70
Hasken Karatu Littafi don Makarantun Firamare na 6 Hausa prel 6.indd 1 9/11/14 10:12 AM

Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

i

Hasken KaratuLittafi don Makarantun Firamare na 6

Hausa prel 6.indd 1 9/11/14 10:12 AM

Page 2: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

ii

Hausa prel 6.indd 2 9/11/14 10:12 AM

Page 3: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

iii

Littafi don Makarantun Firamare na 6

Hasken Karatu

Hausa prel 6.indd 3 9/11/14 10:12 AM

Page 4: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

iv

Longmån Nigeriå PlcFelix Iwerebon House52 Obå Åkrån ÅvenueP.M.B. 21036Ikejå, Lågos StåteTel. (01) 7403967Fåx (01) 4393111E-måil: longmån@longmånnigeriå.comWebsite: www.longmånnigeriå.com

Åreå offices ånd brånchesÅbujå, Benin, Åkure, Enugu, Ibådån, Ilorin, Jos, Kåno, Owerri, Zåriå, Portharcourt ånd representåtives throughout Nigeriå

Åll rights reserved. No pårt of this publicåtion måy be reproduced, stored in å retrievål system, or trånsmitted in åny form or by åny meåns, electronic, mechånicål, photocopying or otherwise, without the prior permission of Longmån Nigeriå Plc.

© Longmån Nigeriå Plc 2014First published 2014

ISBN 978 978 925 104 9

Illustråtions by Franklin Oyekusibe

Hausa prel 6.indd 4 9/11/14 10:12 AM

Page 5: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

v

Abubuwan da ke Ciki

Babi Shafi

1 Tsarinsassau˚arjimla 1 Ma'anar jimia 1 Aiki 2 Tambayoyi 2 Jagora 3

2 Kalmomimasuma'ana∂aya 4 Suna 4 Aiki 5 Siffa 5 Tambayoyi 6 Jagora 7

3 Karatu don auna fahimta 8 Maha˚urcimawadaci 8 Muhimman kalmomi 10 Aiki 11 Tambayoyi 11 Jagora 11

4 Cigabadarubuntunwasika 12 Wasi˚a'yargida 12 Misalanwasi˚a'yargida 13 Tambayoyi 14 Aiki 14 Jagora 16

Hausa prel 6.indd 5 9/11/14 10:12 AM

Page 6: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

vi

5 Ci gaba da rubutun hannu 17 Manyanba˚a˚enHausa 17 anananba˚a˚enHausa 17 Manyantagwayenba˚a˚enHausa 17 ananantagwayenba˚a˚enHausa 17 Manyan wasulan Hausa 17 anananwasulanHausa 18 Manyan wasula masu goyo 18 anananwasulamasugoyo 18 anananwasulamasugoyo 18 Aiki 18 Jagora 19

6 Karatungajerunwasanninkwaikwayo 20 Ma'anar wasan kwaikwayo 20 Wasan gyara kayanka 20 Wasan langa 22 Tambayoyi 23 Jagora 23

7 Rubatattunwa˚o˚i 24 Ma'anarrubutacciyarwa˚a 24 Mu je nema ilmu 24 Baiti 25 Amsa-amo 25 Ma'anarke∫a∫∫unkalmomi 25 Aiki 26 Tambayoyi 26 Jagora 27

8 Dabaruntafiyardarayuwa 28 Ma'anar dabarun tafiyar da rayuwa 28 Matakan tsara rayuwa 28 Îa namiji 28

Hausa prel 6.indd 6 9/11/14 10:12 AM

Page 7: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

vii

'Ya mace 28 Îabarun tafiyar da rayuwa 28 Tambayoyi 30 Jagora 31

9 Shanmiyagun˚wayoyi 32 Ma'anarmiyagun˚wayoyi 32 Illolinshanmiyagun˚wayoyi 33 Muhumman˚almomi 34 Aiki 34 Tambayoyi 34 Jagora 35

10 Wasannindandali 36 Wasan dandali na maza 36 Wasan dandali na mata 37 Wasan dandali na maza 39 Tambayoyi 40 Jagora 40

11 Hanyoyinsadarwa 41 ire-iren hanyoyi sadarwa 41 Hayoyin sadarwa na gargajiya 41 Hanyoyin sadarwa na zamani 42 Tambayoyi 44

12 Hanyoyinsufuri 45 Ma'anar sufuri 45 Hanyoyin sufuri 45 Tambayoyi 47 Jagora 47

13 Bukkukuwan Hausawa 48 BukukuwanSallah˚aramadababba 48 Muhimman kalmomi 50 Muhimmancin bukukuwan 51

Hausa prel 6.indd 7 9/11/14 10:12 AM

Page 8: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

viii

Tambayoyi 51 Aiki 52 Jagora 52

14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman kalmomi 57 Aiki 58 Tambayoyi 58

Hausa prel 6.indd 8 9/11/14 10:12 AM

Page 9: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

ix

Gabatarwa

An rubuta jerin wannan littatafi guda shida mai suna Hasken Karatudonakoyawa∂alibai

namakarantunfiramaredagashekarata∂ayazuwatashida.Anrubutadarussanda

zaakoyartabinsabuwarmanhajarHausawaddaHukumarBincikedaHa∫akaIlimita

Nijeriya(NERDC)tashirya.Darussandakecikinwa∂annanlitattafaisunshafifannonin

nahawudaadabidaal’adunHausawa.Anyiamfanidahanyoyisau˚a˚awajentaimakon

koyardawa∂annanlitattafaicikinsau˚i.Wa∂annanhanyoyisunha∂ada:

1 Akwai shiryayyun tambayoyi, masu sa a karanta darasi, a fahimce shi sosai kafin

bayar da amsoshin.

2 Akwaizanenhotuna,daalamominrubutu,adukwurindayakamata,don˚ara

armasa karatu da ilimantarwa, musamman don gane abubuwan, da ake bayani

sosai.

3 Akwai jagora a karshen kowane babi, don baiwa malami haske game da yadda

zaigudanardakoyarwa,dakuma˚arinhaskecikinwasulitattafan.

Anafatanidan∂alibiyagamawa∂annanlitattafaigudashida,tozaisamicikakkiyar

shimfi∂atafahimtarfanninHausa.Donhaka,muhimmiyarmanufarwannanlittafi,ita

cesamarwamalamaiabubuwandazasukoyarcikinsau˚i,sukuma∂alibaisuga

darussan da ake koya masu a zahiri. Allah ya taimake mu, amin.

Hausa prel 6.indd 9 9/11/14 10:12 AM

Page 10: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

x

Hausa prel 6.indd 10 9/11/14 10:12 AM

Page 11: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

1

Babi na 1

Tsarin sassau˚ar jimla

Ma’anar jimla

Jimla zan ce ne mai cikakkiyar ma’ana, wanda ya ˚unshi tarin kalmomi da ke kan

˚a’idar harshe. Ga wasu misalan jimloli nan:

1 Mudi ya tafi makaranta.

2 Makarantarmu tana da girma.

3 Littafin samir ya fi na Hassan girma.

4 Tattabara ta tashi sama.

5 Samira ˚awar Hassana ce.

6 Ladi ta ∂ebo ruwa.

7 Kare yana bacci.

8 Audu soja ne.

9 Binta ta yi ha˚uri.

10 Yara sun tafka ta’adi.

Duk wa∂annan jimloli da ke sama sau˚a˚a ne. Sassau˚ar jimla tana da sassa guda

biyu muhimmai. Akwai sashen suna da kuma sashen bayani.

Jimla

Sashen suna Sashen bayani

Hasken Karatu Bk 6 .indd 1 9/11/14 8:56 AM

Page 12: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

2

Yawanci sukan zo a farkon jimla, sai kuma sashen bayani da ke bayani kan abin da

aka fa∂a game da suna, ko abin da suna ya aikata. Ga misalan jimloli sau˚a˚a

tare da sassansu:

Jimla

Sashen suna Sashen bayani

Mudi + Ya tafi makaranta.

Ladi + ta ∂ebo ruwa.

Rago + dabba ne.

Audu + soja ne.

Samira + ˚awar Hassana ce.

Wata mata + ta shigo.

Wani yaro + ya tafi kasuwa.

Ba˚ar mota + Mudi ya saya.

Littafi na + ja ne.

Wasu yara + za su zo.

Aiki

A Fito da sassan wa∂annan jimloli:

1 Malam ya yanka rago.

2 Wata tinkiya ta kasa.

3 Ladi ta ∂ebo ruwa.

4 Hausa babban harshe ne.

5 Gidan sabo ne.

6 Yara akwai ˚iriniya.

7 Binta ta yi ˚o˚ari.

8 Audu ya shiga soja.

9 Biri ya hau bishiya.

10 Habu kirki gare shi.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 2 9/11/14 8:56 AM

Page 13: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

3

B Gina jimloli ta hanyar cike guraben da aka bayar a ˚asa:

Sashen suna Sashen bayani

Wani yaro

ya cinye dusa

Malam

sun firgita

Tulu

ta rame

Wasu mata

wanke mota

Riga

dogo ne

Tambayoyi

1 Ware kalmomin da ke nuni da aiki da kuma wa∂anda suke nuni da suna:

tafka tattabara, Hassan, ∂ebo kare, makaranta, tashi, yara, yanka.

2 A tsarin sassaukar jimla wanne ne ya fi muhimmanci tsakanin sashen suna

da kuma sashen bayani?

3 Kawo misalai guda biyar na yankin jumla da yakan zo a shashen suna.

4 Wa∂anne abubuwa ne suke zuwa a ˚arkashin sashen bayani? Kawo su tare da

ba da misalai a cikin jimla.

5 Bayyana ma’anar wa∂annan kalmomi, sannan a yi ˚okarin gina sau˚a˚an jim

loli da su:

a) Girma b) Ta’adi c) Îebo d) Bishiya e) Littafi

Jagora

Malami ya kawo wasu misalan jimlolin a aji, tare da nuna wa yara sassan jimlo-

lin. Sannan ya bu˚aci yara su yi ˚o˚arin misalta kawo makunar sassau˚ar jumla,

da kuma iya ra rrabewa tsakanin sassau˚a da wadda ba sassauka da, don duk

inda suka ga sassau˚ar jumla za su yi saurin fahimta.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 3 9/11/14 8:56 AM

Page 14: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

4

Babi na 2

Kalmomi masu ma’ana ∂aya

Kalma dai zance ne mai cikakkiyar ma’ana, wadda ake nunawa a rubuce ta hanyar

barin fili tsakaninta da yar’uwarta. Misalan kalma sun ˚unshi:

a) Gida b) Abinci

c) Aiki d) Ba˚i

e) Kasuwa f) Gyara

g) Zo h) Tafi

da sauransu.

Kowace kalma muka gani a Hausa, tana da ma’ana. Misali:

a) Gida: Na nufin muhalli ko wurin zama.

b) Abinci: Na nufin abin da akan ci ko akan sha, misali;tuwo ko kunu da sauransu.

c) Aiki: Na nufin aiwatar da wani abu.

d) Ba˚i: Na nufin launi marar haske ko mai duhu.

e) Kasuwa: Na nufin wurin saye da sayarwa da sauransu.

A Hausa akan iya samun kalmomi fiye da guda ∂aya, amma kuma ∂auke da ma’ana

iri ∂aya. Wato dai a nan, ana nufin kalmomi ne iri biyu ko uku ko ma fiye, amma abu

∂aya suke nufi. Wa∂annan irin kalmomi na iya zuwa a sigar suna ko aiki ko sifa da

sauransu.

Ga wasu daga cikin misalan irin wa∂annan kalmomi:

Kalmomi masu ma’ana iri guda

Suna

a) Gida - muhalli

b) Taimako - agaji- tallafi

c) Hula - tagiya

Hasken Karatu Bk 6 .indd 4 9/11/14 8:56 AM

Page 15: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

5

d) Mayafi - gyale

e) Akwatu - adaka

f) Mutuwa - rasuwa

g) Mage - kyanwa - kuliya

h) Salga - shadda

i) Makulli - mabu∂i

j) Talge - ru∂e

k) Hanya - titi

l) Rafi - kogi - ˚orama

m) Kafa - sawu

n) Bango - garu

o) Masai - salga

p) Darbejiya - bedi

q) Awaki - bisashe

r) Farce - ˚umba

Aiki

A yi amfani da wa∂annan kalmomi da ke biye a cikin jimla.

1 haukace - ta∫u

2 kar∫i - amshi - ungo

3 kalli - dubi

4 tafi - je

5 dakata - jira - tsaya

Ga misalan yadda wasu daga cikin wa∂annan kalmomi za su iya zuwa a cikin jimla:

1 Yana da gida = Yana da muhalli.

2 Samira ta sayo ba˚in gyale = Samira ta sayo ba˚in mayafi.

3 Hassan ya sami taimako = Hassan ya sami tallafi = Hassan ya sami agaji.

4 Yaro ya tafi makaranta = Yaro ya je makaranta.

5 Kalli yadda Malam yake rubutu = Dubi yadda Malam yake rubutu.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 5 9/11/14 8:56 AM

Page 16: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

6

Siffa

a) Babba - ˚ato

b) Gajere - guntu

c) Girma - ∂aukaka

d) Lukuti - ˚ato

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Mece ce kalma?

2 Kawo misalan kalmomi guda goma.

3 Ta yaya ake gane kalma a rubuce?

4 Gina jimla da kowace ∂aya daga cikin wa∂annan kalmomi:

a) Allo b) Makaranta c) Kwamfuta d) Sarki e) Tsintsiya

5 Kawo kalmomi da suke da ma’ana ∂aya da wa∂annan kalmomi da ke biye.

a) Tufa b) Farce

c) afa d) Waina

e) Bango f) ofa

g) Kallabi h) Kumallo

i) Ban∂aki j) Ciyawa

6 A Hausa akan samu kalmomi fiye da guda ∂aya, amma ∂auke da __________.

a) ma’ana iri ∂aya

b) ma’ana shida

c) ma’ana ∂aya da wata jumla

7 Kalmomi masu ma’ana iri guda ana samu a __________ da __________ da

__________ da sauransu.

a) jimloli da sauti da wasali

b) suna da aiki da siffa

c) ba˚i da harafi da wakilin suna

8 Kalmar masai ana kuma iya ambatarta da __________.

a) ban-∂aki

b) salga

c) soro

9 Kowace kalma a Hausa tana da ma’ana?

a) A’a ba ta da ma’ana.

b) E tana da ma’ana.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 6 9/11/14 8:56 AM

Page 17: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

7

10 Misalan kalmomi sun ha∂a da __________.

a) buta da tabarma da allo

b) takarda, da, gida, k

c) h, g, w, s, t.

11 Me ka/ki fahimta da kalmomi masu makina ∂aya, kuma ta yaya ake gane su a

cikin jumla?

12 Amfani da kalmomi masu ma’ana ∂aya a lokaci guda zai iya haddasa __________.

a) fahimtar zance b) rashin fahimtar ma’lana ta abin nufi

d) Samar da jumla mai makina e) samar da jumla marar ma’aria

13 Rubuta wani gajeran insha’i wanda zai nuna yadda aka yi amfani da kalmomi

masu makina iri ∂aya, amma kuma kalmomin su bambanta; ta hanyar ja wa

kowace kalma layi a ˚asanta.

14 Me ake nufi da:

a) Hula/tagiya b) Bango/garu c) Farce/˚umba

d) Awaki/bisashe e) Talge/ru∂e

15 Kalmomi masu ma’ana ∂aya suna ba da manana a cikin jumla in an __________.

a) yi amfani da ∂aya an bar ∂aya b) in an yi amfani da dukkasu

c) in an hargitsa su d) in an yi musu alama a ˚asansu

Jagora

Malami tare da ∂alibai su kawo ire-iren wa∂annan kalmomi a cikin aji, tare da

kawo ma’anoninsu. Malami ya kawo wa ∂alibai wasu kalmomi, don ∂alibai su

nemo ma’a noninsu a rubuce a matsayin aikin gida. Sannan daga baya malami ya

yi ˚o˚arin sa yara su gina jumloli ta hanyar yin amfani da wa∂annan kalmomi da

suka nemo makinoninsu a cikin aji a aikace.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 7 9/11/14 8:56 AM

Page 18: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

8

Babi na 3

Karatu don auna fahimta

Maha˚urci mawadaci

An ta∫a yin wani sarki a can wata ˚asa. Sarkin nan ya ˚asaita, kuma yana mulkin ˚asa

babba. Sai dai Allah bai ba shi ∂a nasa na cikinsa ba. Don haka babu abin da ya dame

shi illa rashin wanda zai gaje shi a sarauta, bayan rai ya yi halinsa.

Kullum sarkin nan ya kwanta barci cikin dare, babu abin da yake damunsa illa

tunanin wanda zai gaje shi. Yakan kai can talatanin dare yana ta tunanin mafita. Ana

nan, ana nan, yana yin irin wannan tunani, wata rana da dare kwatsam sai wani tunani

ya zo masa a rai.

Bayan wasu ‘yan kwanaki, sai Sarki ya sa San˚ira ya yi shela a gari cewa, yana

umartar duk matasa da dattawan gari su taru a ˚ofar fada kashe-gari da hantsi. Bayan

duk jama’a ta taru, sai ya yi masu jawabi kamar haka: ‘Ya jama’ata. Kun san Allah

bai arzuta ni da haihuwa ba, don haka ba ni da magaji. Ga shi kuma na tsufa ˚warai.

Yanzu zan fito da gasa ga duk matasan garin nan, amma wa∂anda suke da sha’awar

shiga gasar, zan raba wa kowanne wake ˚waya ∂aya ya tafi ya sami wani abu ya

shuka a ciki. Kowa zai dawo mani da wakensa bayan mako biyu daga yau ∂in nan.

Duk wanda wakensa ya fi kyan fitowa, to shi ne zan dan˚awa sarautata, ni kuma na

huta.’

Hasken Karatu Bk 6 .indd 8 9/11/14 8:56 AM

Page 19: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

9

Dukkan wa∂anda suka kar∫i ˚wayar wake, kowa ya tafi ya sami wani abu ya

shuka wakensa. Wani ya sami ‘yar tukunya, wani ya nemi gwangwani, wani ya nemi

roba, wani ma a cikin ˚o˚o ya shuka nasa waken.

To a cikin samarin da suka kar∫i waken nan, akwai wanda har bayan wajen kwana

biyar nasa waken bai fito ba. Bayan kamar mako ∂aya bai ga ya fito ba, sai ya fara

tambayar sauran abokansa da suka kar∫i waken, ko nasu ya fito? Dukkansu suka ce

lallai nasu waken ya fito. Daga nan sai hankalinsa ya fara tashi. Bayan ya bayyana

wa mahaifansa damuwarsa sai suka ce ya ˚ara ha˚uri, ˚ila shi ma nasa waken zai fito

daga bisani.

Bayan dai wasu ‘yan kwanakin sai ya sami mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya fa∂a

masu cewa shi fa wakensa bai fito ba, don haka zai je kasuwa ya sayo wani waken ya

shuka ko Allah zai sa ya fito, ya yi kyau kafin ranar da za su koma fada. Sai

iyayensa suka garga∂e shi cewa, kada ya yarda ya aikata rashin gaskiya iyakar tsawon

rayuwarsa, komai muhimmancin abin da yake so. Suka tunatar da shi cewa idan fa ya

aikata rashin gaskiya har ya sami sararutar nan, to fa har abada zai ri˚a tuna rashin

gaskiyar nan da ya aikata, kuma za ta yi ta damunsa. Idan kuma ya aikata rashin gas-

kiyar amma kuma waken wani ya fi nasa kyawun fitowa shi bai sami sarautar ba, nan

ma ya yi aikin banza. Suka ce ya yi ha˚uri, domin dai Allah shi ne ke bayar da abin da

Yake so ga wanda Yake so ya bai wa. Saurayi ya ji maganar mahaifansa, ya ha˚ura.

Duk da haka dai bai daina bai wa waken nan ruwa yana kula da shi ba, duk da dai bai

fito ba.

Ranar komawa fada, haka saurayin nan ya ∂auki tukunyar da ya shuka wake ya

je ya bi layi. Duk waken sauran samarin ya yi kyau ˚warai da gaske, domin kowanne

nasa ya fito abin gwanin ban sha’awa. Daga nan sai gaban shi wannan saurayi ya rika

bugawa. Ko yaya sarki zai yi da shi? Ko zai sa a kama shi a ∂aure? Ko korarsa zai sa

a yi, a fitar da shi daga gari?

Sarki ya fara bin layin da samarin garin nan masu gasar neman sarauta suka yi.

Dukkan wanda sarki ya je sai ya ce masa: ‘Wannan shi ne waken da na ba ka ya fito

ya yi kyau haka?’ Sai shi kuma ya ce: ‘E! Ran Sarki ya da∂e!’ Sai Sarki ya ce: ‘Amma

dai ka yi ˚o˚ari. Ka kula da wakenka sosai’. Can sai Sarki ya isa kan wannan saurayi.

Ya ce masa: ‘Kai yaya naka waken bai fito ba? Ko ba ka shuka ba ne?’ Saurayi ya ce

da Sarki: ‘Ran Sarki ya da∂e na shuka, kuma na yi ta ba shi ruwa, amma ya ˚i fitowa.’

Hasken Karatu Bk 6 .indd 9 9/11/14 8:56 AM

Page 20: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

10

Daga nan sai Sarki ya ce masa ya fito ya biyo shi. Saurayi ya yi kamar ya zura

a guje, gabansa yana ta dub! dub! dub! ∂on fa∂uwa. Bayan Sarki ya kai karagarsa,

mutane su kuma sun zuba wa sarautar Allah ido, sai ya ∂aga hannun wannan saurayi

ya ce: ‘Ya jama’ata! Ga wanda zai gaji gadon sarautata’. Sai kowa ya fara mamaki,

mutane suna ta gunaguni suna cewa junansu: ‘A! Yaya wanda wakensa bai fito ba, bai

ci jarrabawar ba, Sarki zai ce shi ne magajinsa?’

Can sai Sarki ya ˚ara cewa: ‘Ku saurara jama’a!’ Kowa ya yi tsit yana jira ya ji abin

da Sarki zai ce. Daga nan Sarki ya ci gaba da cewa: ‘Kowane wake da na bai wa duk

wa∂annan samari ba wake ne da zai iya fitowa ba. Sai da na sa aka dafa waken aka

shanya shi a rana ya bushe sannan na ba su. Kun san kuwa dafaffen wake ba ya iya

fitowa. Duk wa∂anda kuka ga wakensu ya fito lallai ba waken da na ba su suka shuka

ba, wani suka sayo a kasuwa suka shuka ganin cewa wanda na ba su bai fito ba. Shi

kuwa wannan saurayi saboda gaskiyarsa ya hakura ya yi ta bai wa waken da na ba

shi ruwa, yana ta kula da shi har zuwa wannan rana. Kun san kuwa duk wanda zai

yi sarauta ya kamata a ce mutum ne mai gaskiya da kuma ha˚uri da duk halin da ya

tsinci kansa a ciki.’

Muhimman kalmomi

Kalma Ma’ana

1 Talatanin dare Tsakar dare

2 Kwatsam! Ba zato ba tsammani

3 Shela Sanar da jama’a ta hanyar yekuwa

4 San˚ira Sarkin maro˚an baka

5 Karaga Gado ko kujerar zaman sarki a fada

6 Gunaguni Surutai na rashin amincewa da wani abu

7 Magaji Mai gadon wani

8 asaita Daukaka da babban matsayi

9 Rai ya yi halinsa Mutuwa

10 Kashegari Gobe

Hasken Karatu Bk 6 .indd 10 9/11/14 8:56 AM

Page 21: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

11

AikiCike wa∂annan guraben da aka bari ta hanyar amfani da wa∂annan muhimman kalmomi da ke sama.1 __________ suka ga ya duro.2 Nan da nan sarki ya sa __________ ya sanar.3 Saboda tsabar __________, komai yi masa ake yi. 4 Sarki ya yi umarni __________kowa ya zo bakin fada. 5 Tun kafin a je asibiti __________.6 Cikin __________ ∫arayi suka shiga gidansa.7 Sarki ya har∂e a kan __________ rsa.8 Mai __________ ya shiga lungu da sako yana sanarwa.9 Da abin bai yi masa dadi ba, sai ya tafi yana __________.10 Shekararsa arba’in yana sarauta, amma har yanza ba shi da __________.

TambayoyiAmsa wa∂annan tambayoyin:1 Mene ne babban abin da ya dami wannan Sarki?2 Wace hanya Sarki ya bi don sanar da mutane yana nemansu?3 Me Sarki ya bai wa samarin gari, kuma me za su yi da shi?4 Kawo abubuwa uku da samarin garin nan suka yi shuka a ciki.5 Wace shawara iyayen saurayin nan suka ba shi, da ya so sayo wake a kasuwa?6 Shin ya ∂auki shawarar tasu?7 Wane irin wake Sarki ya bai wa samarin?8 Me ya sa Sarki ya za∫i yaron da wakensa bai fito ba?9 Wane irin yanayi saurayin da wakensa bai fito ba ya shiga?10 Kawo halaye biyu da ya kamata a ce wanda zai yi sarauta yana da su?

Jagora

Malami ya samo wasu labarai daga wasu litattafai, a karanta, a yi bayanin tsauraran kalmomin cikin labaran, a kuma amsa tambayoyi. Sannan malami tare da shi da yara su yi ˚o˚arin fahimtar darasin da labarin yake ∂auke da shi tare da nuna wa yara muhimumancin koyi da wannan darasi ko kauce masa a rayuwa saboda illar da take tattare da abin.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 11 9/11/14 8:56 AM

Page 22: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

12

Babi na 4

Ci gaba da rubutun wasi˚a

Wasi˚a ‘yar gida

Irin wannan wasi˚a ita ce wadda ake rubuta wa iyaye da abokai da ‘yan’uwa da

sauran abokan arziki. Ana rubuta wannan wasi˚a don aikawa da gaisuwa ko isar da

wani sa˚o ko kuma don neman wata bu˚ata. Irin wannan wasi˚a na iya kasancewa

daga ∂a zuwa mahaifinsa ko daga aboki zuwa wani abokinsa. Haka nan, tana iya ka-

sancewa a tsakanin ‘yan’uwa ko ˚awaye.

Wannan wasi˚a ba kara zube ake rubuta ta ba, akwai tsari da ˚a’idoji da ake bi

wajen yin ta. Don haka, irin wannan wasi˚a takan ˚unshi abubuwa kamar haka:

1 Adireshin mai rubuta wasi˚a: Ana rubuta adireshin irin wannan wasi˚a ne a ∫arin

hannun dama daga sama.

2 Bu∂ewa: Ana rubuta ta ne daga ∫angaren hagu, wato a ˚asan adireshi da layi

∂aya. Misali, ‘Zuwa ga……’

3 Gabatarwa wadda ta ˚unshi gaisuwa: Wannan ma ana rubuta ta daga ∫angaren

hagu a ˚asan bu∂ewa, wato kafin a shiga gundarin rubutun wasi˚ar. Misali,

‘Bayan gaisuwa mai yawa…..’

4 Gangar jiki: A nan ne mai rubutun wasi˚a yake bayyana duk irin sa˚on da yake

son isarwa bayan ya yi gabatarwa. Akan fara rubuta ta a sakin layi na biyu, wato

bayan an yi gaisuwa.

5 Kammalawa: A kodayaushe, ita ce take zuwa a sakin layi na ˚arshe bayan an

gama bayyana irin sa˚on da ake son isarwa a gangar jikin wasi˚ar.

6 Sallamar rufewa: Ita ce take zuwa a ∫arin hannun dama a ˚asan kammalawa.

Misali, ‘Ka huta lafiya….’

7 Sunan mai rubuta wasi˚a da ala˚arsa da wanda aka rubutawa: Wannan ma yana

Hasken Karatu Bk 6 .indd 12 9/11/14 8:56 AM

Page 23: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

13

zuwa ne a ∫angaren hannun dama, wato ˚asan sallamar rufewa. Misali, ‘Ni ne

naka Mudi’.

Misalan wasi˚a ‘yar gida

Babbar Makarantar Sakandaren ‘Yanmata ta Garki,

Akwatin Gidan Waya, 1234,

aramar Hukumar Garki,

Jihar Jigawa.

22 ga Watan Agusta, 2011.

Zuwa ga Abbana,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da girmamawa, yaya gida da sauran ayyukan

gona. Yaya jikin Mama da fatan ta warware.

Bayan haka, dalilin rubuto maka wannan wasi˚ar shi ne, ina son na sanar da kai

cewar mun kusa fara jarabawa, da fatan za a taya mu da addu’ar samun nasara. Haka

kuma, ina son yin amfani da wannan damar domin na sanar da kai cewa, kayan da

na tafi da shi na abinci sun kusa ˚arewa, ga shi kuma za mu ˚ara kimanin mako uku

a makaranta kafin a yi mana hutu. Da fatan za ka samu ikon aiko min da su. Ina fatan

idan sun samu a ba wa malaminmu Malam Idris ya taho min da su, idan ya zo hutun

˚arshen mako. Ka huta lafiya.

Daga ‘yarka

Samira.

Ga wata wasi˚a da Hassan ya rubuta wa Samir daga makarantarsu ta Tarauni.

Makarantar Firamare ta Tarauni,

Hasken Karatu Bk 6 .indd 13 9/11/14 8:56 AM

Page 24: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

14

Akwatin Gidan Waya, 565,

Karamar Hukumar Tarauni,

Jihar Kano,

11 ga Yuli, 2005.

Zuwa ga abokina Samir,

Gaisuwa mai tarin yawa da fatan komai yana tafiya daidai. Yaya gida da sauran abo-

kai. Da fatan kowa yana nan lafiya.

Dalilin rubuto maka wannan wasi˚ar shi ne, domin na sanar da kai cewa, nan ba

da da∂ewa ba zan yi abin hawa. Mahaifina ya sanar da ni cewa, idan na cinye jara-

bawata ta wannan zangon karatu, to zai saya mani sabon keke. Ina fatan za ka taya ni

da addu’a. Ina nan dai ina fatan idan na gama aji shida a nan, na zo makarantarku ta

Kwalejin Barewa a nan Zariya.

Da fatan za ka isar min da gaisuwata ga dukkan abokanmu.

Naka har kullum,

Hassan Abdullahi.

Tambayoyi

Amsa wa∂nnan tambayoyin:

1 A wane ∫angare ake rubuta adireshin mai rubuta wasi˚a?

2 Me ake fara rubutawa bayan an rubuta sallamar bu∂ewa?

3 A ina ake bayyana sa˚on da ake son isarwa a wasi˚a?

4 Kawo salo iri biyu na rufe wasi˚a.

5 Me yake zuwa a ˚arshen wasi˚a?

agora

Aiki

A Sake rubuta wannan wasi˚a, tare da gyara kurakuren da ke ciki.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 14 9/11/14 8:56 AM

Page 25: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

15

Makarantar Koyon Aikin Likita

Akwahin gidan waya 222

Jihar Katsina

4 ga janairu, 2013

Zuwa ga abokina Mudi.

Gaisuwa mai yawa da fatan kana nan lafiya, tare da iyahinka. Bayan haka, na rubuto

maka wannan wasika ne don in fa∂a maka cewa na gina sabon gida, kuma sati mai

zuwa ma zan tare. Da fatan za ka yi mini addu a.

ni ne abokinka har kullum,

Sadi Mani.

B Sake rubuta wannan wasi˚a da ke biye, tare da gyara kurakuren da aka yi a ciki.

Queen amina college,

P.O.Box 323,

Kaduna,

Kaduna State

6 ga afrilu, 2010

Zuwa ga kawata hadiza,

Ahayye, ayyururui! Na rubuto miki wannan wasi˚a ne don in taya ki murnar aure

da kika yi. An ce an sha shagali, ga shi kuma ni ba na nan. Ina yi miki fatan alheri da

zaman lafiya. Allah ya kawo kazantar ∂aki.

taki a kodayaushe,

Lami Tanko

Hasken Karatu Bk 6 .indd 15 9/11/14 8:56 AM

Page 26: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

16

Aiki

1 Rubuta wasi˚a yar gida zuwa ga malaufiyarka, sannan ka ci cikakken bayani a

kan muhimman sassan da ta kansa, kana yi kana ba da misalai.

2 Rubuta amsar wasi˚ar da wani ∂ankuwanka ya ta∫a rubuto maka bayan ka

aika masa da sa˚on wasi˚a wadda ka rubuta masu da jimawa.

Jagora

Malami ya yi wa ∂alibai bayani dalla-dalla kan matakan rubuta wasi˚a ‘yar gida,

da kuma kowane ∫angare da ta ˚unsa. Malami ya ba wa yara aikin gida domin su

rubuto wasi˚a ‘yar gida. Haka kuma malami ya umarci ∂alibai da su fito gaban allo

su rubuta yadda ake tsara muhimman ∫angarorin wasika don sauran ∂alibai su

gani a aikace. Sannan ya fito musu da gyare-gyaren da ya gani.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 16 9/11/14 8:56 AM

Page 27: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

17

Babi na 5

Ci gaba da rubutun hannu

Manyan ba˚a˚en Hausa

Bı C DÎ F G H J K

L M N R S T W Y

Z

ananan ba˚a˚en Hausa

b∫ c d∂ f g h j k˚ l

m n r s t w y z

Manyan tagwayen ba˚a˚en Hausa

FY GY KW KY W Y SH

TS ‘Y

ananan tagwayen ba˚a˚en Hausa

fy gy kw ky ˚w ˚y sh ts ‘y

Manyan wasulan Hausa

A E I O U

Hasken Karatu Bk 6 .indd 17 9/11/14 8:56 AM

Page 28: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

18

Aiki

A Malami ya karanta wa yara wa∂annan kalmomi, su kuma suna rubutawa a litta-

finsu na aiki da fensiri.

Agogo Aljihu Alkyabba Amawali

Birni Bature Barkono Burodi

ıauna ıarawo ıarna ıuruntu

Carki Carafke Carbi Ciromawa

Dambe Dawa Daddawa Dawanau

Îan∂ano Îaki Îumi Îorawa

Fara Farmaki Fure Farfesu

Gara Gulma Gira Goge

Gyara Gyauro Gyatsa Gyan∂ama

Haki Hausa Hira Harawa

Jaki Jama’a Jere Jima

B Rubuta manyan ba˚a˚en Hausa:

_______________________________________________________________

_______________________________________________________________

ananan wasulan Hausa

a e i o u

Manyan wasula masu goyo

AI AU

ananan wasula masu goyo

ai au

Hasken Karatu Bk 6 .indd 18 9/11/14 8:56 AM

Page 29: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

19

C Malami ya karanta wa yara wa∂annan jimloli da ke biye, su kuma su rubuta a lit-

tafinsu na aiki da fensiri.

1 Zan tafi makaranta gobe da safe.

2 Ina zuwa makaranta sau biyar a sati.

3 Baba ya sayo masara.

4 Ali ya karanta littlafi.

5 Gobe za mu tafi Kaduna.

6 Binta takan je kasuwa.

7 Kande tana kuka.

8 Audu yaro ne mai ˚wazo.

9 Biri ya iya ∫arna.

10 Takalmina sabo ne.

D Malami ya karanta wannan rubutu da ke biye. Yara su rubuta abin da malam ya

fa∂a a cikin littafinsu na aiki.

Bayan mun gama cin abinci, sai muka koma kar˚ashin wata ˚atuwar bishiya mai

inuwa, muka kwanta. Can zuwa yamma, sai muka rin˚a jin wata ˚ara tana doso

inda muke. Duk hankalinmu ya tashi. Kafin ka ce me, sai muka ga ashe wata irin

guguwa ce mai ˚arfin gaske.

Jagora

Malami ya ˚ara ba wa yara ayyukan da suka shafi rubutu. Malami ya duba rubuce-

rubucen da yara suka yi, tare da yi musu gyara a wuraren da suka yi kuskure. Malami

ya gwada wa yara yadda ake rubiutu a allo da ma yadda ake ri˚e fensiri a yayin rubutu.

Rubuta ˚ananan ba˚a˚en Hausa ta hanyar cike gurabun da aka bari:

––– ∫ c d ––– ––– g ––– j ––– ––– l ––– n r ––– t w ––– –––

Hasken Karatu Bk 6 .indd 19 9/11/14 8:56 AM

Page 30: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

20

Babi na 6

Karatun gajerun wasannin kwaikwayo

Ma’anar wasan kwaikwayo

Wasan kwaikwayo na Hausa , wasa ne da ake yi don kwaikwayar wasu halaye na cikin

al’umma don yin gyara ko fa∂akarwa ko garga∂i ga jama’a. Wato wasan kwaikwayo

yana nuni da al’adun Hausawa da ake misalatawa a aikace, wanda ya shafi gargajiya

da kuma zamani. Wasan kwaikwayo yana ∂auke da darussa. Fitattu kuma muhimmai

daga ciki sun ha∂a da:

1 Fa∂akarwa

2 Garga∂i

3 Wayar da kai

4 Hannunka mai sanda

5 Nasiha, da sauransu.

Baya ga wasan kwaikwayo rubutacce ko wanda akan tsara a kan dandali ko na

gidajen rediyo da talabijin, yaran Hausa wa ma kan aiwatar da wasan kwaikwayo a

takaice, a cikin wasanninsu na dandali ta hanyar kwaikwayar wasu halayen zaman-

takewa. Ga wasan kwaikwayo mai taken ‘Gyara kayanka’. Ga wani wasan kwaikwayo

cikin wasannin yara na dandali:

Wasan gyara kayanka

Fitowa ta ∂aya

(Malam Mudi ya ha∂u da Mati, lokacin da yake dawowa daga kasuwa)

Malam Mudi: Mati Barka da rana, daga kasuwa kake ne?

Mati: Barka ka dai Malam Mudi, daga kasuwa nake.

Malam Mudi: Shin ka je taron da malaman kiwon lafiya suka kira a ˚ofar gidan mai

gari kuwa?

Hasken Karatu Bk 6 .indd 20 9/11/14 8:56 AM

Page 31: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

21

Mati: Ban je ba. A kan me kuma suke neman mutane?

Malam Mudi: Sun yi fa∂akarwa ne kan rigakafin kamuwa da cutar kwalara. Ka san

cutar tana da ha∂ari sosai.

Mati: Kai don Allah ˚ayale su. Su sun cika damun mutane da maganga-

nunsu marasa kangado. Allah ai shi ne magani.

Malam Mudi: Kai kuwa Mati ban san lokacin da za ka waye ba. Tun yanshe aka

daina irin wannan tunanin?

Mati: Wannan kai ta shafa. Kanka ake ji wai mahaukaci ya fa∂a rijiya. Ni ka

ga ma tafiyata. Neman kudina ya fiye mini wadannan surutan marasa

amfani.

(Mati ya tafi ya bar Malam Mudi ri˚e da baki yana mamkin kalaman Mati, yana bin sa

da kallo)

Fitowa ta biyu

(Mati ya shiga gidansa, ga shi can suna tattaunawa da matarsa Asabe ta yi ∂aurin

˚iriji)

Asabe: Maigida sannu da zuwa.

Mati: Yawwa Asabe sannunki, yaya akwai ∂an kunu kuwa?

Asabe: Kayya! Ai ba ta kunu ake ba maigida. Îan ragowar kunun ka ga inda

yaron nan sule ya amayar da shi. Tun da ka tafi yake amai.

Mati: Amai kuma? To me ya faru yake amai?

Asabe: Ai har ma da gudawa. Ni fa ina tsoro ko ciwon kwalar nan ne da ake

ta bayani. Ka san an ce kazanta ce take kawo shi. Don haka nake ta

damunka da ka gyara mana ˚ofar ban∂akinmu da ta karye tun tuni.

Dubi yadda ˚uda ke ta yawo a bakin masan can. Ga jujinmu kuma ya

taru ba ka kwashe ba.

Mati: Ke Asabe bana son zancen banza. An gaya miki cewa iya gidan nan

ne ake ˚azanta?

(Sule ya futo daga ∂aki ya fa∂i sharaf a ˚asa,amai da gudawa duk sun ∫ata masa jiki.

Idanunsa sun kakkafe)

Hasken Karatu Bk 6 .indd 21 9/11/14 8:56 AM

Page 32: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

22

Mati: La’ilaha illallah! Asabe yaron nan zai mutu. Don Allah tashi mu ruga

asibiti.

Asabe: (Ta tashi da sauri) Da ma ai na gaya maka maigida. Yanzu ai ka ga

dole ka tafi wajen malaman lafiyar da ka raina. (Sun kinkimi sule zuwa

asibiti)

Fitowa ta uku

(An yi sa’a sule ya farfa∂o, kuma ga likita can ma yana magana da Mati)

Likita: To Malam ka auna arziki. Wanan yaron naka cutar kwalara ce ta kama

shi, kuma da kun ˚ara minti ashirin a gida, ba ku kawo shi asibiti ba, to

do watakila tuni ya tafi lahira.

Mati: Likita mun gode, Allah ya saka da alheri.

Likita: A’a, ba godiya za ka yi ba, abin da yafi kyan shi ne ka kula da tsaftar

gidanka, domin kazanta ce take haddasa irin wannan ciwo.

Mati: Ai na yi hankali Likita. Ni kam daga yanzu ai sai dai in gaya wa wani.

Wasan langa

Wasan langa wasa ne da yara maza suka don kwaikwayar tsarin saurautan Hausawa,

musamman ta fuskar yaki tsakanin wani gari da wani. A waman wasa yara suna kasa

Hasken Karatu Bk 6 .indd 22 9/11/14 8:56 AM

Page 33: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

23

kansu gida biyu, wanda suke daukar kowana kaso a matsayin gari ne guda da sarkin-

sa wanda ake kira ‘ruwa’. Wasan kan dauki siffar yaki, wanda dokin ruwa shi ne sarkin

yaki. bangare guda ne yake fara samar da ‘ruwa’, kuma akwai wurin ‘sha’, wato jikin

wata bishiya ko wani dutse da ake son ‘ruwa’ ya je ya taba kafin a kashe shi.

Ragowar yaran su ne suke shigewa gaban ruwa a matsayin baraden ya˚i. Kowan-

nensu yakan ∂ana lagonsa, ‘yan wancan ∫angare su yiwo kan ‘yan ∫angaren da suke

da ‘ruwa’ don ˚o˚arin cire lagonsu ko kashe ‘ruwa’. Kowane ∫angare yana ˚o˚arin

nuna ya fi ∂aya ∫angaren ˚arfi, ta hanyar ture baraden ya˚in. Kowane ture lago, ana

∂aukarsa a bakin kisa ne, saboda haka ‘yan garin da aka fi ture wa lago ko aka kashe

‘ruwa’ a hannunsu, to su aka fi ˚arfi, kuma an cinye su ke nan.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Mene ne wasan kwaikwayo?

2 Fa∂i darussan wasan kwaikwayo guda uku.

3 Su wane ne suke yin wasan langa?

4 Me ake kwaikwayo a wasan langa?

5 Shin wasan kwaikwayo yana da muhimmanci a rayuwar Hausawa?

6 Wasan Gyara kayanka wasa ne da yake ___________.

a) nisha∂atarwa b) fa∂akarwa c) nuna soyayya

7 Shin Mati ya yi nadamar halayyarsa

a) Ee b) A’a

8 Yan wasa nawa ne suka fito a cinkin wasan?

9 Wata cuta ce ta kama Sule?

10 Ina aka kai Sule don yi masa magani?

Jagora

Malami ya yi ˚o˚arin kawo wa ∂alibai wasu wasannin kwaikwayo, na dandali na

mata da na maza domin su gabatar a aji. Malami ya dubi littafin ‘Wasannin Yara’

na Umaru Dembo ko wasu litaffafan. Malami ya karanta wa yara wani rubutaccen

wasan kwaikwayo, kamar ‘Uwar Gulma’ na Alhaji Muhammed Sada.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 23 9/11/14 8:56 AM

Page 34: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

24

Babi na 7

Rubutattun wa˚o˚i

Ma’anar rubutacciyar wa˚a

Wa˚a wani sa˚o ne da aka gina shi kan tsararriyar ˚a’ida ta baiti da ∂ango da rerawa

da kari da amsa-amo, wato ˚afiya da kuma sauran ˚a’idojin da suka shafi kalmomi da

za∫ensu da amfani da su cikin sigogi da suka sha bamban da na maganar baka.

Mu je neman ilmu

1 Farko Rabbana ma˚agina Allah,

Yau dai nai nufin na yo wa˚en ilmu.

2 Na yi kiran ku duk ku zo bayin Allah,

Ku ji zancen da zan yi don ba ya hammu.

3 Allah yai dare gari kuma ya waye,

Shi ko jahili a kullum sai zulmu.

4 Kowa ya sani fa komai ya canza,

Daddage ka je wajen neman ilimu.

5 Ga wani ya taho yana rara-gefe,

Ya tsuguna a can yana kalen damu.

6 Ni wallahi na yi le˚e na hanga,

Kar fa mu fan∂are wajen neman ilmu.

7 Zan fa∂i ∂an ka∂an na munin jahilci,

Shi ke jefa ∂an Adam a cikin zulmu.

8 Jahilci ka sa mutum a cikin dau∂a,

Kwas san ilmu to fa ba sauran zulmu.

9 In dai ka gano mutum na girman-kai,

In kai bincike fa to ba shi da ilmu.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 24 9/11/14 8:56 AM

Page 35: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

25

10 Ni dai kun ga ba ni ˚aunar jahilci,

Sai mu guje shi kar ya zo ya fi ˚arfinmu.

11 Ya ke ‘yar’uwa ki zo nan saurara,

Domin kar ku tintsira ramin zulmu.

12 Komai kyau a gun budurwa ga ˚ira,

Ba ta farin jini idan ba ta da ilmu.

13 Kai ku taho ku daina yawon iskanci,

Ni me zai hana na je neman ilmu.

14 Wai kyanwa a ce tanai wa kare gwalo,

Ta tsere cikin gida, mu ta bar mu.

15 To ni zan tsaya a nan bayin Allah,

Allah taimake mu gun neman ilmu.

Baiti

Baiti a rubutacciyar wa˚a, shi ne ∂ango ko ∂angwayen(layi ko layuka) da suka ha∂u

suka gina baiti. Baiti na iya kasancewa mai ∂ango ∂aya ko biyu ko fiye. Wannan wa˚a

ta zama tana da ∂angwaye biyu a cikin kowane baiti.

Amsa-amo

Amsa-amo shi ake kira da ˚afiya, wato sautin ga∫ar ˚arshe na kowane ∂ango ko ˚ar-

shen baiti. Akwai amsa-amon ciki, akwai na waje. Amsa-amon wannan wa˚a ta sama

shi ne ‘mu’.

Ma’anar ke∫a∫∫un kalmomi

1 Hammu: Na nufin cuta ko illa.

2 Zulmu: Na nufin tsoro.

3 Rara-gefe: Na nufin kauce-kauce.

4 Kale: Na nufin neman wani abu daga ∂an abin da ya rage.

5 Gwalo: Tsokana ta hanyar zaro harshe.

6 Ma˚agi: Wanda ya samar da abu.

7 Damu: Mommotsa fura da nono domin su hade guri guda.

8 Fan∂are: Kaucewa wani tsari.

9 Tintsira: Fa∂awa wani waje ba tare da shiri ba.

10 Kyauma: Mage kenan.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 25 9/11/14 8:56 AM

Page 36: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

26

Aiki

Za∫i wa∂annan kalmomi da ke biye don cike guraben da aka bari.

kale fan∂are ma˚agi gwalo hammu

damu tintsira zulmu rara-gefe Kyanwa

1 Yaro ya _________ ya buge a ˚eya.

2 Ba ma nufin yin wani _________ ga kowa.

3 _________ ta kame ∫eraye biyar.

4 Wannan aikin _________ ne.

5 Ba shi da gaskiya, ya taho yana _________.

6 Tsofaffi suna _________ a gona.

7 Wani yaro ya yi wa abokinsa _________.

8 Allah ne _________ kowace halitfa.

9 An yi masa ha∂a∂∂en _________ a kasuwar ˚auye.

10 Duk wanda bai bi gaskiya ba, to ya _________.

Tambayoyi

Amsa tambayoyin dake biye, sanan a chike guraben da aka bari.

1 Mece ce rubutacciyar wa˚a?

2 Amsa-amo guda nawa ya rabu?

3 Wane darasi wannan wa˚a ta sama take koyarwa?

4 Îango nawa kowane baitin wannan wa˚a yake da shi?

5 Rubuta wa˚a mai baiti biyu game da makarantarku.

6 A kan me aka rubuta wannen wa˚a?

7 Da me aka bayyana Jahili a wannen wa˚a?

8 In dai ka ga mutum yana _________, to ba shi da ilimi.

a) rowa b) aiki c) girman kai d) wayo

9 Duk kyan budurwa ba ta _________ Idan ba ta da ilimi.

a) girma b) farinjini c) aure d) mutuwa

10 Marubucin wannan wa˚a ya fa∂i abin da yake nufi da wa˚ar a ∂ango na _________.

a) uku b) biyu c) ∂aya d) takwas

Hasken Karatu Bk 6 .indd 26 9/11/14 8:56 AM

Page 37: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

27

Aiki

1 Wana sa˚o wa˚ar muje neman llimu take a∂auke da shi? Yi ̊ o˚arin ka iwo misalai

daga cikin wa˚ar kamar yadda ta zo a ci˚in wannan waje.

2 Me ya bambanta baiti da amsa-amo ta fuskar ma’ana da yadda siffarsu take a

cikin rubutacciyar wa˚ar? Kawo misalai daga wannan wa˚a mai suna ‘mu je ne-

man ilmu’.

10r

Jagora

Malami ya sa yara su rera wannan wa˚ar sannan a kawo masu wani littafi mai

∂auke da gajerun wa˚o˚i. Sanan kuma malami ya musu bayani yadda fadakar-

wan dake chikin wakokin zai amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 27 9/11/14 8:56 AM

Page 38: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

28

Babi na 8

Dabarun tafiyar da rayuwa

Ma’anar dabarun tafiyar da rayuwa

Dabarun tafiyar da rayuwa shi ne yadda ake tsara rayuwa bisa wasu tanade-tanade da

mutum zai ci galaba a rayuwa ta yau da kullum.

Matakan tsara rayuwa

Matakan tsara rayuwa sune matakai da mutum yakan bi na rayuwa tun daga haihuwa

har zuwa mutuwa. Akwai yan bambance-bambance a cikin irin wa∂annan matakai a

tsakanin namiji da kuma mace.

Îa namiji

Iyaye ne sukan ∂auki nauyin tsara wa ∂ansu namiji rayuwa, tun daga lokacin da suka

haife shi, har zuwa lokacin da ya isa aure, wato ya balaga. Daga nan yaro yakan ci

gaba da ∂aukar nauyin kansa da na iyalinsa har zuwa ˚arshen rayuwa.

‘Ya mace

Îaukar nauyin tsara rayuwar ‘ya mace na kan iyayenta ne tun daga haihuwarta, har

zuwa lokacin da za su yi mata aure. Bayan ta yi aure, sai mijinta ya ci gaba da ∂aukar

wannan ∂awainiya har illa ma sha Allah. Idan mijinta ya riga ta mutuwa, kuma Allah ya

sa tana da yaya, to su za su ci gaba da ∂awainiya da ita har zuwa ˚arshen rayuwarta.

Dabarun tafiyar da rayuwa

Mutum ba ya samun ingantacciyar rayuwa, sai in ya yi mata tanade-tanade na musam-

man. Ire-iren wa∂annan tanade-tanade sun kasu kashi-kashi kamar haka:

Hasken Karatu Bk 6 .indd 28 9/11/14 8:56 AM

Page 39: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

29

1 Samun ilimi mai inganci: Ilimi shi ne hasken rayuwa. Don haka matakin farko na

tsara rayuwa mai inganci, shi ne samun ingantaccen ilimi.

2 Bin hanyoyin kiyaye tsaro: Tsaro na da matu˚ar muhimmanci a rayuwa, ta yadda

idan babu shi, to ita kanta rayuwar ma ba za a yi ta cikin jin da∂i ba. Don haka

bin hanyoyin kiyaye tsaro na taka muhimmiyar rawa, wajen samun ingantacciyar

rayuwa.

3 Guje wa yanayin bala’i ko tarzoma: Idan aka ce babu zaman lafiya, to rayuwa

gaba∂ayanta ta shiga wani hali. Don haka guje wa duk wani abu da zai kawo

tashin hankali, babbar dabara ce ta tsara rayuwa mai amfani.

4 Kiwon lafiya: Lafiyar uwar jiki, babu mai fashi da ke. Babu yadda mutum zai samu

damar tafiyar da rayuwa idan babu ingantacciyar hanyar kiwon lafiya. Samar da

isassu, kuma ingantattun, asibitoci da ∂akunan shan magani da kuma isassun

likitoci da malaman kiwon lafiya, za su taimaka matu˚a wajen samar da ingantac-

ciyar rayuwa.

5 Dogaro da kai: Dogaro da kai wajen ˚o˚arin koyon sana’a da samar wa da kai

abin yi, na hana kwa∂ayi da hangen abin wani da ro˚o da sata da fashi da dai

sauran miyagun halaye wa∂anda zaman kashe wando ke haddasawa.

6 Kyautata sana’ar zamani: Kyautata sana’a bayan koyonta, ta yadda za ta tafi

daidai da zamani, na da matu˚ar muhimmanci. Rashin zamanantar da sana’a kan

hana ta ci gaba, wani lokaci ma sana’ar kan iya dur˚ushewa. Idan kuwa sana’a ta

dur˚ushe to rayuwa za ta shiga wani mummunan hali.

7 Kyakkyawar mu’amala: Kyakkyawar mu’amala na ∂aya daga cikin dabarun tafi-

yar da rayuwa. Kyakkywar mu’amala na sanya fahimtar juna da ˚auna da taimako

juna da ha∂in kai a tsakanin al’umma.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 29 9/11/14 8:56 AM

Page 40: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

30

8 Îa’a da biyayya: Girmama mutane da mutunta su, da bin umarnin na gaba, su ne

∂a’a da biyayya. Duk mutumin da ba shi da ∂a’a da biyayya, yakan zama bare a

cikin al’umma, domin babu wanda zai so ya yi mu’amala da shi ko ita.

9 Guje wa karya doka: Bin dokokin da hukuma ta shinfi∂a na nuna wayewar kan

mutum da sanin dabarun tafiyar da rayuwa. Karya doka shi ke jefa mutum cikin

fushin hukuma, wanda a ˚arshe kan jawo wa mutum ∂auri ko horaswa.

10 Guje wa cin hanci da rashawa: Bayar da cin hanci karya dokar ˚asa ne. Babu

yadda za a samu ingantacciyar rayuwa idan cin hanci ya yi katutu a cikin al’umma.

Cin hanci na iya rusa duk wata hanya ta samar da ingantacciyar rayuwa.

11 Guje wa shan miyagun kwayoyi: Daya daga cikin manyan hanyoyin da ke gur∫ata

rayuwa gaba∂ayanta, ita ce shan miyagun ˚wayoyi.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Mene dabarun tafiyar da rayuwa?

2 Îaukar nauyin rayuwar ∂a namiji kan tsaya ne a lokacin da ___________.

a) aka haife shi

b) aka yaye shi

c) ya yi aure

d) ya yi wayo

3 Bayan iyaye ___________ ne kan ∂auki nauyin rayuwar ya mace.

a) ‘ya’ya

b) miji

c) yayye

d) ˚awaye

4 Babbar hanyar tsara rayuwa ta farko ita ce samar da ___________.

a) abin yi

b) ku∂i

c) tarzoma

d) ilimi

Hasken Karatu Bk 6 .indd 30 9/11/14 8:56 AM

Page 41: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

31

5 Mece ce ∂a’a?

6 Kawo hanyoyi biyar na dabarun tafiyar da rayuwa?

7 Shin shan miyagun ˚wayoyi na gur∫ata rayuwa?

a) Ee b) A’a

8 Mene ne dogaro da kai?

9 Shin cin hanci na taimaka wa ˚asa?

a) Ee b) A’a

10 Mece ce kyakkyawar mu’amala?

11 Tsakanin ∂a da iyaye wane ne yake da ha˚˚in kula da yadda za a tsara matakan

rayuwa?

12 Yaushe ne mutum yake ˚o˚arin tanadar wa da kansa ingantacciyar rayuwa?

a) Da zarar an haife shi b) lokacin da ya yi wa rayuwarsa fanadi mai inganci

c) Lokacin da ya yi aure d) lokasin da iyayemsa suka ∂auki ∂awainiyarsa

13 Ya mace rayuwarta gaba ∂aya tana hannun iyayenta tun ___________.

a) haihuwarta b) bayan da ta yi aure c) lokacin da ta rasa mahaifanta

d) a lokacin ˚uruciya

14 Kawo kishiyoyin wa∂annan dabarun tafiyar da rayuwa:

a) Kiwon lafiya b) Kyakkyawar mu’amala c) Samun ilimi mai inganci

d) Shan miyagun ˚wayoyi e) Dogaro da kai f) Îa’a da biyayya

15 Wa∂anne irin bambance-bambance ake samu a matakan tafiyar da rayuwa

tsakanin mace da namiji? Kawo su tare da ba da misalai.

Jagora

Malami ya ˚ara kawo jerin wasu dabarun tafiyar da rayuwa, tare da tattauna su da

∂alibai. Malami ya ba wa ∂alibai damar kawo wasu dabarun tafiyar da rayuwa da

suka sani, da kuma yadda zasu maganta dabarun a rayuwarsu.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 31 9/11/14 8:56 AM

Page 42: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

32

Babi na 9

Shan miyagun ˚wayoyi

Ma’anar miyagun ˚wayoyi

Miyagun ˚wayoyi su ne dukkan wani abin da ake sha, wanda yake sa maye ko yake

birkitar da ˚wa˚walwa ko yake gusar da hankali. Addini ya hana mutum, ya yi amfani

da abin da zai kawar da hankalin da Allah Ya ba shi. Akawai miyagun ˚wayoyin da ake

amfani da su kai tsaye don su gusar da hankali. Akwai kuma wa∂anda ake yiwo su

da niyyar maganin wata cuta, amma ake yin amfani da su ba bisa ˚a’idar likita ba da

niyyar gusar da hankali.

Ga misalan wasu daga cikin miyagun kayan shaye-shaye da ake sha da niyyar

hankali ya birkice:

Hasken Karatu Bk 6 .indd 32 9/11/14 8:56 AM

Page 43: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

33

1 Wiwi: Wani mugun ganye ne da wasu suke sha, kamar taba da niyyar su lalata

tunaninsu. Wiwi tana lalata ˚wa˚walwa har ma ta kai ga hauka.

2 Giya/burkutu: Giya da burkutu wasu nau’o’i na kayan maye na ruwa ne, wa∂anda

idan aka sha su ma suke gur∫ata tunani da birkitar da shi. Idan mutum ya sha su

yakan rasa kuzarin yin ayyuka da rashin sanin halin da yake ciki da kuma kasa

tsayawa wuri ∂aya har ya ri˚a tanga∂i.

3 Sholusho: Wannan shi ma wani mugun nau’i ne na kayan bugarwa. Shi kamar

dan˚o ne na ruwa da ake yin amfani da shi wajen li˚in taya, amma wasu suke

sha˚arsa da niyyar bugarwa. Sholusho yana ∫ata ˚wa˚walwa da tunanin mutum

har ma ya iya haukacewa.

Ga kuma misalan magunguna da aka yi don warkar da cutattuka, Wasu na am

fani da su ta hanyar da ba ta dace ba da niyyar su bugu:

1 Baliyan: Baliyan wani magani ne da hukuma ba ta yarda a sha shi ba, sai likitane

ya rubuta wa mutum, musamman idan ana son maras lafiya ya yi barci. Amma

wasu sukan saya a ∫oye su sha fiye da kima domin su yi ta barci. Yawan yin haka

yana kai su ga lalata ˚wa˚walwarsu da tunaninsu.

2 Nau’o’in maganin tari: Akwai wasu nau’o’i na maganin tari da likita yake rubutawa

bisa ˚a’ida, amma wasu suke saya suna shan fiye da kima, don ya saka su cikin

barci mai nauyi da niyyar su mance wasu matsaloli ko damuwa ko ∫acin rai. Masu

shan irin wa∂annan magunguna, suna yin hasara ta harkokin rayuwa na yau da

kullum, kamar zuwa aiki ko makaranta ko yin ibada.

Illolin shan miyagun ˚wayoyi

Shan miyagun ˚wayoyi yana da illoli ˚warai da gaske. Manya daga cikinsu su ne ka-

mar haka:

1 Hauka: Hauka shi ne mutum ya rasa hankalinsa ko ˚wa˚walwarsa ta daina aiki

irin ta sauran mutane, kamar tunani da sanin ya kamata, har mutum ya ji shi ba

kamar sauran mutane yake ba, ya fice daga cikinsu.

2 Lalata rayuwa: Shaye-shaye na lalata rayuwar mutum. Mai shaye-shaye kullum

nema yake ya sami ku∂i don ya sayi kayan maye. Idan ba shi da ku∂i har sata

yakan yi don ya sami na abin sayen kayan shaye-shaye. Mai shaye-shaye bai cika

iya yin wani abin gina kai ba, domin ko dai ba shi da ˚arfin jiki ko yana cikin barci

Hasken Karatu Bk 6 .indd 33 9/11/14 8:56 AM

Page 44: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

34

ko da yaushe. Mai shaye-shaye hasara ne ga rayuwarsa, da iyayensa, da kuma

al’umma baki ∂aya.

3 Cutattuka: Shan miyagun ˚wayoyi na iya kawo cutattuka da dama, kamar lalace-

war ∫angarorin jiki irin su hunhu da hanta da ramewar jiki kuma mutum ya yi ba˚i

˚irin. Haka nan baki da idanuwansu sukan canza babu kyan gani.

4 Fita daga cikin jama’a: Mai shaye-shaye ko da yaushe yakan ke∫e kansa, ba ya

son yin mu’amala da mutane idan ba ‘yan uwansa masu shaye-shaye ba. Kullum

yana cikin tsarguwa ko za a gane halin da yake ciki. Wannan yana saka shi cikin

˚unci, abin kuma da yake ˚ara masa damuwa, ita kuma damuwar ta ˚ara sa shi

yin shaye-shayen kangarewa.

Muhumman ˚almomi

1 Birkita – Juyar da hankali.

2 Gusar – Kawar da wani abu ko hankali.

3 Bugu – Gushewar tunani yayin da aka sha abin maye.

4 Kima – Mutunci ko fiye da awon da ake so.

5 Ke∫e – Warewa waje guda ko gefe guda.

Aiki

Yi amfani da wa∂annan muhimman kalmomi na sama don cike guraben da aka bari

da wa∂anda suka dace.

1 Audu ya sha ˚waya ta __________ masa da hankali.

2 Ya sha ya __________ ya kasa tashi.

3 Saboda shaye-shaye, kullun sai dai ya __________ wuri guda.

4 Shaye-shaye ya __________ tunaninsa.

5 Kullum sai ya sha giya fiye da __________.

6 Duk wa∂annan misalai ne na miyagun kayan shaye-shaye in ban da ___________.

a) sholisho b) wiwi c) Lemun za˚i d) Baliyan e) giya/burkutu

7 Akwai miyagun ˚wayoyi da ake amfani da su ___________ don su gusar da han-

kali.

8 Nau’o’in maganin tari suna daga cikin ___________.

9 Baki da idanuwa sukan canza ___________.

10 Wiwi wani ___________ da wasu ke sha.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 34 9/11/14 8:56 AM

Page 45: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

35

Tambayoyi

Amsa wadanan tambayoyin:

1 Me ake nufi da miyagun ˚wayoyi?

2 Kawo iri-iren miyagun ˚wayoyi guda uku.

3 Kawo magunguna biyu da wasu suke sha don bugarwa.

4 Kawo illolin shan miyagun ˚wayoyi guda uku.

5 Shin shan miyagun ˚wayoyi yana amfani ga rayuwa?

6 Shin addini ya yi hani ga shan abin da zai gusar da hankali?

7 Me ake nufi da gushewar hankali?

8 Wane nau’i kayan bugarwa ne ake li˚in taya da shi?

9 Shin mai shaye-shaye yake an fanawa mutane wani abu?

10 Bayyana wasu alamu na mai shaye-shaye guda biyu?

11 Wanne irin hali iyayen mai shaye-shaye suke shiga a sanadiyyar

shaye-shayensa?

a) Farin ciki da annashuwa b) Bacin rai da bakin ciki c) Murna

d) Barace-barace e) Kaunar ∂an nasu

12 Hauka da lalata rayuwa manyan hanyoyi ne na __________.

a) sakamakon mara tunani b) masu ˚anya c) masu aikata shaye-shaye

13 Wanne nau’in maganine da Hukuma ba ta yarda a sha shi ba, sai in likita ne ya

rubuta wa mutum, amma ake sha don a bugu?

14 Wani nau’i na mugun kayan bugarwa mai kama da dan˚o na ruwa shi ake

kira __________.

a) Baliyan b) Sholisho c) Madara d) Alawa

15 Tsarguwa da kangarewa da damuwa yanayi ne da __________ kan shiga.

a) yan shaye-shaye b) masu sana’a c) mai yanayin bacci d) ∫arawo

Jagora

Malami ya jaddada wa ∂alibai illolin shan miyagun ˚wayoyi da kawo misalan irin mu-

tanen da suka lalace saboda shan miyagun ˚wayoyi.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 35 9/11/14 8:56 AM

Page 46: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

36

Babi na 10

Wasannin dandali

Wasan dandali abu ne da yara suke gudanarwa wanda ya ji∫inci nisha∂i ko raha ko

walawa. Yana iya kasancewa a cikin magana ne ko a cikin wasa. Wasa dai kishiyar

aiki ne. A yau akwai wasanni da yara suke gabatarwa wa∂anda sun shafi tsarin ra-

yuwarsu ta zamani. Irin wa∂annan wasanni yara suke gabatarwa a makarantunsu

da cikin gidajensu ko cikin unguwanni a matsayin wasannin dandali. Akwai ire-iren

wasannin dandali da suka ha∂a da:

a) Wasannin motsa jiki

b) Wasannin cashewa

c) Wasannin riyawa

Idan yara sun ha∂u, suna shirya wasanni iri-iri wa∂anda suka sha bamban wajen

tsarin gudanar da su. Ire-iren wa∂annan wasanni suna da yawa ̊ warai a ̊ asar Hausa.

Maza suna da irin nasu wasan, haka mata ma suna da irin nasu. Akwai kuma wasan-

nin dandali da maza da mata duka suke yi. Ire-iren wa∂annan wasannin sun ha∂a da:

a) Wasannin ∫uya, misali; burum-burum.

b) Wasannin kamu, misali; Allan baku.

c) Wasannin ∫ata, misali; kulli kucciya.

d) Wasannin kasada, misali; Jemage.

e) Wasannin kuzari, misali; Îan akuyana.

f) Wasannin tamore, misali; Se se se.

g) Wasannin gasa, misali; langa ko jan-igiya.

Wasan dandali na maza

Îan akuyana

Wannan wasan yara maza da ‘yanmata sukan yi shi. Idan za a yi shi, sai yara bakwai

Hasken Karatu Bk 6 .indd 36 9/11/14 8:56 AM

Page 47: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

37

zuwa goma su yi da’ira, su ri˚e hannayensu da kyau. Sai ∂ayansu ya cire hannayensa

daga ri˚o, ya shiga cikin tsakiyar da’irar, su kuma su marmatse su cike gurbin da ya

bari, su ritsa shi a tsakiyar da’ira. Ya zama kamar ∂an akuyan da aka kewaye, ya

rasa mafita. Yana ciki sai ya fara wa˚a, yana zagayawa, su kuma sauran suna amsa

wa˚ar. A lokacin da yake zagayawa cikin da’irar, yana yin wa˚ar, yakan ta∫a wuraren

da yaran suka ri˚e hannayensu, yana kuma kula da su yaran.

Idan ya gano inda suka yi sako-sako, kuma hankalinsu ba ya kan wasan sosai, sai

ya yi maza-maza, ya fice wubub da gudu, ya zarce zuwa wurin sha, su kuma su bi shi

da gudu suna duka. Idan sun dawo, sai su sake yin da’ira, wani ya shiga ya yi kamar

yadda wancan ya yi. haka za su yi ta yi har kowa ma ya samu shiga da’irar. Wa˚ar ita

ce kamar haka:

Bayarwa Amshi

Îan akuyana Damushere.

Ya shiga rumbu Damushere.

Za su kashe shi Damushere.

Nan da wu˚a˚e Damushere.

Nan da takobi Damushere.

Nan da su adda Damushere.

Nan da su lauje Damushere.

Nan da su sanda Damushere.

Nan da kulake Damushere.

Wubub na wuce nan Ina doka ka da yar gora ta.

Wubub na wuce nan Ina doka ka da ∂an kulki na.

Wubub na wuce nan Ina doka ka da ∂an kulki na.

Wasan dandali na mata

Su ma mata suna kafa wasannin ga∂a a dandali da dare. Akwai wasannin dandali na

ga∂a iri-iri. Akwai wasanni irinsu; ‘Îan maliyo-maliyo da wasan Carman Dudu da ‘He

ruwa’ da sauransu. A wasan Carman Dudu ‘yanmata kimanin shida sukan yi da’ira

∂aya ta shiga tsakiyarsu tana ba da wa˚a suna amsawa kamar haka:

Hasken Karatu Bk 6 .indd 37 9/11/14 8:56 AM

Page 48: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

38

I Carman Dudu

Bayarwa Amshi

Carman Dudu Carman Duduwa Carmagade

Akwai wani ba˚o a gidan mai gari Carmagade

Ba ya bashi baya lamuni Carmagade

Baya neman ‘yanmatan gari Carmagade

Ko ya nema wa zai ba shi ma? Carmagade

Yayata landiyo mana Carmagade

anwata landiyo mana Carmagade

Shashina landiyo mana Carmagade

Shegiya mai tsiwar tsiya Carmagade

Carman Dudu Carman Duduwa Carmagade

II Tayalo

Bayarwa Amshi

Wayyo lilon Tayalo Tayalo

An Tayalo Tayalo Tayalo

An Tayalon Baba Tayalo

An Tayalon Gwaggo Tayalo

Hasken Karatu Bk 6 .indd 38 9/11/14 8:56 AM

Page 49: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

39

Sai ˚awar ˚anwata Tayalo

Ban wuri in yi wasa Tayalo

In ba za ki iya ba Tayalo

Ki je gida ki yi kwance Tayalo

Ke ma taho mu yi wasa Tayalo

In ba za ki iya ba Tayalo

Kira ˚awarki ta koya Tayalo

Ni ma da ˚yar na koya Tayalo

Wasan dandali na maza

Wasan langa

Wasan langa wasa ne da yara maza suke yi don kwaikwayar tsarin sarautar Hausawa,

musamman ta fuskar ya˚i tsakanin wani gari da wani. A wannan wasa yara suna

kasa kansu gida biyu, wanda suke ∂aukar kowane kaso a matsayin gari ne guda da

sarkinsa, wanda ake kira ‘ruwa’. Wasan kan ∂auki siffar ya˚i, wanda dokin ruwa shi

ne sarkin ya˚i. ıangare guda ne yake fara samar da ‘ruwa’, kuma akwai wurin ‘sha’,

wato jikin wata bishiya ko wani dutse da ake son ‘ruwa’ ya je ya ta∫a kafin a kashe shi.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 39 9/11/14 8:56 AM

Page 50: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

40

Ragowar yaran su ne suke shigewa gaban ruwa a matsayin baraden ya˚i. Kowan-

nensu yakan ∂ana lagonsa, ‘yan wancan ∫angare su yiwo kan ‘yan ∫angaren da suke

da ‘ruwa’ don ˚o˚arin cire lagonsu ko kashe ‘ruwa’. Kowane ∫angare yana ˚o˚arin

nuna ya fi ∂aya ∫angaren ˚arfi, ta hanyar ture baraden ya˚in. Kowane ture lago, ana

∂aukarsa a bakin kisa ne, saboda haka ‘yan garin da aka fi ture wa lago ko aka kashe

‘ruwa’ a hannunsu, to su aka fi ˚arfi, kuma an cinye su ke nan.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Don me ake yin wasan dandali?

2 Kawo ire-iren wasannin dandali guda biyar?

3 Yi gajeren bayani kan wasan dandali guda ∂aya, na maza ko na mata.

4 Kawo bayanin wasan zamani wanda ya yi kama da na dandali.

5 Kawo sunayen wasanni uku da ka/kika ta∫a yi.

6 Su wanene suke yin wasan langa?

7 Me ake kwaikwaya a wasan langa?

8 Ana kiran yaran da suke shigewa gaban niwa ____________.

a) Baraden kokawa b) Baraden ya˚i c) Baraden hanya

9 A wasan langa ana Sarkar Kowane bangane a matsayin ____________.

a) unguwa b) gona c) ∂aki d) gari

10 Wasa kishiyar ____________ ne.

a) fa∂uwa b) aiki c) yawo d) zama

Jagora

Malamimi ya jagoranci yara su aiwatar da wani wasan dandali a cikin aji ko a wajen aji.

Malami ya dubi litfafin wasannin yara na Umaru Dembo.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 40 9/11/14 8:56 AM

Page 51: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

41

Hanyoyin sadarwaSadarwa na nufin wata tsararriyar hanyar aikawa da sa˚o daga wani guri zuwa wani

ta hanyoyi daban-daban.

Sa˚on da akan aika na iya kasancewa a rubuce, kamar na wasi˚a da makamancin

haka,ko sa˚o na baka da ake son sanar da mutane, ko wasu kayayyaki.

Ire-iren hanyoyin sadarwa

Sadarwa da∂a∂∂iyar aba ce da al’umma suka da∂e suna yi. Don haka akwai han-

yoyin sadarwa, iri daban-daban da akan bi wajen aikawa da sa˚onni. Don haka a nan,

hanyoyin sadarwa sun rarrabu kamar haka:

Hanyoyin sadarwa na gargajiya

Wannan irin hanyar sadarwa ita ce hanyar aikawa da sa˚o ta hanyoyi na gargajiya. Irin

wa∂annan hanyoyi su ne:

1 Kurya: Wata yar ganga ce da akan ka∂a ta don sanar da jama’ar gari da su fito

don tafiya ya˚i. Hausawa na yi mata kirari da ‘Kurya gangar mutuwa.’

2 Kuge: Wani ˚arfe ne da akan ka∂a shi don sanar da mutanen gari su fito zuwa

ya˚i.

3 Tambari: Wata irin ganga ce mai girma da akan buga wa Sarki. Wato ana buga

shi don sanar da jama’a cewa Sarki ya hau ko yana kusa, Hausawa na cewa: ‘In

ka ji tambari sai sarki’.

4 Bindiga: Ana buga bindiga ko kuma harba ta ne don sanar da jama’a cewa sar

ki ya fito, ko ya ˚araso. Haka kuma ana buga bindiga don sanar da garin watan

azumi ko na Sallah.

5 Haya˚i: Ana yin haya˚i don sanar da mutane wani muhimmin sa˚o.

Babi na 11

Hasken Karatu Bk 6 .indd 41 9/11/14 8:56 AM

Page 52: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

42

6 aho: Ana busa shi ne don sanar da ‘yan farauta su fito don tafiya farauta.

7 Kar-ta-kwana: Wannan sa˚o ne da akan aika daga wani wuri zuwa wani wuri cikin

gaggawa, ba tare da sa˚on ya kwana ba. Mai kai wannan sa˚o yakan hau doki ne

ya yi ta sukuwa har zuwa wannan gari. Idan kuwa gari da nisa, yayin da ya ci wani

zango, sai ya bai wa wani da ke kan hanya, shi kuma ya isar da sa˚on.

8 Yekuwa/Shela: Sarakuna ko shugabanni su ke aika san˚ira (maro˚i), ya bi sa˚o-

sa˚o da lungu-lungu na gari yana fa∂a wa mutane wani sa˚o, na umarni ko tuna-

tarwa ko garga∂i ko kuma fa∂akarwa. San˚ira yakan ∂aga murya wajen bayar da

sanarwa.

Hanyoyin sadarwa na zamani

Wa∂annan hanyoyin sadarwa su ne wa∂anda suka samu daga baya, wato bayan zu-

wan Turawa. Irin wa∂annan hanyoyin sadarwa su ne:

1 Na gidan waya/wasi˚a: Gidan waya ko wasi˚a na nufin ofishin aikawa da wasi˚u

kamar fas ofis (post office), ko makamancin haka. Irin wasi˚un da akan iya aikawa

da su ta irin wannan hanya sun ha∂a da:

a) Wasi˚ar kan-sarki : Ita ce wasi˚ar da akan rubuta ta , a sa a ambulan, a sayi

Hasken Karatu Bk 6 .indd 42 9/11/14 8:56 AM

Page 53: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

43

kan-sarki (stamp) a li˚a a jikinta, a kai gidan waya don aika wa da ita inda ake

bu˚ata.

b) Wasi˚ar kar-ta-kwana (esfires): Ita ce wasi˚ar da ake bu˚atar ta isa inda ake

so cikin gaggawa,wato ba tare da ∫ata wani lokaci ba. Akan aika da irin wan-

nan wasi˚a ta kamfanoni irin su DHL ko, UPS ko, Fedex da sauransu.

i) Rediyo

ii) Jarida

iii) Allon sanarwa

iv) Talabijin

2 Na fasahar sadarwa: Wa∂annan su ne hanyoyin aikawa da sa˚o da suka samu

sakamakon bun˚asar fasahar sadarwa ta iska. Daga cikin wa∂annan akwai:

a) Fas (Fax): Wannan hanyar sadarwa ce da ake aika sa˚o rubutacce daga

wani wuri zuwa wani. Wannan hanya ta fara ∫acewa.

b) Wayar tarho da salula: Ita ce hanyar aikawa da sa˚o ta hanyar Magana ko

kuma a rubuce, ta hanyar amfani da wasu lambobi na musamman.

c) Tales (Telex): Wannan hanya ce da ake aikewa da sa˚o, ta wayar tangaraho

ko oba-oba. Wannan ma yanzu ta ∫ace.

d) Intanet: Ita ce mafi sabunta a hanyoyin sadarwa da fasahar zamani ta kawo.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 43 9/11/14 8:56 AM

Page 54: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

44

Ana aika sa˚o na hoto ko na rubutu mai yawan gaske cikin sau˚i da sauri.

Akan aika irin wannan sa˚o ta hanyoyi kamar: I-mel da Fasibuk, da Tuwita da

sauransu.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Mece ce sadarwa?

2 Hanayoyin sadarwa guda nawa muke da su?

3 Kawo hanyoyin sadarwa na gargajiya guda uku.

4 Wasi˚a iri nawa ake iya aikawa ta gidan wasi˚a?

5 Wace hanyar sadarwa ce ta fasahar zamani, aka fi aikawa da sa˚o mai yawa

cikin Sauri da sau˚i?

6 Dukkan wa∂annan hanyoyin sadarwa ne na gargajiya ban da ∂aya.

a) Kuge b) Kurya c) Bindiga d) arfe

7 Gangar da ake ka∂awa don sanar da mutane ya˚i ita ce.

a) Kuge b) Bindiga c) Garaya d) Kuntigi

8 Hanyar sanar da tafiya farauta ita ce __________.

a) Kurya b) aho c) Tambari d) Haya˚i

9 Wanda yake bi sa˚o-sa˚o yana shela shi ne __________.

a) Dan wanka b) Bafade c) Dogari d) San˚ira

10 Hanyoyin sadarwa na fasahar sadarwa sun ha∂a dukkan wa∂annan ban da ∂aya.

a) Fas b) Salula c) Rediyo d) Intanet

11 Tsakanin ˚aho da wayar tarho da salula wance ce hanyar sadarwa ta gargajiya?

12 Wasi˚ar kar-ta-kwana ita ce wasi˚ar da __________

a) ake bukata ta isa cikin gaggawa b) ake jinkirta aika∂∂a

c) ake bukatar ˚arin bayani d) ake aikawa gidan rediyo ko talabijin don

karantawa

13 Wane ne yake aikawa a sanar da san˚ira don ya bi gari yanan fa∂a wa mutane

sa˚o wanda ake kire yekuwa/shela

a) Sarakuna ko shugabanni b) Bafade c) San˚ira d) me unguwa

14 Wayan zuwan Turawa wa∂anne hanyojin sadanwa ne suka samu?

15 Ofishin aikawa da wasi˚u kamar fas ofis ko makamancin haka yana nufin

_________.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 44 9/11/14 8:56 AM

Page 55: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

45

Babi na 12

Hanyoyin sufuri

Ma’anar sufuri

Sufuri yana nufin hada-hadar kayayyaki ko safarar mutane, daga wannan wuri zuwa

wancan, musamman daga wurare masu nisan gaske da niyyar saye da sayarwa ko

kuma don wasu bukatu .Wato sufuri hanya ce ta jigilar kaya ko mutane daga wani wuri

zuwa wani wuri.

Hanyoyin sufuri

Hanyoyin sufuri iri biyu ne kamar haka:

1 Hanyoyin sufuri na gargajiya: Hanyoyin sufuri a gargajiyance, hanyoyi ne da Hau-

sawa suke amfani da su tun tuni, kafin ha∂uwarsu da wasu al’ummu wajen jigilar

kayayyaki. Ire-Iren wa∂annan hanyoyi sun ha∂a da:

Hasken Karatu Bk 6 .indd 45 9/11/14 8:56 AM

Page 56: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

46

a) Tafiya a ˚afa: Wannan ita ce hanya ta farko ta jigilar kaya da Hausawa suka

fara amfani da ita, inda mutum zai ∂auki kaya a ka ko a tafi da mutane a ˚afa

zuwa wasu wurare.

b) Hanya ta biyu: Ita ce ta amfani da jaki ko doki ko takarkari ko alfadari ko kuma

ra˚umi wajen loda masu kaya a yi tafiya da su don yin sufurin kayayyaki.

c) Kwale-kwale: Wannan hanya ita ce ta amfani da kwale-kwale da ake bi ta

ruwa da shi, don sufuri inda akan loda kaya ‘yan ka∂an, don yin safararsu

zuwa wurare masu nisa.

2 Hanyoyin sufuri na zamani: Su kuma hanyoyin sufuri na zamani, hanyoyi ne na

hada-hadar kayayyaki ko mutane daga wuri zuwa wani wuri, ta hanyar yin amfani

da ababen hawa da zamani ya kawo. Wannan hanyar ta sufuri ta fi sauri da kuma

sau˚i, idan an kwatanta ta da hanyar sufuri ta gargajiya. Wa∂annan hanyoyi su ne

kamar haka:

a) Jirgin ruwa: Daga kwale-kwale, sai kuma aka koma ana amfani da jirgin ruwa,

don jigilar kaya daga wuri zuwa wuri. Ana cika jirgin da kaya da kuma mu-

tane a lokaci guda a kai wurare daban-daban. Kasancewar yana ∂aukar kaya

masu yawa da nauyi, an fi yin jigilar kaya da mutane daga wata ˚asa zuwa

wata, da suke da tashoshin jiragen ruwa.

b) Mota da babur da keke: Mota da babur ko keke su ne manyan hanyoyin suf-urin zamani nayau da kullum. Wannan hanya ta da∂a sau˚a˚a harkar sufurin

mutane da kaya a ˚asar Hausa.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 46 9/11/14 8:56 AM

Page 57: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

47

c) Jirgin ˚asa: Ana amfani da shi don da∂a samun sau˚in jigilar kayayyaki masu

yawa, da ma mutane a lokaci guda.Idan aka kwatanta shi da jirgin sama ko

mota,ya fi arahar biya. Jiragen da ake jigilar kaya, akan ∂auki tsawon lokaci

ana yi masa lodi.

d) Jirgin sama: Sannaniya kuma fitacciyar hanyar sufuri a zamanance, wadda

ta fi kowacce sau˚i da kuma sauri ita ce sufuri ta hanyar jirgin sama. Jirgin

sama a matsayin hanyar sufuri ya kawo ci gaba da kuma bun˚asar tattalin

arziki a ˚asa.

Wannan hanya ta fi ∂aukar kaya da mutane masu ∂imbin yawa da kuma

jigilarsu zuwa wurare masu nisan gaske a tsakanin ˚asashe. Don haka a yau

aka fi mayar da hankali a kansa, a harkar sufuri a ciki da wajen ˚asar Hausa

da Nijeriya da kuma duk fa∂in duniya.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Me ya sa ake yin sufuri?

2 Hanyoyin sufuri guda nawa ne?

3 Yi bayani game da hanya ∂aya ta sufuri a gargajiyance?

4 Kawo dabbobi guda uku da ake yin sufuri da su?

5 Îauki hanyar sufuri guda ∂aya sannan ka yi bayani.gora

6 Wa∂anne irin abubuwa ake yin sufurinsu.

7 Wacce ce hanya ta farko da Hausawa suk fara jigilar kaya?

8 Bayyana hanyoyin sufuri na zamani guda uku sannan a yi bayani ∂aya.

9 Dukkan wa∂annan kayan sufuri ne na gargajiye ban da ∂aya.

a) Doki b) Jaki c) Jirgin sama d) Takarkari

10 Hanyar sufurin zamani da ta fi kowacce araha, da ∂ibar kaya masu yawa ita ce

__________.

a) jirgin sama b) jirgin ˚asa c) kar-ta-kwana d) tafiyar ˚afa

Jagora

Malami ya ˚ara yi wa ∂alibai cikakken bayani a kan hanyoyin sufuri. Malami ya yi

˚o˚arin kai ∂alibai ziyara zuwa filin jirgin sama da tashar jirgin ˚asa idan akwai.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 47 9/11/14 8:56 AM

Page 58: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

48

Bukukuwan Hausawa

Bukukuwan Hausawa wasu hanyoyi ne da Hausawa suke bi, don nuna farin ciki da jin

da∂i da taya murna, na wani abin alheri da ya same su. Bukukuwa da Hausawa suke

yi suna da yawan gaske, wannan bai rasa nasaba da abubuwan da suka yi tasiri a

kansu dangane da ko dai al’adu ko addini ko kuma zamananci.

1 Bukukuwan al’adu sun ha∂a: da Bikin kalankuwa da bikin shan kabewa da sau

ransu.

2 Bukukuwan addini sun ha∂a: da Bikin Sallar idi da bikin saukar Al˚ur’ani da sau

ransu.

3 Bukukuwan zamani sun ha∂a: da Bikin nunan amfanin gona da bikin yaye Îali

bai na Jami’o’i da kwalejoji da sauransu.

Har wa yau, akwai bukukuwa da ake yi tun kafin zuwan addinin Musulunci, kuma

bukukuwa ne na yau da kullum kamar su bikin Aure da na Suna da makamantansu.

Har bayan zuwan musulunci an ci gaba da yin wa∂annan, sai dai an sami ‘yan gyare-

gyare.

Bukukuwan Sallah arama da babba

Bukukuwan Sallah arama da Babba nau’o’in bukukuwa ne da Hausawa suke ai-

watarwa duk shekara. Misali:

1 Bikin Sallah arama: Wannan biki ne da ake gudanarwa duk shekara a ranar 1

ga watan Shawwal. Babban dalilin yin wannan biki shi ne domin nuna farin ciki

na cewa an fara azumi, kuma an gama shi lafiya. A wannan rana jama’ar gari da

limamansu, kowa zai yi ado da kwalliya,musamman da sababbin kaya, sannan a

Babi na 13

Hasken Karatu Bk 6 .indd 48 9/11/14 8:56 AM

Page 59: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

49

fita zuwa masallaci don yin Sallar idi.Bayan an sauko daga masallaci,jama’a za a

shiga zirga-zirga gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki don yin gaishe-gaishe. A dai

wannan biki na Sallah arama, ana yin girke-girke da soye-soye da sauran sh-

agulgula irin su ka∂e-ka∂e da raye-raye da bushe-bushen Sallah.

Misali a irin wannan rana Sarakunan ˚asar Hausa da Hakimansu da sauran

masu ri˚e da sarautun gargajiya, suna yin ado su da dawakansu, suna zaga gari

don yin gaisuwar Sallah, jama’ar gari a fito kallo, wanda aka fi sani da Hawan

Sallah. A wasu garuruwan ana yin Hawan Daushe da Hawan bariki da Hawan

Nasarawa.

2 Bikin Sallah Babba: Bikin Sallah Babba kamar bikin sallah arama,ne, biki ne da

al’ummar Hausawa suke yi duk shekara. Shi wannan biki ana yinsa ne a ranar 10

ga watan Zulhajji, domin taya Alhazai murnar sun gama aikin hajji lafiya. A wannan

rana jama’a suna zuwa masallaci da safe, don yin sallar idi kamar yadda ake yi a

ranar Sallah arama.Da an idar da sallah, Liman zai yanka abin layyarsa, musam-

man rago ko wani abin layya da ya sauwa˚a. Daga nan kuma sauran jama’a kowa

zai tafi gida,kowane mai gida ya yanka abin layyarsa. Daga nan kuma a ci gaba

Hasken Karatu Bk 6 .indd 49 9/11/14 8:56 AM

Page 60: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

50

da shagulgula kwatankwacin irin wa∂anda ake yi da bikin Sallah arama. A wan-

nan biki ana ca∫a ado, a yi kwalliya a hau dawakai a yi hawan sallah, har kamar

tsawon kwana biyu zuwa uku; da sauransu.

3 Bikin Maulidi: Bikin Sallar Maulidi, biki ne da ake yinsa a ranar 12 ga watan Rabi’ul

Awwal wato wata na uku a cikin shekarar Arabiyya na kowace shekara. Babban

dalilin wannan biki shi ne, don tunawa da kuma murnar zagayowar ranar da aka

haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W). A irin wannan rana, ana ˚o˚arin

raya wannan dare wato kwanan Maulidi ta hanyar yin karatuttuka da suka shafi

addini, musamman fannonin da suka yi magana a kan darajojin Annabi, da ky-

awawan halayensa da karatun Alkur’ani da su karatun littafin ishiriniya da zikiri

da salatin Annabi da karance-karancen wa˚o˚in yabon Annabi da sauransu har

gari ya waye. Ana kuma yin ‘yan soye-soye, musamman kaji da sauransu.

Bikin Sallar takutaha yana ∂aya daga cikin bukukuwan da Hausawa suke yi.

Idan sati ya zagayo,wato ranar 19 ga wannan wata na Rabi’ul Awwal ake gudanar

da wannan biki da aka fi sani da ‘Takutaha’ ko Sallar Gani, wanda ake yi don mur-

nar tunawa da zagayowar ranar. A wannan rana ta Takutaha da safe sai jama’a

musamman mata tsofaffi da yara su ci ado da kwalliya. Sannan a yi abinci kala-

kala, a kuma ziyarci gidajen ‘yan’uwa da sauran abokan arziki, ana tafe ana rera

wa˚o˚in yabon Annabi da wa˚en ishiriniya, wanda ake kira da yawon takutaha.

Muhimman kalmomi

1 Bukukuwa – Ana nufin hanyoyin nuna farin ciki.

2 Murna – Tana nufin farin ciki.

3 Kwalliya – Tana nufin ado da ˚awata jiki.

4 Sarauta – Shugabantar mutane.

5 Zirga-zirga – Yana nufin yawace-yawance zuwa gidajen yan’uwa.

6 Shagulgula – Ka∂e-ka∂e da bushe-bushe don nuna murna.

7 Darajoji – Tana nufin matsayi.

8 Takutaha – Tana nufin zagayowar ranar haihuwar Annab (S.A.W).

9 Aiwatarwa – Tana nufin gudanarwa.

10 Maulidi – Maulidi na nufin murnar ranar haihuwa.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 50 9/11/14 8:56 AM

Page 61: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

51

Muhimmancin bukukuwan

1 Taya murna da nuna farin ciki.

2 Bayyana tarihi.

3 Koya tarbiyya.

4 Adana kyawawan al’adun Hausawa.

5 Nuna matsayi da darajar azumi da kuma aikin hajji.

6 Fa∂akar da al’umma a kan darajojin Annabi.

7 arfafa dan˚on zumunta a tsakanin dangi.

8 ara wa yara ˚aimi a kan ˚aunar Annabi da kuma koyi da kyawawan halayen

sa.

9 arfafa zumunci.

10 Don nisha∂antanwa da samun annashuwa.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Me ya sa ake yin bikin maulidi?

2 Kawo bukukuwan da suka ji∫inci al’ada guda uku.

3 Ka yi bayanin yadda ake bikin Hawan Sallah a garinku.

4 Fa∂i muhimmancin biki guda uku?

5 Shin biki hanya ce ta nuna farin ciki?

6 Bukukuwan al’ada sun ha∂a da ____________.

a) bikin kalankuwa da bikin shan kabewa da sauransu.

b) bikin saukar Kur’ani da bikin Maulidi.

c) bikin nunan amfanin gona da bikin yaye Îalibai da na Jami’o’i da sauransu.

7 Bukukuwan da Hausawa suke yi tun kafin zuwan musulunci, wato na yau da kul-

lum sun ha∂a da:

a) bikin Sallah da bikin Maulidi.

b) bikin Aure da na Suna.

Jagora8 A gorgajiyance ana yin hawan daushe da _____________ da _____________ a

lokacin ˚aramar sallah.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 51 9/11/14 8:56 AM

Page 62: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

52

Jagora

Malami ya sa ∂alibai su bayar da labarin wani bikin Sallah da suka ta∫a halarta.

Malami ya sa ∂alibai su yi bayanin yadda ake hawan salla a matsayin aikin gida.

Aiki

Za∫i wa∂annan kalmomi da ke biye don cike guraben da aka bari:

Taya muma Sarakuna tasiri

maulidi karatu Babba

1 Bukukuwan Hausawa suna yin su ne don ____________.

2 Bikan saukar ____________ biki ne da Hausawa suke yi bayan zuwan musuluci.

3 Akwai ____________ zamani a cikin bukukuwan Hausawa a yau

4 ____________ da Hakimansu suna yin ado su da dawakansu suna zaga gari don

yin gaisuwar sallah.

5 Bukukuwan salah sun ha∂a da sallah ____________ da sallah ˚arami.

9 Maulidi biki ne da ake yinsa a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal.

a) A’a 12, ga watan Rajab.

b) Ee12, ga watan RAbi’ul Awwal ne.

c) 30 ga watan Ramadan.

10 Bikin Sallah Babba ana aiwatar da shi ne don _____________.

a) murnar haihuwar Annabi (S.A.W)

b) nisha∂i

c) taya Alhazai murnar sun gama aikin haji lafiya

Hasken Karatu Bk 6 .indd 52 9/11/14 8:56 AM

Page 63: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

53

Babi na 14

Zane da kwalliya da tufafin Hausawa

Zane Zane wata alama ce da Hausawa da kuma wasu ˚abilu na sassa daban-daban, na

wannan duniya suke yi da aska a fuska ko a wani ∫angare na jiki, don a bambanta

wata ˚abila da wata, ko mutanen wata daula da wata ko dangi da dangi ko zuri’a da

zuri’a ko don ri˚e al’ada, ko don magance wata cuta, ko kuma don yin kwalliya.

Akwai zane iri uku wato:

1 Zane na tsagar gado: Wannan ita ce wadda ake yi a fuska don nuna asalin mai

ita ko sashin da ya fito. Ana yin zanen tsagar gado ne don nuna asalin wajen uba

ba na wajen uwa ba.

a) Akwai zanen da ke nuna asalin gari ko wurin zama kamar; Katsinanci ko Dau-

ranci ko Gobiranci da sauransu.

b) Akwai zanen da ke nuna asalin ˚abilar da mutum ya fito kamar Barbarci ko

Buzanci da sauransu.

c) Akwai zane mai nuna ma’abota wata sana’ar gargajiya kamar; mahauta ko

manoma da sauransu.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 53 9/11/14 8:56 AM

Page 64: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

54

2 Zane na tsagar magani: Ana yin wannan zane ne domin a fitar da jini daga jikin

mutum, saboda a samu sau˚i ko a warke daga wani ciwo wanda ke cikin jiki. Haka

˚uma, ana yin wannan zane don fitar da matacen jini ko idan ya yi yawa ajiki.

Hausawa sun yarda da cewa idan mataccen jini ya yi yawa a jiki, to yakan yi

sanadiyyar kamuwa da cututtuka iri daban-daban. Akwai zanen tsaga da Hau-

sawa suke yi kamar:

a) Yin ˚aho

b) Yin ∫alli-∫alli

c) maganin jiri

d) Fitar ruwa

da sauransu.

3 Zanen tsagar kwalliya: Wannan zane ake kira jarfa ko shasshawa. Wato ire-iren

zanen da mata kan sa wanzami ya yi musu a fuska ko a wani ∫angare na jikinsu,

domin ado da kwalliya. Ire-iren wannan zane akwai:

a) Kalangui

b) ‘Yar-baka

c) Tagumin-gafiya

d) Tsuguna-ka-ci-doya

da sauransu.

Kwalliya

Kwalliya na nufin yin ado ta hanyar yin wanka d sanya kyawawan tufafi. Don haka,

kwalliya wani fanni ne mai muhimmancin gaske a al’adun Hausawa na gargajiya da

ma na zamani. Kowace irin al’umma akwai hanyoyin da take gudanar da kwalliya. Don

haka, kwalliya a wajen Bahaushe tana nufin mutum ya tsaftace jikinsa, ya kuma ˚ara

da sanya wasu abubuwan ˚yale-˚yale domin jawo hankalin jama’a tare da nufin ya

˚ara sha’awa a idanunsu. Daga cikin ire-iren kwalliyar Hausawa akwai:

1 Kitso: Kitso shi ne tsefe gashin kan mace da kitse shi da ˚awata shi domin ado da

kuma rage tudun gashin. Don haka kitso dai wani abu ne wanda mata Hausawa

suke yi wa ‘ya’yansu mata a kansu, a bisa yana yin zamani. Akwai nau’o’in kitso

da mata Hausawa suke yi tun daga gargajiyarsu, wa∂anda suka ri˚a sauyawa

daidai da zamani kamar haka:

a) Kitson gargajiya: Nawo’in wannan kitson akwai:

Hasken Karatu Bk 6 .indd 54 9/11/14 8:56 AM

Page 65: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

55

i) Tarin kara

ii) Mai ˚wa˚walwa

iii) Zube

iv) Gammo

v) Kalmasa

da sauransu.

b) Kitson wibin: Wannan kitso ne da ya sami Hausawa bayan nasu na gargajiya

kamar haka:

i) Tashin soja

ii) Mai tsani

iii) Mai rana

iv) Zig-zag

v) Shuku mai ayaba

vi) Shade

da sauransu.

c) Îaure-∂aure: Wannan salon kitso ne da Hausawa suka samu daga yara-

bawa. Daga cikinsu akwai:

i) Sizos

ii) Tazarce

iii) Tiri-sita

iv) Haf-fat

da sauransu.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 55 9/11/14 8:56 AM

Page 66: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

56

Kwalli

Kwalli shi ne ba˚in dutse wanda ake daka shi lu˚ui, mata suna amfani da shi a ido don

yin kwalliya. Mata suna ∂ura kwalli a tandu su ri˚a sa wa a ido da mishi. Akwai kwalli

da mata suke amfani da shi a yanzu, wato kajal.

1 Lalle (Kunshi): unshi abu ne da ake yi da lalle wanda kuma ake yinsa a hannu da

˚afa. Mata suna yin adon lalle ne domin kwalliya. Mata suna samun lalle dakakke

mai laushi su kwa∫a da ruwa, sai a yayya∫a a hannu. Akwai nau’o’in ˚unshi ka-

mar;

a) unshin gargayiya: Wannan shi ne wanda ake yi da zunguru ko a ∂a∂∂aure

da leda

b) unshin fulawa

c) unshin salatif

da sauransu.

2 Aski: Aski na nufin amfani da askar aski mai kaifi, domin a aske sumar da ta tsiro

a kan mutumin da ya bu˚aci a yi masa gyaran fuska. A al’adar Hausawa, maza

kawai ake yi wa aski. Akwai Ire-Iren aski kamar;

a) waryar molo

b) Gyaran fuska

c) Saisaye

d) Askin jarirai

e) Zanko

da sauransu.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 56 9/11/14 8:56 AM

Page 67: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

57

3 Sar˚a: Wannan na cikin kayan ˚yali da mata Hausawa suke kwalliya da su a

wuyansu.

4 Dankunne: Wannan ma kayan ˚yali ne da mata suke a∂o da shi a hujin kunnu-

wansu.

Akwai kuma sauran kayan kwalliya kamar:

a) Murjani

b) Tsakuja

c) Jigida

d) Agogo

e) Munduwa

5 Takalma: Takalma makari ne na tafin ˚afa daga rana ko ˚aya wanda ake yi da

fata ko roba ko ˚yalle. Nau’o’in takalma sun ˚unshi:

a) Kwabashu

b) Sukwal

c) Sandal

d) Zita

e) Mu gamu a banki

da sauransu.

6 Bayanin zane da kwalliya da Tufafi: Kamar yadda aka bayyana, zane shi ne

wanda ake yi a fuska don nuna asalin mai ita ko sashen da ya fito. Kwalliya kuwa

tana nufin mutum ya tsaftace jikinsa, ya kuma ˚ara da sanya wasu abubuwan

˚yale-˚yale domin jawo hankalin jama’a. Tufafi kuwa ya ˚unshi kaya wa∂anda

ake sa wa a jiki domin kare jiki daga tsiraici da kuma yin ado. Tufafi ne yake

nuna cewa, mutum ya fito daga wuri kaza, kuma yana da al’ada iri kaza. Tufafin

Hausawa akwai na maza sannan akwai na mata. Har wa yau, akwai na saraki da

kuma na sauran jama’a.

Muhimman kalmomi

1 Daula – Yanki mai yawan ‘jama’a.

2 Zuri’a – Iyali

Hasken Karatu Bk 6 .indd 57 9/11/14 8:56 AM

Page 68: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

58

3 Jarfa – Yana nufin tsagar kwalliya.

4 Lu˚ui – Wato abu ya daku sosai ya zame gari.

5 Kuratandu – Abin da ake yi da fata don zuba kwalli.

6 Zunguru – Dan duma ne da ake yin ˚unshi da shi.

7 Kyali – Kayan wuya da na hannu do na kunne na mata.

8 Shasshawa – Nau’i ne na tsaga

9 Sassa – ıanganuri

10 yalle – Wani yanki ∂an guntu.

Aiki

Za∫i wa∂annan muhimman kalmomi da ke sama don cike guraben da aka bari da

kalmomin da suka dace.

1 Tsohuwa ta yi ˚unshi da _____________.

2 Ladi ta sa mishi cikin _____________ ta sa kwalli.

3 _____________ Sakkwato Shehu Usmanu ne ya kafa ta.

4 Ya sa _____________ ya goge fuskarsa.

5 Wanzami ya yi wa Ladi _____________ do aska.

6 Ta daka kwalli _____________ don sa wa a ido.

7 Nigeriya tana da _____________ biyu. Kudu da arewa.

8 Wanzaman _____________ ne suke yin tsagar kwalliya.

9 Sarkin Kano _____________ gidan Dabo ne.

10 Kande ta sa kayan _____________ a wuyanta da hannayenta.

Tambayoyi

Amsa wa∂annan tambayoyin:

1 Don me al’umma suke yin zane a sassan jikinsu?

2 Kawo nau’oin zane na tsagar gado guda uku?

3 Wane dalili ne ke sa mata yin zanen jarfa?

4 Mece ce kwalliya?

5 Kawo nau’o’in kitson gargajiya do na zamani guda uku-uku?

6 A cikin me mata suke ∂ura kwalli don sa wa a ido.

7 Kawo Ire-iren aski guda uku sannan ka yi bayanin ∂aya.

8 Nau’o’in ˚unshi akwai _____________ da _____________ da na salatif.

Hasken Karatu Bk 6 .indd 58 9/11/14 8:56 AM

Page 69: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

59

a) Gargajiya da dauri

b) Gargajiya da fulawa

c) Fulawa da yaji

9 Dukkan wa∂anna kayan ˚yali ne ban da ∂aya.

a) Dankunne

b) Murjani

c) Zita

d) Agogo

10 Dukkan wa∂annan hulunan Hausawa ne ban da ∂aya.

a) Zanna-bukar

b) Zita

c) Ha∫ar kada

d) Sandal

Hasken Karatu Bk 6 .indd 59 9/11/14 8:56 AM

Page 70: Hasken Karatuapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 6.pdf · viii Tambayoyi51 Aiki 52 Jagora 52 14 Zane da kwalliya da tufafin Hausawa 53 Zane 53 Kwalliya 54 Kwalli 56 Muhimman

60

Hasken Karatu Bk 6 .indd 60 9/11/14 8:56 AM