wanda za a fara rufe wa ido. Wani yana rera wa˚ar saura kuma suna amshi. Duk wanda a ˚arshen wa˚ar ya yi amshi, to shi za a fara rufe wa ido. Sauran yara sukan tsokani wanda aka rufe wa ido da cewa: Burum burum, kanka da borin gya∂a. Ga yadda wa˚ar take:

Hausa Pry 2.indd 37 5/13/14 5:01 PM

38

Bayarwa AmshiMai burum-burum. Ya yi haka.Ban da mai gya∂a. Ya yi haka.Yaya sunan ma∂inkiya? Allura.Yaya sunan abin baba? (shiru)

In Gero Ya NunaSamir da Hassan sun fita dandali don yin wasa. Da suka isa dandali sai suka tarar da abokansu. Hassan ya ce sai su yi wasan ‘In gero ya nuna’. Dukkaninsu suka yarda cikin murna. Suka yi da’ira, kowa ya ri˚e hannun ∂an’uwansa. Hassan kuwa yana tsakiya. Shi ne yake bayar da wa˚a saura suna amsawa. Ga yadda suke wasan:

Hassan: ıe∫∫e∫e ∫eluwa. Masu amshi: ıe∫∫e∫e ∫eluwa. Hassan: In gero ya nuna. Masu amshi: In gero ya nuna.

Hausa Pry 2.indd 38 5/13/14 5:01 PM

39

Hassan: In dawa ta nuna. Masu amshi: In dawa ta nuna. Hassan: Yara ku karya, yara ku karya ku tuma ku ci. Masu amshi: Yara ku karya, yara ku karya ku tuma ku ci. Hassan: In acca ta nuna. Masu amshi: In acca ta nuna. Hassan: Yara ku karya, yara ku karya ku tuma ku ci. Masu amshi: Yara ku karya, yara ku karya ku tuma ku ci. Haka dai suka yi ta yin wannan wasa. In wani ya bayar, sai ya huta wani kuma ya bayar. Da suka gaji sai suka watse. Kowa ya tafi gidansu.

Jagora

Ma˚asudin wannan babi shi ne yara su iya aikata wasu wasanni na motsa jiki domin ˚arin lafiyar jiki. Malami zai ri˚a fita filin wasan makaranta yana sa yara suna yin wa∂annan wasanni da kuma wasu wasannin, kamar Yara ku risa; Allan-baku; Na auno gero; da sauransu. Za a iya nemo littafin Wasannin Yara na Umaru Dembo ko litattafan Tatsuniyoyi da Wasanni na Ibrahim Yaro Yahaya don a ga misalai.

Wasannin YaraA littafi na ∂aya an kawo ma’anar wa˚a da kuma misalan wa˚o˚i. A nan, za a duba wa˚o˚in yara ne.Yara sukan yi wa˚o˚i iri daban-daban. Sukan yi irin wa∂annan wa˚o˚i ne, a dandali wajen wasannin ga∂a ko shallu.

Hausa Pry 2.indd 39 5/13/14 5:01 PM

40

A nan, za a duba rabe-raben wa˚o˚in yara ne dangane da wa∂anda suke aiwatar da su. Akwai wa˚o˚in da suke na maza ne kawai, akwai kuma wa∂anda na yara mata ne ka∂ai.

Wasannin Yara MazaSamir da Hassan sun fita dandali don yin wasa. Sun fara rera wannan wa˚a don kiran abokan wasa kamar haka:

Yan wasa ku fito wasa. In ba ku zo ba a kama ku. Aikin bariki tilas ne. Ba ni na fa∂a ba Bature ne. Baturen ma mai jan kunne.

Da sauran abokansu suka zo, sai suka fara wasa suna rera wannan wa˚a:

Hausa Pry 2.indd 40 5/13/14 5:01 PM

41

Jemage Wa˚a AmshiKai na ˚olin˚oli. Jemage.Kai na kangali kangal. Jemage.Yaro duba duba. Jemage.Yaro dubi sa’anka. Jemage.Îan jilon jilo. Jemage.Kar ka hau shi ya fa∂i. Jemage.Kar ka kama ru∫ago. Jemage.Ru∫ago ba ˚arfi. Jemage.Ba shi ˚warin gwiwa. Jemage.Sai ka fa∂i ka karye. Jemage.Kar ka hau mai gemu. Jemage.

Hausa Pry 2.indd 41 5/13/14 5:01 PM

42

Kar ka hau babanka. Jemage.Yaro dubi sa’anka. Jemage.Na yi nutso na kamo kifi. Jemage.Ko ruwa ban sha ba. Jemage.Na yi nutso na kamo tarwa∂a. Jemage.Ko ruwa ban sha ba. Jemage.Yaro duba duba. Jemage. Wasannin Yara MataBayan Samira ta taya babarta aiki, sai ta tafi gidan su Hussaina, suka fita dandali don yin ga∂a da sauran ˚awayensu. Suka shiga yin wasa suna rera wa˚a kamar haka:

Hausa Pry 2.indd 42 5/13/14 5:01 PM

43

Ayye Yaraye

Farawa: Ayye yaraye-Ayye yaraye, Ayye yaraye-Iye nanaye,

Ayyaraye-Ayyaraye iye.Bayarwa: In ka ga mai gida – in ka ga mai gida ,

In ka ga mai gida a gindin murhu,Sauran tuwo ne bai ishe shi ba.

Amshi: Ayye yaraye-Ayye yaraye, Ayye yaraye-Iye nanaye,

Ayyaraye-Ayyaraye iye.Bayarwa: Can na ga ˚war˚wata – can na ga ˚war˚wata,

Can na ga ˚war˚wata tana jan gemu,Ko dai dau∂a ta ishe ta ne?

Amshi: Ayye yaraye-Ayye yaraye, Ayye yaraye-Iye nanaye,

Ayyaraye-Ayyaraye iye.Bayarwa: Ni ba kishiya - Ni ba kishiya,

Ni ba kishiya nake tsoro ba,Kishi da ’yar boka nake gudu.

Amshi: Ayye yaraye-Ayye yaraye, Ayye yaraye-Iye nanaye,

Ayyaraye-Ayyaraye iye.Bayarwa: Tai maka magani - tai maka magani,

Tai maka magani ka koma jeji,Kai sai ka ce gidan na ubanta ne.

Hausa Pry 2.indd 43 5/13/14 5:01 PM

44

Amshi: Ayye yaraye-Ayye yaraye, Ayye yaraye-Iye nanaye,

Ayyaraye-Ayyaraye iye.

Jagora

Malami ya sa ∂alibai maza su kawo wa˚o˚in, da suka sani na maza ta hanyar rerawa. Haka kuma ya sa ∂alibai mata su kawo irin nasu kuma su rera.

Hausa Pry 2.indd 44 5/13/14 5:01 PM

45

Babi na 11

Gaisuwar na Gaba

Gaisuwar na GabaYadda ake yin gaisuwa ya bambanta. Irin gaisuwar da za a yi da aboki, ko ˚awa ta bambanta da wadda za a yi wa iyaye, ko kakanni. Ga misali, gaisuwar aboki ko ˚awa ba ta cika wuce tambayar yadda aka tashi, ko aka wuni da lafiya ko harkoki na yau da kullum ba. Idan za a gaisar da iyaye ko kakanni, tun daga yanayin da za a fuskance su ake samun bambanci. Misali, idan za a gaisar da iyaye ko kakanni ko na gaba, akwai bu˚atar dur˚usawa ko rusunawa cikin nutsuwa. Kullum Samir da Samira da kuma Hassan da Hussaina suka idar da sallar Asuba, ko suka dawo daga makaranta sai sun gaisar da mahaifansu. Ga Samir da Samira suna gaisar da babansu Malam Audu, bayan sun dawo daga makaranta. Sun tarar da shi yana cin abincin rana.

Hausa Pry 2.indd 45 5/13/14 5:01 PM

46

Samir da Samira: Baba ina wuni?Malam Audu: Lafiya ˚alau.Samir da Samira: Ina gajiya?Malam Audu: Babu gajiya.Samir da Samira: To madalla!Malam Audu: Madalla! Allah Ya shi maku albarka.Samir da Samir: Amin Baba! Mun gode.

Jagora

Manufar wannan babi, ita ce ∂alibai su san yadda ake gaisar da na gaba. Malami ya kawo sauran ire-iren gaisuwa da kuma lokutan da ake yin su ya sa ∂alibai su misalta su.

Hausa Pry 2.indd 46 5/13/14 5:01 PM

47

Babi na 12

Almara IIAlmara labari ne ˚agagge wanda ba lallai ne ya ta∫a faruwa ba. Akwai almara da take auna tunani da kaifin basira da koya dabarun warware wata matsala.

Kura da Akuya da CiyawaWani mutum ne yake da kura, da akuya da ciyawa. Rannan sai tafiya ta kama shi zuwa wani ˚auye a kusa da ˚auyensu. A tsakanin ˚auyukan biyu kuwa, akwai wani kogi wanda sai an haye shi sannan a isa wancan ˚auyen. Kwale-kwale guda ∂aya ne ake amfani da shi don tsallake kogin. Wannan kwale-kwale yana iya ∂aukar abubuwa ko mutane uku ne kawai har ∂an fito. Idan kuwa aka haura haka, sai dai a jira har sai kwale-kwalen ya dawo.

Hausa Pry 2.indd 47 5/13/14 5:01 PM

48

Da mutumin ya isa bakin kogi domin ya tsallaka, sai ya zamana sai dai ko ya bar ciyawa da akuya, shi kuma su haye tare da kura, ko kuma ya haye da ciyawa, ya bar kura da akuya. Don haka, duk wanda ya bari a cikinsu, kafin ya dawo, ∂aya ya cinye ∂an’uwansa. Idan ya bar akuya da kura, kafin ya dawo, kura ta cinye akuya. Idan kuma ya bar akuya da ciyawa, to lallai kafin ya dawo, akuya ta cinye ciyawa. Don haka, idan kai ne yaya za ka haye da su?

Tambayoyi1. Abubuwa nawa mutumin yake ∂auke da su?2. Mene ne a tsakanin ˚auyukan guda biyu?3. Abubuwa nawa kwale-kwale yake ∂auka?4. Shin za a iya tsallakawa da abubuwa biyar?5. Idan aka bar akuya me za ta cinye?

Malami da Karuwa da Sarkin Baka

Wata rana tafiya ta ha∂a Malami, da Karuwa, da Sarkin Baka. Suna cikin tafiya sai suka iske wani ˚aton kogi. Suka yi rashin sa’a kuwa kogi ya kawo ruwa ma˚il, babu damar tsallakawa. Da

Hausa Pry 2.indd 48 5/13/14 5:01 PM

49

isar su sai Sarkin Baka ya dubi Malami ya ce, ‘Malam ina dabara?’ Malami ya dubi Sarkin Baka ya ce, ‘Kowa yayi abin da ya fisshe shi. Nan take Malami ya ∂auko takarda, daga cikin gafakarsa, ya yi rubutu a ciki, ya jefa ta a kan ruwa, ya taka ta ya haye. Karuwa na ganin haka, sai ta zu˚i taba ta busa sama, ta yi tsalle ta shiga cikin haya˚in tabar, ya tsallakar da ita kafin ya baje. Da Sarkin Baka ya ga haka, sai ya ce, ‘Ah! Wani ma ya yi rawa bare ∂an maka∂i?’ Sai ya yi wuf, ya zaro kibiya daga cikin kwarinsa, ya ∂ana ta a bakansa, ya harba. Kafin kibiyar nan ta fice daga bakan, Sarkin Baka ya ∂afe ta, ta tsallake kogin da shi. To wai a cikin wa∂annan mutane guda uku, wane ne ya fi nuna bajinta?

Tambayoyi 1. Mutum nawa tafiya ta kama?2. Me suka tarar a kan hanya?3. Wa ya ce, ‘Kowa tasa ta fisshe shi?’4. Wa ya busa haya˚in taba?5. Wa aka bari a ˚arshe?

Jagora

Malami ya sa yara su warware wa∂annan almara da aka kawo. Sannan ya sa yara su ˚aro wasu labaru, na almara da suka sani, kuma a yi ˚o˚arin warware almarar. Daga ˚arshe ya yi tambayoyi.

Hausa Pry 2.indd 49 5/13/14 5:01 PM

50

Babi na 13

Karin Magana da Maganganun Azanci

Ma’anar Karin MaganaKarin magana wata ‘yar jimla ce gajeriya da mai magana zai fa∂a ta hikima mai ˚unshe da ma’ana mai yawa.

Ma’anar AzanciAzanci maganganu ne masu nuna hikimar sarrafa harshe da ˚warewa.

Misalan Karin Magana1. Mugunta fitsarin fa˚o.

2. Idan za ka gina ramin mugunta, gina shi gajere.

3. Kowa ya daka rawar wani, ya rasa turmin daka tasa.

4. Ido wa ka raina, wanda nake gani kullum.

5. Ba kullum ake kwana a gado ba.

6. Zuwa da kai ya fi sa˚o.

7. Hannunka ba ya ru∫ewa ka yanke ka yar.

Hausa Pry 2.indd 50 5/13/14 5:01 PM

51

8. Îan’uwa rabin jiki.

9. Mai ha˚uri yakan dafa dutse har ya sha romonsa.

10. Alhaki kwikwiyo.

11. Jiki magayi.

12. Labarin zuciya a tambayi fuska.

13. Ba a raba hanta da jini.

14. In hagun ta ˚iya a koma dama.

15. Zuru ta ishi ∂a ido.

Kakkarya HarsheKakkarya harshe maganganu ne na hikima, don koya wa yara iya sarrafa shi. Akan gina kakkarya harshe ne, ta hanyar maimaita wasu kalmomi masu kama da juna, a gina wani jawabi.

Misalan Kakkarya Harshe:1. Salamu alaikum matar Koma∂an-koma∂o.

Maraba da ba˚on Koma∂an-koma∂o.Koma∂an-koma∂o yana nan?Koma∂an-koma∂o ba ya nan.To ke matar Koma∂an-koma∂o,ko za ki ba ni aron komar Koma∂an-koma∂o in kokkoma∂a?

Hausa Pry 2.indd 51 5/13/14 5:01 PM

52

Ni matar Koma∂an-koma∂o, ban ∂auki aron komar Koma∂an-koma∂o na kokkoma∂a ba,Sai kai ba˚on Koma∂an-koma∂o,Zan ba ka aron komar Koma∂an-koma∂o ka kokkoma∂a?

2. Da ˚ato da ˚wa∂o.

Suka tafi yawon ˚oto.ato ya yi ˚oto.Kwa∂o ya yi ˚oto.ato ne zai ˚wace wa kwa∂o ˚oto?Ko Kwa∂o ne zai ˚wace wa ˚ato ˚oto?

3. Haka sulu∫ na sullu∫e silliya a wuyan Salamatu, ashe ban sani ba an yi wa Malam Salihu satar santali a Salanta.

4. Isa Musa, kana ˚urasa.Kawo hamsa a ba Bahausa,

Hausa Pry 2.indd 52 5/13/14 5:01 PM

53

Jagora

Malami ya sa ∂alibai su kawo hanyoyin kakkarya harshe. Haka kuma ya sa ∂alibai su kawo wasu misalan kakkarya harshe da suka sani.

Ta toya masa.Ta sa a tasa.Ka tan∂a ka lasa.Ka san Hausa wuya gare ta.

Hausa Pry 2.indd 53 5/13/14 5:01 PM

54

Babi na 14

idayaidayaA littafi na ∂aya mun ga al˚aluman ˚idaya, daga ∂aya zuwa goma tare da misalai. A nan kuma za a ci gaba da al˚aluman ˚idaya, daga goma sha ∂aya zuwa ashirin (11-20) domin ∂alibai su tantance su. Wa∂annan kalmomin ˚idaya su ne:1. Goma sha ∂aya 11.2. Goma sha biyu 12.3. Goma sha uku 13.4. Goma sha hu∂u 14.5. Goma sha biyar 15.6. Goma sha shida 16.7. Goma sha bakwai 17.8. Goma sha takwas 18.9. Goma sha tara 19.10. Ashirin 20.

Goma sha ∂aya

Goma sha biyu

Hausa Pry 2.indd 54 5/13/14 5:02 PM

55

Goma sha uku

Goma sha hu∂u

Goma sha biyar

Goma sha shida

Goma sha bakwai

Goma sha takwas

Goma sha tara

Ashirin

Tambayoyi

1. Cike wa∂annan gurabu da kalmomin ˚idaya da suka dace. Goma sha ∂aya zuwa ashirin. Goma sha biyu Goma sha uku Goma sha biyar Goma sha takwas Goma sha tara

Hausa Pry 2.indd 55 5/13/14 5:03 PM

56

2. Watannin shekara guda .............. ne. (goma sha uku/goma sha biyu)

3. Mako biyu ya ˚unshi kwanaki .......... . ( goma sha biyar/ goma sha hu∂u)

4. Yatsun ˚afa da na hannu guda ........... ne. (ashirin/goma)5. Goma biyu ita ce............. . ( ashirin / goma sha tara)

Jagora

Malami ya samar da katittikan ˚idaya musamman masu ∂auke da hotuna, sannan ya sa yara su samo wasu adadin ˚wan˚walati da tsakuwoyi don misalta yin ̊ idaya a aikace tare da su a cikin aji.

Hausa Pry 2.indd 56 5/13/14 5:03 PM

57

Babi na 15

Wasan KwaikwayoMa’anar Wasan KwaikwayoWasan kwaikwayo, karantarwa ce a aikace ga jama’a a kan muhimman abubuwan rayuwarsu, ta yau da kullum domin su fahimce su, su rungume su, su kuma yi amfani da su domin kyautata rayuwarsu. A wasan kwaikwayo ana nuni da halaye nagari domin a koya. Haka nan, ana nuni da munanan halaye domin a guje masu. Ga misalin wani wasa:

Misalan Wasan KwaikwayoGa wani wasan kwaikwayo da yake nuna illar ∫ata yara da kuma rashin girmama miji:

Sunan Wasa: Tarbiyya Mai Naso Kashi na Daya

(Malam Usman a zaune a gindin bishiya tare da abokinsaMalam Isa ya yi tagumi)Mal. Usman: Mts!… (ya yi tsaki)Mal. Isa: Malam Usman yaya na gan ka kamar maras

lafiya? Ko aikin ˚asa ka yi ne.

Hausa Pry 2.indd 57 5/13/14 5:03 PM

58

Mal. Usman: A’a, Malam Isa, ba aikin ˚asa na yi ba. Ina cikin tashin hankali ne. Babban ∂ana Shalele ne ‘yansanda suka kama shi.

Mal. Isa: To me ya faru kuma, ko kayan wani ya ∂auka?Mal. Usman: Ko ∂aya! Duk sharri aka yi masa, wai an ce suna

shaye-shaye a kango. Matsalar ma ita ce, yadda zan tinkari babarsa da maganar. Kai, ina cikin tashin hankali!

Mal. Isa: To mu je mu sami Sajan Audu mana, ko a san yadda za a fitar da shi. Ko kuwa yaya ka gani?

Mal. Usman: I to, haka ne, amma kai ba ka san sharrinsu ba ne.

Kashi na Biyu(Sun tafi wajen Sajan Audu)

Mal. Isa: Salamu alaikum, ofisa yau ko kakin ba a sa ba ne? Lallai kam da alama yau kana hutu.

Mal. Usman: Barka dai yalla∫ai yaya ayyuka?Sajan Audu: Mun gode Allah, me ke tafe da ku?Mal. Usman: Wallahi yaron wajena ne aka kama shi jiya wai

suna shaye-shaye.Sajan Audu: Wai ne ma?Mal. Isa: Yalla∫ai taimakawa za a yi.Sajan Audu: Kai ba na son sakarcin banza, yau ne aka fara

kama shi. Ba ka son kulawa da tarbiyyar ∂anka kawai. Mts!… (ya yi tsaki), ku tashi ku ba ni wuri.

Hausa Pry 2.indd 58 5/13/14 5:03 PM

59

(Sun tashi tsamo-tsamo sun fita, daga nan kowa ya kama gabansa ko sallama babu)

Kashi na Uku(A gidan Malam Usman)

Mal. Usman: (Ya shigo gida fuskarsa a tur∫une) Ke! Ina kike ne?

Talatu: Wane tabbataccen ne ya shigo min ko sallama babu?

Laure: Haba Talatu, Maigida ne fa!Talatu: Tab∂ijan! Ai kuwa yau za mu cancare, me ya

kai ki shiga harka ta. Wallahi zan yi maki ∫arin makauniya.

Laure: Allah ya ba ki ha˚uri, ba ni na kar zomon ba.(ta juya ta tafi)

Talatu: Yaya na ganka kamar maras gaskiya? An ba ni labarin Shalele yana caji ofis. Ya ban gan ka da shiba?

Mal. Usman: (Ya yi shiru sannan ya numfasa) Ke me ya sa ba ki da hankali ne? To yanzu ma daga wurin Sajan Audu muke, abin ya faskara.

Talatu: (Ta tura ∂ankwali gaban goshi) Ai kuwa ba za ta sa∫u ba. Juyawa za ka yi ka je ka san yadda za ka fito min da yaro.

Mal. Usman: (Ya yi waje kamar ji˚a˚˚en tsumma, tun daga soro ya fara sumbatu) Wannan bala’i da me ya yi kama, kai wannan shegiya ta sa ni a gaba. Bari

Hausa Pry 2.indd 59 5/13/14 5:03 PM

60

dai na je can caji ofis ∂in ko na yi nasarar fito da shi.

Kashi na Hu∂u(A wajen ‘Yansanda)

Mal. Usman: Yalla∫ai barka da aiki.Kofur Tanko: Yawwa barka. Ko kai ne Malam Usman?Mal. Usman: Ee, nine ranka ya da∂e.Kofur Tanko: To yanzu Sajan Audu ya ce a saki Shalele,

amma ya ce wannan shi ne na ˚arshe, ka ja masa kunne.

Mal. Usman: To, na gode ranka ya da∂e, in Allah ya yarda ba zai ˚ara ba.

(An fito da Shalele suna tafe tare da Malam Usman, amma ya sullu∫e masa)

Kashi na Biyar(A gidan Malam Usman)

Mal. Usman: (Ya yi san∂a ya le˚a gidan don gudun kada matar ta ganshi ba tare da Shalele ba. Sai ya hange shi ta zuba masa abinci yana ci). Salamu Alaikum, Kai wane irin yaron banza ne, muna tafe na neme ka na rasa?

Talatu: (Ta yi farat ta kar∫e zancen) Kai namijin hotiho, ka kasa fito da ∂an naka, sai da Sajan Audu ya yi masa afuwa sannan za ka zo ka ishe mu da surutu!

Hausa Pry 2.indd 60 5/13/14 5:03 PM

61

Mal. Usman: Ashe daman abin da Laure ke fa∂a min gaskiya ne har nake yi mata fa∂a.

Laure: Da ma jiya ina ∂aki na ji ta ba shi ku∂i ya sayo ̊ waya.Talatu: Wallahi ba zan yarda ba. Ka ce zaman ha’inci muke

yi da kai? Kuma idan ka yarda da abin da matarka ta fa∂a maka, to komai za ka yi ka yi ∂in.

Shalele: (Da ya ga rigima ta kaure sai ya sa∂a∂a ∂akin babarsa Talatu, ya kwashe ku∂in dashin da aka kawo mata ya yi tafiyarsa).

Mal. Isa: (Ya shigo gidan) Haba kada ku zama yara mana, me ya sa kuke yin haka?

Talatu: Ai ni ba zan ˚yale ba, zan kai ˚ara, idan ya so ko ita ko ni. Sam ba za ta sa∫u ba, sai dai ya za∫i ∂aya. (Ta figi gyalenta ta yi waje)

(Malam Isa da Malam Usman suka yi waje suka bar Laure a cikin gida)

Darussan Cikin Wasan 1. Illar sangarta yara.2. Matsalar rashin mutunta miji.3. Matsalar kishi.4. Matsalar rashin kula da gida a wajen miji.

Tambayoyi1. Matan Malam Usman guda nawa ne?2. Yaya sunan ∂an sandan da ya sa aka fito da Shalele?3. Ina Shalele yake zuwa?

Hausa Pry 2.indd 61 5/13/14 5:03 PM

62

4. Wanene abokin Malam Usman?5. Yaya sunan kishiyar Talatu?

Jagora

Malami ya ̊ ara fitar wa da yara irin darussan da ake samu cikin wasannin kwaikwayo, ta hanyar karanta masu wasu wasannin. Malami ya sa ∂alibai su kwatanta yin wasan da kansu.

Hausa Pry 2.indd 62 5/13/14 5:03 PM

63

Babi na 16

Tatsuniya

‘Yar Bora da ‘Yar MowaGa ta nanga ta nan ku. Mutum ne yake da matansa guda biyu, Bora da Mowa, kowace kuma tana da ‘ya. Ba a son Bora da ‘yarta a gidan, an fi son Mowa da ‘yarta. Wata rana sai ‘Yar Mowa ta yi fitsarin kwance a kan ˚irgi. Sai aka ce ‘Yar Bora ce ta yi, don haka sai ta je ta wanke ˚irgin a kogin Bagaja. Shi ke nan, ba ta yi gardama ba. Tana cikin tafiya sai ta gamu da kogin tuwon shinkafa da miya da nama. Sai ta yi wa˚a ta ce:

Hausa Pry 2.indd 63 5/13/14 5:03 PM

64

‘Kogi, kogi ko kai ne Ruwan Bagaja, Bagajar gayya ta ‘yan Sarki, Domin ˚irgi aka aiko ni in zo in wanke a Ruwan Bagaja.’Sai wannan kogi ya ce, ‘Ni ba kogin Bagaja ba ne, ni kogin tuwon shikafa ne, in kina so ki zo ki ci’. Sai ‘Yar Bora ta ce a’a, ta ˚oshi. Sai ta wuce. Tana cikintafiya kuma sai ta iske kogin Nakiya da Alkaki. Sai ta yi wa˚a ta ce: ‘Kogi, kogi ko kai ne Ruwan Bagaja, Bagajar gayya ta ‘yan Sarki, Domin ˚irgi aka aiko ni in zo in wanke a Ruwan Bagaja.’Sai wannan kogi ya ce, ‘Ni ba kogin Bagaja ba ne, ni kogin Alkaki da Nakiya ne, in kina so ki zo ki ci.’ Sai ‘Yar Bora ta ce, ‘a’a, ta ˚oshi. Sai ta wuce.Haka dai ta yi ta tafiya har ta je Kogin Bagaja. Ta fara wanki ke nan sai hadari ya taso. Ta duba gaba ta duba baya ba ta ga gida ba. Can sai ta hangi wata ‘yar bukka a dokar daji, sai ta tafi can. Da shiga cikin bukkar nan ta yi sallama, sai ta iske wata tsohuwa. Sai tsohuwar nan ta ce mata ‘Îon Allah ‘yar nan cu∂a ni mana.’ Shi ke nan, sai ‘Yar Bora ta ce ‘To’. Ta fara cuda ta ke nan sai ∫ayan tsohuwa ya ∫urme. ‘Yar Bora ta ce, ‘Wayyo Allah na shiga uku, ni yau yaya zan yi?’. Sai tsohuwa ta ce mata, ‘A’a kada ki ji tsoro, me kika gani a ciki? ‘Yar Bora ta ce kwatashi ne babba da ˚arami’. Sai tsohuwa ta ce mata ta ∂auko guda. Sai ta ∂auko ˚aramin. Tsohuwa ta ce mata ta bu∂a. Tana bu∂awa sai ta ga

Hausa Pry 2.indd 64 5/13/14 5:03 PM

65

˚wai a ciki. Sai tsohuwa ta ce mata, ‘Idan kin tafi ki fasa wannan ˚wan, amma idan kin zo fasawa ki ce ‘In fasa’? Idan kin ji an ce, ‘Fasa-fasa mu sha ruwan ˚wai’, to kada ki fasa. Idan kuwa kika ji shiru to ki fasa.’ Shi ke nan, da ‘Yar Bora ta yi nisa sai ta ce, ‘In fasa?’ Sai aka ce, ‘Fasa-fasa mu sha ruwan ˚wai.’ Sai ta ˚i fasawa, har sai da ta yi tambaya ta ji shiru, sai ta fasa. Tana fasawa sai ga mutane a kan dawakai da kayan ado iri-iri. Suka ∂auke ta ̊ anshi na tashi har zuwa gidansu. Uwarta ta yi farin ciki sosai.

‘Yar mowa da ta ga haka, sai ta ce ita ma ‘yarta sai ta je kogin Bagaja ta wanke ˚irgi. Shi ke nan ‘Yar Mowa ta tafi. Tana tafiya sai ta tarar da kogin tuwon shinkafa da miya da nama. Sai ta yi wa˚a ta ce: ‘Kogi kogi ko kai ne Ruwan Bagaja, Bagajar gayya ta ‘yan Sarki,

Hausa Pry 2.indd 65 5/13/14 5:03 PM

66

Domin ˚irgi aka aiko ni in zo in wanke a Ruwan Bagaja’.Sai wannan kogi ya ce, ‘Ni ba kogin Bagaja ba ne, ni kogin tuwan shikafa ne, in kina so ki zo ki ci.’ Sai ‘Yar Mowa ta ce, ‘Yo sai ma ka ce min in ci ?’ Sai ta zauna ta ci ta ˚oshi. Haka dai ta yi ta yi, duk kogin da ta je sai ta ci, har ta je kogin Bagaja. Ta fara wanke ˚irgi ke nan sai hadari ya taso. Ta duba dama da hagu babu gida, sai can ta hango wata ‘yar bukka a dokar daji. Tana zuwa babu ko sallama sai ta shiga, ta iske wata tsohuwa a ciki. Tsohuwar nan ta ce mata ‘Don Allah yarinya cu∂a ni mana?’ Sai ‘Yar Mowa ta ∫ata rai ta ce, ‘Ke ni fa ban zo ne don in cu∂a ki ba.’ ‘Yar tsohuwa dai ta yi ta ro˚on ta har ta yarda da kyar. Tana cikin cu∂a tsohuwa sai bayan tsohuwa ya ∫urme. Sai ta kama tsohuwa da fa∂a tana cewa ‘Da ma kin san bayanki ba shi da ˚wari kika ce in cuda ki?’ Sai tsohuwa ta ba ta ha˚uri, ta ce mata me ta gani a ciki, sai ta ce ˚wai ne guda biyu. Tsohuwa ta ce mata ta ∂auko guda, sai ta ∂auko babban. Sai Tsohuwa ta ce mata, ‘Idan kin tafi ki fasa wannan ˚wan, amma idan kin zo fasawa ki ce ‘In fasa?’ Idan kin ji an ce, ‘Fasa-fasa mu sha ruwan ˚wai, to kada ki fasa. Idan kuwa kika ji shiru to ki fasa.’ Tana tafiya sai ta ce, ‘Ka ji wannan tsohuwa, wato in fasa inda babu kowa a zo a hallaka ni.’ Shi ke nan, tana zuwa wani wuri sai ta ce ‘In fasa’? Sai aka ce, ‘Fasa-fasa mu sha ruwan ˚wai’. Sai kuwa ta fasa ˚wan nan. Tana fasawa sai ga makafi da kutare a kan jakuna sun fito. Za ta gudu, suka kama ta, suka ∂ora a kan jaki suka nufi garinsu. Suna dosar gari sai gari ya ∂umame da

Hausa Pry 2.indd 66 5/13/14 5:03 PM

67

wari da ∂oyi. Sarki ya tambaya aka gaya masa. Sai ya ce Mowa da ‘Yarta su bar masa ˚asarsa. Shi ke nan, suka fice tare da

kutaren nan daga ˚asarsa. Ita kuwa Bora da ‘yarta suka zama masu arziki sosai, suka ci gaba da rayuwarsu cikin jin da∂i. urun ˚us kan ∫era, ba don gizo ba da na yi ˚arya, da ma ˚aryar na giggilla muku.

Darussan da ke Cikin TatsuniyarWannan tatsuniya ta Mowa da Bora na koya kyawawan halaye don a yi koyi da su kamar haka:1. Ha˚uri2. Biyayya3. Kawaici ko rashin kwa∂ayi

Hausa Pry 2.indd 67 5/13/14 5:03 PM

68

4. Bin na gaba5. Taimako6. Juriya Haka kuma wannan tatsuniya, na nuni da munanan halaye don a guje su kamar haka:1. Rashin ha˚uri2. in bin na gaba3. Rashin kunya4. Taurin kai5. Kwa∂ayi6. Ha∂ama

Tambayoyi1. Wace ce ta yi fitsarin kwance? (‘Yar Bora/ ‘Yar Mowa )2. Shin ‘Yar Bora ta amsa tayin abincin da aka yi mata? (E/

A’a)3. Wanne ne ba halin ‘Yar Mowa ba a nan? (ha˚uri/ kwa∂ayi)4. Shin rashin kunya na da amfani? (Ee/ a’a)5. ………………shi ya sa ‘Yar Mowa ta ci abincin da aka yi

mata tayi. (Rowa/ Ha˚uri/Kwa∂ayi )

Jagora

Malami ya yi wa yara wasu tatsuniyoyi gajeru a aji, tare da fito da darussan da ke cikin wadannan tatsuniyoyi. Malami ya yi wa yara tambayoyi a ˚arshen kowace tatsuniya don ya gane ko sun koyi wani darasi daga tatsuniyar.

Hausa Pry 2.indd 68 5/13/14 5:03 PM

69

Babi na 17

Kulawa da Iyali

Yara suna taimakawa wajen aikace- aikacen gida daban-daban. A littafi na ∂aya mun ga yadda uwa da uba kan taimaka wa iyali. A nan za mu ga yadda yara kan taimaka wajen kulawa da gida.

Muhimman ayyukan yara a gida su ne 1. Share gida da kawar da duk wata ˚azanta. 2. Zuwa aike na kurkusa. 3. Yin wanke-wanke. 4. Taya uwa yin girki. 5. Yin reno. 6. Îebo ruwa. 7. Taya uba wasu ayyukan gona. 8. Taimaka wa uba ko uwa wajen sana’a.

Hausa Pry 2.indd 69 5/13/14 5:03 PM

70

Tambayoyi1. Aikin share-sharen gida na …………………..ne. (uba/ yara)2. Shin sama wa iyali abinci aikin uwa ne?3. Wa∂anne aikace-aikace kake/kike taimakawa dau a gida? 4. Wa∂anne ayyuka ne ba na yara ba a nan? (wanke-wake/

dafa abinci/ yi wa yara wanka/ ∂ebo ruwa)5. Shin yara na da muhimmanci wajen kula da iyali? (E/A’a)

Jagora

Malami ya ˚aro misalai na ayyukan da yara kan yi a gida-jensu. Malami ya sa ∂alibai su tambayi juna game da ayyukan da sukan yi na taimakon iyayensu.

Hausa Pry 2.indd 70 5/13/14 5:03 PM

71

Babi na 18

Karikitan Cikin Gida

Karikitan cikin gida su ne ire-iren kayayyakin da ake samu a gida ciki wa∂anda ake amfani da su kullumm. Wa∂annan kayayyaki ne da Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni da kuma wa∂anda suka shigo daga baya. Wa∂annan karikitai sun ha∂a daA. Na Tsakar Gida:1. Randa2. Fanteka3. Kwangiri 4. Gidauniya 5. Guga Tukunya 6. Bokiti7. Mo∂a8. Kwatanniya9. Ta∫arya10. Turmida sauransu.

Bokiti

Hausa Pry 2.indd 71 5/13/14 5:03 PM

72

B Na Îaki:1. Gado2. Fitila3. Mafici4. Labule5. Bargo Tabarma 6. Luru 7. Gwado8. Matashi9. Tabarma10. Asabari da sauransu.

Tambayoyi1. Me ake nufi da karikitan cikin gida?2. Kawo misalan karikitan cikin gida guda biyar?3. Ware wa∂anda ba karikitan cikin gida ba a nan. (Tabarma,

mota, mo∂a, akuya)4. Samira tana yanka nama da ………. . (ta∫arya, ˚o˚o, wu˚a)5. Ana rufe ˚ofar ∂aki da ………… ( tukunya/ asabari)

Jagora

Malami ya samo wasu daga cikin wa∂annan kayayyakin, ko hotunansu don nuna wa ∂alibai su a aji. Malami ya nuna wa yara amfanin kowanne daga cikin kayayyakin, da yadda ake amfani da su sannan ya sa su ambaci wa∂anda suka sani.

Matashi

Hausa Pry 2.indd 72 5/13/14 5:03 PM