61
FIM, SATUMBA 2001

Mujallar FIM - September 2001

  • Upload
    vokiet

  • View
    1.127

  • Download
    91

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Page 2: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001 1

tare da IBRAHIM SHEME

Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba

�Yan fim ku shiga IntanetMU LE}A MU GANI

A LOKACIN da nake karatu a Ingila, a cikin 1993, nata~a rubuta wata }asida don neman wata hukuma ta]auki nauyina in yi karatun digiri na uku, wato Ph.D.

Na rubuta }asidar ne a kan yadda sabuwar hanyar sadarwa taInternet (bari mu ce mata Intanet a nan) za ta iya shafarrayuwar mutane a }asashe masu tasowa. A lokacin, hukumarda nake son ta ba ni ku]in ba ta waiwaye ni kan }asidata bahar na baro }asar, ga shi kuwa su suka ce in rubuto. Kila daiban burge su ba, kila kuma jigon }asidar bai dace dabu}atunsu ba, kila kuma babu ku]in. Kila kuma...

To, bayan dawowata, na ]an yi aiki a mujallar Hotline amatsayin edita (da ma ni ne editan kafin tafiyata }aro karatu).Ba a da]e ba, a cikin 1995, sai na ]auko }asidar nan nakakka~e ta, na yi mata kwaskwarima, na buga ta a cikinmujallar da taken, �Internet: The New Battlefront.� Watodai Intanet za ta zama sabon fagen daga na ya]a labarai dabayanai na duniya. To, wannan tsokaci tuni ya zama dahir. Ayau, Intanet ce babban dandalin musayar ra�ayi a duniya. Anan ake cusa ra�ayi, a yi musayar ra�ayi, a yi kasuwanci, a yiwa�azi, da sauransu. Ga wanda bai gane ba, a gurguje Intanetwata kafa ce ta ya]a bayanai ta hanyar komfuta. A cikinta zaka iya fa]in abin da ka ga dama da inda ka ga dama. Sannanza ka iya samun labarai da bayanai daga kafofi ba iyaka;kuma kai ma za ka iya gaya wa mutane hajarka ta sayarwa,ka }ulla hul]a da mutane a }asashen duniya. Shi ya sa nakekwatanta Intanet da sararin samaniya kuma na kira ta kasuwarduniya ta wa]anda suka san duniyar.

Amfanin Intanet ga duk wani mai sana�ar fim ba }arami bane. {aramin misali shi ne, idan kai furodusa ne, za ka iyagaya wa duniya cewa ka yi fim iri kaza, ga farashinsa, gayadda za a same shi a saya. Kwanan baya ina duba Intanet,sai na ga ana tallar fim ]in {asarmu Ce na Sadiq |alewacikin wani adireshi wai shi [email protected]. Ina jin shika]ai ne fim ]in Hausa da ake tallatawa a kasuwar ta duniya� abin kunya malam! Ka san ko nawa kwafen fim ]in yake?$22.95! Sadiq wayayye ne, shi ya sa yake tallarsa a Intanet,ya bar su o�o suna rigima da dillalai a Kano.

Kwanan nan kuma na ga wani adireshi (website) na Intanetmai suna Hausafilms.com, wanda wasu �yan Legas (ka ji fa!)suka bu]e don tallata finafinan Hausa. Ko su Maikano sunsan da su, oho! Sannan akwai rubuce-rubuce da dama da akayi a kan finafinan Hausa ko a kan rayuwar Hausawa duk acikin Intanet. Bayan haka, akwai wurare da yawa da za kashiga cikin wannan kasuwa ta duniya, ka ga yadda ake shiryafim a tsanake, da kayan aiki na zamani, da tarihin rayuwarhamsha}an �yan fim na duniya, da sauransu. Duk mujallunnan na fim da suka yi suna a duniya, wato irin su Empire,DVD Now, Stardust, Filmfare, da sauransu, akwai su a Intanet.Kuma kyauta fa suke, illa dai kawai ka biya ku]in tarho dakake amfani da shi a duk lokacin da kake cikin Intanet ]in.

Akwai wurare da dama (business centres) a garuruwanmua yanzu wa]anda suke hul]a da Intanet, ana ce masu internetcafes (amma dai business centres ne da ka sani). Yadda za kashiga a yi maka photostat haka za ka shiga ka hau komfuta]insu ka shiga Intanet, ka biya in ka }are. Ni ina biyan N10ne a kan kowane minti ]aya da na yi, a business centre ]inda nake zuwa. Naira gomar me, irin wannan lagwadar!

A gaskiya, ya kamata duk wani ]an fim da ya amsa sunansa(furodusa, darakta, ]an wasa, dillali) ya ri}a shiga Intanet.Akwai mataki na farko mai sau}i. Ka fara da mallakaradireshin e-mail naka na kanka. Misali, Hauwa Ali Dodo za

ta iya mallakar adireshi kamar haka:[email protected], ko a ce Hindatu Bashir na [email protected], da sauransu. Iyan-Tama zai iya [email protected], Ibrahim Mandawari ya [email protected], da sauransu. Nawa ake kashewaa sami adireshin e-mail? N300 kacal (e, ]ari uku, ba dubuuku ba!). Kuma daga nan ka daina biya, ya zama naka.

Kwanan nan na biya ma wani furodusa ku]in e-mail, nasamar masa adireshin, kuma har ya fara aiki da shi. Rannanda kansa ya kawo mani hirar da aka yi da jarumin Indiya ]innan Sunny Deol, ya samo daga adireshin Intanet na mujallarFilmfare ta Indiya. Yanzu duk mai son ya fa]a wa HafizuBello wata magana dangane da fim ]insa, sai kawai ya aikamasa ta adireshinsa [email protected]. Ka jarraba kagani; shi kuma Hafizu zai maido maka da amsa kai tsaye.

Kuma wani da]in e-mail shi ne in dai ka aika da sa}o, tonan take zai isa, ba sai an kwana an wuni ba; kuma sa}onkaba zai ~ace a hanya ba. Ba ruwanka da tsiyar �yan post office.

Wani abin mamaki shi ne, masu kallon finafinai da damasun tsere wa �yan fim ]in, domin yawancinsu suna daadireshin e-mail nasu na kansu (dubi filinmu na wasi}un e-mail ka gani; ka]an ma kenan). Suna so su ri}a yi wamasoyansu wasi}u muhimmai, amma ba dama sai ta hanyarmujallar Fim. Ai ya dace a ce dubban masoyan Ali za su iyarubuto masa ta [email protected]. Don Allah, Ali, ka samie-mail mana; N300 fa, furodusan Mujadala!

Yanzu a ce Fati Mohammed tana da adireshin e-maillokacin da aurenta ya zo; haba, ai da wasi}unta sai dai akawo roka ta ]auke su zuwa gidan Mai Iska, a ware ]akiguda a kimshe su. Ta sami abin karatu kafin ta yi ~atan wata.

Kuma kada fa a ]auka daga e-mail shikenan. Ina! Ai wannanwani ]an }aramin mataki ne na aikawa da wasi}u cikinruwan sanyi. {asurguman �yan fim na duniya suna bu]e}aton dandali na Intanet ne mai suna website. Idan kana dawebsite, to za ka iya saka tarihin rayuwarka da na kamfaninka,da hotunanka da na iyalinka da na ofis ]in ka; da wani sashena fim ]in ka don ka kwa]aita wa mai saye ya ji yana son sa,daga nan sai ya aiko maka da ku]in ta hanyar Intanet, kaikuma ka aika masa da faifan. Misali, wani Bahaushe da kezaune a Indonesiya zai iya duba website ]in Yakubu Lere(Lerawa.com?) don ya san ko sabon fim ]insu ya fito. Zaiiya kallon wani ]an sashe da aka saka na fim ]in, har ya jiyana son sayen fim ]in; shikenan, sai kawai ya ga daloli sunshiga asusunsa na banki. Wannan dama har ina!

Amma masu fim na Hausa su sani cewa fim mai inganciake so a waje, domin duk wanda ke zaune a Amerika (yakalli Airforce One na Harrison Ford ko finafinan StevenSpielberg), ba zai gamsu da kwamacalar da Hausawa ke yiba, sai dai don ko ya tuno da gida. Don haka tilas furodusoshisu }ara bu]e bakin aljihu, su ri}a yin fim da manyankyamarori da makirfo da fitilu na zamani. Ga �yan Kudu nansun yi mana fintinkau a wannan fagen. Indiya fa da akamaye gurbinsu, ko da ma can da inganci suka fito, kuma haryau da kayan Hollywood suke aiki, ba na ]aukar bikin sunaba. Furodusoshi da daraktoci da dama za su tuna cewakwanan baya wani dillalin finafinai a Intanet ya aiko manida wasi}a daga }asar Afrika ta Kudu, yana son finafinanNijeriya irin na Hausa. Na mi}a sa}on ga �yan fim ba iyaka.Amma }a�idojinsa sun fi }arfinsu. Sai dai kuma yanzu suMandawari da Iyan-Tama sun yun}uro, sun yi shootingkwanan nan da kyamarar Betacam. Saura kuma mu ji su aIntanet, sun je cin kasuwar sararin samaniya.

Page 3: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 20012

Auren Su Fati Da Maijidda ZaiGirgiza Duniyar Shirin Fim!

duniyar finafinan Hausa ta girgiza sabodarashin Fati da Maijidda shi ne saboda irinyadda �yan wasan biyu suke darajantar dawannan sana�ar. Haka ma suka bayar damuhimmanci wajen kare mutuncinwasanninsu tare da zumunci mai yawa, wandahar ta kai idan kana kallonsu ba za ka ga watafallasa wacce za ta sanya ka yi da-na-saninkallon wasansu ba. Kowacce ba ta yi butulcia kan jigon shigowarta wasan ba. Irin yaddasuka nuna ta hirar bankwana da suka yi amujallu, sun nuna wa jama�a cewa ba sun zoduniyar finafinai ba ne domin sha}atawa, a�asun zo ne domin yin hannunka-mai-sanda batare da wata barazana ba, za ka iya fahimtardarasi har ka zama nagari ga al�umma ba tareda an kira sunanka ba tunda kowa yanakuskure, kuma da man mutum ai ajizi ne.

Ire-iren auren da Fati da Maijidda sukagyara a kan ilimantarwarsu da soyayyar dasuka gina a kan tsarin rayuwarsu sun fitar damata u}ubar zargin cewar ba su da wanimuhimmanci ko matsayi a cikin al�umma. Ada, tarbiyyar �ya�yanmu mata da samari talalace har saboda rashin fa]akarwa ya zamasaura-}iris al�adunmu su kasance na Turawada Indiya da sauran }abilun da ba namu ba,wanda Allah Ya taimaka aka samu ire-iren suFati da Maijidda sun janye duk wani jin kaiko yaudara na lokaci sun shigo wannan sana�adomin bayar da tasu gudunmawa, su ilimintarda jama�a, su kauce wa rayuwar yaudara, sugina rayuwar da babu da-na-sani. Wannanlamari ya haifar da alheri inda wasu gidaje daa da ke cikin tashin hankali sun samu fa�idadaga ~arakar zamani da taso ta na}asa zumunciga gidajen. Ha}i}a abin al�ajabi ne gare mu akan yadda za mu kasance bayan tafiyarsu akan rayuwar finafinan Hausa da ingancinsu.

Irin yadda Maijidda ta kasance �yar wasamai ]a�a, hankali da tunani, ga kuma biyayyaga furodusoshinta da daraktoci, abin sha�awane a yau ta nuna wa mijinta irin wannan horonfiye da yadda take fitowa a finafinanta. Natabbata tana fitowa kowane fim ne da burindomin mai kallonta ya wadatu da hikimartada }warewarta, to a yanzu ta kula da mijintafiye da hakan. Duk da yake an yi ta ya]a jita-jitar cewar ta shigo fim ne domin ta �kori�Fati ko kuma domin tana da }walisa, ammakuma jita-jitar da tsegumi duk tseguma ba suhau kanta ba, ya dace a gidan miji ta yi amfanida wannan tunanin ta guje wa duk tsegumada za a iya kawo mata dangane da mijinta.

Rayuwar fim a yanzu ta wuce ga Maijidda;wannan rayuwar ta zama tarihi sai kuma labariidan an yi nisha]i a gaba, domin an shigawata sabuwar rayuwa da ba a jiran furodusa,darakta, mai kwalliya, mai kunna fitila, mai

FATI MOHAMMED:

A LOKACIN da ta zo Sokoto inaKatsina, lokacin da na je Kano kuwatana Kaduna wajen gudanar da wasan

fim. Na share fiye da wata biyar ina canzatsarin ayyukana domin mu sadu da Fati donin ji tabbataccen bayanin aurenta a lokacin,amma kuma ban samu ganinta ba har saibayan lamarin auren ya yi nisa. Watau �yanmakonni zan bar Nijeriya, na ha]u da ita awani wurin ]aukar fim da nake zon shi ne na}arshe kafin a sanya ranar ]aurin aure dabakin �Gala.� Na dai je wurin ne dominsaduwa da wani abokina wanda yana cikinmasu shirya fim ]in. A gaskiya ganina daFati, watau Zubaina, Marainiya, kai da sauransunaye barkatai da ake yi mata, na tausayamata ne a kan irin rayuwar da na san ta fitodaga cikinta a yanzu ta shirya da finafinaizuwa wata sabuwa da za ta shiga ta zamawuri ]aya, watau aure dodon mata, rayuwarda ba ruwanta da furodusa ko darakta. Irinyadda Fati cikin natsuwa ta amsa mani wasutambayoyina, da kuma kasancewar ina ]ayadaga cikin masu sha�awar finafinanta tunlokacin da ta soma, ya nuna a zahiri tana damutunci da girmama ba}o.

MAIJIDDA ABDULKADIR:Na ha]u da ita kusan watanni biyu da fara

shigarta yin fim ]in Hausa, amma ban ta~anuna sha�awar magana da ita ba sai bayanwatanni kusan shida, bayan har finafinantasun fara shiga kasuwa sosai. Na ji da]i ainunirin karamcin da ta nuna mani, a lokacin dana yi mata wasu tambayoyi a kan rayuwar�ya mace dangane da finafinan yau da ake yi.Ta nuna min ita �ya ce a kan cika al}awarinlokacin da ta ba ni na mu yi hira da itamusamman. A cikin fahimta Maijidda tasaurari duk tambayoyina tare da ba ni amsarwa]anda take iyawa.

A yau ga rayuwar finafinan Kano, kai gaHausa baki ]aya, wa]annan ��yan matan�guda biyu ba }aramin jari ba ne a kan kowanelokaci. Tafiyarsu ba }aramar asara ba ce gaci-gaban finafinan Hausa, wadda za ta iyajanyo girgizar duniyar finafinan Hausa natsawon lokaci mai yawa. Amma kumatafiyarsu alheri ce ga kowane Musulumin}warai, a kan sun za~i rayuwa ce wacce idansun tsare ta, to ha}i}a tafarkinta zai zamaabin alheri gare su a gobe }iyama. Duk waniwanda ke son finafinansu, mafi alheri shi neya yi masu addu�ar fatan alheri a kan wannanauren da suka yi.

Babban dalilin da kowane mai kallonfinafinan Hausa zai iya bayarwa cewa ha}i}a

RA’AYI BA GABA BA NE

Fa]i Son Ka

]aukar hoto, ko kuma mai wa}a balle maikula da �yan wasa, �yan rawa ko wurinkwanciya ko bayar da ku]in jinga. Rayuwace ta neman lada, da ha}uri da kare mutuncidomin neman tsira gobe }iyama; ba rayuwace idan an sa~a ana iya komawa wajen wanifurodusa ba.

Ita Fati, duk da yake a yanzu ta fi kowace�yar wasa farin jini a duniyar finafinai, zai yiwuya a ce kai tsaye sunanta ya ~ata nan take.Irin yadda mujallar Fim ta yi wa takenlabarinta na bankwana, �Shi Kenan Ta Tafi!�,ya sa mutane da yawa fitar da hawaye, tunani,ka]uwar zuciya da jan dogon numfashi naajiyar zuciya saboda irin yadda ta shigazuciyar jama�a. Ganin Fati tana iya ri}ekowane matsayi a fim ya sa jama�a na tunaninzahiri ba wata da za ta iya shigewa takalminta.A bayyane yake Fati takan yi iyakacin}o}arinta wajen ganin ta }ir}iro ko kuma tayi wani abu da zai burge jama�a a duk lokacinda take wasa. Daraktocinta sun fi kowa saninhakan a wajen fim. Fati ba ta da wani da za aiya cewa domin sun fita tare ake son fim]inta. Duk wanda ke kallon fim ]inta yanada tabbacin cewar tana ri}e kowane matsayi,ba dole sai da wani fitaccen ]an wasa ko �yarwasa ba. Irin yadda ta fitar da wasu sukazama fitattun �yan wasa, a fili yake.

Ina iya tuna wata rana a garin Kasablankana }asar Marokko, muna kallon fim ]inMarainiya, sai aka nuno inda Fati ke ro}onmijinta (Ali Nuhu) dangane da wata matsalatsakaninsu. Sai abokina Jafar ya kada baki acikin mamaki ya ce, �Ina ma a ce wannanrayuwar ta gaske ce!� Shin Fati za ta iya yiwa mijinta na zahiri hakan? To ya dace Fati tatsare amanar mijinta. Duk abin da takekoyarwa a fim, to ta yi amfani da shi fiye dahakan a ]akin mijinta.

Ya dace mazajensu su yi ha}uri da surutanda za su iya biyo baya wa]anda wasu za suce ya dace a yi kaza ko kada a yi kaza,musamman ga mijin Maijidda tunda shi ba]an wasan fim ba ne.

Maijidda da Fati sun ci kasuwa kuma harabada kasuwa ta yi auki. Ha}i}a lokaci zaiiya tabbatar da cewar sun bar gi~i mai yawaa kyakkyawar rayuwar tarbiyya, mutunci,}wazo da fahimta. Sun yi abin da kowa keso, sun shigo ana murna da su, sun tafi anafarin ciki da irin sunan da suka samu.

Sai mu ce da sauran, }alubalenku! Muga naku domin taya ku farin ciki!

Yusuf Dingya]i ]an jarida ne mai zamankansa a Sokoto.

DAGA

YUSUF DINGYADI

Page 4: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

10 ga Agusta, 2001

Zuwa Ga Shugaba,{ungiyar Masu Shirya Fim ta Jihar Kano,Kano.

�Yalla~ai,

Mu �yan Hukumar Daraktocin kamfanin �Fim Publica-tions,� masu wallafa mujallar Hausa ta wata-wata mai sunaFim, mun rubuto maku wannan takarda ne domin mu sanarda ku wani hari ba bisa doka ba wanda wani ]anmuhimmmiyar }ungiyar nan taku mai suna AuwaluMohammed Sabo ya kai a kan biyu daga cikin marubutanmujallar a Kano.

Domin }arin bayani, za mu gaya muku dalili da yanayinda suka sa aka yi wannan hari. Akwai shaidu da yawawa]anda za su iya tabbatar da wannan labarin.

A ranar Asabar, 4 ga Agusta, 2001, da misalin }arfe 5:20 na yamma, shi wannan furodusan, Auwalu MohammedSabo, ya tu}o mota zuwa ofishin mujallar Fim na Kano dake lamba 22, Zaria Road, Gya]i-Gya]i. Wani gardinsa,mawa}in nan na fim, Mudassiru {asim, shi ya rako shi. Daisarsu, sai suka tarar ma�aikacin wurin guda ]aya ne kawaiya rage, domin sauran sun tashi aiki da }arfe 5. Wannan koshi ne Malam Ashafa Murnai Barkiya, editan mujallarBidiyo, wanda kuma marubuci ne na musamman na itamujallar Fim. Sai Ashafa ya tarbi mutanen da fara�a, yanatsammanin sun kawo ziyarar arziki ne irin wadda �yan fimsukan kawo wa mujallar a kowace rana. To amma saiAuwalu ya mayar masa da zagi da tsinuwa da ashariya dasauran nau�o�in hari wa]anda suka sa~a wa dokar }asarnan. Da fari, shi Ashafa bai ma san dalilin wannan tsinuwada ashariya ba. Amma ba a da]e ba ya gane cewa Auwaluyana bobotai ne sakamakon rashin jin da]insa da watawasi}a da aka buga a cikin Fim ta watan Agusta, 2001,wadda ta fito a Kano a wannan ranar. Ashafa ya ma kasamagana saboda wannan zagi da Auwalu yake ta kwaramasa shi da mawallafin mujallar, Malam Ibrahim Sheme,wanda shi ma bai da]e da barin ofis ]in ba kafin Auwaluya diro ba zato ba tsammani.

Daga cikin muggan kalaman da Auwalu ya yi a wurin,wa]anda mutane da dama da suka taru a wurin sun ji yanaambata su, akwai wa]annan da za mu lisssafa:

* Ya ce in da a ce ya zo da makami, to wallahi da sai ya

sassari Ashafa (wato ya halaka shi);* Kuma daga yanzu ko menene aka sake ambata a kan

kamfanin �Sarauniya Films� a cikin mujallar Fim, towallahi zai kashe duk wani ma�aikacin mujallar da yagamu da shi;

* Kuma idan wani mutum daga mujallar Fim ya kuskuraya sake zuwa ofishin � Sarauniya Films� ko ma wajajenwurin, to ya ba �yan daba na ita unguwar da yake, watoGwammaja, su sassare shi (wato su kashe shi);

* Kuma ya yi rantsuwa da Allah (SWT) cewa zai yi dukabin da zai iya yi don ganin }arshen mujallar Fim da masubuga ta (wato zai kashe su kenan).

* Da sauran ire-iren wa]annan kalaman.

Duk wani ro}o da ban-ha}uri da Ashafa ya ri}a baAuwalu ba su yi wata fa�ida. Hasali ma a cikin fushinsa nazautuwa sai Auwalu ya fizgo wata kalanda da ke jikinbango ya kekketa ta. To da Ashafa ya ga halin da Auwaluyake ciki (ga wata kwalbar lemo da aka sha kan tebur), saiya yi dabara har suka fito wajen ofis ]in, zuwa haraba,inda ]imbin jama�a �yan kallo suka taru, ciki har dawa]anda suke da ofisoshi da shaguna a wurin da kumamasu cewa a kan titi. A gabansu Auwalu ya ci gaba dasurfa ashar kan ma�aikatan Fim, yana cewa, �Iyayenku ne�yan daudun!� tare da al}awarta musu mugun gani. Kai,sai ma ya ce ai ya tuno cewa yana ]auke da wani makamia �yar }umbular motarsa, kuma ya soma kici-kicin bu]e tadon ya ]auko shi ya kashe Ashafa. Sai mutane suka tilastawa Ashafa cewa ya gudu, kuma ya gudu ]in ya tsallakababban titi a guje. Da Auwalu ya ga haka sai ya ]aukiwani }aton dutse ya jefe shi, amma ya kuskure gindinkunnensa da �yan incina. Ashafa ya sami wani ]an aca~aya hau ya bar wurin.

Hari Na 2Da misalin }arfe 7 na wannan yammar (wato kamar awa

]aya bayan wula}ancin da aka yi wa Ashafa), Auwalu yaci gaba da farautar �yan mujallar Fim a Sabon Titi, indayawancin �yan fim suke. A lokacin, ]aya marubucin namu,Kallamu Shu�aibu (Musa), wanda bai san abin da kefaruwa ba, ya ziyarci kamfanin �Ibrahimawa Production�,anan Sabon Titi. Sai ya tarar da wani gungun �yan fim suntaru, irin su Mansir A. Shariff da Zulkifilu Muhammad, dakuma Auwalu Mohammed Sabo. Da farko, Mansir ya nemiya hana Kallamu }arasowa da ya hango shi yana zuwa,domin an taru ne ana sauraren cika-bakin da Auwalu ke yia kan harin da ya kai a ofishin mujallar Fim. To ko daAuwalu ya }yalla ido ya ga Kallamu, wanda shi bai sanabin da ya faru a ofis ba a goshin magariba, sai shi Auwalu

SANARWA TARE A KAWO KUKA A KAN HARINDA WANI FURODUSAN FIM, AUWALU

MOHAMMED SABO, YA KAI A KAN MARUBUTAGUDA BIYU NA MUJALLAR FIM

(An fassaro wannan takardar daga ta Turanci da aka mi}a)

Page 5: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

kawai ya auka masa, ya ci kwalarsa ya sha}e shi, yanadukansa da haurinsa ba ji ba gani. Bugu da }ari yana tafurta wasu kalamai irin wa]anda ba a bugawa donkarantawa. Har sai da mutanen da ke wurin suka tarusannan da }yar suka ~am~are shi daga jikin bawan Allannan ]an jarida wanda bai san hawa ba bai san sauka ba.Mutane masu tausayawa suka janye Kallamu suka tsaidatasi suka cusa shi a ciki, suka ce don Allah ya bar wurin, ayayin da shi kuma Auwalu aka ri}e shi kam yana ta haure-haure tare da hargowar shi tilas a sake shi don ya kasheKallamu. Sai bayan sama da awa ]aya ne ma sannanKallamu ya ji dalilin da ya sa Auwalu ya nemi ya kasheshi, wato a lokacin da mawallafin mujallar, IbrahimSheme, ya ziyace shi a gida don ya ba shi labarinarangamar Auwalu da Ashafa. Shi ma Ibrahim a nan ya jilabarin na Kallamu.

Me Ya Jawo Wannan Dabbancin?A cikin wannan daren, Ibrahim Sheme ya je neman

Auwalu a ofisoshin shirin fim a Sabon Titi inda ya ji an cean gan shi, saboda su tattauna wannan al�amari. To ammasai Mansir A. Shariff da daraktan fim ]in nan, HafizuBello, suka hana shi }arasawa ofishin �Sarauniya Films�don su ha]u, suka ce Allah ka]ai ya san abin da zai faruidan shi da Auwalu suka ha]u a lokacin.

To me ya jawo wannan mugun fushi da kai hari marasma�ana? Shi dai Auwalu Sabo shi ne shugaban kamfaninnan na masu shirya fim wanda ake kira �Sarauniya Films,�wa]anda ofis ]insu yake kallon Asibitin {ashi na Dala dake Kano. A cikin fitowar mujallar Fim ta watan Agusta (ashafi na 7), an buga wasi}ar wata mace mai suna FannaAbu, wadda daga Kano ta rubuto. Da gani, ita mai rubutuntana daga cikin mutanen da suka kalli wani sabon shiri na�Sarauniya Films� mai suna Sartse. Ta rubuto ne tana kukakan yadda ]aya daga cikin �yan wasan fim ]in ya ri}a]abi�a kamar ]an daudu. Ta shawarci Sarauniya da sudaina nuna irin wannan ]abi�ar a finafinansu domin sutsare kyakkyawan sunan da suka yi a harkar shirya fim]in. (Ga kwafen wasi}ar nan mun ha]o muku).

To wai wannan wasi}ar ce ta harzu}a Auwalu, ta sa yashiga fushi irin na zautuwa.

’Yan Jaridar Da Yake Son KashewaMu a matsayinmu na Musulmi, mun yi imani da cewa

Allah ne ke rayarwa kuma shi yake matarwa. To amma a}asa wadda take da dokoki da hukumomin shari�a, baikamata mutum ya yi wasa da barazanar da Auwalu ya furtacikin jama�a ba, kuma yake ci gaba da furtawa.

Mutane ukun da Auwalu ya yi harin kashewa (ko mayake hari har yanzu), fitattun �yan jarida ne wa]anda sukayi karatun jami�a a kan aikin jarida ko suka sami iliminsaa gidajen jarida:

1. Ibrahim Sheme (Mawallafi): Ya kammala karatunsaa Jami�ar Bayero, Kano, inda ya sami digiri a cikin 1989 afannin Watsa Labarai (Mass Communication). A shekararda ya fita ma, shi ne aka bai wa Kyautar [alibi MafiHaza}a a Fannin Watsa Labarai, kuma shi aka ba Kyautar[alibi Mafi Haza}a a Tsangayar Fasaha Da NazarinAddinin Musulunci ta jami�ar. Wa]annan suna daga cikinmanyan kyaututtukan da jami�ar ke bayarwa, wa]andakowa yana son su. Har ila yau Ibrahim ya samo digiri na

biyu a aikin jarida daga jami�ar nan mai suna �Universityof Wales� da ke birnin Cardiff, a }asar Birtaniya, a cikin1994. Ya rubuta littattafai da dama, kuma yana aikinjarida tun daga 1989, inda ya ri}e mu}amai kamar sumataimakin edita ko edita a shahararrun kamfanoninjaridu irin su jaridar Nigerian Tide (a Fatakwal), da TheReporter, Nasiha, Rana, Hotline, and New Nigerian (aKaduna). A yanzu shi ne editan adabi na jaridar mako-mako ]in nan mai suna Weekly Trust. Bai da]e ba da ri}emu}amin Daraktan Bincike a hukumar tunawa da tsohonmataimakin shugaban }asa, wato �Shehu Musa Yar�AduaFoundation,� a Kaduna. Yana da aure da �ya�ya.

1. Kallamu Shu�aibu: Ya sami digiri daga Jami�arAhmadu Bello, Zariya, a cikin 1991, a fannin harkokin}asashen waje da diflomasiyya (International Relations).Ya da]e yana aikin jarida a gidajen jaridu da suka ha]a damujallar Hotline da ke Kaduna, inda ya ri}e mu}aminBabban Marubuci. Shi ma yana da aure da �ya�ya.

3. Ashafa Murnai Barkiya: Ya sami digiri a AikinJarida daga Jami�ar Bayero, Kano, a cikin 1995. Yanaaikin jarida tun da ya gama jami�a. Ya ta~a zama babbanmarubuci a jaridun Shield/Garkuwar Arewa kafin ya dawomujallar Fim. Shi ma yana da aure.

Ba mun kawo wa]annan tarihi namu ne don nuna isa kowani bagu ba, a�a mun kawo su ne don mu nuna cewawa]annan mutane uku da Auwalu ya yi wa barazanar (koyake wa barazanar) yi wa kisan gilla, �ya�yan Nijeriya newa]anda suka yi karatu mai zurfi a kan aikin da sukeaiwatarwa a yanzu. Mun yi amanna da cewa ba za mu ta~a}o}arin ~ata sunan wani ]an fim da gangan ba domin yinhakan zai sa~a wa }a�idojin nan na aikin jarida wa]andasuka gindaya lallai ]an jarida ya tsare gaskiya a aikinsakuma ya ba kowa ha}}insa. A ganinmu, mujallar Fim tatsaya kai da fata a kan wannan amannar, kuma ta tsaya akan tunanin cewa harkar fim ]in Hausa ta wannanzamanin, wadda har yanzu jaririya ce, tana bu}atar ataimaka mata ta girma ta hanyar kawo rahotanni masuda]i da muhawarori a cikin natsuwa. Mu a ganinmu abinda muke ta yi kenan, kuma hakan ya sa sana�ar fim ta kaiinda take a yanzu. Ba shakka, Fim ce mujallar da ke kangaban kowace mujallar Hausa a Nijeriya a yau.

�Sarauniya Films� da MuMun ]auka cewa �Sarauniya Films� suna daga cikin

abokan hul]armu na gaskiya, kamar yadda muka ]aukidukkan sauran ofisoshin shirya fim manyan da }ananan.Auwalu da }anensa Aminu Mohammed Sabo (daraktanfim wanda yake karatun Watsa Labarai a Jami�ar Bayeroyanzu) suna daga cikin masu shirya fim wa]anda muka yi}o}arin }ulla kyakkyawar dangantaka da su a cikinshekara ]aya da rabi da ta wuce. A da, ba su son �yan jaridaa cikin harkarsu, to amma a hankali sun nuna sun aminceda mu bayan sun fahimci kyawun hul]armu daabokantakarmu da sadaukarwarmu a aikinmu. Hasali ma,mun sami amincin Aminu ta yadda har ya zo yana sakatallar finafinansa a cikin mujallar Fim, sannan shi maAuwalu yana tallar wasu abubuwan nasa, wato kamarshagon �business centre� wanda suka bu]e kwanan baya. Acikinsu babu wanda ba mu buga hirarsa ko labarinsa amujalla ba a lokuta daban-daban (kama daga auren}annensu Fati Abubakar da Jamila Moh�d Sabo, zuwa hiraa kan rayuwar Aminu), kuma mukan tuntu~e su don jin

Page 6: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

ra�ayinsu kan al�amuran da suka shafi sana�arsu. MujallarFim ta sha buga wasi}un masu karatu masu yabon�Sarauniya� (amma Auwalu bai ta~a cewa ya gode ba). Kai,ko a fitowarmu ta watan Agusta, fitowar da Auwalu yakekuka da ita har yana karya doka kuma ya hana saidamujallar a shagon Sarauniya, mun buga talla shafi ]aya taSarauniya inda suke taya Fati Mohammed murnar aurenta.Dukkan tallace-tallacen Sarauniya a bashi muke buga su,har da ita ta }arshen, sai daga baya su biya.

A gaskiya, mun mun ]auka cewa mu abokan Auwalu nena }ut da }ut ta yadda ko lokacin da Malam IbrahimSheme ya kafa sabuwar mujallar nan mai sharhi kanfinafinai (wato Bidiyo) a cikin watan Yuli 2001, sabon fim]in Sarauniya ne (Garwashi) aka sa a bangonta ba tare dasun biya ko sisi ba, sannan aka buga sharhi kan fim ]insuna Sartse kusan shafi biyu. Kuma kimanin kwana ukukacal kafin Auwalu ya kawo harinsa na karya doka,Ibrahim ya ziyarce shi a Sarauniya inda suka tattaunaharkar fim, musamman ma irin labaran Sarauniya da akebugawa a mujallun biyu. Suka rabu lafiya lafiya, ana wasada dariya.

Don haka ka ga kenan mu ba mu da wani mugun nufi akan Sarauniya ko Auwalu ko wani nasu. Wasi}ar daAuwalu ke fushi da ita ba wata ba ce daban da tabambanta da ]imbin wasi}u irin wannan wa]andamujallar Fim take bugawa tun daga 1999. Ba mu mukarubuta ta ba, kuma ba mu buga ta don mu ~ata sunan dukwani mai ala}a da Sartse ba. A gaskiya ma, an za~o ta nedaga cikin wasi}u masu tarin yawa da aka aiko a kanbatun nan na fim ]in Sartse. Da yake mun san �yan fim dadama ba su son a soke su ko }iris, za mu iya fahimtar daAuwalu dalilin buga wasi}ar in da a ce ya nuna rashin jinda]insa ta hanyar hankali da wayewa. Kuma ai idan shiAuwalu ba zai amince da ha}urin da za mu iya ba shi alokacin ba, yana iya kai }ara a kotu. Wa]annan su nehanyoyi mafi hankali da sanin ya-kamata maimakon kaimummunan hari da mugun makami.

KukanmuBayan Auwalu Sabo ya kai mana hari, mutane da dama,

�yan fim da wa]anda ba �yan fim ba, sun bayyana matu}aral�ajabi a kan wannan halin assha nasa, sun yi Allah-wadaida shi, kuma sun jajanta mana. Hasali ma, wasunsu masuson ganin harkar fim ta ci gaba da bun}asa, kuma suna sona ci gaba da yin zaman lumanar da ke akwai a harkar, sunro}e mu a kan don Allah kada mu kai shi }ara duk da yakehakan kowa ke zato za mu yi.

A ha}i}anin gaskiya, mun yi matu}ar mamakin wannanhalayya da Auwalu ya nuna a wannan zamani na wayewarkai, kuma mun yi ba}in cikin yadda mutumin da muka]auka abokinmu ya butulce mana haka. Muna ba}in cikincewa mutum kamar Auwalu, wanda muka ]auka natsattsene wanda shi ne ma ya kamata a ce ya hana wani ya cizarafinmu haka idan ya ji labari, amma shi ne zai nemikashe mu kuma har ya ]auki hanyar kashe mu ]in.

Abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, mun damu a kanodar da ya ce ya bayar a halaka mu tare da wannanmujallar abar so ga kowa, wadda ta yi wa �yan fim dasauran jama�a aiki tu}uru, amma a ce wai a ga bayanta kota halin }a}a. Muna jin tsoron abin da zai same mu daiyalanmu da sauran abokan aikinmu a nan gaba,musamman tunda har an shigo da ta�addanci a matsayin

wani mummunan zango cikin wannan harka ta shirya fim]in Hausa wadda take bun}asa a kullum. Shi ya sa mukayanke shawarar mu rubuto maku wannan takarda, kumamu aika wa hukumomin da abin ya shafa, domin amatsayinku na wa]anda suka yi amanna da bin doka, zaku ]auki mataki da wuri-wuri kuma yadda ya dace. Har ilayau mun mi}a wannan magana ga lauyoyinmu don su masu shawarce mu kuma su ]auki mataki.

Muna yin Allah-wadai da babbar murya da wannan harina Auwalu da kuma mugun nufin da ya furta a kanmu,sannan muna kira ga }ungiyarku/hukumarku kamar haka:

1. Ta samar da kyakkyawan yanayi inda za a kareaikin jarida kuma a bun}asa shi, musamman a Arewa;

2. Ku ja kunnen Auwalu Mohammed Sabo a kanmugun aikin da ya ba kansa ba kunya ba tsoro;

3. Ku sa Auwalu ya rubuto mana takardar ba da ha}urita hanyar }ungiyarku/hukumarku a kan harin da ya kaimana bisa karya doka;

4. Ku fahimci cewa idan har wani mugun abu ya samemu a yanzu ko a nan gaba, to Auwalu M. Sabo ne za akama da laifi;

5. Ku san cewa ba za mu }yale ba idan a nan gaba aka}ara kawo mana irin wannan harin, domin za mu nemiha}}inmu a kotu;

6. Ku yayata wannan magana a tsakanin membobin}ungiyarku domin ta zama hani ga sake faruwar irinwannan hari da bai kamata ba a kanmu; sannan

7. Ku shawarci �ya�yan }ungiyarku su guji aikata dukwani abu da zai tayar da hankalin al�umma, ko ya lalatazaman lafiya da bun}asar sana�ar fim na Hausa.

Mu ne naku,

�Yan kwamitin daraktocin kamfanin �Fim Publications�:

Malam Ibrahim Sheme da Alhaji Garba Dangida

Mun aika da wannan takarda ga:1. Daraktan hukumar tsaro ta SSS na Jihar Kano2. Mai Girma Gwamnan Jihar Kano3. Mai Martaba Sarkin Kano4. {ungiyar Furodusoshi ta Arewa5. {ungiyar �Yan Wasa ta Jihar Kano6. {ungiyar Daraktocin Fim ta Jihar Kano7. {ungiyar �Yan Fim ta Nijeriya (MOPPAN), reshen

Arewa8. Kwamishinan �Yan Sanda na Jihar Kano9. Kwamishinan Shari�a na Jihar Kano10. Kwamishinan Ya]a Labarai, Matasa, Wasanni da

Al�adun Gargajiya na Jihar Kano11. Shugaban {ungiyar �Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ),

Abuja

da kuma lauyoyinmu:12. Mamman Nasir & Co., Kaduna13. S.H. Garun-Gabbas & Co., Kano

Page 7: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Aminu Ali Zango

ce na yi abin da ba daidai ba amma ban san na yi ba, to idan na karanta sai in gyara.Shawarar da zan bai wa masu buga wannan mujalla ita ce mutum ya ri}e gaskiya.

Duk abin da mutum zai yi, to ya sa gaskiya a gaba. Ba don komai na fa]i haka ba, saisaboda ita irin wannan mujallar, masu ]auko mata labarai za su ji abubuwa da dama.Wani idan an buga labarinsa sai ya ce an rage masa, wani kuma ya ce an }ara masa. Tokamata ya yi ma�aikatanta su sa gaskiya a duk abin da za su yi don Allah. Duk abin damutum ya fa]a a ri}a rubuta masa haka; kada a rage, kuma kada a }ara. Duk wanda yasa gaskiya zai ga aikinsa na tafiya daidai.

AMINU ALI ZANGO, fitaccen dan wasa:MUJALLAR Fim tana nisha]antarwa da sanin me harkar fim take ciki, idan da gyara agyara, idan da yabo a yaba. Babu alamar mujallar Fim tana ]aukar labarai na ~atanci,

6

Abin da ya sa muke karanta mujallar

Zulkifilu Muhammad

ZULKIFILU MUHAMMAD, fitaccen dan wasa:NI Zil}ifilu Mohammed, tabbas ina karantamujallar Fim. Ina kuma karanta ta ne don mutumya sami sanin abubuwa kan sana�arsa da shi kansa.Ga kuma shawarar gyara harkar fim da jama�a dadama ke rubutowa. Ka san wani gyaran ba za kasani ba sai wani ya fa]e shi daga waje.

To ina ba masu mujallar Fim shawara su }aradagewa su ci gaba da ayyukan da suke na alheri.Fatarmu shi ne mujallar ta koma kala gaba ]ayakamar �Stardust� da �Film Fare.� Mujallar Fimabokiyar tafiya ce.

JAMILA HARUNA, fitacciyar ’yar wasa:INA karanta mujallar Fim saboda in }aru daabubuwa � kamar masu rubuto mana wasi}u,kamar kuma abubuwan da suka shafe mu mu �yanwasa, wanda in na ga an fa]i wani abu da ba daidaiba, zan san yadda zan yi in gyara, ko da kuwa ni

Maryam Danfulani (Mashahama)

saboda ko hira suka zo yi da mutum sukan zo darikodarsu ne su ]auki maganarka, sannan idan suntashi bugawa su sa hoton mutum. In kuma waniabu ne ya ha]a ka da wani sai sun bi kowannenkusun ji ta bakinsa. Mujallar Fim ita ce best ]ina,sannan sauran suka biyo baya.

MARYAM MOH’D DANFULANI, fitacciyarfurodusa/’yar wasaNI kuwa ke karanta mujallar Fim. Dalili kuwa donmasu ita ba za su yarda in karanta gaibu ba. Kokuma in sayi mujalla, bayan na karanta mutum yace min shi ba haka ya fa]a ba. To saboda ba su yinwannan }arya da }age shi ya sa ba na }yashin cireku]ina in zauna in karanta. Duk abin da sukarubuta zan iya fa]a a gaba kuma in rantse sabodana san ba za su yi }arya ba.

Ina ba su shawara don Allah don Annabi, daidaida }wayar zarra a guji yin }arya da }azafi. Shi fa

Ahmed S. Danjummai

Jamila Haruna Yakasai

Allah ba mutum ba ne; yana nan a madakata, in ka cuci mutum sai ya saka masa. Dukabin da za su fa]a su zauna su tsage gaskiya. Tunda hanyar abincinsu ne, kada yakasance suna cin haram, su zamanto halal ]insu suke ci.

AHMED S. DANJUMMAI, sabon furodusa/dan wasaINA karanta Fim saboda ganin irin }wazo, kwarjini da hikimar da ke cikinta, wanda abisa gaskiya yana da bambanci da wasu mujallu da ke son koyi da Fim. Domin kuwaakasarin labaran da Fim ke ]auka tana ]auka ta hanyar finafinai na Hausa wa]andasuna isar da sa}wanni da kuma ]aukaka harshen Hausa ita kanta. Ba kamar wasu dake cika mu da labaran da ba su da sahihanci ba, a nan yabon gwani ya zama dole.

Page 8: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Wacece Mace?

ITA dai mace, raunanniyar aba ce wacce lan}wasa ta kotayar da lan}wasarta ba zai yi wuya ba, saboda rauni.Don akwai hadisi ingantacce da yake cewa, �Annabi

Muhammad (SAW) ya ce, �An halacci mace daga autanha}ar}arin namiji, don haka a yi a hankali da su, don raunanane�.�

Wannan hadisi shi ne damar da maza suka samu wandasuke amfani da ita wajen nuna wa mata cewa sun fi su }arfida iko a fannin rayuwa, ba don komai ba sai don sun ]aukaraunin da mace take da shi kamar }as}antarwa ne. Kumawani abin lura shi ne komin }an}antar yaro sai ka ji yanacewa MATA AI BA SU DA HANKALI.

Wannan magana ta riga ta ginu a zukatan maza, don hakakankare ta yana da wahala. Duk da cewar akwai wani hadisiningantacce da ya yi umarni da cewar a bi uwa har sau uku,kafin a ce a bi uba. Za kaga uwar ba ta isa ma tayi magana ba balle ma abi abin da ta ce saboda�ya�yan nata da mazanba su maida ita komai ba.Wannan mutane biyu da�ya mace ke rayuwa dasu shi ne da mijinta dakuma �ya�yanta. Kafin inci gaba da sharhina, barima mu duba mu ga waiita macen wacece ita,kuma wane mataki takantaka kafin ta kai gatsufanta?

AKWAI MATAKAIKASHI SHIDA:

Jaririya, {waila,Budurwa, Baliga,Gwanduwa, sai kumaTsohuwa.

Wa]annan su ne matakai shida da kowace mace take hawakafin ta koma ga Mahaliccinta. Kuma ga bayanai a kankowane mataki:

1. Jaririya: Ita jaririya ita ce wadda tun daga ranarhaihuwarta iyaye za su zuba ido a kanta; tun daga farkonkoyon zamanta, rarrafe, da kuma koyon tafiya. Ba kasafaitakan ha]u da rigimar rayuwa ba, sai dai ciwo � irin zazza~inha}ori, }yanda, da shan inna; su ne hatsarin da ke tattare dayarinya jaririya.

2. Kwaila: Wannan mataki shi ne lokacin �ya mace tana

fita tallace-tallacen da kan jawo masifa ko ~atan yarinyar.3. Budurwa: Matakin budurci yakan kama daga shekara

12 zuwa 16. Wannan tsakanin shi ne mafi hatsari a gurin�ya�ya mata, domin idan babu kyakkyawar kulawa dagawajen iyaye, to fa komai na iya faruwa. A wannan tsakani nesuke koyon kowane irin she]anci ko kuma su gwada shi inhar da tsautsayi.

4. Baliga: Wannan shi ne matakin da �ya mace idan takai shi takan fara jininhaila. Shi ne iya cikarda za ta yi ta ]aukarciki a duk lokacin danamiji ya kusance ta.Kuma kowace ~arnama a wannan lokacinne take faruwa sabodakomai na cikinta yaha]u, hatta zuciyartata riga ta nutsu; takaniya za~ar abin da takeso, domin ta balaga.

5. Gwanduwa:Wannan shi nematakin kamala damutunci ga �ya mace,yayin da takaishekara 25 zuwashekara 40. Ita cewadda ta mallakihankalinta, ta yi

haife-haife, kuma ta san ba}i ta san fari a harkar rayuwa.Domin wannan lokacin ta gama kammaluwa.

6. Tsohuwa: Wannan shi ne matakin na }arshe na tsufa akan mace yayin da ta bai wa shekara 50 baya. A wannanlokaci sha�awar namiji takan fita daga zuciyarta. A wata intsufanta ya yi yawa za ta zama �ya�yanta su ne iyayenta, donhankalinta ya fara fita daga jikinta.

daga

BALARABA

RAMAT YAKUBU

Wannan shi ne sabon filin da muka yi muku al}awarin zai fara fitowa amujallar Fim ta watan jiya. To, an sami wani kuskure, shi ya sa bai fito ba,sai yanzu. A cikinsa, Hajiya Balaraba, wadda shahararriyar marubuciyarlittattafai ce, kuma furodusar fim ]in Sai A Lahira, za ta ri}a yin tsokaci akan rayuwar iyali, musamman irin namu na Musulmai. Don haka ne ma tasoma share fage da amsa tambayar �Wacece Mace?� Muna fatan za a amfanada bayanan da za ta ri}a yi.

’Ya’ya mata: Gwanda tun tana karama ake tankwasa ta

7

shekara biyar zuwa shekarasha biyu. Akwai ha]ari akan mace ga wannan kashidon ta fara yawo a titi. Awannan lokaci ne iyayekan sanya ido a kanyarinya, domin takan jemakaranta ko kuma takan

* Za mu ci gaba insha Allah a Fim ta watan gobe, indaHajiya za ta yi }arin bayani a kan wa]annan rabe-rabe namatakan rayuwar �ya mace. Ku biyo mu.

Page 9: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

8

Muna maraba da wasi}un masukaratu. A tabbatar an sa cikakkensuna da adireshi, kuma a yirubutu mai kyau. A ta}aitabayani. A aiko da sauri zuwa gaEdita, FIM, P.O. Box 10784,Kano. Tel.: 062-417347;243112E-mail:[email protected]

Wasi}u

MAWALLAFIIbrahim Sheme

*DARAKTA

Alh. Garba Dangida*

MATAIMAKIN EDITAHamisu Mohammed Gumel

*WAKILAI

Kano: Kallamu Shu’aibu, MuhammedNasir, Yakubu Ibrahim Yakasai;

Kaduna: Iro Mamman, Aliyu AbdullahiGora II;

Jos: Sani Muhammed Sani;Katsina: Bashir Yahuza;

Sokoto: Bashir Abusabe*

MARUBUTA NA MUSAMMANAshafa Murnai Barkiya

Danjuma KatsinaHalima Adamu Yahaya

*KASUWANCI

Mukhtar Musa DikwaSadiya Abdu Rano

*HOTO

Bala Mohammed Bachirawa*

KOMFUTAMary Isa Chonoko,

Mohammed K. Ibrahim*

MASHAWARTAAlh. Kasimu Yero, Dr. Abubakar A.Rasheed, Alh. Yusuf Barau, Hajiya

Balaraba Ramat Yakubu, Alh. Sa’idu M.Sanusi, Alh. A. Maikano Usman,

Alh. Habibu Sani Kofar-Soro*

LAUYOYIMamman Nasir & Co., Kaduna

S.H. Garun-Gabbas & Co., Kano

Mujallar FIM (ISSN 1595-7780) tana fitowane a kowane wata daga kamfanin Fim Publi-cations , No. 142, Zaria Road, Gya]i-Gya]i,Kano, Nijeriya. Ofishinmu a Kaduna: S. 11,Ibrahim Taiwo Road, saman asibitin �Ya�uMemorial,� gefen Kasuwar Barci, Tudun Wada,Kaduna. A aiko da dukkan wasi}u zuwa gaMujallar FIM, P.O. Box 10784, Kano. Tel.: 062-417347, 243112. Adireshinmu na E-mail:[email protected]. Ba a yarda a sarrafakowane ~angare na wannan mujalla ba tare daizini a rubuce daga mawallafanta ba. Maisha�awa zai iya karanta Fim kyauta a ko�ina aduniya ta hanyar Internet ta wannan adireshin:www.kanoonline.comHa}}in mallaka (m) Fim Publications

NI a rayuwata, ban ta~a soyayyar data girgiza ni ba, kuma ta tsunduma

ni a cikin bege, irin soyayyata da FatiMohammed. Allah Ya bar mu tare har}arshen rayuwarmu amin. A gaskiyarashin Fati Mohammed ba }aramin ragekallon wasan Hausa zai yi ba, musammanma ga masoyan jarumar kamar ni. Dukda cewa aure shi ne alheri amma wallahimun yi rashi. Sai dai da yake akwai wata}awata kuma masoyayiyata, Abida, da]an dama-dama.

Shawarata ga Fati, wato Mrs. SaniMusa Mai Iska, ita ce: don Allah don sonmanzonsa Fati ki daure, ki cije, ki ha}uraki zauna da Sani tsakani da Allah. DonAllah Fati, kina da kirki, ga ri}on amana,ga addini, ga son jama�a. To dan Allah kici gaba da hakan. Allah Ya sa albarka, amin.

Hassan Ibrahim,No. B24, Jajere Road, Badikko, Kaduna.

FATI KI BURGE SANI SHI MAZUWA GA MUJALLAR FIM,

MUN gode wa Allah da Ya ba mu damar rubuto wannan wasi}adon taya jarumar finafinai (The best of the rest), Fati Mohammed, murnar

aure. A gaskiya Fati kin ciri tuta, Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya sa wajenzamanki ne. Don Allah ki ba mara]a kunya. Kamar yadda kike burge masukallon finafinai Allah Ya sa haka za ki yi wa Sani.

Sani, Allah Ya taya ka ri}on Fati da uwargidanta. Mun yi rashinta ammaaure shi ne mafi alkhairi. Daga }arshe don Allah muna so mujalla mai farin jinita ba mu tarihin Hadiza Mohammed.

Maryam da Rahina,

Abubakar Mahmud Gumi College, P.O. Box 679, Kaduna.

immediatepast

edition

(ISSN 1595-7780)Jagorar Mujallun Hausa

Muna sanar da abokan hul]armu cewa ofishinmu na Kano yatashi daga inda yake yanzu. Mun koma gida mai lamba 142,Zaria Road, Gya]i-Gya]i. Kwatancen gidan shi ne idan ka baroofishinmu na da, ka nufi wajen �Dangi Roundabout�, kafin ka}arasa gidan mai, daidai �Glass House� daga ~arin yamma, akwaiwani farin bene hawa ]aya. Nan ne ofishin. Wato in kuma kataso daga �Dangi Roundabout�, da ka wuce gidan mai, dagahannun dama, ofis ]in yana nan. Idan har ba ka gane wurin ba,to ka je can ofishinmu kusa da �Fly-over,� za a kawo ka har indamuke. Sai ka zo.

Sabon Ofishinmu A Kano

A LKWYAKUZUWA

MUJA

MUNwasi}fa]i gw amutaAlhasya fKumukusa bda maiya wmutuyana kyautKumukomako kKwalKumudubi UwarTawaka san shi. Sina furoddarakdingaKwalwasan

SON FATI YA GIRGIZA MIN RAYUWAZUWA GA MUJALLAR FIM,

Page 10: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Wasi}u

Duk wani wanda yake so yafa]i wani abu muhimmi a kanharkar finafinan Hausa,to a Mujallar FIM zai so ya fa]imaganarsa...

* an fi karanta ta* ga kyan tsari da yawan shafuka* ga hikimar lafazi* ga kamanta gaskiya* ga isa kowace jiha* ga fitowa a kowane wataShirya fim ba tare da tallata shi ba kamar harara a duhu ne. Me zai hana ka sa tallarka a cikin FIM?

Jagorar Mujallun Hausa

YI HATTARA DA MUGGAN KAWAYEZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto maku wannan wasi}a don in nuna farin cikinmu a filina taya Fati Mohammed murnar auren da ta yi. Da fatan Allah

Ya ba da zaman lafiya. Da fatan ba za ta bi shawarar }awayen banzaba. Domin }awar banza ce ba ta son ka yi aure.

Ina mi}a gaisuwa ta musamman ga Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu,Abida Mohammed, Hindatu Bashir, A.A. Sharif, Sani Danja, IshaqSidi Ishaq, Biba Problem, da Maijidda Abdul}adir (ita ma muna tayata farin ciki).

Najia Farouk,F.G.G.C. Minjibir, P.M.B. 3414, Tel: 633119 or 663247,

Kano.

SAMBARKA, MAIJIDDA DA FATIZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasi}a ne don na nuna farin cikina ga aurenMaijida Abdul}adir da kuma auren Fati Mohammed da Sani

Musa Mai Iska. Allah Ya ba da zaman lafiya.Kuma ina mi}a gaisuwata ga Abida Mohammed, Fati Sulaiman.

Kuma Allah Ya raya wa Halima ]anta, Allahumma amin.Raliya Muhammed Inuwa,

No. 30, Janzuma Road, Unguwar Mu’azu, Kaduna .

KI KARO ILIMIZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in ba Fati shawarar ta koma makaranta saboda ganin baiwarda Allah Ya ba ta. Lokaci bai wuce ba.Ko kuma ta samu malama da za ta koya mata Turanci da karatu

kawai. Idan ta yi haka, ko daga ]akinta yi haka ko daga ]akinta za tasan abin da duniya take ciki. Kuma ita ma za ta iya aiko da natashawarwarin da ra�ayoyi ba tare da wani ya rubuta mata ba. Abin nufia nan shi ne ba wai ta tafi kenan ba ta zama tarihi. Muna nan saurarenta. Shi kuma angonta, ina ro}o gare shi da kada ya kulle ta da yawa.Ba mu ce ta yi fim ba, amma ta }ara ilimi don ta zama mai ba dashawara ga �yan mata matasa, kuma za ta iya zama furodusa ita ma.

Don Allah ku duba wannan shawara da idon basira. Allah Ya albarkaciauren, amin.

Asiya N Hassan,

P. 8, Dutsin-ma Street, T/Wada, Kaduna.

YI KOYI DA MANZON ALLAHZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah Fati ki yi koyi da mai sunanki, wato Fatima �yarAnnabi Muhammad (SAW). Ki zauna lafiya zauna lafiya da

mijinki da kishiyarki. Kin ga kamar a fim ]in da kika yi, AljannarMace na 2, an zuga ki, amma ba ki ]au zugar ba. Don Allah Fati karki ba mu kunya.

Hauwa’u Bello,No. 2, Opposite Sultan Bello, Mosque, Kaduna.

MUN YI FARIN CIKI DA AURENZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasi}a ne domin taya tauraruwata, FatiMohammed, da angonta Sani Musa Mai Iska murnar auren da

suka yi, da fatan Allah Ya ba su zaman ha}uri, kuma Ya zaunar da sulafiya, Ya ba su zuriya ]ayyiba, amin.

Sannan zan yi amfani da wannan dama domin mi}a godiya gamasu wannan mujallar, don tunani da suka yi wurin }ir}iro manawannan mujalla mai farin jini. Allah Ya saka masu da alheri, amin.

Mohammed Rabi’u Usman (El-Rabs),

Malam Audu Mai Hafizai, Abuja Road, Rigasa, Kaduna.

ALLAH YA BU HAKURIN ZAMAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku mi}a cikakkiyar taya murnata ga Fati Mohammed daMaijidda Abdul}adir da Allah ya sa suka yi aure. Haka kuma su

ma mazan, wato Abubakar da Sani Mai Iska. Ina fatan Allah Ya ba suha}urin zama da matansu, amin.

9

Page 11: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Wasi}uBayan haka ina son ku mi}a gaisuwata ta musamman ga Wasila

Isma�il, Ali Nuhu, Isah Ibrahim, Ibrahim Mandawari, Tahir Fage.Halima Hassan Kuyello,

P.M.B. 001, Birnin Gwari LGA, Jihar Kaduna.

FIM BA FATI BA NA KALLONSAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA matu}ar ba}in ciki da zan daina ganin Fati a fim. Kai ko da mana zamanto idan fim ba Fati a ciki ba na kallonsa.Mohammad Haladu,Limawa, Dutse, Jihar Jigawa. Kaduna Tel: 062-411347.

ALHERI GA FATI DA MAIJIDDAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA taya wasu murnar samun ci-gaba da suka yi, ta fannin aure. Sune Fati da Maijidda. Allah Ubangiji Ya sanya albarka a cikin wannan

aure, amin.Ina fatan za ku isar da sa}on gaisuwata zuwa ga Abida Moh�d,

Hajara Usman, Wasila Isma�il, Ibrahim Mandawari da kuma babbanmasoyina Rabilu Musa (Ibro).

Murtala Umar,Central Bank of Nig., P.M.B. 2151, Katsina.

GA TAMBAYOYINA BIYUZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ina da tambayoyi guda biyu da nake so ku yi }o}ariko samo mini amsoshinsu:

1. Shin wai me ya sa shahararren mawa}in nan Yakubu Muhammadba ya fitowa a fim yadda za a san shi a fosta? Mu dai mun san shi}warai ta hanyar da ya shahara, amma a rubuce kawai muka san shiba a fosta ko a hoto ba. Don Allah ku daure ku buga mana hotonsa acikin mujallarku domin mu san shi sosai.

2. Shin menene cikakken sunan jarumar nan wacce ta fito a matarAlasan Kwalle a cikin Izaya, kuma jarumar fim ]in Laila. Kuma a inatake a cikin Kano?

Ina so Yakubu da ita wannan jaruma su daure su aiko mani dahotunansu.

Daga }arshe ina mai matu}ar yaba wa Ibrahim Sheme bisa irin}o}arinsa, da kuma }warewa da ya yi kan aikinsa. Allah Ya taimaka,amin.

Aliyu Sani Sheme (Gambo),c/o Abubakar Sani, First Bank of Nig. Plc., No. 29, Cresent

Road, S/Gari, Zariya, Jihar Kaduna.

Malam Ali, ka duba cikakkiyar hirarmu da Yakubu a Fim ta Agusta2001, don ka ga dalilinsa na }in bayyAna fuskarsa a finafinai. Nabiyu, sunaN jarumar Izaya da Laila, Aina�u Ade, kuma a Sabon Titia Kano take aiki.

SHIN HAJJO TA YI AURE?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so ku mi}a mani gaisuwata ga Hauwa Ali Dodo da Abida dakuma mama Hajara Usman, saboda ina sha�awar kallon fim ]insu.Shin a kan rikicin Wasila da Lere, sun shirya ko ba su shirya ba?Wai da gaske ne Hajara Usman ta yi aure?Dada, Jummai Abdullahi Ribah,Danko Wasagu, Jihar Kebbi.

Hajjo ba ta yi auren da muka ba da labarin za ta yi ba. Su kumaWasila da Lere, idan sun koma zumuncinsu na da, za ku ji.

WAI ’YAN WASA SUN YI HATSARI?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku sanar da ni gaskiya a kan cewa wai �yan wasa sun samuha]ari a hanyar Kaduna.Na biyu, shin da gaske ne Ibro zai fito takarar gwamna? A }arshe

ina mi}a gaisuwata ga jarumar shirn Tallafi da kuma �yan wasa baki]aya. Kuma Allah Ya taimaki ma�aikatan mujallar Fim.

Nafisa Husaini MRD,Danko, Wasagu, Jihar Kebbi.

Ba gaskiya ba ne cewa �yan wasa sun yi ha]ari; in da haka ta faru(Allah ya kiyaye!), da kun ji a wannan mujallar. Shi kuma Ibro, yata~a cewa zai yi takarar gwamna, amma bai sake bin maganar ba.

ABIDA, KI ‘CE WANI ABU’ MANA!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA gaisuwa ga ma�aikatan mujallar Fim tare da yaba maku a kannamijin }o}arin da kuke yi wajen isar da sa}on sada zumunci

tsakanin mu makaranta mujallar da kuma �yan fim. Ina so mujallarkuta isar mani da sa}ona ga jarumata, wacce na fi son gani a cikinfinafinan Hausa, Abida Mohammed. Na ga cewa shahararrun �yanwasa mata suna komawa furodusoshi, amma ita har yanzu ban ji ta yimotsi ba. A nan ina nufin Abida ya kamata ki ce wani abu saboda kinuna mana fahimtarki da kuma basirar da Allah Ya ba ki. Ina fatan zaki yi }o}ari ki }ago wani labari mai da]i, sannan kuma ki juya ki yifito da shi a fim. Daga }arshe ina gaisuwa ga Sani Musa Danja,Sulaiman Gambo, Musa Abdu, Abida Mohammed, Aina�u Ade(Laila), Hauwa Ali Dodo, Maryam [anfulani, Hadiza Kabara, AlhajiGarba [angida, Ibrahim Sheme, da [anjuma Katsina.

Hamisu Ali Dan Kaura,U/Kaura, Ama Layin, Malam Salihu Near Amadu Sarkin

Fulani House, Katsina.

ASHAFA, HALIMA DA GALIN MONEYZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA man abin da yake ci min tuwo a }warya shi ne rashin sanincikakken tarihin Yakubu Muhammad, na da]e ina takaicin abin.

Kawai cikin sau}i sai ga shi kun sanar da ni a Fim ta 20. Kai, dukinda ka ajiye ma�aikatan mujallar Fim sun wuce nan. Fata dai AllahYa }ara muku dubun haza}a da fasaha, amin. Don ko a yanzu na barkaranta mujallar fa na wuce wawa a kallon finafinan Hausa, don Fimta zama da ni wayayye.

Ina son ku ba ni tarihin marubucinku Ashafa Murnai Barkiya. Nabiyu kuma wacce Halima Adamu Yahaya ce a cikin marubutanku?Kuma meye matsayin wakiltarku da Galin Money yake yi? Ya kamatamu rin}a ganin rahotanninsa.

Muhammed Abdullahi,Dawakin Gombe, Kusa Da ‘Borehole’, Babbar Kasuwa,

P.O. Box 411, Tel-072-221138, Gombe.

Ba kai ka]ai ba ne ka ta~a rubuto wasi}ar neman tarihin Ashafa.Wani daga Jihar Borno har tababa yake yi ko Ashafa Bahaushe ne �don shi bai ta~a jin Bahaushe mai suna Ashafa ko Murnai ba. Ga dai]an ta}aitaccen tarihinsa nan ya bayar:

�An haife ni a ranar 15 ga Mayu, 1966 a garin Barkiya da ke cikin{aramar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina. Na yi karatun firamare a�Kufan-Agga Primary School� (1973-79). Daga nan sai na zarce�Government College,� Katsina (1979-84). Lokacin da na gama bansami damar wucewa gaba ba. Sai na tafi Kano na fara koyon kasuwancihar tsawon shekara ]aya.

�A shekarar 1985 na je �Katsina Polytechnic� na yi kwas ]in sharefagen difiloma. Ban zarce difiloma ba sai na sake dawowa Kano na cigaba da kasuwanci har tsawon shekaru biyu. Sai dai kuma a 1987 na]an sami tangar]ar kasuwa. Ganin haka sai na koma tallar jarida(vendor). Gaskiya tun daga nan na fara sha�awar aikin jarida kumana }uduri aniyar zama ]anta. Sai na bar tallar jarida na koma �College

10

Page 12: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

of Advance Studies� (CAS), Zariya, a 1988-1990. Daga nan kumasai na zarce kai tsaye Jami�ar Bayero da ke Kano inda na karanciaikin jarida (Mass Communication). Na gama a shekarar 1994/95.

�Ni dai Bahaushe ne. Sunan Ashafa ya samo asali ne daga kalmarasshifa�a wadda take nufin waraka ko ceto. Sai aka ra]a min sunaMuhammadu Asshifa. Bambancin karin Larabci da Hausa ne ya saake kira na Ashafa, kuma shi ya bi ni har yanzu. Murnai kuwa la}abine da Hauswawa kan sanya wa ]an da aka haifa bayan mahaifiyarsata da]e Allah bai ba ta haihuwa ba, ko kuma wanda aka haifa bayanan haifi mata da yawa kafin a haife shi. Na yi aiki a kafanin jaridunShield Weekly da Garkuwar Arewa da ke Kano tsakanin watan Agusta1999 zuwa Janairu na 2001. Ina da mata ]aya tal da na aura ranar 5ga Fabrairu, 1999. Yanzu ni ne editan mujallar Bidiyo.

�Ashafa.�To, muna fatan ka gamsu. Halima da kake tambaya, Halima Adamu

Yahaya ce da ka sani, wato �yar wasan nan wadda ko a cikin fitowarwannan watan akwai hirarta. Abin da yawanci ba a sani ba shi neAllah ya yi mata baiwar iya rubutu da Hausa mai ma�ana, shi ya samuka ]auke ta tana yi mana rubutu, koda yake yanzu yawancinrubutunta (wanda sharhi takan yi kan finafinai) ya koma cikin mujallarnan mai suna Bidiyo.

Shi kuma Galin Money, a da mun ]auke shi ya wakilce mu aZariya. Amma da aka yi watanni bai aiko da ko �A� ba, sai muka ciresunansa daga cikin mujallar.

WASILA DA BALARABA SAI MANYAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA matu}ar }aunar wannan mujalla mai farin jini, saboda tana bamu haske. Allah Ya ja zamaninta, amin. Ina so in yi amfani da

wannan damar domin yin tsokaci a kan furodusoshi da daraktoci.Da farko don Allah game da Wasila da Balaraba, a san irin matsayin

da za a ri}a sa su a fim. A daina ha]a su da samari; gaskiya zai fidacewa a ha]a su da irin su Shehu Hassan, Ibrahim Mandawari koTahir Fagge, saboda girmansu bai dace da su Ali Nuhu ko Ahmed S.Nuhu ba. Ina fatan za a gyara. Kuma don Allah Wasila ta daina taunacingam a fim.

Sai kuma maganar sa Turanci a fim. Ai wannan ya zama ingausa,kuma bai dace ba. Kuma yawan kwaikwayon Indiya bai dace ba.Kamar fim ]in {udiri da Kada Mage, duk finafinan Indiya akakwaikwayo.

Daga }arshe ina mi}a gaisuwata ta musamman ga jarumi AlhassanKwalle, Ibrahim Maishinku, Sani Musa (Danja), sai Aina�u Ade.

Hajiya Binta Muhammad (Mai Kifi),No. 40, Liberia Street, Malali G.R.A, Kaduna.

HADIZA IYAN-TAMA ZAN AURAZUWA GA MUJALLAR FIM,

IN Allah Ya yarda idan na gama makaranta, Allah Ya azurta ni, saina auri Hadiza Iyan-Tama.Ina so a gaisar min da shugaban furodusoshi na Arewa, surukina,

Alh. Hamisu Lami]o Iyan-Tama. Kuma in Allah Ya yarda nan gabasai na dawo Kano saboda Hadiza.

Aminu M. Sada,Govt. College, P.M.B. 6004, Funtuwa, kuma No. 31,Maska Road, Funtua, Jihar Katsina.

TAYA FATI DA JAMILA MURNAZUWA GA MUJALLAR FIM,

ALLAH Ya }ara maku basira, da fasaha bisa wannan gagarumaraniya da wayar da kai da kuma sada �yan wasa da masu kallon

fim da kuke yi. Bayan haka na karanta labarin auren Fati Abubakar da�yar�uwarta Jamila Mohammed Sabo. Ina fatan Allah Ya ba su zamanlafiya tare da mazajensu! Kuma Allah Ya ba su zuriya tagari, amin!Kuma ina kira ga sauran �yan wasa mata da su sani cewa, �ana bikinduniya ake na }iyama.�

Bayan haka na yi jinjina ga Hassan Salisu Narayi da wannan

babbar gudummawa ta shi wajen wa}e mana mujallar Fim da ya yi.Sannan ina mai taya shi godiya da kyautar da Fim ta yi masa.aga}arshe sai gaisuwa ga dukkan masu karanta mujallar Fim mai farinjinin gaske.

Gambo Adamu,Community Higher Islamic College, Damaturu, P.M.B.

1106, Damaturu, Jihar Yobe.

WASILA, DA INA DA HALI...!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so a mi}a gaisuwata ga jaruma Wasila Isma�ila, saboda ina}aunarta. Da ina da hali sai na aure ta. Allah Ya raba ta da ma}iyanta

a ko�ina suke!Bayan haka ina so ma�aikatan mujalar Fim su san cewa ina ]aya

daga cikin masu yawan karanta mujallarsu kuma ina jin da]intasosai. Ina fatan Allah Ya ]aukaka su fiye da haka, amin.

Alhaji Sule Ba Yawa,I.B.B, Modern Market, Kano Line, No. 2, Off AF. Bank,

Kano.

HIRA DA ASID, KUN KYAUTA MANAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA ji da]i da kuka yi hira da taurarona, kuma ]an wasan da kowake so, wato Aminu Shehu Ilu Dambazau (Asid). Yabon gwani

ya zama dole, domin duk wanda yake kallon finafinansa, to dole yajinjina masa.

A }arshe ina mi}a gaisuwata ga Ibrahim Maishinku da Ali Nuhu.Auwal K. Yahaya,Stirling Civil Engineering, P.O. Box 393, KM 6, Mando

Road, Kaduna.

MUJALLAR FIM SHA-YABOZUWA GA MUJALLAR FIM,

IDAN muka yi la�akari da irin gagarumar gudummawar da mujallarFim take bayarwar a duniyar finafinan Hausa, za mu iya cewa ita

ce fatilar duk wani ]an wasa har ma da masu shirya fim. Dalilin da yasa na ce haka kuwa shi ne, mujallar tana haskaka �yan wasa a idonjama�a da kuma wayar da kai game da wannan sana�a tasu. Don hakaya cancanci su yaba mata. A kullum mujallar Fim cikin yabo take,idan muka yi la�akari da irin yawan wasi}un da jama�a suke aikamata a kan namijin }o}arin da suke don wayar wa jama�a kai a kanfinafinanmu na Hausa da kuma ha~aka al�adarmu da yarenmu.

Bayan haka mujallar tana kore mana jita-jitar mutane game da �yanfim, kuma ta wayar mana da kai game da abubuwan da suke faruwaa duniyar finafinai. Shi ya sa Fim ta doke duk wata mujallar Hausa aArewacin }asar nan, musamman mai bayar da labarin finafinan Hausa.Ina son in yi amfani da wannan dama in yi kira ga ma�aikatanmujallar da su }ara }o}ari wurin inganta mujallar ba tare da nuna sonkai ba a tsakanin �yan wasa.

A }arshe zan yaba wa mawallafin mujallar Fim, Malam IbrahimSheme. Sannan ina gaida ma�aikatan mujallar. Allah Ya taimake kuYa kuma kare ku daga sharrin masu sharri.

Mahmud Ibnu Abubakar (M.T.A.M.),No. K Y 12, Bima/Zango Road, T/Wada, Kaduna.

ALI NUHU SARKI, HINDATU GIMBIYAZUWA GA MUJALLAR FIM,

KU ba ni fili a cikin wannan mujallar domin in isar da sa}ongaisuwata ga shahararren ]an wasan kwaikwayo, Ali Nuhu,

sarkin sarakuna, son kowa }in wanda ya rasa, da kuma gimbiyar-gimbiyoyi, Hindatu Bashir, �kin fi sauran mata aji�. Allah Ya }aramaku }arfin gwiwa.

Daga }arshe ina ro}on mujallar Fim da su taimaka su ba ni cikakken

Wasi}u

11

Page 13: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

adireshin wa]annan taurarin, ko kuma lambar wayar da za a iyatuntu~arsu.

Zainab Ahmed,No. 17 Kaura Crescent, Kagoro by Express Road, T/

Wada, Kaduna.

ABIDA, KINA BURGE NIZUWA GA ABIDA MOHAMMED,

DALILIN da ya sa na rubuto maki wannan wasi}a tawa shi ne,domin in gabatar maki da kaina da kuma yadda kike a zuciyata.

A gaskiya Abida kin kasance mai burge ni. Kuma ina mai matu}arsha�awarki da irin wasanki. A gaskiya ban ta~a ganin fim ]in da kikafito bai yi kyau ba.

Allah Ya }ara ]aukaka ki Ya kuma ba ki miji nagari ki yi aure,amin.

Hadiza Yusuf,No. 20, Bakori Quarters, Tel: 064 443089, Bakori, Jihar

Katsina .

ALI, A RIKA ZUWA GANIN GIDAZUWA GA MUJALLAR FIM,

KU gaya wa Ali Nuhu ya ba mu kunya, domin kuwa muna jin shiBama ne asalinsa. A nan aka haife shi. Amma kuma ko ziyara ba

ya kawo mana. Ku tambaye shi mei ya sa duk garin Bama muna farinciki da yaron ya yi nasara, amma kuma ya bar mu da musunce-musunce. Ya kamata ya zo mu gan shi ido da ido a garin Bama.

Alaye Mallam Aji,Bukar Tela Ward, Bama, Jihar Borno.

SANI DANJA KA BURGE NIZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN wannan wasi}a shi ne don na mi}a gaisuwata ga SaniDanja kan yadda yake taka rawarsa a fim, kamar a Maciya,

Madubi, Tangaran, Nagari da dai sauransu. Sa}on gaisuwa gamasoyiyarka wato Asiya Sani Danja.

Fadimatu Sani, Ibrahim

Gombe.

A BA LERE LAMBAR YABO A BANAZUWA GA MUJALLAR FIM,

A GASKIYA Yakubu Lere ya cancanci a yaba masa, saboda ba asamu wani furodusa da ya shirya fim da ya burge, kuma ya dace

da wannan zamanin, kamarsa ba. Idan aka duba, za a ga cewar fim]insa na Wasila da kuma Adali, finafinai ne da suka nuna mana yaddaake zaman soyayya tsakanin ma�aurata da kuma yadda wasu sukesanya cin amana a cikin zamansu da iyalinsu. Saboda haka Lere yakamata a ba shi lambar yabo ta wannan shekara.

Ibrahim (Naniya),Majidadin Galadiman Malali, Kaduna.

WURIN GYARA A FURUCIZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku ba ni ]an fili don in yi tsokaci a kan fim ]in Furuci. SuAli Nuhu suka dawo daga Saudiya da suka je wurin haihuwa.

Daga nan ne fa labarin ya samu tangar]a wacce har ma ]an shekara11 ya lura da ita bayan mun }are kallon. Ya ce, �Baba me ya sa ba ayi bikin haihuwar da Alhaji ya samu ba?� (Yana nufin KabiruMaikaba).

Ba amsar da zan ba shi. Na ga lallai ya dace a ce wanda ya rarrabaku]i don jin labarin ya samu abin da yake ta bi]a, matarsa ta samu

ciki, ya yi abin da ya fi wannan idan ya samu! Ina cikin wannantunanin ne na ji muryar Abdurrahaman ta ce, �Baba, me iyayen AliNuhu suka ce game da tafiya da ciki da dawowa ba shi, ko an mantada su ne?� Wohoho, yaran zamani! A nan na }ara shiga zurfin kogintunani. Ku ji fa! Yaro ]an shekara 11 da wannan tunani. To ni ma daisai in mi}a tambayar gun furodusa da daraktan fim ]in. Na tabbatarda samun ciki da rasa shi abin yin murna ne da jin ciwo saboda hakakamata ya yi a nuna ~acin ran iyayen Ali Nuhu game da abin da ya far.Ko ana nufin cewa an ~oye wa iyaye cikin ne? To, in har an ~oye waiyaye, shi aboki fa? Ba mu sake jin ]uriyar abokin Ali na }ut da }utba, ballantana mu ga rawar da ya taka a wajen nuna ~acin ransa gameda yadda cikin da Balaraba ta je da shi wurin haihuwa ya ~ata!

Gaskiya, koda yake duniyar fim na iya maida abin da bai yiwuwaa fili ya yiwu, kamata ya yi a lura da cewa mutane ne masu tunani dabasira za su kalli fim kafin ya gutsire shi wai wata}ila idan watawa}a ta samu shiga, koda yake ba zan ga laifin darakta da furodusaba sosai saboda na lura yanzun wa}a ce ke tafiyar da fim ]in Hausaba labari ba. Idan wa}a ta yi da]i, labari ba sai ya zo da tsari ba.

Don Allah ku taya ni warware ru]un da ya kama ni. Yanzu hakaduk fim ]in da na duba na Hausa sai na ga wasu manyan gi~una daya kamata a cike don labarin ya yi tasiri da tsari. Na ]auki Furuci nedon da shi da ma ya farkar da ni daga dogon barci na kallonfinafinanmu ba tare da yin nazarinsu ba.

Zan dakata nan, sai mun sake duba wani fim tare da Abdurrahamwata }ila ya }ara sosa mani }wa}walwata ta hanyar tambayoyi.

Masta Alko,Sokoto.

A ri}a sa cikakken adireshi a kowace wasi}a don Allah.

ALLAH JIKAN AMINU DA MAIJIDDAZUWA GA MUJALLAR FIM,

ZAN yi amfani da wannan dama in mi}a sa}on ta�aziya ga iyalanAminu Hassan Yakasai da mahaifiyar Maijidda Mustapha. Allah

Ya yi wa wa]annan mamata rahama, Ya ji }ansu, ku kuma Allah Yaba ku ikon juriya da wannan babban rashi da kuka yi. Mu kuma intamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani, amin.

Sannan kuma ina kira ga �yan wasa mata don Allah ku ri}a yinaure kamar yadda na ga sauran sun yi domin su yawaita haihuwa,domin Annabi Muhammadu (SAW) yana cewa, �Ku ri}a yawaita amarmari domin samun zuriya domin in yi bugun gaba da ku a ranarAl}iyama. �Don kun ji na ambaci mata kada ku zaci da su nake, toa�a, har da mu maza nake; kuma wannan ba ga �yan wasa kawai tatsaya ba, duk ilahirin jama�ar Musulmi take.

Don Allah kuna samun wasi}una kuwa? Don gaskiya ina lissafawannan ita ce ta uku wacce na aiko maku, amma ba ku buga ba, donhaka na ga ya dace in yi wannan tambayar. Daga }arshe ina mi}agasuwata ta musamman ga Ibrahim Sheme da sauran ma�aikatanmujallar Fim. Allah Ya taimake mu baki ]aya, amin.

Nasiru B.A. Hassan,Nufawa Sokoto North, Office Adiris Sokoto, Central

Market Shop, No: T.S. 15.170, P.O. Box 2115, Tel: 060 –232839, Jihar Sokoto.

ALLAH YA KARE BALARABAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NI dai babu abin da za mu ce maku marubuta wannan mujalla maifarin jini a wurin jama�a sai Allah Ya ja zamaninku baki ]aya,

amin, summa amin.Ina ba Balaraba shawara ta kama kanta kamar yadda ta fa]a a cikin

mujallar Fim ta baya. To don Allah ki yi amfani da duk abin da kikafa]a, kuma Allah Ya kare ki daga sharrin ma}iya.

A’isha Yahaya, da Umar Faruk (Milo),C.D. 30, Tamaske, No. CK 10, Zango Road, T/Wada,

Kaduna.

Wasi}u

12

Page 14: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

LERE, BARI WASU SU FADAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA sanar da ku cewa ni mai ra�ayin finafinan Hausa ne }waraida gaskes, saboda yanzu haka ban da wani kaset sai na Hausa.

Bayan haka ina sanar da ku cewa ban ma san ko akwai mujallar Fimba sam, wallahi sai da na samu Fim ]in Wasila, a ciki ne na ga tallarta.To sai na aika gida Jamhuriyar Nijar na ce a samo min mujallar. Saiaka sayo min ita, amma kuma ta watan Mayu 2001 ce . To a cikintane na samu adireshinku na Intanet, na kuma samu bayanai da dama,wa]anda na ji da]in samunsu }warai da gaske!

To yanzu ina so don Allah ku ba ni  Fili in ba da ra�ayina gameda rikicin Wasila. Maganar Yakubu Lere ya yi cewa shi ya fi }arfinmawa}i da ]an wasa, ni a ganina ya yi kuskure }warai da gaske.Saboda Lere ya san cewa ba a iya yin fim ba tare da ]an wasa bada kuma mawa}i ba, saboda finafinan kashi 70 % sai da wa}o}i.Sannan kuma ya ci mutuncin kansa da kansa saboda ai shi ma ]anwasa ne. Kuma zancen cewa shi babba ne kuma mai ku]i ne, ai bashi ya kamata ya fa]a ba, wa]anda suka san shi }warai su yakamata su fa]a!Malam Oumaten Atta,1329 A Kittatinny St Harrisburg, Pennsylvania 17104, U.S.A. Phone:(001)717-232 7318;A Jamhuriyar Nijar kuma: Malam Oumaten Atta,Tel:(00227)74.10.17.BP.10981, Niamey Rep:Du Niger.E-mail:[email protected]    

TUBARKALLA DA AIKINKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in taya dukkan ma�aikatan mujallar Fim murna a kankyakkyawan aikin da suke yi, musamman wajen kawo mana labaran

nishadi a cikin sauki. Ya yi kyau }warai, don haka tubarkalla. Ina sonin yi amfani da wannan damar in taya Fati Mohammed da Sani MaiIska murnar aurensu da yi masu fatan alheri. A }arshe ina so edita yaisar da gaisuwata ga Ali Nuhu, Ishaq Sidi Ishaq, Abida Mohammed,Saima Mohammed, Hadiza Ibrahim (takwarata), Ibrahim Madawari,Aminu Shariff (Momo) Aminu Acid, Mo]a, Ibro, Sani Danja, Tsigai,da Ahmed S. Nuhu. A gaskiya fasaharsu na burge ni.

Hadiza Ibrahim,[email protected]

Wasi}u ta hanyar �E-mail�Muna so masu aiko da wasi}a ta hanyar Intanet su ri}a sa cikakken sunansu da adireshinsu, ba adireshinsu na Intanet kurum ba. Muna

da damar mu }i buga duk wasi}ar da ba mu yarda da ita ba ko don ba ta ]auke da cikakken suna da adireshi

Adireshinmu shi ne:[email protected]

13

An fassaro wannan wasi}ar daga Turanci. Edita

’YAN FIM KU BUDE WEB PAGEZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto ne don na ba �yan fim shawara a kan ya kamata a ce}ungiyar �Arewa Filmmakers� su bu]e web page nasu (fage na

musamman a intanet) wanda za su sa dukkan wasu �yan wasa tare dabayanansu, domin hakan zai sa a rin}a saurin gane �yan wasa, yakasance duk wani bayani da mutum yake so game da wani ]an wasada ya bincika sunansa zai ga hotonsa, shekarunsa, yawan finafinansa,da sauransu. Gaisuwa da fatan alheri ga duk wanda ya karantawannan sa}o nawa.

Karibu [email protected]

NI MA GA HOTONA NANZUWA GA MUJALLAR FIM,

GAISUWA mai yawa tare fatan kuna nan lafiya kamar yaddamuke a nan lafiya, amin, da kuma yadda kuke ]awainiyar yau

da kullum. Allah ya }ara taimakawa, amin.Ni ma ga hotona nan domin sakawa a filin Abokanmu kamar

yadda kuka ce a aiko da mai kyau mara duhu. Ina kuma son a isar minda gaisuwata ga Zulkifilu Muhammad, Alhassan Kwalle, UmarYahaya (Bankaura), Hamisu Lami]o Iyan-Tama, Hindatu Bashir daJamila Haruna.

A }arshe ina fata za ku rubuto min da amsa ta hanyar e-mail don intabbatar da wasi}ata ta same ku. Ku huta lafiya.

Aliyu Ibrahim Madaki,Government Health Office, Zaria, Jihar Kaduna.

[email protected]

KU BUNKASA ADDINI DA AL’ADUZUWA GA MUJALLAR FIM,

BAYAN na fito a Filin Abokanmu a wannan mujallar maimuhimmanci ta Agusta 2001, akwai wasu mutane daga cikin

masoyana da suka same ni gida da ofis suna sukar fitowata }uru-

HASSADA BA ZA TA KASHE ‘FIM’ BAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA sanar da ku cewa kushe da hassada, munafunci da tsurku dagulma da tsegumi da kuma kutungwila da jaf�i duk ba za su hana

mai rabo ya kai ga rabonsa ba. Gaba dai gaba dai mujallar Fim! Donkuwa babu dawowa da baya da yardar Ubangiji. Daga }arshe sa}ongaisuwata ga dukkan ma�aikatan Fim, kamar su Rabilu Musa (Ibro)da Tahir M. Fagge da Sani Musa (Danja).

Ibrahim Adamu (Ciba Boy),Usman Garba (Kawu Mai Tebur), Sabon Gari, Gashua,

Dist. Head Office, P.O. Box 16, Gashua, Jihar Yobe.

SAIMI, FARIN JINI YA JAWO MAKIZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA jajanta wa shahararriya kuma }wararriyar tauraruwa, SaimaMohammed, a kan abin da ya same ta a Gala ta Kaduna, kamar

yadda na karanta a wata fitowa ta wannan mujallar, cewa ta ha]u dafushin wasu fitsararrun �yan kallo. Da fatan ba za ta damu ba. Farinjininta ne ya ja mata.

Daga }arshe kamar yadda na karanta a wata fitowa kuma filinMalam Zur}e, an ce Saima �yar asalin }asar Nija ce, to idan haka neina so ku ]an ba ni ta}aitaccen tarihinta, ko kuma ku zanta da ita idanda hali.

Sada Suleiman,Ibrahim Metal Contruction, near Union Bank, Jibia

Kauran-Namoda Road, Jibia, Jihar Katsina.

Ba kasafai muke maimaita tarihin ]an fim ba bayan mun ba da shia baya. Don samun tarihin Saima, ka duba Fim ta 2.

KUNA MATUKAR KOKARIZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son bayyana maku irin }auna da ra�ayin da nake yi wa abin dada kuke gabatarwa. A gaskiya kuna }o}ari fiye da yadda ake zato.Suleiman Ja’afar,Ja’afar Muhammad Suleiman, Hausa Department,

Sokoto State Polytechnic, P.M.B 2356, Sokoto.

Wasi}u

Page 15: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

}uru sanye da sunana da adireshina a wannan mujallar. Hujjarsu itace ina mai goyan bayan Shari�ar Musulunci kuma ga shi sun san nida girman sarauta da aka gada tun lokacin jihadin Shehu Usmanu,amma ina goyan bayan fim da ake yi, saboda haka a ganinsu ban yidaidai ba.

Duk wanda ya san abin da yake yi idan yanayin wani abu dajama�a suke ganin ba daidai ba ne, ba zai yi hushi ba ne kawai Jama�aba su yi na�am da wannan abin ba. Sai ya yi anfani da wannan damarwajen fahimtar da su da wannan abin don su fahimta. Saboda haka nena yi amfani da wannan damar domin in ba da hujjata cewa wasankwaikwayo na da rawar da zai taka wajen ya]a addinin Musuluncitare da bun}asa kyawawan al�adunmu na Hausa. Zan ba da hujjata akissance, kamar yadda na ji daga bakin wani mai wa�azi ranar Juma�ayana cewa:

�Akwai wasu mata su biyu Turawa da suka haihu lokaci guda aasibiti guda, ]aya ta haifi ]a namiji, ]ayar ta haifi ]iya mace. Saidukkansu mata biyun nan kowacce ta ce ita ce ta haifi ]a namiji. Sairigima ta kaure har babban likitan asibitin ya kasa raba gardamar. Saiya ce, �Akwai wani Musulmi da ya dame mu da wa�azi yana cewawai komai za a same shi a cikin {ur�ani.� Saboda haka idan abinnashi gaskiya ne, bari ya je ya same shi domin {ur�ani ya bayyanamashi wadda ke da ]iya mace.

�A lokacin da likitan nan Bature kuma ba Musulmi ba ya je yasamu bawan Allah Musulmi ya ce masa ga matsala, sai ya bayyanamasa cikin {ur�ani wacece ta haifi ]a namiji, wacece ta haifi mace?Malamin nan da ya ji bayanin likita sai ya ce masa }warai da gaskeakwai hukunci a cikin Al}ur�ani! Sai ya samo mo]a (kofi) biyu yasanya alamu a kowane kofi ya umurci likita da ya tatso nonon kowace]aya daga cikin mata biyu a kofi daban-daban. Bature da ya samiganin matan nan ba ko jariran da suka haifa ba. Sai likita ya je ya aikawato ya zo da nono kofi biyu. A lokacin da bawan Allah ya ga ]ayanonon ya fi ]ayan kauri, sai ya shaida ma likitan cewa matar da ke danono mai kauri ita ce ke da ]a namiji kuma ]ayar ita ce ta haifi mace.Domin {ur�ani ya ce: �Arrijalu }awwamuna alal nisa�i bi mafaddallallahulah.� Ma�ana, namiji na da rabon mata biyu na daga abinda Allah Ya falala (daga arziki). Saboda haka likitan jin haka sai yagaskata, ya yi imani, kuma matan biyu masu rigima su ma suka ba dagaskiya. Allahu Akbar!

To a nan fim yana da tasiri domin sanya irin wannan }issa a cikinfim zai fahimtar da wa]anda ba su fahimci addini ba, zai sa wasujama�a masu yawa su amsa kiran Allah. Domin fa]in Manzo (S.A.W):�Ka isar da sa}ona ko da aya ce.�

Na biyu, fim na da tasiri wajen fa]akar da �yan�uwa domin saninmuhimmancin ilimantar da �ya�yanmu da matanmu, musamman yanzuda muke da rauni wajen mata Musulmi masu ilimin kimiyya kamarsu aikin asibiti. Da wannan fim zai nuna mana fa�idar barin matarmutum ta yi karatu kan fannonin da suka shafi kiwon lafiya ko aikinasibiti.

Bayan haka kuma akwai al�ada ta Hausa wadda Musulunci baisoki irin wa]annan al�adun ba kar masu su hawa doki ko hawanungunci ko kiran walima ko aikin gaiya da kuma sana�o�i irin namu.Idan ana amfani da wa]annan abubuwan a fim to zai taimaka wajentsara mutuncinmu da addininmu. Ba wai a sanya ku]i a gaba ba amance da addini, balle al�ada.

Da wannan jawabi nawa zan dakata domin komai mutum zai yi toya tabbatar yana da hujja ta gaskiya. Wassalam.

Kabir M.Lemu,Kaduna North Local Govt., P.M.B. 2019, Kaduna.

NA GOYI BAYAN MUSA B. GARKIZUWA GA MUJALLAR FIM,

A HA{I{ANIN gaskiya, na goyi bayan Musa Bello Garki a kanbu}atar }ir}iro da wata mujalla ta Hausa kamar Tell domin

labaru na gida da na waje. Ina da bu}atar in har za a yi mujallar, a safilin wayar da jama�a a kan komfuta domin a gaskiya an bar mu abaya a wannan fanni. Kai in har za yi a shirye nake domin na amsatambayoyi a kan wa]ansu darussa kan komfuta daidai gwargwadon

sanina.Gaisuwa ga Ali Nuhu, Ibrahim Mandawari da Hamisu Iyan-Tama.Dayyabu [email protected]

INA SON ‘FIM’ TA SHEKARAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto ne domin in tambaye ku hanyar da zan bi domin in rikasamun mujallar Fim a kowane wata. Ina son kowane wata in

samu a aiko mini ta adireshina na P.O. Box 63, Wukari, Taraba State,nawa zan biya a shekara, da kuma rabinta?

Bayan haka idan akwai wata jarida ko mujalla da kuke bugawadon Allah ku turo mini da farashinta na shekara da kuma adireshin dazan biya ku.

A }arshe nawa kuke tallace-tallace a wannan mu jalla mai farinjinni domin ina son in tallata hajjata a mujallar Fim. Ina fata za ku bani bayani.

Usman Abdullahi Magungu,[email protected]

Malam Usman, mun aiko maka da amsa ta adireshinka na �e-mail.�

A DAINA MAIMAITA BASIRAR WANIZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan kuna lafiya, Allah ya ja zamanin Ku. Don Allah in sonku ba ni fili domin in bayyana kuskuren da furodusoshi suke yi.

Rigar �Yanci da ake kurantawa, basirar Dare [aya suka yi amfani dashi, Haka kuma Sar}a}iya Nigerian film ne, Authority, da Tsumagiya,da dai sauransu. Me ya sa furodusoshi ba za su yi amfani da tasubasirar ba? Ina fatan za su daina yin wannan kuskuren. Na gode.

Ina son a mi}a gaisuwata zuwa ga Ishaq Sidi Ishaq, Tukur S.Tukur, Ibro, Bashir Bala (Chiroki) Ibrahim Mandawari, Tahir Fagge,Jamila Haruna, Amina Garba, Kabiru Maikaba, da Hindatu Bashir.

Amina Ibrahim (Ozoza)P.O. Box 697, [email protected]

KIRA GA ’YAN WASA MATAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan takarda domin in tunatar da �yan wasa mata,musammam wa]anda suke Musulmai, cewa ku sani fa duk

wani ~angare da kuka ]auka a kowane wasa, zai iya shafar yanayinrayuwarku a gobe, in har ba a yau ba. Ku bar daka ta �yan wasa mazawa]anda komai munin ~angare da suka ]auka bai cika bin su natsawon lokaci ba kamar yadda yakan iya bin �ya mace wadda ta ]aukiirin wannan fannin.

Ya kamata ku yi bincike ku ga cewa a cikin �yan wasa maza dakuke wasa tare da su, nawa ne ke da aure kuma matansu suna wannanwasa, kuma nawa ne ke da �ya�ya mata wa]anda suke yin wannanwasa? Abin da bincikenku ya nuna maku ya isa ishara a gare ku.

Allah ya yi mana jagora.Abubakar Muhammad Kanti,P. O. Box 2891, Abha, Saudi Arabia.sanibu keti <[email protected]

SAKO DAGA JAMHURIYAR NIJARZUWA GA MUJALLAR FIM,

NI �yar makaranta ce a �Collège MARIAMA� (wato KwalejinMaryama), a Yamai, Jamhuriyar Nijar. Wannan shi ne karo na

farko da na sami damar karanta wannan mujalla taku wadda ba taya]u ba a }asarmu Nijar. Kuma abubuwan da ta }umsa sun }ayatarda ni matu}a. Saboda haka ne na yanke shawarar rubuta maku wannanwasi}a.

A gaskiya, ina daga cikin warina �ya�yan Nijar �yan 14 masusha�awar kallon finafinai da wasannin kwaikwayo na Hausa, domin

14

Page 16: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

suna taimaka muna }warai da gaske wajen na}altar wannan harshenamu na gida, da kuma sanin tarbiyya da al�adu da ]abi�un Hausawana ainahi da kuma wa]anda zamani ya kawo.

Wata}ila za ku yi mamakin ganin ina amfani da datattun kalmominHausa. To lalle, ba abin mamaki ba ne, domin kuwa mahaifina, maiaiki a Majalisar Dokokin }asarmu, babban masanin harsunan gidane. Yanzu haka, a gidanmu, muna ajiye da litattafan Hausa fiye da]ari.

Bayan wannan bayani , ina so in mi}a sa}on taya murna zuwa gaFati Mohammed da Sani Musa (Mai Iska) da Tahir MuhammedFagge, da kuma Maijidda Abdul}adir, saboda auren da Allah yaazurta su da shi. Bayan haka, ina mi}a sa}on gaisuwata na musammanzuwa ga dukkan masu taimakawa a wallafa wannan mujalla ta Fim.Ina kuma mi}a wannan gaisuwa zuwa ga dukkan �yan wasankwaikwayo na Hausa, maza da mata. Kuma ina bu}ata, idan da hali,

Six20advert

IN K

AN

O: C

age 2/3 Near H

angout, Zoo R

oad; Cage 2, opp. M

ini Stadium

, Kw

anar T/W

ada;&

in GU

ME

L: Cage 5, opp. E

mir Junction, M

aigatari Road, G

umel, Jigaw

a State

KU HADA NI DA HINDATU DA ALIZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA ro}onku da ku ha]a ni da Hindatu Bashir da Ali Nuhu dakuma fatan za ku yi mani amsa ta adireshina na �e-mail�. Na gode.Fatima Muhammad Inuwa,Nassarawa/Jahun, [email protected]

Malama Fatima, mun tabbatar Hindatu da Ali za su ga wannansa}on naki. Muna fatan za su tuntu~e ki ta hanyar adireshinki na�e-mail� . Mun gode.

su aiko mani da hotunansu. Idan kuma Allah ya kawo wasu daga cikinsu ziyaraa Jamhuriyar Nijar wata rana, ina fatan su tuntu~e ni a unguwar � NouveauMarché� (nuvo marshe) inda }ofar gidanmu take kallon kamfanin inshora na�UGAN�, ko kuma su bugo tarho mai lamba: 74 36 42.

Ga hotona nan inda ake yi mani kitso, }anwata Rayyanatou na kusa da ni. Idanya kasance wata matsala ta faru, ba ku sami bu]a wannan hoto ba daga �e-mail�,ku yi }o}ari ku sanar da ni, sai in aika maku shi a ambulam ta hanyar gidan waya.

Daga nan zan yi sallama da ku, da fatan zan sami amsa da gaugawa, ta �e-mail�ko ta wasi}a, ko kuma ta tarho.

Madaniya Abdouraouifou Sidi,s/c de Monsieur Abdouraoufou SIDI, Assemblée Nationale, B.P.

12234, Niamey-Niger; Téléphone: 00 (227) 74 36 42. E-mail:[email protected]

KIRA GA HINDATU BASHIRZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ku ba ni fili a cikin wannan mujalla da ke kan gabadomin in isar da sa}o ga Hindatu Bashir.

Hindatu, ke }wararriyar �yar wasa ce; ba wanda zai ce ba haka ba ne. To ammamatsalar ita ce kina yin amfani da Turanci a inda ya dace da inda bai dace ba.Wannan ba zai yi wa harkar fim kyauta ba. Ai ko a finafinanmu na Turanci(Nigerian films) idan ta kama wani ya yi magana da wani yare, in dai ba Turanciba ne, sukan yi }o}arin fassara shi da Turanci don mutane irinmu. To, ke sai kiri}a yin Turanci a fim ]in Hausa, to yaya kike tsammanin kakata tsohuwa tafahimce ki? Mu, dukkanmu muna fahimtarki in kin yi Turancin, domin na gan kia wasu finafinan Turanci. Duk da yake matsayin da suke ba ki ba muhimmai bane kuma ba ki samun damar ki yi magana sosai a fim ]in, a}alla mun san kin iyaharshen, kuma mun san kusan kowa da ke fim ]in Hausa ma ya iya.

Don haka zan ji da]i idan za ki ri}a yin magana da Hausa a fim ]in Hausa, kiyi Turanci a inda ya dace kurum.

Don Allah kada ki ji haushi da abin da na ce domin ni �yar kallo ce kawai.Kawai ki ci gaba da }o}arin da kike yi. Ke tauraruwar gaske ce. Sannan ku madaraktoci don Allah ku kula. Na gode.

Hadiza Ibrahim Ozoza,No. 1 Bechar Street, Wuse Zone 2, [email protected]

Mun fassaro wannan wasi}ar daga Turanci. Malama Hadiza, mun ba Hindatukwafen wannan wasi}ar da kika rubuto da Turanci ta �e-mail.� Muna fatan tatuntu~e ki.

WASAN KANAWA: LAIFIN ISHAQ NEZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so ku sanar da jamaa cewa Yakubu Lere da Ali Nuhu ba su dalaifi (kan wasan Kanawa da Zazzagawa) a cikin fim ]in Wasila. Babban mai

laifi shi ne darakta Ishaq Sidi Ishaq, kasancewarsa mutumin Kano, koda yake daiwasa ake yi. Gaba dai gaba dai mujallar Fim!

Jamilu Haris,[email protected]

Malam Jamilu, a nan gaba ka sa cikakken adireshinka don Allah. Edita.

15

Page 17: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

ABOKANMU

Musa Magaji,Works Dept., Zango LocalGovt., Zango, Jihar Katsina

Sa’adatu Ibrahim,No. 24, Jajere Road,Badikko, Kaduna

Fatima Mohammed Rimi,Naval Headquarters,Lagos

Yusuf Tela Doka, MaryamaAlh. Sani, da ZinatuddiniYusuf Doka, 22, Gyadi-Gyadi, by Flyover, Kano

Amos Joshua Yakawada,P.O. Box 300, KATARDA,Funtuwa, Jihar Katsina

Wasu masu karatu suna aiko da hotuna marasa kyau: ko sun yi duhu,ko wanda ke ciki ya yi nisa. Ba za a iya amfani da irin wa]annan ba!A tabbatar hoto ya fito ra]au, kuma a sa cikakken adireshi.

Hadiza Ahmed Wafa,’Yankara, Faskari LocalGovt. Area, Jihar Katsina

Furodusoshi da darektoci da ’yan kasuwa masu dabara dahangen nesa ne suke saka tallarsu a cikin mujallar Fim

Usman Moh’d Deboa,Government House, P.M.B.0011, Gombe, Jihar Gombe

Laminou Gonda,Ibn Al-Arzy Street, Al-Hindaweyyah, Saudi Arabia,E-mail: [email protected]

16

M.D. Hassan ibn Ali Dogo (a hagu) da Yahaya Inusa GyaraSamun Sa’a, Akurba, Dogo Petroleum Nig. Ltd., PO Box20, Lafia, Jihar Nassarawa

Yahaya Ahmed Dalibi,Mashasha Photo Studio(ZACAS), P.M.B. 1107,Gusau, Jihar Zamfara

Humaira Ibrahim,No. B.24, Jajere Road,Badikko,Kaduna

Page 18: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Daga ALIYU ABDULLAHI GORA II,a Kaduna

A RANAR Asabar, 18 ga Yuli,2001 tun daga misali }arfe8:30 na safe jama�a suka yi

cincirindo a }ofar shiga filin wasa naAhmadu Bello da ke Kaduna tare dakokowar neman sayen tikitin shigakallon wasan �Gala� da aka shirya dontaya Fati Mohammed da Sani Musa(Mai Iska) murnar aurensu da aka]aura a Kano. An yi bikin a Kadunasakamakon hana yinsa da �yan Hisbasuka yi a Kano. Su dai �yan Hisba, sune }ungiyar mutanen da ke son ganinlallai an ri}a aiki da Shari�ar da aka}addamar a Kano. A Kaduna, ba a}addamar da Shari�a ba tukuna.

Duk da kasancewar yawancinmutane ba su san da bikin ba, wandaa ranar Laraba, 25 ga wata ne, akafara sanarwarsa a rediyo, jama�akimanin 5,000 sun samu halartarbikin. Yayin da fili ya cika da jama�a,kowa na jiran ganin amarya da angodon ya kashe }war}watar idonsa, sukuwa masu gabatar da shirye-shiryenbikin suna fama da abin da kegabansu. Zuwa can sai ga ma�auratansun danno; ai fa nan wuri ya yamutse,kowa yana so ya ta~a amaren.Jami�an tsaro suka hana. Da }yar daiamarya ta samu inda ta tsugunnacikin �yan kallo, shi kuwa ango yakama gabansa, sama ko }asa, ya baramarya daga ita sai }awayenta gudahu]u a zaune.

Inda aka ]an so a samu tangar]ashi ne yayin da �yan Kaduna suketa}ama da cewa �yan�uwansu abokansana�arsu ke da bikin, ya sa suka yoho~~asa don taimakawa su ga angudanar da bikin yadda ya kamata,amma sai �yan Kano suka ri}a aiwatarda komai su ka]ai ba tare da sahannun �yan Kaduna ba. Abinka da]an koyo, yamutsin jama�a ya sasuka kasa gabatar da ko da ]aya dagacikin shirye-shiryen bikin. Tilas sukaba masu wuri wurinsu, wato �yanKaduna. Nan da nan sai wuri yakimtsu, aka gabatar da manyan ba}i,

wato �yan tsirarun furodusoshin da sukasamu halartar bikin daga Kano da Kaduna.Daga Kano dai, furodusan da wakilinmuya iya shaidawa shi ne Umar Bawa Dukku,wanda shi da ma dole ya zo, tunda su nejiga-jigan da suka shirya bikin. DagaKaduna kuwa, furodusoshin da wakilinnamu zai iya shaidawa a wajen bikin basu wuce biyu ba, wato Abdullahi MaikanoUsman da Aliyu Abdullahi.

Bikin ya samu goyon bayan da yawadaga cikin �yan wasan Kano. Sai daimutane sun ji haushin rashin ganin AliNuhu, Ahmed S. Nuhu, da Abida.

Masu gabatar da shirye-shirye dai sukaci gaba da aikinsu, inda suka fara dagabatar da wani wasa na ban dariya wandaIbro, Ciroki, Katakore, [an Wanzan,Tsigai da sauransu suka yi. An ]an ]aukilokaci ana yi, sai amarya da }awayentasuka tashi zuwa wani ]aki. Wakilinmu yaruga ya bi su har cikin ]akin, amma ganawada ita ya gagara saboda yawan mutane,wanda tun sojoji suna bugun mutane harya kai ga su ma sun gaji da bugun. Bayan]an }an}anen lokaci kuma amarya ta fitota koma mazauninta.

Zaunawarta ke da wuya, aka fara gabatarda wasu daga cikin wa}o}in finafinai.Yakubu Muhammad ne ya fara bu]ewa dawa}ar fim ]in Mujadala na 2; Ali Baba yagoce da ki]a shi ko Yakubu ya goce dawa}ar, �A Yau {arshen Mujadala Ya ZoBabu Tankiya�. Bayan Yakubu kuma sai

Fati da Sani a wurin bikinsu

Sharu Sidi Sharifaiya yi wa}ar JuyinMulki, daga shikuma saiMusbahu M.Ahmad wanda yarera wa}arSangaya. Anacikin gabatar dawa]annan wa}o}ine jama�a sukafara gangarowazuwa dandamalinda mawa}an sukesuna yi masu li}i.Duk da cewa anshawarci iyayenbikin cewa kada subar mutane su fara

zuwa don yin li}i, saboda gudunyamutsewar wurin, ina, mutanenka sunaganin ku]i, ai ba ruwansu da yamutsi.Da ma mai neman kuka bare an jefe shida kashin awaki. Ai fa nan jama�a sukafara ]urarowa suna li}i. Kafin ka cekwabo wuri ya cika da mutane, aka rasayadda za a yi wurin ya kimtsu, duk dairin }o}arin da sojoji da �yan sanda keyi.

Jama�a ba su ankara ba, sai ga �yansandan dawaki guda uku sun shigo filina sukwane, suna bugun mutane ba ji bagani. Kan ka ce kwabo fili ya gyaru.Bayan mawa}an sun gama baje kolinsu,sai kuma aka ba ango da iyalinsa fili.Sani da Fati da kuma kishiyarta, watouwargida Talatu tare da �yarta Nusaiba,suka hau dandamalin suna ]aga wamasoyansu �yan kallo hannu. A kandandamalin ne Sani da Fati suka rerawa}ar bankwana, inda suna cikin yi Fatita ~arke da hawaye. Jama�a da damasun hau sun yi masu li}i da ku]i kamarruwan sama. Tun Dukku yana kallonyaransa suna tsintar ku]i, har shi ma yakasa daurewa ya du}a da kansa. Bayanango da amarya sun gama, sai sukasauko gaba ]ayansu suka nufi indamotarsu take don su shiga.

Wakilinmu ya yi }o}arin ya tattaunada Fati, amma abin ya gagara sabodayawan mutane da jami�an tsaro. Haka

�Gala� ta yi kyau agarin da ba �yan Hisba

17

RAHOTON MUSAMMAN

Bikin Fati:

Ci gaba a shafi na 18

Page 19: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Kano yake!

Wanene shi? Sai a rubuto da sauri a gaya mana.

dai suka shiga motarsusamfarin Marsandi 190 farasal, mai lamba AG Abuja 92RSH, suka tafi.

Ba da jimawa ba, sai gaangon ya sake dawowa shika]ai inda ya haudandamalin ya yi ta ~ari daku]i yana li}a wa mawa}ada �yan rawa. Tun da ya shigafilin nan bai rufe bakinsa bahar aka tashi, ba abin da yakeyi sai dariya. Daga can kuwa}ofar shiga sitadiyon ]in,masu tsaron }ofar gajiya sukayi, suka bu]e }ofar kowa yayi ta shiga kyauta maimakonbiyan N100.

Da Sani Mai Iska ya saukodaga dandamali kuwa,wakilinmu ya yi iyakar}o}arin su tattauna, ammasai angon ya nuna masa cewaba zai yi wu ba. Ya yi wawakilin namu al}awarin suha]u a wani ]aki, amma daga}arshe, sai gogan naka yakwashe matansa suka ficedaga filin ba tare da sanin�yan kallo ba.

Fitar �yan wasan Kanokuwa bayan an tashi dagabikin, sai da jami�an tsarosuka tashi tsaye, sannan sukasamu sararin fita da motarsu.

GASA TA 10

Wanene wannan?Wannan ]an yaron da kuke gani, ba yaro ba ne a yau. Magidanci ne. Domin kuwa an ]aukiwannan hoto nasa ne kimanin shekaru 30 da suka wuce, lokacin yana }arami.

Jarumin finafinai ne da dama a yau, kuma furodusa/darakta.

Satar amsa: La}anin sunansa ya yi kama da na wani mashahurin ]an siyasa marigayi. Kuma

Bikin tarewar Halisa ya yi armashiTaro ya yi taro ya zuwa

}arfe 9, sannan Halisa daangonta Muhammad Talal,wanda ]an sanda ne a garinJidda cikin }asar Saudiyya,suka iso wurin tare da�yan�uwa da abokan arziki.

Daga nan mai ki]an �yanSudan a wurin ya dakata, akaba Sirajo Mai Asharalle fageshi ma ya cashe. Amarya daango da abokan arziki sukami}e suka taka rawa yayinda jama�a suka shiga yi masuli}i. Shi ma Sirajo, ya kwashinaira a wannan daren.

Wakilinmu ya lura da cewafarin ciki ya rufe uwar Halisa,Hajiya Hauwa, a wurin,domin ta aurar da �yar autarta,sauran yayar Halisa, watoIzzatu.

An rarraba abinci da abinsha. Ba a tashi daga bikin basai wajen }arfe 12 na dare,

sannan aka fara watsewa.Bayan kwana biyu,

wakilinmu ya so ya zanta daHalisa, amma aka samikuskure; yaron da ta turo ofis]inmu a kira shi zuwagidansu bai gano ofis ]in ba.Da wakilinmu ya yi }o}arin

Muhammad Talal

Daga IRO MAMMAN,a Kano

18

Ci gaba daga shafi na 17

Galar Fati

{ARSHEN tika-tika, tik!Bikin nan na tarewar

�yar wasa HalisaMohammed, wanda akada]e ana jira, ya zo ya wuce.An yi walimar a ranarAlhamis, 16 ga Agusta, 2001a otal ]in �Lebanese Club�da ke Kano.

Walimar, wadda aka fara yida misalin }arfe 10 na dare,ta sami halartar ]imbinjama�a wa]anda suka ha]ada �yan�uwan amarya da naango, da �yan fim, da sauranjama�a. Abin mamaki,ma�auratan ba su yayatabikin ba, domin mutane dayawa sun je wurin ba tare daan gayyace su ba. Ko wakilinmujallar Fim da ya halarciwalimar, ya tsinci labarin nea gari da misalin }arfe 8:30,sannan ya garzaya zuwawurin.

Halisa Mohammedganinta daga bisani, bai cinasaba ba, domin ba a }arakwana biyu ba Halisa daTalal suka koma Saudiyya.Amma mun ji an ce ba za a yiwatanni da yawa ba nan gabaza a yi bikin suna. Allah yanuna mana ranar, amin.

Page 20: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

RAHOTON M

USAMM

AN

An ritsa da su Sani S.K. da Dumbadis a cikin shirin Badali 1

Daga WAKILANMU

TUN lokacin da aka fara shirya finafinanHausa na bidiyo suka fara fuskantar}alubale daga wa]anda ba su maidahankalinsu ga harkar ba. Babba daga cikinwa]annan }alubale kuwa shi ne shin yaza a yi daraktoci da furodusoshi da kumasu kansu �yan wasa su karkato ra�ayin

Hausawa daga nisan da suka yi na kallon finafinanIndiya? Ba fim ]in Indiya ne ka]ai ya shiga zukatanmatasan Hausawa ba, a�a har da na Caina da kuma ya}insoja na Amerika. Sun yi nasarar haka ne kuwa dominsha�awar da matasan ke yi na ganin ana kece rainitsakanin abokan gaba; shi ya sa za ka ga akwai da yawadaga cikin finafinan ko da jigonsu na soyayya ne to,warwarar jigon ta }are da fa]a tashin hankali ko ya}i.

Masu shirya finafinan Hausa sun fara cimma samunwannan nasara tasu ta hanyar nuna mutane masumugayen hali a cikin finafinai irin sigar na Indiya koAmerika. Sun yi hakan ne kuwa ganin cewa munafinci

’Y AN TA’ADDA A FIM:

Cikinsu akwai zarata irin su Shu�aibu Lawan (Kumurci),Ibrahim Y. Ibrahim (Sinana), Jazuli {azaza, Sani S.K., TijjaniAsase, Delemi Ibrahim (Daula) da kuma wa]ansu daban.

Irin yadda sukan gudanar da aika-aikarsu yana }arakwa]aita wa wani ~angare na jama�a, musamman matasa,ma�abota shiga sinima, sha�awar finafinan Hausa. Wa]annan�yan ta�adda na girgiza zukatan matasa da kuma firgita matanaure ganin cewa gidan da kuma duk suka dira sai sun barba}in labari � ko dai rai ya salwanta ko kuma su tara wa maitsautsayi gajiya ta hanyar yi masa bugun ~adda-kama.

To, duk da yadda basawan fim ]in Hausa ke burge wasu�yan kallo, akwai mutanen da suke ganin sanya irin wannanharka ta tashin hankali a fim ]in Hausa bai dace ba. Aganinsu, ana koya wa matasa muguwar ]abi�a ne, inda za sutashi da tunanin cewa rai ba a bakin komai yake ba. To suwaye basawan nan? Mujallar Fim ta shafe watanni a}allahu]u tana za}ulo maku wasu daga cikin wa]annan �yanta�adda kuma ta yi hira da su. Wakilanmu sun lura cewasama da kashi 95 cikin ]ari na irin wa]annan �yan wasan aKano suke, kuma ashe ma ba wani yawa gare su ba, ana daita maimaita su ne a finafinai. A yanzu dai ga su:

19

ko sharrin da ake }ullawa a cikinfim bai isa wadatar da �yan kallonisha]i ba. Daga nan ne aka farasamun bayyanar basawa a cikinfinafinan Hausa.

Wasu daga cikin finafinanfarko da aka fara da wannan sigashi ne wani fim mai suna �Yan[aukar Amarya wanda aka yi dasunan wata }ungiya tun lokacinda �yan ]aukar amarya sukaaddabi Jihar Kano. Za a iya cewaMu�azzam Boss ne jagoran farawannan siga, lokacin da ya fitoa finafinai kamar su Tsuntsu MaiWayo, In Da So Da {auna,Bakandamiyar Rikicin Duniyada kuma Karambana. Wa]annansu ne finafinan �yan kasuwa dasuka fara nuna action.

Yanzu da abin ya }ara ha~akakuwa. An }ara samun yaramatasa masu sha�awar fitowa dasigar �yan ta�adda �yan kisangilla ko kuma ri}a}}un ~arayi.

Page 21: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

SHI Ibrahim (wanda akafi sani da sunaMu�azzam ko kuma

�Bos�) tun can kafin shigowarwasan Hausa a finafinai yayi suna. Wannan suna dai na�Boss� shi ake masa la}abi dashi tun daga shekarar 1981,lokacin da suke yin wasancanis a gaban �yan kallo.Farkon fitowarsa sai IbrahimMu�azzam ya yi irin shigarbasawa na finafinan }asarSin. Tun daga wancanlokacin kuwa sai sunan�Boss� ya kama shi kamarkurwa. Don haka kada ka]auka wai don su o�o sunayin fim ]in bidiyo neMu�azzam ya sami sunan.

Ya fara harkar fim ]inHausa tun kafin kamfanoninshirya finafinai su fito.Mu�azzam ya shaida wamujallar Fim cewa hasali madai su ne suka fara yin fim nabidiyo a Kano. �Mu muka yifim kan �yan ]aukar amaryada suka ta~a addabar JiharKano can baya.� Wannanfim, inji Mu�azzam, shi nefarko da wata }ungiya tashirya, wanda ba shiringwamnati ba ne ko kamfani.

Da aka tambaye shilokacin da ya fara harkar fimna bidiyo kuma na kamfani,sai ya ce tun lokacin da akafara �action film�. A ta}aicedai, da shi aka yi shirinTsuntsu Mai Wayo, In Da SoDa {auna, BakandamiyarRikicin Duniya da kumaKaren Bana. Wa]annan su neya kira �action� na farko.

�To kai me ya sa kakesha�awar fitowa a mugu?�Wannan tambayar ce ya amsada cewa, �Dalili shi ne nakaranci duk inda mai laifiyake }arshensa ba ya kyau.�Kuma Mu�azzam shi ya sa yaza~i yin hani da wannan]anyen aiki ta hanyar nunaillarsa a finafinan Hausa. Yakuma shaida cewa yana jinda]in harkar don}wa}walwarsa na }arabu]ewa idan yana�mugunta.�

Wani abin da mai karatuzai fahimta a nan shi neIbrahim Mu�azzam kusan shine ]an ta�adda na farko aharkar finafinai da ya yi fice.

�saboda babu furodusan daya ta~a rubuta fim ]in da nayi na fita da }yar.�

�Ni fa yadda nake jinkaina da kuma yadda nake jida wa]annan yara matasa(Sinana, Kumarci, {azaza,S.K., Asase), to idan za mu yi�training� na wata shida saimun fi jaruman Indiya.�

�Indiya fa ka ce!� injiwakilinmu cikin mamaki.Shi kuwa Mu�azzam sai maya }ara da cewa shi fa yanada �training� ha]a]]e najikinsa, kuma shi ka]ai ne�Black Belter.� Wannanjarumi kuwa inji Mu�azzamshi ne Akshay Kumar. �Banda shi sauran duk abin dasuke yi shirme ne.�

A halin yanzu daiMu�azzam bai cika fitowa afinafinai ba. Sai dai yanakoya wa yaran basawa yaddaake tu�annati a gidankoyarwarsa da ke kan titin�Court Road� a unguwarGya]i-Gya]i da ke Kano.

Ba ga irin su BakandamiyarRikicin Duniya wasufinafinan da ya yi can bayasun ha]a da Wake [aya,Bilkisu da wasu da yawa.Finafinansa na baya-bayanan kuwa, akwai irin suSai A Lahira, fim ]in da yasamu lambar yabonta�addaci, da Ba}in Dare, SaiDa Dangan, Imani,Marainiya, da sauransu.

Irin sigar da Mu�azzam kefitowa da ita, takan bai wajama�a mamaki. Shi da kansaya shaida wa wakilinmucewa, �Wallahi, malam,akwai wani jami�in tsaro daya ta~a zuwa yana bincikenawai ko ni ]an fashi ne.�Wannan jami�in tsaro dai yakalli Mu�azzam ne a cikinMarainiya, shi ya sa ya yimasa mummunar alamartambaya.

Sai dai kuma shi a ganinsaduk irin jaruntaka damuguntar da ya yi, idan yazauna ya kalli fim ]in sai yaraina kansa. A cewarsa, haryanzu bai yarda yana fim ba,

Duk inda mai laifi yake }arshensa ba kyau – MU’AZZAM (‘BOSS’)

Kashe mutum a wurina ba waniabu ba ne, amma...

– SHU’AIBU LAWAN (‘KUMURCI’)

Mu’azzam ya yi shigar ‘nigogi’ a cikin ...Sai A Lahira

BABBARmatsalar daS h u � a i b uL a w a n(�Kumurci�)yake fuskantaa cikinjama�a ita cemummunarfahimtar daake yi masata ]an daba.Ba wani abuya janyomasa wannanba sai irinsigar da yakefitowa da itaa cikin fim.Bugu da }arikuma a zahiriduk wandaya gan shi zaitabbatar da

BASAWA/’Y AN TA’ADDA

20

Page 22: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

cewa Shu�aibu ya yi daidaida irin masu halayen da yakefitowa da siffarsu.

Sai dai wani abin sha�awaga Kumurci shi ne yi ba ]aniskan kan titi ba ne kamaryadda wasu ke yi masawannan fahimtar. Tun yana}arami ya sami tarbiyyarilimi domin kafin ya farashirin fim sai da ya kammalakaratun difloma a �School ofTechnology,� Kano, inda yakaranci zane-zane (�Art andDesign�).

Amma kuma gurguwarfahimtar da masu kallon fimke yi masa, tuni ta daina ~atamasa rai. �Ni dai na san cewaabin da nake yi yana burgejama�a. To ashe kuwa dukabin da jama�a za su kalla suyi sha�awa sai ka dage kanyin sa,� inji shi.

A ~angaren halaka jama�ane Kumurci ya ciri tuta,domin har bugun }irji ya yicewa shi bai san iya wa]andaya halaka a fim ba. �Kashemutum a wurina ba wani abuba ne, amma a fim.� HakaKumurci ya furta wawakilinmu, ya kuma }ara dacewa, �azale, da ta fa]a kanmai tsauyi shi kenan, sai daiwani ba shi ba.�

Wata tambaya da aka yi waKumurci ita ce, shin dagawane lokaci ne kisan gilla yazame masa jiki? Sai da yatsaya ya tunana, daga nan yayi dariyar }eta, ya ce,�Wallahi da Hauwa Ali Dodona fara. Ita ce na kashe a cikinHalacci.�

Saboda kisan gilla yagame masa jiki, Kumurci yabayyana cewa inda duk yafito a sigar mutunen kirki,kamar cikin fim ]in Hauwa,shi sai ya ji kamar ba fimyake yi ba. Ashe ba zai canzawani role ba, ya daina fitowamugu ba? Sai gogan naka yace, �Ni fa na riga na sabama}ure wuyan mai }ararkwana. Ni mugu ne, sana�ata mugunta, kuma da itanake cin abinci. Kai, ba zandaina mugunta ba harMahadi ya bayyana (ammaa fim).�

Kumurci dai ya tabbatarda cewa ha}i}a har a zahiriakwai masu tsoronsa. �Akwaima wata �yar wasa da ta ce bata iya ha]a ido da ni,� injishi. To yara }anana fa?

Kumurci, wanda ya samiwannan sunan a fim ]in a fim]in U}uba, ya ce, �Waniba}on yaro ya gan ni sai yashige }ar}ashin gado.�

Wani abu da Kumurci kan

yi shi ne yakan zauna ya kalliirin ta�addar da ya yi a cikinfim. Abin takaici, ba nadamayake yi ba. Sai dai ya yi �Da-na-sani da na fi hakamugunta, to da fim ]in ya fi

kyau.�Duk da wannan �ta�asa�

da yake yi, shi ma, kamarkowane ]an wasa, Kumurciya dage da cewa malami nemai karantar da jama�a.

SANI S.K. yana dagacikin manyan �yanwasan fim a yau. Ya

fito a finafinai daban-daban.Sun ha]a da Mu}addari,Badali, Dr. Gulam, Garari,Muradi, Jaza�i, Hamayya,{unci, Jumur]a, Karamci,Dace, da wasu wa]anda maba su fito ba tukuna. Wasanda yakan yi iri-iri ne, ammaa yanzu an fi kallonsa amatsayin bos. A cikin Badaline ya fara cirar tuta amatsayin bos.

Wani abu da jama�a ba susani ba game da shi shi nekafin shigarsa wasankwaikwayo, mawa}i ne nabegen Manzo (S.A.W.), ko dayake har yanzu idan angayyace shi yakan je ya ta~a.

Mafi yawan wa}o}in dayake yi na yabon Annabiwa}o}i ne na finafinanIndiya yake maidawa sigarna Hausa. Wasu daga cikinsusun ha]a da wa}ar �Hotiho,�da wa}ar �Karati� da �AbiHayat.�

Za a iya cewa S.K ya yi wawannan harkar shiga sojanBadakkare idan aka dubihalin da yake ciki kafin yashige ta. �Bayan na gamasakandare ta Gwale ashekarar 1988 kuma na je�Kano Polytechnic,� sai nafara aiki a Asibitin Murtalainda na shekara goma a can,�inji shi. Ba a nan ya tsaya ba,sai kuma ya je ya yi wanikwas wanda da ya gama saiya koma aiki a hukumarsamar da wutar lantarki ta}asa (NEPA). �A can watanashidda kacal sai na rubutatakardar barin aiki na kamaharkar wasan Hausa gadan-gadan.�

An haifi Sani S.K. a[andago, Kano, a gida mailamba 105, a ran 12 gaFabrairu, 1968. Ya faramakarantar firamare a[andago, a wata sabuwarmakaranta da ake ce mataMaitasa, inda ya gama a

1981. Bayan nan sai ya shigamakarantar sakandare taGwale, inda ya }are a 1988.Ya fara aikin gwamnati a1989 kafin ya shigamakarantar kimiyya dafasaha inda ya yi difloma. Saidai ya ci gaba da aiki ama�aikatar lafiya. Ya yi aikia asibitin Murtala, inda yashekara goma.

Mafi yawancin �yan fimsukan fara ne da }ungiyoyi,inda daga nan akan gogemasu }umba. S.K. ma ya yiirin wa]annan }ungiyoyininda ya fara harkar wasankwaikwayo na da~e a cikin1989, a wata }ungiya wacceake kira Mai}usurwa abayan Gidan Makama cikinbirnin Kano. Daga baya yashiga ha]a]]iyar }ungiyar�yan wasa ta jiha, watau KanoCouncil of Artists. �Abin daya ba ni sha�awa,� inji shi,

�shi ne irin yadda na ga �yanwasan suna ciyar da al�adunHausa gaba ta hanyarnisha]i. Sannan kuma gafa]akarwar da suke yi wandatana taimakawa matu}a gayawajen shiryar da al�umma.Sai na ga ni ma ya kamata inbayar da tawa gudunmawarta wannan ~angaren.Wannan shi ne ya ba nisha�awa har na tsundumacikin wannan harkar.�

To me ya sa da ya shigashirin fim sai ya bi layinmugaye? Da aka yi masawannan tambaya sai yabayyana cewa, �Farko dai aisha�awar darakta ce kesanyawa,� har aka ga ya daceda ya yi wani role. �Ni aikowane ~angare aka saka nizan iya fitowa. Zan iyafitowa matsayin dolo ko maiban dariya, ko kuma mugu,�inji shi. Maganar

Sani S.K. a matsayin dan sanda

Na ji da]in kisan da muka yi a Badali

BASAWA/’Y AN TA’ADDA

– SANI S.K.

21

Page 23: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

ta�addancin da S.K ketafkawa fa? Sai ya kada bakiya ce, �Irin ta�addancinailhama ce daga Allah, fasahace; domin idan ka lura ko asifar mugunta na fito nakanri}a yin ]an barkwanci, dagabaya kuma in murtukefuska.�

Akwai masu kallon S.K. amatsayin mugu na gaskesaboda yadda ake ganinsa afim. S.K. ya ce, �Da ma alakulli hailin in an ba ]an wasarawa ya taka ba a yi ne dominhalinsa kenan ba. An yi nedomin masu kallo daal�umma masu halayya irinwannan su daina. Kuma ai ako wace al�umma za ka iyasamun irin wa]annanmutanen a cikin malamai.Kowa da irin yadda Allah Yashi.�

S.K. ya kuma jawohankalin masu yin wanihasashe cewa wasu �yanta�addar sun fara rage tashenwasu, ya ce, �Kowa ailokacin da Allah Ya tsagamasa yake ci. Babu wandaya isa ya bai wa wani abin daAllah bai ba shi ba.� Ya }arada cewa babu wanda zai hanamutum abin da Allah Ya bashi.

S.K ya yi farin ciki da irinrawar da yake takawa a cikinfim sai ya bugi }irji ya ce, �Awannan role ]in na halakajama�a da dama amma fa acikin fim.� Daga cikin ta�asarda ya tafka kuwa S.K. yanuna cewa ya fi son kisan daaka yi cikin Badali. �Ba nina kashe ba, na dai ba daumarni an yi, kuma na jida]in kisan; ta�addanci na yia ciki yadda ya kamata.�

Sani ya fara fitowa ne awani fim ]in bidiyo mai suna[andugaji. A ganinsa, idanya }ididdige yawanfinafinan da ya yi ya zuwayanzu sun kai guda 67. Dama kuma ya yi wa]ansuwasannin ba a kaset ]inbidiyo ba, wato irin dirama]in nan ta da~e, irin waddasukan yi a }auyuka haka dakuma idan an gayyace suwajen wata hidima: biki ne,taron suna, da dai sauransu.

A harkar fim, babu irinrawar da S.K. bai taka ba.Daga cikinsu, ya ce shi daiya fi }aunar furodusa kodarakta ya ba shi duk rawar

da ya ga ya dace da ita.�Saboda haka ba ni da za~i;duk abin da aka sa ni cikinikon Allah zan iya. Ko nabanza ne ko na kirki ne indai ce S.K. ri}a zan yi }o}ariin ga na kare ha}}ina wajenin gamsar da jama�a da kumaisar da abin da ake }o}arin aisar a wannan wuri.�

S.K. yakan fito a wajen bandariya, ko azzalumi komamutumin kirki. Daga cikinwa]annan nau�o�i wanne neya fi burge shi?

�Duk abin da aka ba ni inaso tunda dai abin dai nunine ga jama�a. Saboda hakain ka ba ni na zaluncin zanyi }o}ari in ga azzulumannan idan suna zalunci waneirin ho~~asa suke wajenaiwatar da abin. In aka ba ninikan yi }o}ari in ga na kareha}}ina a kai.�

Fim ta tambayi Sani, dagacikin ]imbin finafinan da yayi, wanne ne zai ce ya fizama }alubale a gare shi?Amsa: �Duk fim ]in da na yi}alubale ne a gare ni, kumafarin jini suka }ara mani.�

Shin ko ya ta~a samunmatsala ko a }yamace shisaboda wata rawa da ya takata zalunci a cikinfinafinansa? S.K. ya ce,�Kamar misali a Badali, nataka rawar zalunci ammafuska biyu, saboda akwaiinda nake bayar da dariya.To maimakon jama�a su

}yamace ni sai wannan bandariyar ya jawo mani farinjini. Domin na samu kashi 95bisa ]ari na masoyasakamakon wannan role dana taka a Badali.�

A cikin Muradi ya fito amatsayin ]an giya inda yari}a sha yana yin tatil.Menene ra�ayin iyalansa kanirin wannan rawa da ya taka?

S.K.: �Burge su na yi suiyalan nawa. Domin sun sanni ba ]an giyar ba ne. Sannansun san abin da ya da]a bani }warin gwiwa shi neyadda suka yaba da rawar,suka ce na dace da ita }warai.Ban ta~a ]an]ana za}i ko]acin giya ba.�

S.K. yana daga cikin �yanwasa wa]anda suke da burinsu ma su yi nasu finfinan. Yace, �Gaskiya na da]e inawasan fim na kaina; wannanal�amarin na bar shi ga AllahYa yi mani za~i. Amma kumako da ban shirya ]in ba toalhamdu lillahi, domin koyanzu na samu alherigwargwado kuma an san ni awannan harka.�

Kada mai karatu ya yitunanin cewa kamfanin nanna �S.K. Entertainment,�wanda ya yi finafinai irin na�camama�, na Sani S.K. ne.A�a, ba nasa ba ne.

Mun tambayi Sani kowane alheri zai ce ya ta~asamu sanadiyyar wannansana�a da ba zai mance da shi

ba? Sai ya ce, �Tab]ijam! Aiin na ce zan }irga irin alheranda na samu... Suna da yawa.Kyaututtuka, yabo ne, ga sunan. Amma daga cikinsuyabo da addu�ar da ake yimani sun fiye mani dukiya.Ina samun yabo }warai dagaske daga yara, manya,maza da mata. Ina godiya gamasu yi mani wannan fatanalheri. Alheri na samu kumaina kan samu }warai dagaske. Sai dai godiya ga Al-lah.�

S.K. yana da mata ]ayawadda ya aura a cikin 1992,yana da �ya�ya biyu, kumana uku yana nan kan hanyaa lokacin hirarmu da shi.

Babban burinsa shi ne Al-lah Ya sa su rabu da kowalafiya. �Kuma ina kira gamasoyana da su ri}a bayarda shawarwari kan wani abinda suka ga na yi ko waniaboki ko abokiyar harkarwasan nan suka ga ya yi badaidai ba. Suna iya bayar dawannan shawarwari ta tarho,ko kai tsaye wajenmu kokuma a bayar a rubuce. A cewane wuri kaza bai yi ba, kokuma mun ga fim na wanekaza ya kamata a ce ku yikaza ku yi kaza. Idan mukaduba muka ga wurin sai mugyara. Ba a ri}a tsangwamarmutum in ya fito a watarawar da aka ba shi wacce bata da kyau ba. Dominkoyarwa muke yi.�

TUN farko da ya shigaharkar finafinan Hausabai shiga da sigar

mutanen kirki ba, a ]anta�adda yake fitowa. IbrahimY. Ibrahim, wanda aka fi sanida suna Dumbadus koSinana, ya bayyana irin jinda]in aika-aikar da yaketafkawa a fim. Dukabubuwan ba wanda zai soSinana yana sha�awar ganinya mayar da }ananan yaramarayu, yana kuma farin cikiidan ya ga ya mur]e wuyanwanda tsautsayi ya gitta akansa.

An haifi Ibrahim aunguwar Gwammaja da kecikin {aramar Hukumar Dalaa birnin Kano. Ya yi karatunfiramare a �[antata Primary

Ba zan daina kisa ba har tsufana! – IBRAHIM SINANASchool,� ya zarce zuwamakarantar Arabiyya ta�School of Arabic Studies�(S.A.S.), Kano, ya koma�Technical School,�Bagauda, inda ya gama.Kuma ya yi karatu a �Poly-technic.� Ya yi harkarkasuwanci kafin ya shigaharkar fim.

Dumbadus ]an shekara 31,ya fara shiga harkar wasanHausa kimanin shekaru ukuda suka shu]e. �Ba zanmanta ba, na fara ne lokacinda fim ]in Dijangala ya fito.Don a lokacin ne na yi wanifim wanda ya fito tare daDijangala.� Ya ci gaba dabayyana wa wakilinmu cewaabin da ya sa ya shiga fim,shi mutum ne mai yawan

kallon fina-finan Amerika daNigerian films na Inyamurai.To sai ya ga ya kamata irinsasu fito su ba da gudunmawaa harkar.

Sai dai wani abin tambayashi ne yadda ]an wasan ya]auki hanyar fitowa amatsayin mugu (bos) a dukfinafinan da yake fitowa.Wannan tambayar ya amsa tada cewa, �Mu masufa]akarwa ne, muna nunacewa idan mutum maimummunan hali irin namuya aikata abu, to za a nunamasa }arshensa ta yi muni.Wannan shi ne dalilin da yasa na za~i wannan matsayidon in nuna wa jama�a cewahanyar zalunci ba hanyarkirki ba ce.�

BASAWA/’Y AN TA’ADDA

22

Page 24: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

TIJJANI Asase matashine ]an shekaru 28 dahaihuwa. Tun a cikin

1991 ne ya ]auko hanya tata�addanci a cikin fim,lokacin da ya fito akinBakandamiyar RikicinDuniya. Bayan wannanlokacin, Asase ya yi ta}o}arin fitowa da wata sifar,musamman ta fagen samari�yan soyayya amma abin yafaskara. Ko shakka babu,wannan yana da nasaba dairin sigar da Allah Ya yi masa.

�An sha saka ni a ~angarensoyayya ba ta dace da ni ba,ba ni da sigar da zan yi rawain musku]a nan in musku]acan. Ni ba ]an daba ba ne,amma kamannuna sun nunahaka,� inji Asase, wandawani dun}ulallen ba}in }atone. Bayan ga cewa ba}i ne,}wala}walan idanunsasukan }ara masa armashiwajen fitowa da muguwarsifa a cikin fim.

Wani abin mamaki da ke

Ibrahim dai ya fito ashahararrun finafinan dasuka ha]a da Badali, Wa}i�a,Alaqa, {azafi, Ba�asi,Jumur]a, da sauransu. Shinko zai iya lisssafa yawanmutanen da ya kashe ko yajikkata a fim? Sai ya kadabaki ya ce, �Ni yanzu ban saniyakar adadin jama�ar da nakashe ko na raunata a cikinfim ba.�

Ibrahim Y. Ibrahim, wandaya samo sunan Dumbadus afim ]in Badali, ya shaida waFim cewa shi fa a wannanharka da yake yi ba ya jinkunyar fa]akar da jama�a takowace siga, musammantunda mutane sun fara ganemuhimmancin sa}on da �yanfim na Hausa suke isarwa.

A nan, sai ya fa]a dababbar murya cewa, �Niyanzu a shirye nake a ce gani na fito fim tare da ]iyataFa]imatu Zahara�u, kuma ace an tura ni na je na mur]emata wuya.� Ya ce wannanai }aramin aikinsa ne. �Bazan daina ba har tsufana. Aifa]akarwa ce, ba gaske bane, tunda munanan halaye nemuke nuna ma wa]anda keda irin wannan halin sudaina.�

Shi ma ya ta~a fa]awacikin irin halin }uncin.�Wata rana na je wani gidadon na gaisa da mara lafiya.Ko da aka ce ga Dumbadus,sai kawai wata tsohuwa tatashi tana kora ta. Har sai data kai ga tsohuwar nan ta]auko itace ta fara dukana,wai ni mugu ne. Aka batsohuwar nan ha}uri,� inji]an wasan.

Ya furta cewa a duniyarfinafinan Hausa, yana so ari}a ha]a shi wasa da TijjaniA s a s e ,Shu�aibu Lawan (Kumurci)da kuma Jazuli {azaza. �Kasan idan muna tare a cikinfim, to ~arnar ta fi da]in yi.�

Duk da }arfin da Allah Yaba shi, ]an wasa Sinana yafa]a mana shi bai fi kowa bakuma daidai yake da kowa.�Ma�ana, duk abin da nakeyi ai shiri ne, daidai nake dakowa, kuma duk abin da zaiiya firgita mutum ya yi ro}oga jama�a su fahimci cewashi sauran mutanen da kefitowa a matsayin basawacikin fim, to ba halinsu ba

ne.� Ya kuma nuna takaicin yadda wasu mutane suke yi waKumurci kallon ]an daba bayan kuwa a zahiri ba ruwansada �yan daba a rayuwarsa.

tare da Asase shi ne yaddamahaifinsa ya ]aure masagindi yake ta�addanci ba jiba gani a cikin finafinai.�Mahaifinsa idan yana kalloya ga ana dukana sai ya yi tamurna. Ita kuwa matata saita ce me ya sa ban yi }o}ariba?� A ta bakinsa, ya samigogewa ne ta fannin iyafitowa da sifar ]an dabasanadiyyar yanayin da yatsinci kansa a ciki can baya.�Ban yi dabanci ba, ammanakan ga yadda sukemu�amalarsu, shi ya sa nagoge da iya fitowa dawannan sifa.�

A garin Ha]eja ne aka yiwa Asase tare da Shu�aibuKumurci kyauta ta mamaki.Ba ku]i ne aka she}a masuba ko wa]ansu kayan alatu.Wanda ya ba su kyautar shi atsammaninsa ko a zahiri�yan daba ne ba a cikin fimka]ai ba. Adda ce wani ya yimasu kari da ita maimakonku]in da zai li}a masu.

�Wani kuma lokacin dakowa ke yi mana li}i da nairasai ya li}a mani watazandamemiyar wu}a,� injiAsase. Kuma mutumin ya cemasa don Allah ya ri}a fitowafim da wu}ar.

Asase dai ba ba}on masukallon finafinai ba ne.Bakandamiya ya fara yi canbaya. Ya fito cikin Mujaza,Jumur]a, Taqidi (bai fito ba),Lalura, Badali na 2 da kuma

Ban iya soyayya ba sai mugunta!

– TIJJANI ASASE

Ibrahim Y. Ibrahim (Sinana)

BASAWA/’Y AN TA’ADDA

23

Page 25: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

�wa]ansu da ba su fito bakusan guda talatin,� inji shi.

Wani abin lura dangane dawa]anan basawa kuwa shi neba kullum ne suke kwana agado ba. Baya gamummunan }arshen da sukeyi a cikin fim a wurin shoot-ing sukan yi katari datsautsayi har abin ya kai su

KAMAR yadda Kanotake ta}ama da samunKumurci a matsayin

]an wasan da ya shahara afagen fitowa ]an ta�adda acikin finafinan Hausa,Kaduna ma tana da nata.Kuma ya }ware, ya kumacancanci fitowa bos. Sabodaduk fim ]in da ya fito, maikallo zai iya mantawa dacewa Bold Max..

A tattaunawar da ya yi dawakilinmu a Kaduna, ]anwasan ya yi cikakken bayania kansa, tare da cin gyaranwasu basawa da cewa yaddasuke wasa a matsayin basawaa fim, suna tafka kuskure.Kuma shi a wurinsa, aikin�yan daba suke yi, ba nabasawa ba.

Shi dai Abubakar Musa,wanda aka fi sani da BoldMax, ya ce fitowar da yakeyi a matsayin bos,sakamakon bu}atarfurodusoshi da daraktoci ce,wa]anda su ne suka ga ya

Iya ha]a mugunta a fim ya sa ake sa ni a bos! – BOLD MAX

ga jikkata. Asase ya ce shidai ya gode wa Allahshigarsa wasan kwaikwayodomin kafin ya shiga shimutum ne mai bala�inzuciya. �Sai ga shi yanzusaboda cu]anya da jama�adaban-daban da nake yiyanzu ba na yin gaba dakowa.�

A }arshe dai ya nuna cewashi babu abin da ya fi so acikin fim kamar a ce �yau gashi fa]a ya kama daga mu saiTahir Fagge bayan munkashe matarsa mun kashe�ya�yansa mun kashe dukwata zuri�a da ke gidansa shika]ai ne ya rage.� Tijjani yace to a nan masu kallo za su

ga cewa airin halin da Tahirke nunawa ya shiga ai ko su�yan wasa hankalinsu kan basu cewa tamkar ba dirama ceTahir ]in yake yi ba.

An haifi Asase a unguwar[andago. Ya yi karatunfiramare da na sakandare aGwale. Yana da mata ]ayamai suna A�ishat.

matsaloli abin ya faskara.Ya yi aiki a Ma�aikatar {asada Safiyo (Land andSurvey) ta Jihar Kano harshekaru biyar. A yanzu hakakuma yana aiki ne a fanninlafiya a {aramar HukumarFagge.

Fim ]insa na farko shi neBirgimar Hankaka wandahar yanzu bai fito ba. Ya

24

cancanta ya fito a wannan matsayin.Da wuya a iya kawo sunayen

dukkan finafinan da Bold Max yafito a cikinsu, amma ya fito a Ishara,Ana Bikin Duniya, Dare [aya, [an{alamba, Sara Da Sassa}a da kuma{addara. Kuma a wa]annan duk amatsayin bos ya fito.

Akwai wani suna da aka fi saninsada shi a cikin finafinai, wato MeGuba. Mun tambayi Bold Max meya sa ya fi son a kira shi da wannansunan? �Ba ni na ba kaina wannansuna ba,� inni shi. �Mutane ne sukasanya mani saboda ganin yadda naiya ha]a mugun abu a cikin fim.�

To yaya zai kwatanta kansa damutane irin su Kumurci, wa]andasuka riga suka yi fice a fagen fitowabos? Max ya ce: �Ai Kumurci babos yake fitowa ba, yana fitowa nea matsayin ]an ta�adda, wanda aketurawa ya aikata mugun abu a biyashi. Kuma yanayin yanda yakewasanshi ba haka bos yake yi ba.Domin shi za ka ga ya fito yana ihuyana cika baki. Ba yanda za a yikana bos ka yi irin wannan, sai daiyaranka su yi. Misali, ka ga kamarDumbadus, wanda ya fito bos ]inBadali, ka ga wannan shi ake kirabos. Saboda haka akwai bambancitsakanina da Kumurci.�

Da aka tambaye shi ko wane fimya fi burge shi daga cikin finafinanda ya yi, ba tare da wani ~ata lokaciba sai Bold Max ya amsa: �AnaBikin Duniya.�

Fa}at.

“Ai Kumurci babos yake fitowa ba,

yana fitowa ne amatsayin dan

ta’adda, wanda aketurawa ya aikata

mugun abu a biyashi. Kuma yanayin

yanda yake wasanshiba haka bos yake yiba. Domin shi za kaga ya fito yana ihuyana cika baki. Bayanda za a yi kana

bos ka yi irinwannan, sai daiyaranka su yi.”

Aikina in maida yara marayu – KAZAZA

JALULI {azaza ba ba}oba ne ga masu kallonfinafinan Hausa. Kamar

sauran basawa, shi ma yasamu ]imbin masoya dakuma ma}iya dalilinazabtar da mutane da yakeyi. An haifi {azazashekaru 37 da suka shu]e.Ba makarantar firamare yafara ba, sai da ya yi shekara

shida a makarantarIslamiyya ta Malam Nasiru,�Muhassi�u Sheikh NasiruKano.�

Daga nan kuma sai yakoma �{ofar Na�isa PrimarySchool� a cikin 1978, yagama a 1982. Ya fara karatua makarantar �HealthTechnology� ta Kano,amma saboda wasu

BASAWA/’Y AN TA’ADDA

Abubakar Musa (‘Bold Max’)

Page 26: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

shiga harkar fim ne a cikin1995. To me ya sa ka komahanyar ta�addanci? Sai yakada baki ya ce,�Ta�addanci ya fi ci. Shi yasa nake sha�awarsa.� Dagafarawarsa zuwa yanzu kuwa{azaza ya ce, �Na jikkatamutane da dama ba su}irguwa, na maida iyayenwasu }ananan yara da damamarayu�.

Wasu daga aikinfinafinansa su ne Kara DaKiya shi, U}uba, Jumur]a,Aziji, Badali 2, Lalura,Ta}idi da kuma wasu dadama.

Kamar yadda ake ganinwasu basawa a tsorata, tohakan ya ta~a faruwa gaJazuli {azaza. Sai dai waniabin da jama�a za su so suji shi ne, {azaza ya ta~ayin malanta a makarantarIslamiyya. Shi ya sa yanzuhaka idan ya ratsa cikinwasu unguwannin, yara dadama kan rusuna su gaisheshi bayan sun kira shi dala}anin Shehi, Malam,Uztaz ko Anikallahu. Saidai shi ma ya ba da labarin

25

BASAWA/’Y AN TA’ADDA

A cikin shirin Kunci, Kazaza ne ya fasa wa Sani S.K. ciki

irin ba}ar wahalar da ya ta~asha a fa]an }arshe cikinwasu finafinai. �Duk lokacinda muke fa]a da TahirFagge, to shi da gaske dukanka zai yi. Ko dai ka kare kokuma ka ci duka. GaskiyaTahir Fagge ya ba ni wahalaa cikin A}ida, Halacci, daMu}addari.

To Jazuli sana�a ka ]aukiwasan Hausa ko fa]akarwa?Sai ya amsa da ce, �Ga ba]aya. Domin ciki nake samunabin ~atarwa kuma fa]akarwace nake yi. Akwai wata ranawani mutum ya zo ya sameni har gida ya ce wai ya gaabin da na yi a cikin fimkuma ya ga }arshena.�{azaza ya }ara da cewa saimutumin ya shaida masacewa ta ya yi niyyar cinmutuncin }anen babansa. Saiya tuna dole a sirinsa yatonu kuma ba zai ji da da]iba.

A }arshe dai Jazuli ya ceshi zai iya barin wasan Hausaidan aka ~ata masa rai tunda�bai zama dole gare ni ba.Ka san ni ina da zuciyasosai,� inji shi.

Kuna da labarin cewa shahararren kantin saida finafinan nan na�Mutunci Video Complex� sun dawo?

Gyara zama ka sha labari!A wannan karon mun tanadi finafinai iri-iri domin abokan

hul]armu na yau da kullum, kamar na Hausa, Indiya, Amerika,Canis, da sauransu.

A ~angare ]aya kuma akwai kasa-kasai, haka zalika muna sayarda kaset-kaset na rikoda da kuma mujallun finafinan Hausa dominmasu karatu.

Muna maraba da masu sayen ]ai-]ai ko sari.Biyan bu}atar abokan cinikinmu shi ne burinmu.Domin }arin bayani sai a tuntu~e mu a babban ofishinmu da ke:No. 64, Sultan Abubakar Road, Sokoto;ko a bugo wayar tarho: 060-23056;ko rassanmu da ke:No. 5 da 6, Zaria Road, Opp. Bauchi Road, Sokoto.da No. 46, Modibbo Adamu Road, Opp. Marina Mini

Market, Sokoto.

No. 64, Sultan Abubakar Road, P.O. Box 2072, Sokoto. Tarho: 060-230526

ALLAH GATAN BAWA!

Alh. Aminu MutunchiManajan Darakta

MUTUNCI VIDEO COMPLEX

Page 27: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 200126

DUK wanda bai san HADIZAKABARA ba yana da sauranaiki. Kamar yadda marigayi

[an�anace ya ce, lokacin da yakewa}ar Shago, �Ya zo zaka duniyakamar bai zo ba/Kamar zuwan kareda aboki...� Ba za mu }arasa ba muce, �Ko ya }aura ba a gafarta mai�! Agaskiya, a cikin wannan shekarar ta2001, Hadiza ta fara zama tauraruwarda duk inda aka duba a sararinsamaniyar shirin fim, za a gan ta.Kamar yadda ita kanta ta ce, in dai zaa lissafa fitattun �yan fim mata matasaguda uku, to ita ce ta ukun. A lokacinda muka yi hira da ita, Fati Moham-med tana nan ba ta yi aure ba, kumaHadiza ta ce ita ce ta biyu. Ka gakenan yanzu da ba Fati, Hadiza tazama ta biyu. To wacece ta ]ayankenan a yanzu? Amsa: ko dai AbidaMohammed ko Hadiza Kabara!

Ba a banza Hadiza take kallon kantaa matsayin mai gadon FatiMohammed ba. Domin rawar da tataka a finafinai kamar su [abi�a,Tallafi, {auna, Sawun Giwa,Ganganci, Inganci, {udiri, dasauransu, sun sa da yawa a Kano anamata kallon ]aya daga cikin �yanwasa mata wa]anda ake rububinsu ayanzu. Da ma su furodusoshi dadaraktoci, irin su Hadiza suke so susamu su sa a wasanninsu, domin kuwa

Y A R I N Y A S A B O N Y A Y I

H A D I Z A

da iya wasa, da kuma...To ko Hadiza Kabara za ta

iya cike wagegen gi~in daFati ta bari a fagen fim? Kokuwa ganganci ake yi da akecewa za ta iya ]in?

Can a kwanakin baya,kafin Fati ta yi aure,wakilinmu KALLAMUSHU�AIBU ya zauna daHadiza sun tattauna. Mun yinufin mu buga labarinta acikin fitowarmu ta auren Fati(wato watan jiya). Yawanlabarai ya sa muka aje hirar agefe sai a wannan watan.

Manufarmu ita ce mutanesu karanci ko wacece Hadiza,kuma su san irin ra�ayoyinta,sannan su tambayi kansushin za ta iya ta~uka waniabu a nan gaba?

Allah ne Masani.Yanzu dai ga ku ga Hadiza

Kabara:

Fim: Hadiza, muna so kifara gabatar da kanki ga masukaratunmu, kuma masukallonki a fim.

Hadiza: Bismillahir-rahamanir-Rahim. SunanaHadiza Kabara. An haife ni a

Selling face dole ne, cewar �

Auren da Fati Mohammed ta yi a ran 16 ga Yuli ya sa ana ta tunanin wa zai mayegurbinta. Sunan da ake ta maimaitawa shi ne HADIZA KABARA, wadda ta nuna

kwarewa a finafinai kamar su Dabi’a da Ganganci. Shin ko Hadiza tana da dabi’ar data sa Fati ta yi suna, ko kuwa dai ganganci mutane ke yi da suke cewa za ta iya?

Kuma wacece Hadiza Kabara?

wannan yarinya ta nuna cewa in dai batun fim za ayi, to ita murucin kan dutse ce, sai da ta shiryasannan ta fito. Hadiza dai ga kyau, da za}in murya,

Page 28: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

unguwar Yakasai cikin Birnin Kano a ran 22 ga watanOktoba, 1976. Ina da shekaru shida muka koma (unguwar)Panshekara da zama. Nan na yi makarantar firamare. Na faramakarantar sakandare a makarantar koyon kasuwanci, �Com-mercial College,� Kano, kafin daga baya a mayar da ni

Fim: To daga cikin finafinan da kika yi, wanne ne za ki ceya fi kwanta maki a rai, kuma menene dalili?

Hadiza: A gaskiya duk finafinan da na yi ba wanda baikwanta mani ba.

Fim: A wanne kika fi shan wahala?sakandaren �yan mata da ke|a~ura ta Jihar Jigawa, indana }are.

Fim: A wace shekara kikafara wasan kwaikwayo?

Hadiza: Na fara harkarfa]akarwa ne a bara, wataushekara ta 2000. Kuma nafara ne da wani fim mai sunaMaigari Ya Waya. Ba zan iyatuna sunan kamfanin da yashirya fim ]in ba. Ammasunan furodusansa Hassan.Sannan kuma na yi wani fim]in mai suna MalamKarkata.

Fim: Menene ra�ayiniyayenki da farko da suka jiza ki shiga harkar fim?

Hadiza: Da farko iyayenaba su so in shiga wannanharkar ba saboda irin yaddaaka ri}a zuga su, ana cewaduk wadda take yin fim ba tada natsuwa kuma duk waiwadda ke yin fim ba ta jinmaganar iyayenta, da sauranmaganganu irin na ~atancida kushe, da niyyar aharzu}a su su hana ni. Ammadaga baya, wata}ila bayansun yi bincike, sun ganoharkar ba haka take ba, saisuka bar ni.

Fim: Sunyi makaranta ne?Hadiza: Dukkansu sun yi

makaranta.Fim: To kawo ya zuwa

yanzu, kin yi finafinai za sukai nawa?

Hadiza: A gaskiya ba zaniya lissafa su ba da ka.

Fim: Ki }iyasta.Hadiza: A }iyasce za su kai

goma sha.Fim: A kan me za ki ]ora

nasarar da kika samu har akerububinki?

Hadiza: (shiru na tsawonlokaci) Zan iya dangantaabin ga ikon Allah da kumacancantata, wadda dadacewata ya sa fundusoshinke gani ya kamata a ce ni sukasa.

Fim: Kina nufin ba kiyawon �Ina-da-fim,� watauabin da ake ce wa sellingface?

Hadiza: Selling ai ya zamadole saboda sana�a ce, nemanabinci ne, kuma neman�yanci ne.

Fim: Selling face ]in?

Hadiza: Daga cikinfinafinan, ba wanda na shawuya a cikinsa kamarGanganci da kuma [abi�a.Dalili kuwa shi ne a cikinsana fito a matsayin matarmijin da ba shi da aiki. Nasayar da kayan ]akina da dukabin da na mallaka na ba shiya tsaya takara saboda ba shida ku]i, ya kuma ce shi bazai yi aikin gwamnati da zaa biya shi dubu takwas ba.Ya tsaya takarar ciyaman yaci, amma abinka da]an�adam, sai ya yo manikishiya ya rin}a wula}antani.

Fim: To Hadiza na san baza ki rasa jin irin wa]ancanmaganganu da aka ri}a fa]awa iyanyenki ba lokacin daza ki fara fim, cewa �yan matafim fitsararru ne marasakamun kai. Yaya kike ji idankin ji irin wa]annan kalamaikuma ana danganta su gareki?

Hadiza: A gaskiya abinyana }ona mani zuciya. Yana~ata mani rai }warai matu}a.Sai dai ina }yalewa ina binsu yadda suke so. A hankaliza su gane gaskiyar abin watarana. Wannan yana faruwamusamman daga �yan�uwa~angaren dangin babata dababana.

Fim: Kin ta~a yin aure?Hadiza: A�a ban ta~a yin

aure ba. Muna nan muna jira,muna addu�a Allah Ya kawomana nagari.

Fim: Kina ganin sa}on dakuke }o}arin isarwa yana yintasiri?

Hadiza: {warai kuwa,yana yin tasiri matu}a.Domin ta dalilin fa]akarwarda muka yi mata sunafahimtar mazansu. An ragemuguwar al�adar nan taauren dole. {iyayya kullumraguwa take yi. An ragezalunci wajen rabon gado.Ha}}in ma}wabtaka yana}ara inganta; kai darussan dajama�a ke koyo ta sanadiyyarwannan harka ba sulissaftuwa. Abin yana datasiri.

Fim: Amma wasu na ganinkuna yin sa~anin abin da

Hadiza: E.Fim: Kin san ko menene selling face?Hadiza: A! Selling face shi ne ka kai kanka wajen furodusa

ka ro}e shi, �Don Allah don Annabi ga ni na zo ina so kataimake ni ka sa ni a fim.� Ko ba haka ba, iye?

Fim: Kin yi maganar cancanta da farko, sannan daga bisanikika dawo kika yi maganar selling face. Ba ki ganin yawonsellling face na sanya a jefar da cancanta a sanya mutumwasa domin sanayya ko wani dalili amma ba cancanta ba?

Hadiza: E gaskiya ne. Amma duk da haka, ka san furodusako daraktan da za ka je wurinsa ka yi masa selling face.Saboda haka ba kowane furodusa ko darakta ba ne za ka jeka yi wa selling face. Sai wa]anda suka san mutuncin kansu.Irin wa]annan ai dole ne ka je wajensu ka yi masu sellingface.

27

Hadiza da ciki ... a matsayin kanwar Zik, cikin Maqabuli

“Ka san furodusa ko daraktan da za ka jewurinsa ka yi masa selling face. Sabodahaka ba kowane furodusa ko darakta ba

ne za ka je ka yi wa selling face. Saiwadanda suka san mutuncin kansu. Irinwadannan ai dole ne ka je wajensu ka yi

masu selling face.

Page 29: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 200128

kuke koyarwa a wasanku inkun fito kun shiga al�umma.

Hadiza: E, gaskiya acikinmu akwai �yan }alilanda kan yi irin abin da ake}orafi, amma ba kowa neyake haka ba. Ka sanHausawa sun ce wake ]ayashi ke ~ata miya.

Fim: Wanene ya kawo kicikin wannan harka?

Hadiza: Tijjani Ibrahimdarakta shi ne ya fara kawoni Industry.

Fim: Na san sha�awar wani]an wasa ko �yar wasa kowani fim ne ya ba ki }waringwiwar shiga wannan harkata fa]akarwa. Za mu so ki yi}arin bayani.

Hadiza: {warai kuwa. Afinafinai dai wa]anda sukasanya mani sha�awa har naga ni ma ya kamata in shigain bayar da tawagudunmawar wajenfa]akarwa akwai Allura DaZare da Abin Sirri Ne. A �yanwasa mata kuwa ba ni dakamar Fati Mohammed. Amaza kuwa kusan kowa yanaburge ni.

Fim: A matsayinki na maifa]akarwa, ko wace rawa akace ki taka za ki iya takawa?

Hadiza: A gaskiya bakowane role zan iya yi ba.Ba zan yi role ]in da zai jamani zagi ba.

Fim: Kuma ke maifa]akarwa ce?

Hadiza: E! Amma dole induba mutunci. Kuma kar kamanta, mutane da yawa baza su fahimci abin ba.

Fim: Yawanci akan yizargin cewa yawan finafinaida jaruma ke samu ya dogarane a kan ha]in kan da takeba furodusoshi da daraktoci,kuma wannan ha]in kan anayi masa mummunar fassara,ke ma kin gane abin da akenufi. Shin idan aka yi la�akarida irin ]aukakar da kikasamu cikin ]an }an}anenlokaci, ba ki ganin za a iyacewa wata}ila kina bayar dairin wannan ha]in kankenan?

Hadiza: Gaskiya masutunani irin wannan sunaaikata laifi. Kuma ina ganinsuna yi ne kurum dominhassada. Furodusoshin nansuna ba ni fim ne sabodaganin cancantata ga wasanda suke ba ni.

Fim: Daga cikin finafinanda kika yi, wanne ne kikeganin shi ya fito da ke?

Hadiza: Gaskiya ba ni dakamar fim ]in nan Nagari 2da Tallafi. Domin saboda susuka sa har in na wuce sai kaji ana kirana ana cewa,�Yarinya mai mangwaro.�

Fim: Yaya kike ji in anzagaye ki ana �Yarinya maimangwaro�?

Hadiza: A gaskiya ina jinda]i }warai, koda yake wanilokaci abinyakan takura ni.Amma in na yit u n a n i nmasoyana ne,ba na jin komaisai da]i.

Fim: Waneburi kike so kicimmawa awannan harkar?

Hadiza: In zama tauraruwaa wannan sana�a, ta yaddaduk inda aka zauna sai an yimaganata.

Fim: Idan aka ce kikwatanta kanki, wanematsayi za ki ba kan ki?

Hadiza: Idan akwai taurarina ]aya zuwa na biyu to inaganin zan fito a ta uku a in-dustry a halin yanzu.

Fim: Kamar su wa kikeganin suna gabanki? Kilaakwai Fati wadda kika cejarumarki ce. Sai kuma wa?

Hadiza: Gaskiya Fatijarumata ce.

Fim: To yanzu in Fati tatafi kina jin za ki kama kamarmatsayi na biyu kenan?

Hadiza: In Allah ya yarda,insha Allah, ina sa rai dahaka. Ina ro}on Allah ya bani irin basirar Fati.

Fim: Akwai �yan wasa dake ganin kamarfurodusoshi basu biyansuyadda yakamata. Kina dairin wannanra�ayin?

Hadiza: Ni aganina anabiyana kamaryadda yakamata; har

yanzu ba a ta~a ci maniha}}ina ba.

Fim: Kina ganin shirin fimna Hausa na bu}atar gyara?

Hadiza: Idan har za a yigyara sai dai wajen fitowawasa. Wasu �yan wasa sai ace a zo }arfe takwas, wani saisha biyu zai zo. Ya kamata ayi gyara a nan. Sai ka ga a

wani lokacin dole sai ancanza wani ya yi wasan wanida bai zo ba.

Fim: An ta~a canza ki akaba wata matsayinki?

Hadiza: A gaskiya an ta~ayi mani a wani fim, kodayake dai ba wani babban fimba ne, aka sanya watayarinya ta hau role ]inasaboda ban zo da wuri ba.Kuma wallahi na ji haushinabin, amma na ha}ura dominlaifina ne; ni ce ban zo dawuri ba.

Fim: Kukan yi ciniki kafina fara?

Hadiza: E, wani lokacimukan yi ciniki kafin a fara.Idan kuma ba mu yi cinikiba in an gama ku]in da sukeba ni ina ganin sun yi mani.

Fim: To kamar nawa kikanyanke ma kanki ku]i?

Hadiza: (dariya) A gaskiyaba zan iya fa]a a shafinmujalla ba domin abin sirrine.

Fim: A cikin �yan wasamata, da wa kika fi so a ha]aku wasa?

Hadiza: In dai stars ne(manyan taurari), kowa inason wasa da shi.

Fim: Idan ba stars ba ne fa?Hadiza: Idan ba stars ba ne

aka ha]a ka da su akwaifargabar rashin sabawa a yita ]auka ana sakewa (taketwo). Amma in taurari akaha]a ka da su ba za ka yifargaba ba. Kuma akwai}alubale idan aka ha]a ka dastars.

Fim: A maza kamar da wakike so a ha]a ku?

Hadiza: Kamar BaballeHayatu, Ali Nuhu, dasauransu.

Fim: A cikin �yan wasamanya, wanene da kumawacece gwanarki?

Hadiza: A mata, HajaraUsman da Amina Garba. Amaza, ina son wasan suShehu Hassan Kano,Abdullahi Zakari, KabiruMaikaba, IbrahimMandawari, da sauransu.

Fim: Yaya yawantsegunguma a fagen fim, koyana damunki?

Hadiza: To ni ban damu dakowa ba kuma ba na da abokiko abokiyar fa]a. Ina shirida kowa, saboda haka nitsegumin Industry kusan ince ban san shi ba. Munazaman lafiya.

�Ina ro}onAllah ya ba

ni irinbasirarFati�

Page 30: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Fim: Hajiya Tsigai, ahalin da ake ciki, menenera�ayinki game da aure?

Tsigai: Alhamdu lil-Lahi; Gaskiya gara da kayi mani wannan tambaya,domin ka sosa mani indayake yi mani }ai}ayi. Watoakwai wasu mutane da sukezargin cewa wai mata sunashiga harkar fim ne dominsu tallata kansu su samumasu aurensu. To, idan harha}armu za ta cimma ruwa,to lallai mun da]a ]aukakasunnar AnnabiMuhammadu (S.A.W.).Kuma kowa ya tabbatar dacewa, mu abin alfahari nea gare mu, Halisa ta yi aure,Fati Mohammed ta yi aure,

WAKILINMU ALIYU A. GORA II ya da]e yanajuyayin shawarwarin da wasu �yan kallo sukekawowa, wai ya dace Rabilu Musa (Ibro) da

Usaina Gombe (Tsigai) su auri juna. Mun sha jin wannanmagana a wurin jama�a, musamman wa]anda suke ganincewa saboda dacewar da �yan wasan biyu suka yi da juna,to ya kamata Ibro ya cike �ta hu]u,� tunda yanzu uku gareshi, ya sa Tsigai ]aki kawai.

Wani abu da mutane ba su damu da shi ba shi ne, shinmenene ra�ayin su su Ibro da Tsigai, tunda dai ba aurendole za mu yi musu ba? Tsigai dai ta ta~a yin aure, har

tana da �ya�yanta tagwaye. Shi ko Ibro, a gidansa }usurwa]aya ce ka]ai zai kalla bai ga mace ba. Shin ko zai cikewannan }usurwar da abokiyar aikinsa da }ut da }ut, kumamatarsa a fim, wato Tsigai? Wannan tambayar tana cikinran Aliyu A. Gora II a lokacin da ya yi kici~is da Ibro daTsigai a Kaduna a ranar Litinin, 16 ga Yuli, 2001.

Don haka sai ya zaunar da Tsigai, yana so ya ji idan �yana son auren. Bayan sun gama kuma, sai ya kira Ibro shima ya ji ta bakinsa. A fahimtar da Aliyu ya yi, da }yar neauren nan zai yiwu. Ko menene dalili? Ku karanta dakanku ku ji!

A U R E N I B R O D A T S I G A I :

Ban ga abin sha�awa ga Ibro ba,ballantana in aure shi � inji Tsigai

Tsigai: E, to � (dariya) ba su }irguwa, don abin sirri ne!(dariya).

Fim: Kuma daga cikinsu har yanzu ba ki ga wanda ya yimaki ba?

Tsigai: Ka san duniya an ce in za ka yi aure ka auri wandakake so. Amma mu wani lokaci ba haka muke ba. Sai munanan muna ta ro}on Allah Ya za~a mana mafi alheri. Kumahar yau dai a kasuwa nake.

Fim: Yanzu dai ba ki da tsayayye wanda yake son ki daaure kenan?

Tsigai: E, to, haka ]in ne dai. A je a yanda ka cen.Fim: Wane irin mutum kika fi so da aure?

Halima Adamu ta yi aure, sannan Maijidda Abdul}adir ta yiaure.

Don haka, ni zan ce muna alfahari. Kuma da ni da mukejira, daga Hauwa, zuwa Hindatu da na bayanmu duka munafatan insha Allahu ko yau in akwai mai son mu... Don munada wani abu, wasu suna so su auri �yar fim, amma sai su cewai saboda ku]in da kake samu ko irin abubuwan da mukesamu, wai ba za su bari mu yi aure ba. Ba haka ba ne. Mu�ya�ya ne wa]anda sunna ta haifa. Kuma a shirye nake daduk wanda ya zo yau, matu}ar ya yi mani, kuma hankalinmuya zo daidai, insha Allahu zan aure shi.

Fim: Yanzu mutum nawa ne suke son ki da aure?

29

Page 31: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Tsigai: To, sai in ce ma]an�uwa, ni ba ni da za~ia nan. Ni dai na fi sonmutum kamilalle wandazan }aru da shi ta hanyaraddini. Saboda haka Al-lah Ya ha]a ni da mai sonsunnar Annabi (S.A.W).

Fim: Wane hukuncikika yanke game dashawarwarin da jama�asuke ba ku cewa ya kamataki auri Ibro?

Tsigai: A gaskiya nasamu sa}o daban-daban,ba ma a nan gida ba, cewaya kamata in auri Ibro.Kuma ba da da]ewa ba nata~a garga]ar mutane, nagaya masu ni, addininMusulunci bai haramtamu yi aure da Ibro ba,tunda ba uwarmu ]ayaubanmu ]aya ba, kuma bamu sha nono ]aya ba.Amma ni, a tunanina, kaiko a mafarki, gaskiya banta~a tunanin cewa Ibro ]ane namiji ba, balle ma inyi sha�awarsa in aure shi.Kullum ina ganinsa a]an�uwana ne na jini. Ara�ayina ni dai ba ni dasha�awar mu yi aure. Dasekan ]ayan kuma banta~a ganin wani abinsha�wa a gunsa da yaburge ni ba. Don in na gamace ma tana son Ibro saiabin ya ri}a ba ni mamaki,in ce me ta gani a jikinsa?Ta ]auka shin namiji neshi Ibro?

Don ni ina ganinsakamar dai alal misali}awata ce kawai; niganinsa nike mace kawai.Ban ga wani abin sha�awaa jinkinsa wanda ya burgeni ba, illa ta fannin sana�ada �yan�uwantaka.

Domin ni, zan ce�yar�uwarsa ce, }awar shice, ina shiga gidajensa, insame shi har wurinmatansa. Iyalanshi dukamukan zauna mu yishawara don magancematsalolin da kegabanmu. Don haka niban tabbatar da cewa Ibro]a namiji ba ne wanda harzai ba ni sha�awa ko dazuwa nan gaba mu yi aure.Don na ]auke shi mace ne�yar�uwata.

Fim: To, MalamaTsigai, mun gode.

Fim: Ibro, akwai watadangantaka ce ta musammantsakaninka da [an�azumi Dafe-Dafe. Ganin yadda ka fiye sonzuwa ka yi wasan da~e a gidansana wasan gargajiya da ke nanKaduna, wato Marhaba?

Ibro: E, kusan in ce,dangantakar da ke tsakanina dashi, dangantaka ce wadda tunmuna }anana muka taso. Kumani kusan ma in ce a Kaduna babuwanda muka sani da tarar jama�acikin raha da fara�a irinsa. Kasan Hausawa sun ce shimfi]arfuska ya fi shimfi]ar tabarma.Ai mutumin da zai zo ya sakifuskarsa ku yi fara�a, shi ne yakamata a ce ka saurara.[an�azumi, tun muna }anana,tun ma kafin mu fara harkarkaset, muke tare da shi. Sabodahaka mu a Kaduna, in dai wasane a dandamali, babu wani wurida za mu je in ba wajen[an�azumi Dafe-Dafe ba.

Fim: Kasancewarka }wararre,fitacce, kuma shahararren ]anwasa, kana ganin lokaci bai yiba na daina wasan dandamali,ka tsaya ga fim kawai?

Ibro: A�a, ai ni ban wuce ba.Domin wasan dandamali ]innan ma ni na fi ji da shi a kanwasan kaset ]in. Wasan kaset aiana yi ne don kyautata wa wasu.Amma in kyautata wa kaina ne,to na fi son wasan dandamali.

Fim: Me ya sa ka fi son kashirya finafinai a kan rayuwar}auye, maimakon ka ri}a ta~ozamani?

Ibro: Hauwasa sun ce, kayanaro abin banza ne, duk ranar damai abin ya kar~i abinsa, to dolene ka koma naka. Duk wandaya ce ba shi da }auye, yana ]ankaruwa ne. Amma muwasanninmu da muke yi na}auye, duk wanda ya ce bai yimasa ba, nake gaya maka, to saidai in ]an karuwa ne. Amma ina birnin aka kaife ka, ka tambayiina }abarin kakanka yake, za kasame shi a }auye. Saboda hakamu wa}e-wa}en nan da wanitsukewa ni ba zan iya ba. Dominwannan tun kafin in taso nikeganin Indiya ne suke yi, su Ca-nis. To ni ko ]an Nijeriya ne,kuma ]an Kano. Saboda haka

me zai kai ni in aro abin dawani yake yi? Ni nawa nakeyi. Abin da iyayena na ga suntaso a ciki shi nake bi. Kumaina nan a kan bakana. Idanna ce zan yi na birnin zaniya; ba wai iyawa ne ban iyasa siket da �yar riga, mu yiwannan na }aryar da ake yi.Saboda haka mu dai munanan a kan bakanmu.

Fim: Ganin yadda kukasha}u da Tsigai, akwai watawadda kake ganin za ta iyamaye gurbin Tsigai, idan amisali (abin Allah ya kiyaye)Allah Ya kawo rabuwarku daita?

Ibro: E, to, ba zan iya cewakomai ba. Amma dai ka sanba za ka ja baka ba kibiyaba. To haka muke da Tsigai.

Fim: To yanzu misali idanrabuwarku da Tsigai ta zo, zaka bar wasan kwaikwayo ne,ko ko za ka samo wata ne kuci gaba da yi tare?

Ibro: Ana yi. Akwaifinafinan da na yi ba ita ma.Ana yi ko ba ta nan, da yaketana yawan tafiye-tafiye, koba ta nan ana yi, ba wai yi neba a yi ba. Amma in daizunzurutun wasan ake so, to

a same ni, ni da ita.Fim: Shin za ka iya auren

Tsigai?Ibro: (dariya da mamaki)

Tsigai? Em� kai, ai niTsigai ban ga abin sha�awa ajikinta ba. Ni fa, Allah, da inasha�awarta da tuni na aureta. To ni ban ga abin sha�awaba, ni wanda ma ya tsaya daita yana zance sai in ga shime yake so � sai ya zamama abin kallo a wurina. Meya gani? Allah�. Wallahi,wallahi ko wani ne na ga tatsaya da shi har kallon shinake yi in ga shi me ya kallaa jikinta ne na sha�wa?Wallahi!

Fim: To amma yanzu kanada wata shawara da za ka baita Tsigai a kan aure?

Ibro: E, ai kullum munanan, ka san abu ne daga Al-lah. Kullum muna nan munayi mata addu�ar Allah Yakawo mata nagari.

Fim: Kana nufin kenanyanzu Tsigai ba ta da wandayake nemanta da aure?

Ibro: Akwai. Ai ko daakwai ai dole ka yi addu�aAllah kawo nagari.

Fim: To Ibro mun gode.

Ban ga abin sha�awa ajikin Tsigai ba � inji Ibro

30

Page 32: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Fim: Mutane za su so su jidalilin dawowarki harkar fim.

Halima: To ni yanzu bansan abin da zan ce maka ba,tunda da ma ko wa ya san nia kan harkar nan ya san ni.Yanzu a ce don aurena yamutu kuma na dawo, atambayi wani dalilin da yasa na komo? Kowa dai ya sanyadda harkar fim take; in daimutum ba aure ya yi ba, yanazaune kawai, ba fa yadda zaa yi a ce ba zai ]an ta~a shiba, ko ba da yawa ba ne; koya yake dai a ta~a.

Fim: Me ya sa ba ki barihar yaron da kika haifa ya yi}wari ba tukuna?

Halima: Wannan wani abune daban kuma. Yaro in dailafiyayye ne ai magana tariga ta }are. Kuma yanzu maai ya yi }wari.

Fim: Ko iyayenki sunamince ki koma harkar fimyanzu?

Halima: Sai da na tambayimahaifana. Amma akwai dayawa wa]anda muke abinarziki da su da suka ce kar inkoma. Amma za a ga kamar

ko ban yarda da shawararsuba ne. Kuma ba haka ba ne.Kowa shi ya san abin da yakedamunsa. Shi ne kawai ya sa.

Fim: Me mahaifin Al-Amin ya nuna da ya ji cewakin fara yawo da shi kinashirya fim?

Halima: Wannan maganace daban. Wannan ma ba tataso ba. Don kuwa in da agidansa nake sai ya hana nifita unguwa da shi?

Fim: Idan ta kama anabu}atar jinjiri don yin fim,ko za ki iya sadaukar da shia yi fim da shi?

Halima: Al-Amin ba naHalima ba ne ita ka]ai;ubansa yana da ha}}i akansa, ni ma ina da ha}}i akansa. Kuma ko me zan yi,in dai a kan kansa ne, dole innemi shawarar babansa. Bani da ra�ayin wai in hana Al-Amin yin wasa. Amma sai fada yardar mahaifinsa, tundani in ta ~angarena ne maganace mai sau}i. Amma idanbabansa ya yarda zai iyazuwa ya yi kowane irin fimda aka gayyace shi ya je yayi.

Fim: Ya zuwa yanzufinafinai nawa kika yi tun da

kika yada wankakika dawoharkar fim?

Halima: E, toka ga yanzu mashirin da nake yi�location� zanfita (wurin]aukar fim). Inda ka kai mawajen }arfegoma ba za kasame ni ba.Akwai wani fimda mu ka yi (maisuna) Sassarfa afarkon wannanwatan. Akwaikuma wandamuka yi� ba suma sa masa sunaba, ko kuma daina ce ban tsaya

Halima ta dawo ruwa, ta ce ��Al}awarin Allah ba ya tashi!�

K UN dai san ta; ba ta bu}atar wata doguwargabatarwa. Kamar jiya-jiyan nan ne muke tare daita a fagen shirin fim na Hausa. Sai ta zo ta yi aure

ta tafi.A lokacin da HALIMA ADAMU YAHAYA ta yi aure a

cikin watan Yuli 2000, kowa ya taru ya taya ta murna.Rugun]umin bikin ne aka ri}a tunawa a lokacin bikinFati Mohammed na kwanan nan. Babu wanda ya yitunanin }addarar da ke gaba. Amma kash! sai auren naHalima ya mutu a cikin watan Nuwamba 2000, abin yakasance kamar wasan yara. Sai dai kuma kamar yaddakuka karanta a wannan mujallar, Halima ta fito da ciki ]anwata sama da wata biyu. A Fim ta watan Disamba 2000 harmuka rubuta cewa, �Wakilan wannan mujallar sun yilissafin cewa kafin Halima ta dawo fim sosai, sai can cikinshekarar 2002.� Dalilinmu shi ne mun ga za ta yi goyonciki, ta yi reno har ta yaye, kafin ta koma fim tunda shi nesana�ar da ta fi sani.

To, Halima dai ta nuna mun yi kuskure domin kuwa ayanzu har ta koma harkar fim. Cikin �yan watanni biyu kouku da suka gabata ta shiga finafinai da ]an dama,wa]anda za su fito nan gaba ka]an. Kuma tana cikinshirya wasu.

Fitacciyar �yar wasan, wadda ta ci gasar �Best Actress� abikin ba da kyaututtukan finafinai na Arewa a bara, tahaifi Muhammad Al-Amin a }arshen watan Mayu na bana,wato yanzu watanninsa uku da �yan kwanaki. A lokacin damuka yi wancan tsokaci a cikin Disamba, mun ]auka saita yaye shi sannan ta nemi abin yi. To amma kamar yaddata ce a wannan hirar da suka yi da wakilinmu HAMISUMOHAMMED GUMEL, duk da yake akwai wasu abokanarzikinta wa]anda suka ce mata kada ta koma harkar fimamma �kowa shi ya san abin da yake damunsa.�

Wani abu da muka lura da shi shi ne har yanzu Halimatana da farin jini a gun furodusoshi da daraktoci, dominhar sun fara rububinta. Su kansu masu kallo za su so ta neidan ta yi masu yadda suke so a fim. To tunda ko}warewarta ba ta yi rauni ba (a siffa da murya tana nanyadda take), ga alama za a }ara damawa da Halima AdamuYahaya a cikin watanni masu zuwa a fagen fim, kafin ta yiwani auren kenan.

na ji sunansa ba, tun da iya�scenes� ]ina kawai na je nayi. Sai kuma Miras. Sai kumawani D.P.O., amma sunashirin canja masa suna.

Fim: Su kenan ba wasu?Halima: A�a, ba wasu, sai

dai nan gaba.Fim: Kwanan baya kin je

Jos inda kika yi kwanaki.Shin wane fim ne kika yikuma da sanin uban yaronkikike yin doguwar tafiya irinwannan da shi?

Halima: Ku ina ruwankuda zancen mahaifin yaro?Halima kuka zo magana daita kuma a kan Halima za kuyi magana. Ba ruwana dababan yaro!

Fim: Da saninsa kika tafi?Halima: A�a, mijina ne shi

yanzu da zai san in zan yitafiya?! Da a gidansa nakeshi ne wannan sai da izininsazan yi tafiya. Amma yanzuba a }ar}ashinsa nake ba.Saboda haka menene sai naje na tambaye shi don zan yitafiya?

Fim: Ma�ana, ya san kinatafiya da yaron?

Halima: To duk inda uwaza ta ai dole sai da ]anta ko?Da ma an yaye shi ne, shi ne

Halima Adamu Yahaya

31

Page 33: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

wannan za a iya barinsa agida. Amma duk inda uwa zata ai sai da ]anta za ta tafi.

Fim: Wasu na cewa in sune Halima ba za su dawo fimba. Me za ki ce wa masufa]ar wannan kalami?

Halima: Su me ya sa masucewar in su ne Halima sukafa]i haka? Sai a tambayo sutukuna sai in ba da amsa.

Fim: Wane bambanci kikafara fuskanta a wurin ]aukarfim da ma gaba ]ayan harkarfim sa~anin lokacin da kikekafin wannan auren da yamutu?

Halima: To gaskiya ni daiban ga wani bambanci ba.Bambanci ]aya na gani kozuwa biyu. Da, yawan gutsiri-tsomar da ake yi, a yanzukamar na fuskanci haka ya]an ragu ka]an. Saboda muda a lokacinmu ba mu daha]in kai. Amma ka ga yaranyanzu da suke cikin harkarfim suna da ha]in kai sosaida sosai, ba kamar irinmu ba.Kuma ko da irin gulmar waniza a kawo, wato za ta iya tashi� a �yan set ]in yanzu fa, tayi uwa ta yi makar~iya ta ceto wallahi ba ta yarda ba,saboda suna aminci dawaccan. Kawai daibambancin da ake samukenan, amma ni ban ga wanibambancin abu ba. Sai daida yake ka san duk abin damutum ya da]e bai yi ba dolezai ]an ji ba kamar yaddayake da ba.

Fim: Kina jin za ki iyamaimata tashen da kika yican baya kafin ki yi aure?

Halima: Wannan kumawani nufi ne na Allah, tundakamar mace ce take da ciki,ba ta san abin da za ta haifaba. To komai Allah Ya nufizai faru, saboda al}awarinAllah ba ya tashi! Amma koban yi tashe yanzu ba, ai nayi da. Kuma alhamdu lillahi,abin da nake so na riga nasamu.

Fim: An sha rubuto mikiwasi}un jaje na mutuwaraurenki. To yanzu ko kin faratunanin sake yin waniauren?

Halima: Me zai hana! Aurene fa ya haife ni, kuma sai ince ba zan yi aure ba?

Fim: To Halima mun gode.Halima: Godiya nake ni

ma.

WA{AR TA�AZIYAR A.H. YAKASAI (DIRECTOR)

Allahu Akbar duniyaAllahu Akbar rai da zuciya

Allahu Akbar Aminu Hassan me sanayyaDuk mai rai dole ya zamto matacce matacciya

Haka Rabbi ya }addara wa halittun duniyaDuniya zancen banza mai tumfafiyaKin haifi soyayya da }agar }iyayya

Yau ga shi kin raba mu da darakta abin biyaMai haba-haba da kowa har mai Izaya

Tubalin shirya fim Kano birniyaKwandon hikima mai ]iban ruwa da gayya

Dogo mai fararen aniyoyar ci-gaban Nijeriya.*

Yanzu shikenan ka tafiGaninka sai ko a mafarkin duniya mai dafi

Ko kuwa hotonka mai kyan sa ai tafiAllah ka gafarta wa Aminu Hassan ba haufi

Ka yafe kura-kuransa na zafiKyautata makwancin bawan Allah, li-Ilafi

Allah kyautata makwancin Maijidda Mustapha ta tafi.

Daga IBRAHIM B. LAWAN DIRECTORNo. 134, Tudun Wazirci, Kano.

WA{AR MUJALLAR FIM

Tandun labarai Mujallar Fim tsaf da keNisha]antau kike, Fim sumul da ke

Idaniyar masoya Fim, tar da keKin wuce mota jirgi wane keke

Ibro Sheme lallai ka yi dariya.*

Fim fatanya uwar nome kalmomin Hausa[as kika zauna a gadon cin gasaKin tsaro labari kamar ma lasa

Kina ta nisha]antar da B. Lawan Director maci masa Ah lallai kya yi fahari a duniya!

Kin zubo labari tamkar kina santiA lokacin shan dage-dagen Kanawa �yan a-ci-bati

An ce a Zazzau ma har takardinki ake ci santiKo ko su ji}a sunanki su sha a fati

Abdulkareem Mohammed ya yaba miki da aniya.*

Fim, saki jikinki ki rangwa]aIdan kin so ma ki tafiya da yau}i da ga]aKi shewa da gwalli don ba ki da mara]a

Tunda dai Tijjani Ibrahim ya ba ki yabo sa]a-sa]a Wallahi kina burge mu nan duniya.

*Ku sha kuruminku makarantan gabas da na yammaFim na nan da zaratan ma�aikata }arfinsu ya tama

Labarin Bankaura, Wasila ta sha dumaManya Lere, Mandawari waye ya fi dama-dama

Fatan alheri gare ki Fati, maya maya.

Daga IBRAHIM B. LAWAN DIRECTORNo. 134, Tudun Wazirci, Kano.

32

Page 34: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

L A B A R A I

shahararren fim ]in nan mai sunaLaila, ta bayyana rashin jinda]inta game da yadda ake yi wamatan da ke fitowa a finafinanHausa na zamani kallon marasamutunci duk kuwa da cewa baduka ne aka taru aka zama ]ayaba. Don haka ta yi kira ga jama�ada su ri}a yin adalci wajenfayyacewa tsakanin �yan wasamasu mutunci da �yan wasamarasa mutunci.

FIM wata babbar hanya ce daake amfani da ita wajen

fa]akar da jama�a tare dailamantar da su kan al�amuransuna addini da kuma al�ada da sukashafi halin zamantakewar duniya.

Fitacciyar �yar wasan HausaAina�u Ade ita ce ta yi wannanbatu yayin da take zantawa dawakilinmu a kwanakin baya. Tace koda yake ra�yinta ne ya sanyata fa]a harkar fim, amma dagabisani ta fahimci irin rawar da�yan wasan ke takawa wajenfa]akar da al�umma kan wanimahimmin abu da ke ya]uwa acikin al�umma.

Ta ba da misalin wanimagidanci wanda matansa biyukullum a cikin tashin hankali dajuna suke. Amma bayan matansun kalli fim ]in nan mai sunaAljannar Mace, sai suka sasantada juna suka koma suna zamanlafiya kamar yadda suka faro afarkon zamansu tare. Ta }ara dacewa wannan yana }ara tabbatarda muhimmanci da kuma tasirinfinafinai a cikin mutane,musamman matasa.

Aina�u, wacce ita ce jarumar Aina’u Ade

Fim yana gyara al’umma– inji Aina’u

Daga BASHIR YAHUZA,a Katsina

{UNGIYAR MataMarubuta ta Nijeriya

(Women Writers Associationof Nigeria), reshen JiharKatsina, ta karrama wasumuhimman mutane uku da}ungiyoyi, cikinsu har daMawallafin mujallar Fim,Malam Ibrahim Sheme. Awani gagarumin taro damatan suka ha]a a zauren tarona Hukumar Al�amuran Matada ke Filin Samji a Katsina,a ranar Talata, 24 ga Yuli,2001 ne aka rabakyaututtukan da }addamarda sabuwar mujallar}ungiyar.

Sauran mutum uku da aka

karrama su ne matarGwamnan Jihar Katsina,Hajiya Turai Umaru Musa

�Yar�aduwa, da warafitacciyar mace, HajiyaMurjanatu Katsina.Kyaututtukan karramawarda }ungiyar ta ba mutanenuku wata kyakkyawargarkuwa ce da aka sassa}a,aka ]an]ashe ta da tambarin}ungiyar.

Haka kuma an ba wasu]alibai mata kyaututtukanda suka lashe, a sakamakongasar insha�i da }ungiyar tasa wa makarantunsakandaren mata na JiharKatsina. An ba Sa�adiyaKamil Hassan ta G.G.T.C.Charanci kyautar ta ]aya, saiHafsat Aminu ta G.G.C.Katsina, da Umma SaniAbdullahi ta G.G.S.S.Shargalle, wa]anda aka bakyaututtukan satifiket.

Tun da farko, taron yasamu halartar manyanmutane maza da mata, cikikuwa har da shugaban taro,Mai Girma GaladimanKatsina, Mai Shari�aMamman Nasir, da kumawakiliyar matar GwamnanJihar Katsina, Hajiya MariyaAbdullahi (KwamishinarAl�amuran Mata).

A wajen taron, wanda akafara da misalin }arfe 11 nasafe, an gudanar damuhimman jawabai najaddada muhimmancin

An karrama mawallafin mujallar Fimda matar Gwamnan Katsina

ilimin mata.Wakilinmu ya tattauna da

shugabar }ungiyar, MalamaTalatu Wada Ahmed, inda tabayyana dalilan da suka sasuka karrama wa]annanfitattun mutane guda uku,inda ta nuna cewa, sun bamatar gwamnan Katsinawannan kyauta ne, sabodala�akari da yadda take }arawa mata gwiwa wajen bi]arilimi. Sannan ta nuna cewasun karrama Ibrahim Shemene saboda kasancewarsagwarzon ]an jarida, kumamarubuci, sannan mawallafi,wanda ya da]e yanataimakon al�umma,musamman mata, inda yakeagaza masu wajen wallafalitattafansu.

Shi dai Sheme, ya da]eyana agaza wa matamarubuta, musamman tahanyar wallafa littattafansua kamfaninsa �InformartPublishers,� da kuma bugahirarrakinsu a jaridu irin suWeekly Trust inda a yanzuyake da shafi biyu a dukJumma�a a matsayinsa naeditan adabi na jaridar.

Ita kuwa HajiyaMurjanatu Katsina, TalatuWada ta ce sun karrama ta nesaboda kasancewarta mace tafarko da ta fara aikin jarida aKatsina, kuma mace ta farkodaga Arewacin Nijeriya da tafara aikin jarida a }asashenwaje. Hajiyar ta ta~a yin aikia gidan rediyon MuryarAmurka a Washington D.C.

Haka kuma, duk dai awurin wannan taro, }ungiyarmarubutan ta }addamar dasabuwar mujallar rubuce-rubuce mai suna WRITAGears, inda babban mai}addamarwa, AlhajiAbdurrahaman [anmalam([an Madamin Daura) yataimaka da N100,000. Shi maMalam Ibrahim Sheme ba abar shi a baya ba; ya sayikwafe biyar na mujallar akan N5,000.

An kammala taron lafiya.

Hajiya Talatu Wada Malam Ibrahim Sheme

33

Page 35: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

L A B A R A I

Daga BASHIR ABUSABE,a Sokoto

A RANAR Laraba, 1 gaAgusta, 2001, aka sake

bu]e katafaren kantin saidafinafinai ]in nan na �MutunciVideo Complex� da ke Sokoto.Wannan ya biyo bayan gamagyaran Titin Sultan Abubakar acikin garin da aka shafe tsawonwatanni ana yi.

Babban manajan wurin, AlhajiAminu Mutunchi, ya shaida wamujallar Fim cewa an sake bu]ewurin ne sakamakon kiraye-kirayen da jama�a abokanhul]arsa ke yi ne. �A wannankaron mun dawo domin muwadatar da abokan hul]armu daingantattun finafinai iri-iri,� injishi, ya }ara da cewa da ma daiabokan hul]ar tasu sun san suda ingantattun kayayyaki.

Shi dai �Mutunci VideoComplex,� wanda yake da rassaa warwatse a cikin birnin naShehu, ya shara wurin sayar dafinafinai. Wani mutum dawakilinmu ya yi kici~is da shi

yayin da yake fitowa daga shagonya shaida wa Fim cewa mutaneba su ji da]i ba lokacin da akarufe shagon a kwanakin bayadomin kuwa nan ne wurin dasuke samun kasa-kasai da ]umi-]uminsu, �sannan ga su danagarta.� Mutumin wandadarakta ne a wata ma�aikta, yace, �Musamman yadda aka tsarashagon ya yi daidai da na zamani,kuma mu �yan boko za mu ji da]isaboda su kansu tsari da tsaftasuna da fa�ida a kowane lamarimutum yake yi.�

Wasu matasa kuwa da sukehul]a da �Mutunci VideoComplex� sun nuna jin da]insuda sake bu]e wurin domin, acewarsu, bayan rufe wurin saisashen ya yi tsit, amma yanzunhidima ta dawo �as normal,�kamar yadda ]aya daga cikinsu

Kantin ‘Mutunchi Video Com-plex’ ya dawo a Sakkwato

ya ce. Mutane da dama sun yabada irin yadda kantin yake gudanarda ayyukansa wajen kawofinafinai da ]umi-]uminsu.Wasu da suke fa]ar albarkacinbakinsu sun ce, �Kai ka ce aKano ]in kake!� Wani mai kallonfinafinai ya ce, �Lallai AlhajiAminu Mutunchi ya mutunta mu,mu Sakkwatawa, da ya samarmana da wurin sayen finafinaina zamani mai mutunci.�

A nasa ~angaren, AlhajiAminu Mutunchi ya yi kira gafurodusoshi da su tabbatar dasuna yin finafinai masu ma�anada koyar da tarbiyya tagari �bawanda za ta }ara dagula al�amuraba.�

Saura da me? Jama�a na nansun zuba ido su ga fitowar fim]in da aka ce Aminu Mutunchina shirye-shiryen yi.Alh. Aminu Mutunchi

Daga MUHAMMEDE NASIR,a Kano

{UNGIYAR wasan Hausa tagarin Rurum da ke cikin

{aramar Hukumar Rano ta JiharKano, ta bi sahun }ungiyoyimasu karrama mujallar Fim.{ungiyar, mai suna �DashereYouth Dramatic and CulturalAssociation,� ta bai wa mujallartakaradar shaidar lambar yabo(Certificate of Award) sabodaabin da }ungiyar ta kira �wayarda kan jama�a da mujallar fim keyi.�

Da yake mi}a kyautar yabonkwanan baya, sakataren}ungiyar, Malam MuhammadSani Isma�il, ya bayyana cewa,sun ba Fim kyautar ne �ganincewa babu wata mujalla ta Hausada mutum zai karanta ya ji yagamsu da sa}on da ake sonisarwa kamar mujallar Fim.�Wannan, inji sakataren, ya nunacewa ba }aramar gudunmawamujallar ke bayarwa ba wajenwayar da kan jama�a ba.�

Malam Muhammad ya }ara dacewa ba Fim ce ka]ai suka

karrama ba, domin }ungiyar tasuta karrama shugaban {aramarHukumar Rano, Alhaji LawanShu�aibu Rurum, da kuma wanikansilansu mazaunin Kano maisuna Alhaji Abdulkarim[an�asabe.

Shi kuwa sakataren ku]i na}ungiyar, Malam SulaimanAlhassan Tata, ya bayyan a cewa

Al�ummar Rurum sun }ara karrama mujallar Fimko shakka babu daga ]an abinda suke karantawa a mujallar Fim,�Babu abin da za mu iya cewasai dai kawai muna alfahari daita.�

An dai kafa }ungiyar wasanHausa ta Dashere shekaru ukuda suka gabata. Tana gudanar dawasannin da~e na al�adu. Ta ta~awakiltar {aramar Hukumar

Rano a wasannin al�adu na }asa.Da yake kar~arsu, Mataimakin

Edita a lokacin (editan mujallarBidiyo a yanzu), Malam AshafaMurnai Barkiya, ya yaba dahangen nesan da }ungiyar ta yihar ta tuna da mujallar Fim. Yakuma gode wa }ungiyar amadadin mawallafi da sauranma�aikatan mujallar baki ]aya.

Ashafa Murnai barkiya yana karbar kayutar daga hannun Muhammad Sani Ismai’il

34

Page 36: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

L A B A R A I

Miji da mata sun du}agaban }uliya saboda fim

Fatima Ahmed

Daga MUHAMMED NASIR, aKano

A RANAR 25 ga Yuli,2 0 0 1 ,

wani mutum mai sunaMalam Ahmed Abdullahi yaaika da wata takarda cikinharshen Turanci zuwaofisoshin furodusoshin fimda ke Sabon Titi, Kano.Kanun takardar shi ne:�Not i f i ca t ion /Warn ingRegarding Fatima Ahmed(Mrs.),� wanda in an fassarashi shi ne: �Garga]i Game daFatima Ahmed (MatarAure).� Wasu daga cikinbayanan da takardar ta }unsasun ha]a da cewa:

1) �Fatima Ahmed mataraure ce daga unguwarBadawa cikin Kano a{aramar HukumarNasarawa.�

2) �A ranar 30 ga Afrilu,2001, Fatima ta gudu dagagidana ta koma gidankawunta. Bayan kwana 20sai na ri}a jin ana ya]a ji-ta-ji-tar cewa wasu furodusoshisun fara yin fim da ita.�

3) �A bisa dukkan alamuwani ~ata-gari ne ya yaudarimatata Binta (Fatima) don taje ta yi fim tun tana gidana.�

4) �Ta bar gidana bayanmun yi haihuwa biyar tare,kuma �ya�yan suna nan tagudu ta bar mani.�

Takardar ta ci gaba dacewa mijin matar, watoAhmed, ya yi bincike aSabon Titi, har ya gano anfara saka ta a fim. A kan hakane yake garga]infurodusoshi da cewa Fatimamatarsa ce, kuma wanda dukya saka ta a fim har fuskarta

cewa ba shi ne ya ]aura aurenba, Sheikh AminuddeenAbubakar ne. Da akatambayi mai unguwa koyana da masaniyar aurenyana nan ko ya mutu, sai yace, �Ai shekarun da da]ewalokacin da aka yi auren. Nadai san suna rikici.�

Wani bincike da Fim ta yikuma ya tabbatar da cewaFatima ta je kamfanin shiryafinafinai na �Iyan-TamaMultimedia�, ammamanajojin ofishin suka }ikar~arta har sai da ta kawotakardar amincewa dagaiyayenta. Furodusa AhmedEl-Kanawy na kamfanin yace, �Bayan sun aiko takardariyayen nata, su uku sun zohar nan ofishin suka nanatamana cewa ]iyarsu ba ta daaure kamar yadda ita ma tashaida mana cewa bazawarace, ta ta~a yin aure har da �ya�ya biyar.�

Sai dai kuma lokacin daFim ta tuntu~i MalamAhmed Abdullahi, ya }arananata cewa shi har yanzubai sake ta ba, gudu ta yi takoma gidan kawunta. Kanbatun wasi}ar da iyayentasuka aika wa kamfanin �Iyan-Tama� kuwa, Ahmed ya ce aiwannan wasi}a (waddamujallar Fim tana dakwafenta) cike take dakurakurai domin wani MistaOcito ne ya sa mata hannu,ba mahaifinta Mista Fridayba. Ya kuma yi tsokaci dacewa wani kuskuren da kecikin takardar shi ne, yaddashi Ocito ya kira Fatima dala}abin �Miss,� wato waddaba ta da aure.

Ana wata kuma sai gawata; yayin da shi Ahmed ke

ta fito a akwatin talbijin, toya shirya amsa tambayoyi agaban al}ali. An nuna cewaan aika da takardar gahukumomin gwamnati dafadar Mai Martaba SarkinKano da Majalisar Malamai.

Wannan takarda ta fa]o ahannun mujallar Fim a ranarda aka raba ta. Ba tare dawani ~ata lokaci ba, saiwakilinmu ya fara bincikenwannan bahallatsa. Bincikenfarko da ya yi, ya nuna cewaAhmed mazaunin unguwarBadawa ne a gida mai lambaWB/NZ/BD/094. [an asalin{aramar Hukumar Bakori taJihar Katsina ne wanda aunguwarsu aka fi saninsa daA.A. Yana aiki ne a bankinU.B.A. da ke lamba 14 kantitin Abdullahi Bayero, cikin

da mujallar nan ta tsinci ra]e-ra]in cewa mai unguwarBadawa ne ma]aurinaurensu, wakilinmu ya yitattaki zuwa wurin maiunguwar, Alhaji Idris Jawa.

�Yalla~ai ya fara bayyanacewa lokacin da Fatima tamusulunta, wurinsa ta farazuwa amma sai iyayentasuka nuna rashin yardarsu data auri A.A. �Da na ga iyayensun ]auki lauya, sai na ceabin ya fi }arfina, sai daikotu,� inji Alhaji Idris Jawa.A ta bakinsa, an yi ta tafkashari�a a kotu inda daga}arshe al}ali ya hukuntacewa Fatima ta auri Ahmed]in kamar yadda takebu}ata.

Sai dai a nan Mai UnguwaJawa ya yi wa Fim matashiyar

35

Shin Fatima Ahmed ta shiga harkar fim bayan mijinta ya sake ta, ko kuwa dai haryanzu tana da aure? Al}ali ne zai raba gardamar

r u k u n i nke~antattung i d a j e nNassarawa.

A h m e dya ha]u daM a l a m aFatima al o k a c i nt a n ab u d u r w a .�Yar asalin} a b i l a rKalaba ce.Sunanta naainihi shi neEkaete. Tamusuluntan esanadiyyarha]uwarsuda Ahmed,suka yial}awarinaure.

Lokacin

Page 37: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

L A B A R A I

barazanar yin shari�a da dukfurodusan da ya saki fim]insa a kasuwa da Fatima aciki, sai ita kuma Fatimar tamaka shi a kotu tana cewaya sake ta ya hana ta�ya�yanta. A ranar 29 gaAgusta ne aka aje za a farasauraren }arar a babbarkotun �Yankaba.

Wani bincike na mujallarfim ya nuna cewa Fatima tata~a zama memba a }ungiyarwasan Hausa ta �DaboDramatic Association� da keGwammaja, Kano. Hakakuma binciken ya nuna cewata yi finafinai sama da gudabiyar wa]anda ba su fito batukuna. Wata majiya a �Al-Muhossen Film Production�ta furta cewa matar ta fito acikin wani fim nasu wandabai shiga kasuwa ba haryanzu. A fim ]in, mai sunaMungunta, Fatima ta fito amatsayin jerin zugar �yanrawa. �Ba wai wani role maiyawa ta yi ba,� injimajiyarmu.

Mujallar Fim ta nemi jinta-bakin mahaifinta Fatima,wato Mr. Friday, ba a sameshi ba. Amma matarsa, waddata shaida wa wakilinmu cewaba ita ce mahaifiyar Fatimaba, ta bayyana cewamahaifiyarta na can garinsua yankin Kalaba. Dawakilinmu ya tuntu~e ta kanko akwai igiyar aure yanzutsakanin Fatima da Ahmed,sai ta kada baki ta ce daburokan, �If e no divorce amhow e go fit park her kayacomot from hin house?�Ma�ana, idan bai sake ta ba,to ta yaya har ta kwasokayanta daga gidansa? Daganan sai ta ce ba za ta }aracewa komai ba sai dai mijinta.

Tuni dai ta kwashekayanta daga gidan Ahmedtun bayan kwana biyu daAhmed ]in ya raba wafurodusoshi takardar jankunne. Wata}ila kuma dongudun kada ta kwashe�ya�yanta daga gidan, sai shiAhmed ]in ya kwashe su yakai }auyensu A/Kanawa dake Jihar Katsina. Ita kumatana }alubalantar hakan daya yi. Ga alama, kuma kotuce ka]ai za ta raba wannanmatsananciyar gardamar.

36

N EMAN MalamaFatima Ahmed ba shida wuya, amma

katarin ganinta tamkarneman }wandala ne a cikin}ai}ayi. Bayan wakilinmuya yi nema ya gaji, sai yasake jaraba sa�a. RanarLahadi, 26 ga Agusta, ya sakekomawa unguwarsu Badawada ke }arshen Kano ta fuskargabas. Sallama da mahaifintawakilinmu ya yi, maimakona koma a kira Mista Friday,sai kawai ya ga wata mata tafito. �Ina ganinta sai na yiajiyar zuciya kuma nawangale baki ina fara�a donna ha]u da abin da nakenema ruwa a jallo,� injiwakilin namu.

Ba tare da wata-wata bakuwa, bayan sun gaisa sai yakama aikin da ya kawo shi:

Fim: Fatima mun samikwafen wata takarda damijinki Ahmed ya raba wafurodusoshi. Ko kin san daita kuma kin karanta ta?

Fatima: Na san da ita,}warai kuwa.

Fim:A ciki ya ce ke haryanzu matarsa ce bai sake kiba. Shin menene gaskiyarwannan batu?

Fatima: {arya yake,babu aure tsakaninmu. Illaiyaka kawai ba ya so in yifim don ya ga muna da �ya�yani da shi. Ni kuwa na ga tundaba ku]i gare ni ba kuma basana�a nake yi ba, kuma bawani mai ba ni gare ni ba, shiya sa na yanke shawararshiga fim don in ri}a samun�yan ku]in kare wasumatsaloli, tunda ni dai baiskanci zan je in yi don insami ku]i ba. Shi ya sa nashiga fim.

Fim:Da ya sake ki ]in, yaba ki takardar saki?

Fatima: Ya ba nitakarda, kuma sadakin da yabiya na aurenmu ya kar~iabinsa.

Fim: Na wane ku]in

*

TM

M

ac}scYntkskFimff}hA

akfaHmzw

kmAkHYmKmk<ykr

A

GBBP0

AktwtA

sadakin?Fatima: N5,000 ne.Fim:To ga shi Ahmed shi

yana cewa bai sake ki bakuma�

Fatima: (ta katsetambayar) Kai bari ma ka ji,ni ce fa na yi }undumbalarauren nan. Don Saboda inaure shi na sa~a da iyayenada dangina. Kai har bugun}irji na yi na kai iyayena}ara, su kuma har lauyoyisuka ]auka.

Fim:An ce bayan an bugaa kotun Gwagwarwa saial}ali ya ba da izinin a ]auramaku aure inda SheikAminuddeen ya ]aura auren.Haka ne?

Fatima: W a n n a nmaganar akwai gyara. Akotun �Yankaba ne, kuma shial}alin ya ]aura mana aureba Aminuddeen ba.

Fim:Yanzu kuma kin kai}ararsa a kotun �Yankaba.Shin kan wane dalili?

Fatima: A kan yana~ata min suna da kuma ya bani �ya�yana ya sa na kai}ararsa, don al}ali ya wankeni in ci gaba da yin fim ]ina.

Fim: A cikin takardar daMalam Ahmed ya raba, ya cezai kai }arar duk wani

furodusa da ya fito da fim]insa kasuwa muddin akwaiki a cikin fim ]in.

Fatima: Bai isa kai }ararfurodusoshi ba. Yanzu hakada ku]in mutane a hannunawanda zan yi masu fim. Idanmuka gama shari�a da shi zanje in yi masu fim ]in su. Ahalin yanzu na daina zuwaofishin kowa don kada a ri}ayi min kallon wula}anci. Kasan ya bi ofisoshi ya ~atamin suna.

Fim:An ce finafinanki dukba su fito ba. Ko za mu iyajin sunayen wasu dagacikinsu?

Fatima: Ka ga daiakwai Hargitsi, sai Buri,Mugunta, Matsayi, RomonRogo, da wasu ma wa]andaban san sunansu ba. Ka sanwani fim ]in fitowa ]aya zaa kira ka ka yi, wani kumasai bayan an gama ake sanyamasa suna.

Fim: Fatima, a cikintakardar dai ya ce tun kinagidansa, kafin ki gudu, akazo aka yi maki romon kunnehar kika ri}a fita kina zuwafim. Yaya gaskiyar wannanal�amari take?

Fatima: {arya yake,ba ina gidansa ba ne! Yayaza a yi in yi haka inaMusulma? Ka tuna fa,musulunta na yi har na ~atada iyayena don naMusulunta kuma na auriAhmed. Yanzu kuwa don yaga cewa ba ni gadara dakowa, babu mai goya minbaya, shi ya sa zai yi minhaka. To a wannan karon saiiyayena suka ce don ta ~atamana ba za mu rabu da�yarmu ba. Shi kuma sabodanaci ya }i ya rabu da ni. Kaga waccan ]in can (Fatimata nuna wata mata zata shigacikin gida), wallahi wallahiita ce Mum ]ina, ita ta haifeni, amma saboda ba}in cikin

Don ya ga ba ni gadara da kowa ya sazai yi min haka – inji Fatima

Fatima Ahmed

Ci gaba a shafi na 45

Page 38: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

DA }yar ne hassada, ba}inciki da kuma rashin sanin

ya-kamata za su ta~a barinfurodusoshin Jihar Kaduna suha]a kansu har su ci moriyarshirin fim kamar saurantakwarorinsu da ke Jihar Kano.[aya daga cikin furodusoshinKaduna, Nasiru MaiwadaAnchau, wanda shi ne ya shiryafim ]in Tasiri, wanda ke shirinfitowa nan ba da da]ewa ba, shine ya furta haka yayin da yakezantawa da wakilinmu a Kaduna.

Furodusan ya }ara da cewa,wani babban mugun abin da ke}ara jawo wa furodusoshin jiharci-baya shi ne, mafi yawancinlokuta za ka ga furodusoshinsuna ba}in ciki su ga ]an�uwansuya shirya fim ]in da ya kar~u gajama�a. Ya ce da zarar ka shiryafim mai kyau, sai ka ji an fara}ananan maganganu na ~atancida kushe, maimakon a taya kamurna da kuma addu�ar Allah Yaba da sa�a, ko da ba a taimaka

Hassada ke hana mu ci gaba � Nasiru Anchau

maka da wani abu ba.Nasiru ya yi kira ga sauran

furodusoshi �yan�uwansa da suyi wa Allah su dubi wannanal�amari da idon rahama, su zo ataru a ha]a kai a taimaka wa juna,matu}ar ana son ci gaban harkarshirya finafinai a Jihar Kaduna.

Nasiru Maiwada Anchau

R A H O T O

Daga ALIYU A. GORA II,a Kaduna

ABIN ban sha�awa ne daburgewa }warai dagaske ganin yadda �yan

wasan fim na Kano ke cinduniyarsu da tsinke. Wannan yasamo asali ne daga ha]in kansu,da kuma irin yadda }anana dagacikin suke yi washuwagabanninsu biyayya.

Abin takaici, a Kaduna ba hakaabin yake ba, domin kuwa babuwata }ungiyar da aka ta~a yiwadda ta ci nasara saboda babuha]in kan �yan wasa. Hasali ma,}ananan �yan wasan, fitattu dakuma sababbi, ba su san da wata}ungiyar �yan wasa a Kadunaba, ballantana shuwagabannintasu nemi wata biyayya daga garesu. Wannan ya sa �yan wasanKaduna suka kasance kara-zubekawai, kullum cikin zaman jirantsammani suke.

KO ZA A SAMI HADIN KAN ’YAN FIM NA KADUNA?

wakilinmu cewa lallai wannan}ungiya akwai ta ba tun yau ba,kuma rashin biyayya da kumarashin ha]in kan �yan wasan,laifin shugabannin ne.

Musa, wanda ya yi bayanikafin saukar da suka yi har akayi za~e kwanan nan, ya lissafanasarorin da }ungiyar ta samutun daga ranar da suka haukujerar mulki, ya ce, �Mun kar~iragamar mulki a bara ne. Munfara gudanar da aiki aka samurikicin Kaduna, wanda ya hanamana ci gaba a ayyukanmu,wanda da yanzu za~a~~un sunma samu shekara ]aya a ofis.�

Da yake kwatanta ha]in kan�yan wasan Kano da na Kaduna,Musa ya ce, � Ai idan anamaganar �yan wasan Jihar Kano,ba za a yi na Kaduna ba, domintazarar ta yi yawa, kwatantawarma ba za ta yiwu ba. Na je Kanoba sau ]aya ba ba biyu ba. Idanka ga yadda �yan wasa ke

Tsohon sakataren ri}o na}ungiyar �yan wasan Kaduna,Malam Musa MohammedAbdullahi, ya tabbatar wa

girmama Shehu Kano, kai ba mashi ka]ai ba, akwai mutanekamar su Tahir Fagge,Mandawari, su Hamisu Iyan-Tama, wa]anda a Kano dai ayanzu su ne shuwagabanni, idanka ga yadda ake girmama su abindole ya ba ka sha�awa.

�Amma idan aka zo JiharKaduna, za ka ga akwai matsalolidaban-daban. Amma ni a ganina,matsaloli da ake samu a Kaduna,daga shuwagabanni yake. In ance shugabanni, ba ina nufin muda ke ri}e da mu}ami a yanzuba. A�a, kafin mu zo akwai wasu.Shuwagabannin da muka samukafin mu, shuwagabanni ne dani zan kira su �kura mai fa]an takai bakinta.� Ba su da tunaninkowane ]an wasa, ba su datunanin yaya za mu ingantawa]anda suke biye da mu. Suabin da suka sani kawai shi nekansu. Ba su damu da ci-gabanduk wani }aramin ]an wasa ba.�

Laifin shugabanninmu na da ne � inji Musa

Ya }ara da jawo hankalin sauranfurodusoshin cewa duk wandake tunanin akwai wata matsala

tsakaninsa da wani, to don Allahya manta, a yafe wa juna, a cigaba da abin ya kamata.

Don Allah ku ba muha]in kai! � inji Ability

KAFIN za~en da aka yikwanan baya, {ungiyar

Furodusoshi ta Jihar Kaduna takasance a cikin rikici da rashinha]in kai. Tabarbarewar}ungiyar har ya kai ga wasu dagacikin furodusohin kowa ya kamagabansa tare da magoya bayansa.

Mutane da dama sun aminceda ra�ayin da Nasiru MaiwadaAnchau ya furta. Babban mugunabin da ya ba da gagarumargudummuwa wajenta~ar~arewar }ungiyar shi ne,duk lokacin da aka samu ]ayadaga cikin furodusoshin ya shirya

wani fim da ya kar~u ga jama�a,to idan ba a yi hankali ba, zaizama tunkiyar ware, abin zun]ekuma abin zagi, maimakon a tayashi murna tare da yi masakyakkyawar adddu�a.

Idan mai karatu bai manta ba,a kwanan baya wasu daga cikinshuwagabannin furodusoshinsuka yi wa sakataren ya]a labaran}ungiyar na lokacin ingiza-mai-kantu-ruwa, inda ya yi wata~am~armar da har ta kai shi gashiga gidan yari.

To Hausawa dai sun ce komaitsawon dare, gari zai waye kuma

37

Musa Moh’d Abdullahi

Page 39: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

R A H O T Okomai nisan jifa, }asa za ta.{ungiyar furodusoshin ta yi taroa Zariya a ranar Laraba, 27 gaYuni, 2001, inda aka saukedukkan shugabannin, nan takekuma aka na]a shugabanninri}on }warya a }ar}ashinshugabancin Adamu BelloAbility. Shugabannin ri}on}wayar da aka na]a su ri}e}ungiyar kafin a yi zabe sun ha]ada:

1. Adamu Bello (Ability)2. Abdullahi Sa�idu Bello3. Nuhu Imrana4. Nasiru [an Maliki5. Hajiya Fatima.Wakilinmu ya tattauna da

Ability don jin ta bakinsa a kanal�amarin. Ga yadda hirar takasancewa:

Fim: Su furodusoshin naKaduna, su ne suka amince dasu rushe kansu, suka kuma na]aka shugaba?

Ability: {warai da gaske. A,to zan na]a kai na ne? Ai ba zanna]a kaina ba. {ungiya ce ta kirataron membobinta na jiha gaba]aya, suka taru, aka tattauna akasauke kowa kuma nan take akana]a ni a matsayin shugaba.Kuma ina da membobi guda hu]uwa]anda za mu tafiyar daharkokin }ungiyar nan na tsawonwata biyu, kafin lokacin da zamu shirya za~e, a za~i wandamutane ke so.

Fim: Su wa]annan membobinaka guda hu]u kana ganin baza a samu mishkila ba a kan su,ganin cewa ba furodusoshi ba newa]annan jama�a suka sani?

Ability: Wato akwai wanirashin fahimta da wasu ke yi.{ungiya ce fa ta furodusoshi, koba haka ba? Kuma wa]annanmutane }ungiya ta tattabar dacewa su furodusoshi ne. Kumamutanen nan an ga cancantarsune. Ko an san su ko ba a san suba, idan mutum dai ya cancantaana iya na]a shi a kan kujerar daaka ga ya dace.

Ni kaina ai an zarge ni da cewani ba furodusa ba ne. Amma kumakowa ya sani ina da fim yanzu a}asa mai suna Karama. To ammada yake su shugabannin }ungiyarsun tabbatar da cewa ni furodusane ka ga har yanzu ina nan cikin}ungiyar, kuma har ma ga shiyanzu na samu mu}aminshugabancin }ungiyar na ri}o.

Fim: To kana ganin wasu

furodusoshi da aka ta~adakatarwa ba su da ha}}in a aikemasu da wasi}u cewa za a rusheuwar }ungiya?

Ability: Babu wanda ba a aikawa takardar gayyata cewa akwaitaro ba. In mutum ya ce bai saniba, to wannan kuma... Amma nia sanina da kuma bincikena, dukwani wanda yake ]an }ungiyane na furodusoshi, ya san dawannan taro da aka yi, kuma angayyace shi.

Fim: Daga cikin wa]anda akadakatar ]in akwai wanda ya samuhalartar taron?

Ability: {warai kuwa. KamarUmar Isma�il na Zariya, shi nefurodusan fim ]in Umar. Yahalarci wannan taro.

Fim: To su wa]annan mutaneda aka za~a su ri}e shugabancinita wannan }ungiya tafurodusoshin Kaduna, wace iringudunmawa suka ta~a badawaga }ungiyar, wanda ya sa sukacancanci a za~e su a matsayinshuwagabannin ri}o?

Ability: Wannan, }ungiya tasan gudunmawar da suka bayartunda har ka ga ta za~e su a kanwannan al�amarin. In kuma kananeman cikakken bayani a kan iringudunmuwar da suka ba}ungiya, kana iya tuntu~artsohon shugaban }ungiyar kosakataren shi.

Fim: Yaushe za ku yi za~enshugabannin dindindin?

Ability: Tsarin rushe gida, to a

ne suka nemi a sauke su don araba su da wasu matsaloli na}ungiyar da suka sha }arfinsu?

Ability: E, to, ko dai akwaimatsala ko babu, lokacinsu daiya yi na su sauka don wa]ansusu hau. Saboda haka an saukesu, sun kuma sauka. In suncancanta kuma suna da ra�ayi, suzo su tsaya takara a za~e su.

Fim: Me ya sa aka yi taron aZariya, maimakon a Kaduna?

Ability: To da ma a }a�idar}ungiya shi ne, idan an yi taro aKaduna, taro mai zuwa a Zariyaza a yi.

Fim: A matsayinka na sabonshugaban wannan }ungiya, wanemataki kuka ]auka don ganin kamagance matsalolin da ka taras?

Ability: Kai, alhamdu lillahi,na ji da]in wannan tambaya daka yi mani! Wato a gaskiya inaso in yi amfani da wannan dama

in ro}i duk wani furodusa da yasan shi furodusa ne a JiharKaduna, da cewa don Allah, yayi yi ha}uri ya kwantar dahankalinsa, a zo a ha]u a ]inke~araka, a }ara dan}on zumunci.Mai ra�ayin tsayawa takara yafito ya nuna. Idan da an yi kura-kurai, to yanzu dama ta samu damutum zai iya gyara kuskurennan, ta hanyar tsayawa takararza~e. Saboda haka ina kira gadukkan �yan }ungiya da su zosu ba ni ha]in kai mu samu mutsaya a shirya wannan za~e, aza~i shugaban da ya cancanta don}ungiyar nan ta zamaingantacciya kuma }a}}arfa.

Fim: Wane mataki za ka ]aukadon ganin ka samu goyon bayatare da ha]in kan furodusoshinda kuka ta~a dakatarwa?

Ability: To, }ungiya dai ta ceta dawo da wa]annan mutane,amma da shara]in in sun biyaku]a]en da aka sa masu na }a�idaN5,000, kuma na tabbatar dacewa duk mai son }ungiyar nanN5,000 ba wani abu ba ce a gareshi. Kuma mataki na biyu da na]auka shi ne, da zarar mun zaunamun tattauna da sauranmembobina, za mu ]auki watadama mu zagaya zuwa ga kowanefurodusa da ke Jihar Kaduna harofishinshi ko gidanshi donro}onshi da tattaunawa da shi daba shi ha}uri tare da nemanshawarwarinshi game da yaddaza a samu cin nasarar wannanza~e.

Fim: Shin a halin yanzu andam}a maka duk wasu kayamallakin }ungiyar?

Ability: In Allah Ya yarda munsa ranar da za a yi hand-over(taron mi}a kadarori), kuma za ayi insha Allah.

Fim: To Ability mun gode.Ability: Ni ma na gode.

tabbatar da cewaan gudanar daza~e kafin watabiyu. Sabodahaka in Allah Yaso nan da watabiyu za mu kiragagarumin taro na�yan }ungiya indaza a tattauna kumaa yi za~e don aza~i sababbinshugabanni.

Fim: Menenesanadin rushe itaainihin }ungiyarta furodusoshinKaduna?

A b i l i t y :Lokacinsu ne yayi. Don haka yasa aka ce su saukaza a yi za~e.

Fim: Sut s o f a f f i nshuwagabannin

Mohammed Bello ‘Ability’

�Yan wasan Kadunasun yi shugabanniA RANAR Lahadi, 5 ga

Agusta 2001 ne akagudanar da za~en shugabannin}ungiyar �yan wasankwaikwayo ta Jihar Kaduna.Za~en, wanda aka gudanar aharabar gidan Rediyon Tarayyana Kaduna da misalin }arfe biyu

da rabi na rana, ya sami halartar�yan wasa masu rajista da}ungiyar.

Haka kuma tsofaffinshugabannin ri}on }warya na}ungiyar ne suka shugabancitaron tare da zama al}alan za~en.

Tsofaffin shuwagabannin na

38

Page 40: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Malam Yahuza A. IluShugaban ’yan wasan Jihar Kaduna

R A H O T Oshugaba ba tare da hamayya ba.Yayin da aka kammala dukkanza~u~~ukan, Sani Magaga(wanda ya fito a matsayin mijinWasila a fim ]in Wasila 2), yanuna rashin amincewar kayen daabokin hamayyarsa A.S.Muhammad ya yi masa a yayinda suka fafata wajen nemanmu}amin mataimakin shugaba,inda A.S. ya samu zunzurutun}uri�u har 54u, yayin da shi kumaMagaga ya samu }uri�u takwas.

Ga dai jerin sunayen za~a~~unshugabannin:

1. Yahuza A. Ilu � Shugaba.2. A.S. Muhammad �

Mataimakin shugaba.3. Isah I. Isah � Babban

sana�a tamu.Fim: Da ma can ka ta~a nuna wa �yan wasan kwa]ayinka na

neman shugabancin }ungiyar?Yahuza: Ina nan ofishina aka turo wasu wakilai suka gaya mani

cewa sun zo ne su shaida mani cewa sun ga ni ka]ai na cancanta inshugabance su a wannan }ungiya. To duk da yake na amsa masu,ban saki jikina ba har zuwa ranar da aka yi wannan za~e.

Fim: Yanzu wane }udiri kake da shi dangane da wannan }ungiya,don samun ci gaban da ya fi wanda ake da shi da?

Yahuza: A gaskiya abu na farko shi ne tarbiyya. Alal ha}i}a, duk}ungiyar da aka ce ba tarbiyya, to duk al�amuranta sun lalace. Abinda nake nufi a nan shi ne, dole ne mu kasance masu ladabi, masu

ri}on }warya, masu murabus,sun ha]a da Alhaji Haruna[anjuma (Mutuwa Dole), amatsauyin shugaba, da MusaMohammed Abdullahi amatsayin sakatare. Sauranmu}arraban da ba su da ofis ashugabancin na ri}on }warya sune Yusuf Barau, AminuMuhammad, Adamu Garba, dakuma Abubakar Cigari.

Kafin a fara gudanar da za~en,sai da al}alan za~en suka gabatarwa da taro da irin tsare-tsaren dasuka yi, yadda ba za a samu zargiko tsegumi daga kowane ~angarena Jihar Kaduna ba. Al}alanza~en sun bayyana cewa sunkasafta jihar zuwa shiyya-shiyyahar zuwa shiyyoyi hu]u. Hakakuma duk mu}aman }ungiyar,an kasa su gida hu]u yaddakowace shiyya za ta samu kashi]aya ba tare da nuna fifiko a kanwata ba. Ga yadda kasafinshiyyoyin ya kasance, tare da irinmu}aman da kowace shiyya tasamu:

SHIYYA TA [AYA: Ta ha]ada }ananan hukumomin Cukun,Birnin Gwari, Igabi, Kagarko,Kajuru, Kaduna Ta Kudu, dakuma Kaduna Ta Arewa.Wa]annan }ananan hukumomi,su aka ba mu}aman shugaba,ma�aji, mai binciken ku]in}ungiya, mataimakiyar shugabarmata da kuma �ex-officio�(mashawarci) na ]aya.

SHIYYA TA BIYU: Tana}unshe da }ananan hukumominZariya, Sabon Gari, Giwa, Soba,Kudan, da kuma Ma}arfi. Sukuma su aka ba kujerun babbansakatare, sakataren shirye-shirye,shugabar mata da kuma �ex-officio� na biyu.

SHIYYA TA UKU: Su neIkara, Kubau, Lere, da kumaKauru. Su kuma su ke dasakataren ku]i.

Bayan an gama bayyana yaddawannan kasafi ya kasance,tsohon sakataren }ungiyar yabayyana cewa duk wanda bai yirajista da }ungiyar ba, ba zaisamu damar tsayawa a za~e shiba, kuma ba zai iya za~en waniba. Wannan ya sa nan take wasusuka yi ta sayen fom na rajista akan N100, suka kuma cika nantake, don su samu damar tsayawaa za~e su, ko kuma su za~a.

An dai gudanar da za~enlafiya, inda Malam Yahuza A. Iluya samu nasarar cin za~en kujerar

sakatare.4. Binta Aliyu � Sakatariyar

ku]i.5. Balaraba Ciroma � Ma�aji.6. [anlami A. Maska �

Mai binciken ku]in }ungiya.7. Abdullahi A}ilu � Jami�in

ya]a labarai.8. Shu�aibu Ibrahim �

Sakataren shirye-shirye.9. Elesha Sambo � Sakataren

jin da]in jama�a.10. Abu Likoro � Shugabar

mata.11. Rashida Bello�

Mataimakiyar shugabar mata.12. Muhammad Idris Kauru �

Al}alin }ungiya.

Bayan an kammala za~en, saitsofaffin shuwagabannin}ungiyar suka mi}a wa sabonza~a~~en shugaban }ungiyar, M.Yahuza A. Ilu, kundin tsarinmulki na }ungiyar, sannan kumadukkan taron aka amince da ranarLahadi, 19 ga Agusta 2001, tazama ranar da kwamitin ri}o zaimi}a dukkan kadarorin }ungiyarga sababbin shugabannin. Hakadai aka tashi yawanci ana farinciki. Wasu kuwa sai dai ha}urindole, domin ta ciki na ciki.

A ranar Asabar, 25 ga Agustaaka rantsar da sababbinshugabannin.

Zan }wato wa �yan wasan Jihar Kadunaha}}insu � inji Yahuza A. IluSABON za~a~~en shugaban

}ungiyar �yan wasankwaikwayo na Jihar Kaduna,Malam Yahuza A. Ilu, ya lashitakobin }wato wa dukkan �yanwasan jihar ha}}insu daga dukwanda ya yi yun}urin dannemasu ha}}i a fagen shirin fim.Shugaban ya bayyana hakan nea ranar 8 ga Agusta, 2001, yayinda yake bayyana wa wakilinmu}udurinsa da kuma matakan dayake shirin ]auka don magance]imbin matsalolin da }ungiyartake fuskanta wa]anda ya taras.Ya tattauna ne da wakilinmu aofishinsa da ke Ma�aikatar Ya]aAl�adun Gargajiya da ke kan titinWaff, Kaduna.

Ga yadda hirar ta kasance:Fim: Malam Yahuza, me za ka

ce dangane da nasarar da AllahYa ba ka na cin wannan za~e?

Yahuza: Alhamdu lillahi,godiya ta tattabata ga Allah da Yakawo mu har ya kasance na samuwannan mu}ami na shugaban�yan wasan kwaikwayo na JiharKaduna. Alal ha}i}a, babu abumai da]i irin a ce an wayi garijama�a sun same ka sun ce,�Wane, muna so ka jagorance mu.Kai ka]ai muka ga ka cancanta.�To alhamdu lillahi an je an yi za~ennan, bu}atata ta biya na kasanceshugaba. Kuma insha Allahwa]anda suka nuna cewa sunaso in jagorance su ]in nan, inzan tsaya tsayin daka, tare dataimakon Allah, in ga na }watomasu �yancinsu game da wannan

39

Page 41: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

R A H O T Okuma gaskiya da ri}on amana.Sannan kuma za mu tace irinfinafinan da suke gur~atayaranmu. Kuma za mu ga cewaha}}i tsakanin ]an wasa dafurodusa an samu kyakkyawarfahimta a tsakanin juna. Wataukowa ya ba kowa ha}}inshi, mukuma ko da an samu watamatsala, za mu tsaya mu ga ansasanta an ci gaba. Sannan kumaduk fim ]in da za yi, sai munduba dangantakarshi da addinitukun.

Fim: Wane irin mataki kakeshirin ]auka game da rashinha]in kan �yan wasa dafurodusoshin Jihar Kaduna,wanda yake addabar harkar shirinfim a jihar?

Yahuza: Ni insha Allah zan yi}o}arin in ga na samu ha]in kai,daga furodusoshi har zuwa �yanwasa da kuma mu da aka za~a.In Allah Ya yarda za mu yi }o}arimu ga mun kasance tsintsiya-ma]aurinki-]aya don ci gabanwannan al�amari.

Fim: Ko akwai wani matakida gwamnatinka za ta iya ]aukaa kan �yan wasan da suka }i yinrajista da wannan }ungiya dagangan?

Yahuza: Ko da yaushe shimutum ajizi ne. Ka ga yanzumatsalar da ake ciki ita ce, idanyau kuka yi yarjejeniya dafurodusa, to shi furodusan ya yi}o}ari, kana gama yi mashi fimya biya ka ha}}inka. Amma idanka samu wata matsala ba ka darajista da mu, ka ga ba ruwanmuda kai. In ma zuwa ka yi bai biyaka ba, ko kuma wata matsala tasame ka, ba mu da damar mu sabaki. Amfanin rajista ]in shi ne,za mu kare maka ha}}inka. Inwani abu ya same ka za mu yi}o}ari mu ga mun yi abin da yadace. Kuma ni a gwamnatina,akwai taron }ara wa juna ilimida za mu dinga yi tsakaninmu da�yan wasan. Za mu dinga nunamasu ha}}o}insu, da kumayadda shi kanshi wasankwaikwayon yake, da kumayanda amfaninshi yake garayuwar al�umma baki ]aya.

Fim: Akwai matakin da za ka]auka a kan duk wani furodusanda ya ci zarafin wani ]an wasaba tare da ha}}i ba?

Yahuza: Wannan }ungiya daaka kafa, ba wai an kafa ta ba nedon ta kama fa]a da furodusoshia kan �yan wasa, kamar yadda

wasu suke tunani, a�a. Ni dai anawa mulkin ba haka nake tunaniba. Na }addara cewa na zo don

Daga ALIYU A. GORA II,a Kaduna

[AN wasan nan Sani IdrisKauru (Mo]a) yana ]aya

daga cikin �yan biki wa]anda akayi wa sane a ranar ]aurin aurenFati Mohammed da Sani Musa(Mai Iska) a Kano kwanan baya.Mo]a ya bayyana wa wakilinmucewa babu shakka sai a ranar yatabbatar da yana da masoyadomin irin yadda jama�a suka yomasa caa sai ya ji a lokacin daidaiyake da gwamna.

Mo]a ya ba mu labarin kamarhaka, �Muna isa wajen ]aurinauren a cikin motar Alh. Nata�alaAliyu sai jama�a suka fahimcicewa ina cikin wannan mota.Shikenan sai suka yo caa kamarsu ]auki motar nan sama, ana�Sai Mo]a! Allah Ya tsare ka!�da dai sauran kalamai irinwa]annan. Allah ka]ai ya saniyakar yawan wa]annan mutane.

mu samu fahimta tsakaninmu dafurodusoshi yadda za mu tafiyarda al�amarinmu ga baki ]aya, su

su ji da]i, mu ma mu ji da]i.Muna fatan wannan }ungiya tafi ta kowace jiha ban sha�wa.

�Yan birni sun yi wa Mo]a �fafalolo� a bikin Fati

�Ganin yadda wa]annanmutane suka hana ni sa}at sai gaIsa A. Isa ya iso da besfa, ya ce,�To Mo]a ka hau in isar da kaiwajen ]aurin auren.� Hawana keda wuya, mun fara tafiya, jama�asuka sauko da ni }asa daga

wannan mashin.�Aka dinga carafke da ni ana

jefawa sama ana cafewa, wasuna yi mani kirari. Wasu suka farajan hulata wai ita suke so, sunacewa su suna son su sami waniabu daga gare ni. Ni ko ba abinda na yi sai kawai na dafe hulata.Ashe aikin banza nike yi! Dukabin nan da ake ciki ashe�fafalolo� ake yi mani. Ban ankaraba sai da na sami kaina sannanna fahimci duk ku]in da nake dasu an lalabe. Aka bar ni ba kosisi.�

Da wakilinmu ya tambaye shiko nawa ne ku]in aka sace masa,sai Mo]a ya ce shi wallahi ba zaiiya tuna adadin ku]in ba. Kumada aka tambaye shi yadda aka yiya dawo gida Kaduna, sai ]anwasan ya ce ai dole ta sa ya je yanemi Yakubu Lere a otel ]in daya sauka, ya yi masa bayanin abinda ya faru. A nan ne furodusanna Adali ya ba shi ku]in mota.

Sani Idris Kauru (Moda)

Auwalu Sabo ya hanasayar da Fim a GwammajaSHUGABAN ofishin shirya

finafinai na �SarauniyaFilms� da ke Kano, Alh. AuwaluMohammed Sabo, ya ba daumurnin kada a sake sayar damujallar Fim a kantinsu da kedaura da Asibitin {ashi na Dalada ke unguwar Gwammaja aKano.

Wannan ya biyo bayan fushinda shi Auwalu ya yi saboda watawasi}a da mujallar ta buga a shafina bakwai na fitowarta ta watanjiya inda wata mace ta yi kuka akan wata irin fitowa da wani ]anwasa ya yi a shirin Sartse wanda�Sarauniya Films� suka yi.

Shi dai Auwalu, yana shiri daFim sosai kafin watan jiya,domin haka ne ma yake kar~armujallar yana sayarwa a kantinsa.Wannan ya sa a duk makekiyarunguwar ta Gwammaja babu indaake sayar da mujallar kamarshagon �Sarauniya.� To yanzu anbar sayarwa.

Tun da farko, fusatar daAuwalu ya yi ta sa ya fizgi motaa ranar da mujallar ta fito a Kano,ya doshi ofishin Fim da ke kantitin Zariya a Gya]i-Gya]i, indaya kai wa ma�aikatan wurin hari.Ya yi ashariya a ofishin ta fi saushurin masa}i, yana cewa,�Iyayenku ne �yan daudun!�sannan ya ]auki wani }aton

dutse ya jefi wakilinmu AshafaMurnai Barkiya da shi, yakuskure shi, ka]an da ya sameshi a gindin kunne.

A harabar ofishin, furodusanya yi rantsuwa tare da sujada harsau uku cewa ko tsafi zai yi saiya karya mujallar tare da masubuga ta. Kuma ya bayyana cewaya ba �yan daba odar su kasheduk wani ]an mujallar Fim dasuka }ara gani a Gwammaja.

Wannan abu ya ba �yan fim dadama mamaki, ganin cewaAuwalu shugaba ne a harkar fima Kano, wanda bai kamata a ji kowani yaronsa ya yi wannanhalayyar ba.

Da aka waiwayi mawallafinFim, Malam Ibrahim Sheme, akan maganar, sai ya ce, �Mu mun]auka Auwalu abokinmu ne. Niabin ya fi }arfina, tunda anamaganar kisan gilla ne.� Ya ce bazai }ara cewa komai ba saikwamitin daraktocin mujallar sunyi taro a kan maganar tukuna.

Auwalu Mohammed Sabo

40

Page 42: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Har yanzu da sauran gyara–

Fim: A gurguje kuma a ta}aice za muso mu san tarihin gwarzon namu?

Mika�il: Assalamu alaikum warahamatullah. Rabbish rahli sadari wayassirni amri wahlul u}datan min lisaniyab }ahu }auli!

Mika�il dai ba gwarzo ba ne, watahalitta ce ta Ubangiji, an kuma haifeshi a ranar 16 ga Fabrairu, 1974, watokimanin shekaru 25 da suka wuce. Nayi karatun firamare (1979-81) damakarantar firamare ta Magwan (1981-88), inda ban da]e a can ba n a dawoJSS Karoji, inda na yi �Junior secondaryschool� ]ina (1988-90). Bayan nankuma na tafi makarantar kimiyya dafasha ta Dawakin Tofa. Ban da]e dakammala ta ba na tafi makarantar horarda hafsoshin soja ta Kaduna, watauNDA. Zuwa wani ]an lokaci Allah(SWT) bai yi nufin zamana a can ba,suka koro ni, ko na koro kaina, ko kosuka koro ni, da ni da kaina gaba ]ayana dawo Kano. A yanzu ina Jami�arBayero ta Kano ina aji hu]u. Inakarantar Geography.

Fim: Yaushe fara harkar fim, kumame ya ba ka sha�awa har ka shiga?

Mika�il: Abin da ya ba ni sha�awa akan wannan shi ne kasantuwar yau dana taso a gidanmu, muna yara ba ayarda mu kalli fim ]in Indiya bayawanci sai dai mu kalli na yara(cartoon) film ko kuma finafinan bandariya. Saboda yawan kallon wa]annanfinafinan yakan sa rayuwa ta komatamkar tasu. Wato ko cikin sa�annina]abi�ata ta fita daban. Ina cikin wannanhali ne, na fara kallon shirye-shiryengidan talabijin na Kano. Ha}i}a hakanya da]a sa mun karsashi a kan sha�awarwasa a cikin talabijin, musamman nashirin da ake yi na wannan lokacin

wato shirin Barmo da [anmagori. Awannan lokacin sai in ce [anmagorida Barmo su ne silar shigata harkar fim]in Hausa. Kuma har yanzu nakan gansu da wannan }imar.

Fim: Mutane suna ganin salonwasanka ya fi ta�alla}a ne a kan nabarkwanci, wato comedy. Shin kakantaka wata rawa baya ga irin wannan ]in?

Mika�il: A kaf duniyar finafinai baburawar da ta fi wahala kamar wasanbarkwanci. Koda yake har yanzu ba zance ba mu da comedy a nan ba, amma a

zahirin gaskiya ~angaren comedy~angare ne da ya fi kowanne caza kai;dole ne mutum ya zamanto mai yawan}ir}ira, watau creativity kenan a

Sarakan barkwanci: Gidigo da Ibro

Mika’il Gidigo

da ya yi sai ya ba ka dariya.Gaskiya ne na ta�alla}a ga wasan

barkwanci, amma fim ]ina na farko bacomedy ba ne, kuma har yanzu ina yin

41

T A T T A U N A W A

Turance. A cikin da}i}a ]aya ana sonka }ir}iri abin da zai bai wa mutumdariya amman kuma ba ta sigar wautaba. Akwai lokacin da aka tambayi wanijarumi a Amerika, yaya za a yi mutumya zama mai barkwanci a cikin fim? Saiya ce, �Change of face!� Watau launafaska. Har yake cewa bari in yi mukununi. Nan take ya sauya fuskarsa wajensau biyar. A wannan lokacin duk sauyin

Da wuya ne ka ce ba ka san Mika�ilu Gidigo ba. Domin kuwa wannan ]an wasanya fito a finafinai da daman gaske, kamar su Marainiya 2, Badali 2, Furuci 1&2,Alhini 2, Sai A Lahira 2, Kalas, Tafarki, Ajizi, Ajali, {arshen Zamani, {awataKishiyata, Juriya, Jigal, Rabin Jiki, Al}ibla, da sauransu. A fagen fim na Kano(Kallywood), an fi saninsa da sunan Gidigo. Ban da wasa, yakan rubuta labarinfim (screenplay). A ran 23 ga wannan watan ne za a ]aura masa aure da wata �yarwasa a Kano. Shin wanene Gidigo? Menene ra�ayinsa a kan harkar fim? Gidigo,wanda ya kusa gama karatunsa a Jami�ar Bayero, Kano, yana da muhimmanra�ayoyi, wa]anda ga su mun kawo maku da ]umi-]uminsu. A ci lafiya!

Page 43: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

wa]anda suke ba na ban-dariya ba. Zaniya ba ka misali da wasu finafinan,kamar su: Agola, Juriya, Jimami, IdanKunne Ya Ji, da dai sauransu. Akwaima wanda zan fara kwanan nan inshaAllah zan fito a matsayin lauya. Wasukuma nakan fito ne a matsayinintelligence inspector (sufeto maibincike).

Fim: Wa ya fara sa ka a fim da farko?Mika�il: Allah Ya ji}an Aminu

Hassan Yakasai! Shi ne ya fara yi manidarakta a fim ]in Hausa, a cikin fim ]in}ungiyarmu ta Jigon Hausa.

Fim: Wanne fim ne?Mika�il: In Kunne Ya Ji. Bayan shi

kuma na yi Saki Na Dafe, wanda a nanne na fara barkwanci. Daga shi kumasai na yi Sai A Lahira.

Fim: Ka yi finafinai kamar nawa?Mika�il: Na yi finafinai sama da

talatin, daga ciki akwai Marainiya 2,Badali 2, Furuci 1&2, Alhini 2, Sai ALahira 2, Kalas, Tafarki, Ajizi, Ajali,{arshen Zamani, {awata Kishiyata,Juriya, Jigal, Rabin Jiki, Al}ibla,Martani, da Sidi}u, inda nake gode waAllah ina comedy. Amman zai yiwahala ka ga comedy da na yi a wannanfim ]in irinsa na sake yi a cikin wanifim ]in, ba na maimaici a wajen wasana,kuma ko da fita ]aya na yi maka, zaiwuya ka ga na sake irinsa a wani fim]in.

Fim: Daga cikin finafinan nan wanneza ka ce shi ne kamar bakandamiyarka,wanda shi ne ya fito da kai?

Mika�il: To, na yi finafinai da damaamman a zahirin gaskiya mutane sun fikirana da wani abu da na yi a cikin fim]in Furuci, watau inda na ce, �Hancinciki da falo ne.� Kuma ka ga mu mukayi screenplay ]insa ni da babbandarakta Tijjani Ibrahim. Kamar a yanzuma duk inda na le}a sai ka ji yara dazarar sun gan ni sai su fara �Hancin cikida falo ne!� Ba ma ga yara ka]ai ba harmanya; in ma suka nace sai in ce musu�Kai kun ga an ma yi masa taga!� In nasamu na lalla~a su sai in gurgura ingudu in bar su suna dariya.

Fim: To yaya abin ya samo asali?Mika�il: Wato bayan mun gama abin

da darektan fim ]in watau TijjaniIbrahim ya sa mu mu yi, a lokacin inari}e da yaron a hannuna, sai ya ta~ahancina. Kamar yadda na gaya ma, dukmai wasan ban-dariya sai ya zamto mai}ir}ira, nan take na ce, �Liyu, liyu! Toto to ab to hancin ciki da falo ne!� Inafa]in hakan duk wa]anda suke wajensuka bushe da dariya. Shi ne jama�a suka]auki wannan sarar ta �hancin ciki dafalo ne.�

Fim: To shi sunan Gidigo, a ina kasamo shi?

Mika�il: Sunan Gidigo a stage drama(wasan da~e) na samo shi, a makaranta,

domin mukan yi wasan kwaikwayo naTuranci a jami�a, a kulob ]ina naGalaxy Entertainment Club. Munacikin wasan ne aka kai ni kotu, al}aliyake tambayata sunana, shi ne na cemasa, �Honourable Thief Gidigo!� Akace, �Meye Gidigo?� Sai na ce, �SunanLarabawa ne.� To daga nan shikenansai Gidigo ya bi ni, don a lokacin macewa na yi a gidan dagacin Madina akarene ni. Amman a zahirin gaskiya bason sunan nake yi ba, don ban yi kamada Gidigo ba. Gidigo ai rusheshenmutum kenan. Ka ga kamar kai a iya cema Gidigo!

Fim: Cikin finafinanka, wanne ne zaka ce ya zama }alubale a gare ka wandaka sha wahalar da ba za ka manta ba?

Mika�il: Kamar Martani kenan.Muna daji a kan duwatsu larura ta tashisaboda Allah ya jarabce ni da larurarmatsalar idanu; sama da shekaru gomasha ]aya ina fama da shi. Muna cikindajin ne idona ya tashi, wanda har takai ni ga aman jini, sanadiyyar ajiyemedical glasses ]ina (tabaran likita) dana yi, kuma ga ni cikin rana har na wanitsawon lokaci. Amman duk da hakansai da na yi abin da muka je yi ]in.Babban abin takaici a wannan fim ]inshi ne har yanzu furodusan fim ]inUmmaruru, watau Umar Shayabo, bai}arasa biyana ha}}ina ba, tun kafinAzumi har yau.

Fim: Wasu suna ganin finafinanmusun ta�alla}a a kan al}ibla ]aya ne,soyayya; akwai sauran matsaloli dasuke addabar al�umma, amma ba a cikalura da su ba sai soyayya ka]ai dakwaikwayon Indiya.

Mika�il: Ina tambayar ka tasa gaba amatsayina na ]an wasa ko kuwa amatsayina na mai rubuta tare kuma datsara labari (screen play)?

Amarya da ango daga ran 23 ga wannan watan: Mika’il tare da Salmat

Fim: A matsayinka na ]an wasa, mairubuta wasa da kuma wa}a.

Mika�il: To, a gaskiya na kasa fimkashi uku: akwai wa]anda suke yin fimdon ra�ayi, akwai wa]anda kuma sukeyin fim don neman ku]i tare kuma dailimin fim kowanne iri ba tare datantance kyan labarin ba; aji na biyukuwa zai iya yin kowanne ku]i; aji nauku kuma zai yi fim ne don ilimintarwa.A ha}i}anin gaskiya ni ban taso dakallon fim ]in Indiya fim ba, kuma haryanzu ba na kallonsu. Su masukwaikwayon ko kuma ]aukar fim ]inIndiya su juya in dai har labarin nasuzai ilimantar to kuwa sun fa�idantar dajama�a. Finafinan da nake kallo gudauku ne: na ban-dariya, na ya}i, dabestsellers (wato irin wanda ya shafilabarin wani iyali ko zamantakewa). Inkuwa muna tare da kai ka sa fim ]inIndiya, to kuwa zan tashi.

Fim: A ta}aice dai ba ka gamsu dairin finafinan da suke ]aukar tsarin fim]in Indiya ba kenan?

Mika�il: In dai tsarin Indiya ne, bangamsu da su ba, bil hasali ma ina ganindakushewar basira ce, koda yake su maIndiyawan suna satar finafinaun wasu,yawanci kamar na Larabawa komakamantansu, ko ga sigar wa}a ma,mafi akasari wa}o}in Larabawa sukelaunanawa. Amma ni idan har kana sonka burge ni, to ka }ir}iri labarinka dakanka, domin duk wanda ke da fasahar}ir}ira to ni ina girmama shi a rayuwa;ka zamto mai }ir}ira, bayan ka }ir}irarkana ka zo ka baje wa mutane, su gamsu,to ha}i}a ka ciri tuta.

Fim: To daga cikin abokan sana�arkawanene gwaninka?

Mika�il: A yara Ali Nuhu. A manyakuma Tahir Fagge da Mandawari. A~angarena na wasannin ban-dariya, zan

42

Page 44: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

iya wasa da kowane ]anwasa, kana kuma babu wani]an wasa da zai yi minkwarjini har in kasa wasa dashi. A fahimtar juna kumababu kamar mutum ]aya, shine Al}asim Al-Mustapha ([an Ibro), domin kuwa munfahimci junanmu tare da shita yadda har in ya ]aukomagana na san inda ta dosa,ni ma haka. Sannan bayan shiko sai Sani Garba S.K. Agaskiya, na son wasa da S.K.

Fim: To daga cikin yaramatasa mata wacece wasantayake burge ka?

Mika�il: Babu, domin haryanzu ba mu da �yar wasanda take she is flexible (za taiya kowane wasa) kuma ta ceshe is superstar. Kuma ina}alubalantarsu (a kan haka).Dalili kuwa shi ne har yanzuba mu da mace wacce takeyin wasan ban dariya, donhaka ba ni da gwana.

Fim: To a cikin dattawa fa?Mika�il: A mata Mai Aya,

a maza kuma [anhaki.Fim: To wanne bambamci

za ka iya fitarwa tsakaninwasa irin na da da na yanzu?

Mika�il: Bambancin dayawa. Na farko su (irin su[anhaki) suna yi ne donsadaukarwa, mu kuwa yanzusana�a ce. Haka nan kuma tawajen tsarin aikin mun fidaraktocinsu na wancanlokacin ganin aikin a zahiri,kana kuma a wancan lokacinmatsalolin ta~ar~arewaral�umma bai kai na yanzu ba,kuma a lokacinsu ina ganinkamar sun sadaukar darayuwarsu ne wajen ya]amanufofin gwamnati agidajen talabijin nagwamnati. Ina ganin gidajentalabijin na gwamnati ba suyi wa su [anhaki adalci ba.Misali Alhaji Buguzum yarasu ta sanadiyyar ciwonsankarar }wa}walwa. Kamar[anhaki a yanzu yana famada larurar ido. Amma me akayi musu? Mutanen da sukasadaukar da lokutansu wajenya]a manufofin gwamnatinwancan lokacin, a ce a yanzusuna fama da irin wa]annanmatsalolin fim.

Da a waje suke dadukkansu babu wanda yakeba miloniya ba ne. Ashe anatafiya da taimako. Waninsuyake ce min a wancan

lokacin wasunsu ma girki suke yisu tafi da shi domin ciyar da kansu,amma saboda kishin ilimantar dajama�a ba su damuwa. Haka kumaba su hanyar Garki ba su hanyarGumel, ba su tunanin yin hatsari ahanya, sun ba da ransu gaba ]ayaga aikin.

Fim: Menene ra�ayin iyayenka dafarko da ka fara yin wasan fim?

Mika�il: Ran da na gaya musu maummana kyauta ta yi min don sunfahimci zamaninsu, ubanaBagumulu ne, masarautar Gumel(Maigatari) ummana kuma �yar nanYakasai ce.

Fim: Kyautar me ta yi ma?Mika�il: Ko }uli-}uli ne ko gya]a

ce ba ruwanka, don ban sam ma ba,ko dai sai ka ji?

Fim: E! (dariya).Mika�il: To na }i in fa]a! (dariya).Fim: Maganar aure fa, kana da

burin auren �yar fim?Mika�il: {warai kuwa �yar fim ma

zan aura; insha Allahu a watanSatumba ma za a yi bikin.

Fim: Gidigo wanne buri kake sonka cimmawa a wannan sana�ar tafim?

Mika�il: Babban burina shi nejama�a su ilimantu da abin da nake}o}arin ilimantar da su, in ko hakanya samu to bu}ata ta biya.

Fim: To me za ka ce dangane da}orafin da ake yi na cewa ku �yanfim ba ku aikata abin da kukeuilimantarwa?

Mika�il: Akwai wa]anda suka]auka su wasa suke yi. Ka tunaajujuwan guda uku da na gaya ma abaya. Amma malami nagari shi newanda zai ]a~~aka abin da ya koyar.

Fim: Meye hasashenka a kanharkar fim?

Mika�il: Na ba ka nan da shekarabiyar in muna raye, harkar fim sai tazama sai wane da wane. Misali, ayanzu kowane kamfanin shirin fimyana da nasa �yan wasan da ya ri}a,wasu kuma �ya�yansu suke sakawa,wasu }annensu, saboda sun sansana�a ce mai }arfi.

Fim: Ko furodusoshi suna biyankuha}}inku kamar yadda ya kamata?

Mika�il: A gaskiya ba a san darajar�yan wasa ba har yanzu, ammalokaci ka]an za a fara sanin darajar�yan wasa,. Ni ina ganin duk jaruminda ya yi fim to ya ci halinsa. Sabodahaka ina ganin da sauran gyara,kuma duk wanda ya ce ana biyanha}}i kamar yadda ya kamata, toma}aryaci ne, bai son fa]in gaskiya.Wasu ma sai ka yi musu fim ]in su}i biyanka ha}}inka. Dazun nan naba ka misalin Ummaruru.

Fim: Mun gode.

SANARWA:Za a ]aura auren Mika�il Gidigo da Salmat

Baba Ali a gidan Alh. [anwawu da ke Fagge,Kano, da misalin }arfe 10 na safe a ran Lahadi,23 ga Satumba, 2001. Kamfanonin shirya fimna �FKD,� �Fasaha� da �Home Alone� sunashirya wata walima ta burgewa dominabokinsu Mika�il. Allah ya kai mu!

Dubi hira da Salmat a shafi na 57. �Edita.

SUNA: Baba Ali BossSUNAN RANA: AliSHEKARU: 25MAHAIFA: KanoMATSAYIN KARATU: N.C.E.AURE: BabuWASU FINAFINAI DA KA FITO CIKINSU:

Martani, Lalura, Ajali, Ba�asi, Matsayi, Badali,Juyin Mulki 2, da sauransu.

SUNAN DA KA FITO DA SHI: DageKAYAN DA KA FI SON SAWA: Wanda Allah Ya

hore�YAN WASAN DA KA FI SO: Kowa da kowaABIN DA KA FI SON A YI MA KYAUTA DA SHI:

Ku]iHALAYEN DA BA KA SO: Wula}anciHALAYEN DA KAKE SO GA MACE: Kare mutunciINDA KA FI SON KA ZIYARTA: Amerika

MU SAN �YAN WASA

Baba Ali Boss

Dage

43

Page 45: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

R I K I C I

Daga BASHIR ABUSABE,a Sokoto

GA dukkan alamu,ba�yan fim na jihohinKano da Kadunada

Filato ka]ai ne suka iya rikiciatsakaninsu ba. Sakkwatawama ba }ashin yadawa ba neafagen rigingimu a ya-su-ya-su cikin harkar fim. A da,halin ha�ula�i da }ungiyarmasu shirya finafinai ta JiharSokoto (SSFMA) ta shiga yatashi daga kanta sakamakonfarfa]o da ita da �ya�yantasuka yi bayan labarin damujallar Fim ta ta~a bugawa.Sai dai wani abin ba}in cikishi ne mugun halin ya aukawa }ungiyar �Rima Films�da ke �Sokoto Guest Inn� acikin birnin na Shehu, wurinda �yan fim na garin sukamaida tamkar dandalinsu.

Duk wannan kuwa ya biyobayan kwance wa }ungiyarzani a kasuwa da ]aya dagacikin shuwagabannin}ungiyar kuma wanda shi nesilar kafa }ungiyar ya yi. Al-Mustapha Abdullahi(�Musty�) shi ne ma�ajin}ungiyar kafin ya sallamikansa bayan ya yi zarge-zarge a kan }ungiyar. Dagacikinsu har da zargin kaka-gida da shugabannin}ungiyar suka yi damu}amai, da rashin iyamulki da kuma rashin ci-gaban }ungiyar.

�Musty� ya yi i}irarin cewaai ko majalisar }olin }asarnan ba ta kai su taro ba ammaba wani ci-gaba da aka samua }ungiyar; in ma har akwai,bai wuce zarge-zarge dagulmace-gulmace da ke taya]uwa a ciki da wajen}ungiyar.

A cewarsa, bayan fitarsudaga kamfanin na �RimaFilms� shi da abokinsa ShehuGarba, sai abubuwa suka cigaba da ta~ar~arewa, indadaga }arshe tilas aka yo

gungu aka zo ana ro}onsuda su koma }ungiyar dominganin irin ci-bayan da takeyi bayan fitarsu. Su �Musty�sun amince amma bisashara]in sai shugabanninsun sauka an sake wani za~e.

Ga alama dai ana bu}atarsu Mustapha a wannan}ungiyar domin kuwa nanda nan shugabannin sukasauka ]in. Sai dai akwaiwa]anda Al-Mustapha yakira �munafukan,� wa]andaba su ji da]in wannan abinba domin, inji shi, wai idanba su ba ba wanda ya iyamulki kamar yadda sukecewa, sannan kuma su kewahala kan kamfani daga}arshe suka ce su ne suka sanmanyan mutane wa]anda zasu ba su ku]i.

Al-Mustapha ya ce dalilinda ya sa ya kira su�munafukai� shi nemembobin sun ba su amanasun ci, sannan kullum cikinshe}a masu }arya suke idansuka yi masu al}awari susa~a. �Kalmar azaba tatabbata ga shugabanniazzalumai� inji MustySokoto.

Sai dai Al-Mustapha ya yihamdala ga Ubangiji dominkuwa kamar yadda ya ce�ya�yan }ungiyar Rima sungano }arairayin da ake masu.Har ya yi rantsuwa cewadaga cikin shugabanninkamfanin ba mai iya karekansa daga zargin da yakemasu, kuma ya ce yana saneda irin yadda suke zagayawawurin manyan mutane sunakar~ar ku]i amma sai su jefaa aljifansu.

Amma kuma tsohonma�ajin }ungiyar ya ceshugabannin sun sauka nebisa ga yarjejeniyar da sukayi tun da farko. Sai dai waniabin mamaki ba za~e aka yiba,sai dai kawai aka ce anna]a Malam Sa�ad shugabankamfani na je-ka-na-yi-ka,Bashir Ahmed Umarmataimakin shugaba dakuma [alhat A. Jaba amatsayin sakatare. Sai daiwata majiyata fa]awa Fimcewa Bashir Umar ya }ikar~ar mu}amin mataimakinshugaba saboda shi ba ]an}ungiya ba ne, shi kumashugaba da sakatare sai sukanemi a ba su wu}a da namasannan suna son yin aikinsuba tare da hannun tsohonshugaba ko sakatarensa ba.

Da sababbin shugabanninsuka yi taro sai suka tsigeAmina Jummai Yakubu amatsayin jami�ar ya]alabarai na kamfanin.

�Wannan abin bai yi wasaurayin Amina da]i ba,� injimajiyarmu, domin kuwa, acewar majiyar, Ahmed[anjummai, tsohon sakatare,shi ne babban saurayinta.Nan da nan tsofaffinshugabannin suka ]aukimatakin gaggawa, inda nantake suka sake tarwatsasababbin shugabannin,kuma suka sake mayegurbinsu na gado.

Da yawa wa]anda sukahalarci wannan taron sun yikukan cewa ba a son gaskiya.Tun daga wannan lokacinmutuncin manyanshugabannin ya }arazubewa. Sai dai wani ihubayan hari da shugaban}ungiyar IbrahimMohammed ya yi shi neyashirya za a ba wasushugabanci amma za su yiaiki kafa]a da kafa]a da sutsofaffin shugabannin. �Ka jishugabanci irin na kamfaninRima da ba ya tafiya bisatafarkin tsarin mulki!� injiwani ]an }ungiyarda yace asakaya sunansa.

Shugaban �yan tawayen}ungiyar, Al-Mustapha, yayi kira ga shugabannin}ungiyar da kuma duk wanimai sha�awar maida raddi da

Yadda rikicin Rima ya dabaibayeSakkwatawa

Al-Mustapha Abdullahi,furodusan Tsautsayin

Shagwaba

Ahmed S. Danjummai,Sakataren ‘Rima Films

Production’

Da sababbin shugabannin suka yi taro sai suka tsige AminaJummai Yakubu... �Wannan abin bai yi wa saurayin Aminada]i ba�... Nan da nan tsofaffin shugabannin suka ]aukimatakin gaggawa, inda nan take suka sake tarwatsa sababbinshugabannin, kuma suka sake maye gurbinsu na gado.

44

Page 46: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

ya fito ya kare kansa. �Kumanan gaba zan }ara fasa }wai,inda zan fa]i sirrin abin dashugabannin Rima suketabkawa, sirrin TsautsayinShagwa~a 2 da kuma abinda ya hana shi fitowa,�injishi.

Mujallar Fim ta waiwayi~angaren shugabannin daake zargi. Mai magana dayawunsu, Ahmed S.[anjummai, ya }aryata wasudaga zarge-zargen, sai dai yatabbatar da wasu. Misali, yanuna cewa an je bikon su Al-Mustapha bayan tawayen dasuka yi wa kamfanin sai daiya ce abokinsa B.A. Umar neya sa a je. Haka zalika kanzargin cewa sun kankamemulkin kamfanin,[anjummai ya yi wanka maikama da jirwaye domin kuwacewa ya yi duk wanda akaba wani mu}ami, to shikenanba sake kiran taro. Yace,�Kuma su wa]annan mutaneba wani mai son ci-gabanwannan }ungiya, shi ya samu kuma muka maida shikamar gado.�

Sai dai kuma [anjummai

ya }aryata cewa kamfanin baisamu wani ci-gaba ba tsawonshekaru biyar da kafa shi. �Inma rashin ci-gaban ne, to ya

Amina Jummai Yakubu,‘Tsohuwar’ Jami’ar Watsa

Labarai

samu asali daga wurinsuMustapha, domin su sukakafa shi tun cikin 1996, muba mu shigo ba sai 1998,�injishi. Ya }ara da cewa lokacinda suka shirya waccan

yarjejeniya da suka je bikonsu �Musty� ba su yi maganaraje maganar a je a rukuni ba.�An dai yi maganar canje-canje,� inji shi.

Game da }orafin cewasababbin shugabanni sunnemi a ba su wu}a da namakuma har sun fara ]aukarmataki a kan budurwarsaAmina, [anjummai ya ce,�Su wa]annan sababbinshugabannin su suka bu}acemu domin mu koya masu suma su iya.� Game da Aminakuwa, ya ce duk Rima ba maiaiki kamarta kuma tasadaukar da ranta amma saia yi mata wannan butulcin,saboda an nuna mata}iyayya }iri-}iri? �Shi ya saba mu yarda ba, kuma ni babudurwata ba ce ko alama;zaman da muke yi da ita nekawai na mutunci.�

Da yake magana kan tsarinmulkin }ungiyar kuwa,sakatare [anjummai cewa yayi, �Muna da shi; in ana songanin shi yana nan. Kuma daaka ce ina kar~ar ku]i wurinmanyan mutane, ba gaskiyaba ne. Tsautsayin Shagwa~a

1 da ni aka fitar da shi? Ai kaga da taimakon da mukesamu da kuma bashin damuke ciyowa muka fitar dashi. Ko ko shi wanda ya yimaganar ya ba da ku]i wurinfitar da fim ]in?�

Sai dai kuma wani labarida muka samu da ]umi-]uminsa ya nuna cewa }arinbarazana na }ara hawa kan�Rima Films,� domin kuwamasu dandalin da �yan Rimada kuma mafi yawan �yanfim na Sokoto ke taruwa,wato �Sokoto Guest Inn,� sunfatattaki �yan Rima ]in dakuma duk wani ]an wasa dayake wannan wurin wanda yayi kama da Dandalin Matasana Fagge ga �yan fim a Kano.Mai yiwuwa wannan bai rasanasaba da yadda masu wurinsuke ganin ana dabdala daholewa da kuma caku]ewarda maza da mata ke yi awurin ba tare da doka ko odaba, duk kuwa da cewa anaShari�a a Jihar Sokoto.

Masu nazarin al�amarinsun ce ba shakka wannanrikici zai shafi ci-gabanharkar fim a Jihar Sokoto.

45

na auri Ahmed ta bar garinnan ba ta komo ba saishekaranjiya (24/8/01) samada shekara takwas. Ni Fatimada na yiwa iyayena haka narabu da su na aure shi, ammaka ga yadda ya yi min!

Fim:Mu koma kanshigarki fim.

Fatima: Ka gane ko?Shi ya sa na ji da]in waniabin da Iyan-Tama suka yi.Lokacin da na je sai suka ceba za su ]auke ni ba sai nakawo takardar amincewadaga iyayena tunda na ce bani da aure. Da na kawotakarda ban tsira ba, saiAhmed ya fara bi yana ~atamin suna. Da suka ga hakasai suka ce in kawo iyayena.Kan wannan ne kuwa sukataka har Iyan-Tama suka cesun amince in yi fim tundaba jarin da zan kama wata

sana�a gare ni ba, kuma basu }aunar in bar gida inayawon iskanci.

Fim:Ina takardar da yasake ki? Ko zan iya ganinta?

Fatima: Na maida takotu saboda shari�ar da mukeyi, tunda can aka ]aura manaaure shekarun baya da sukawuce.

Fim:Sai batun gudu. Yarabuta cewa daga gidansakika gudu kika arce gidankawunki Mista Ocito.Gaskiya ne?

Fatima: Ba gaskiya bane.

Fim:To idan ba gaskiya bane, ya aka yi kuka rabu?

Fatima: Rigima mukayi da shi. Ni na saka �ya�yanamakaranta. Ku]in makarantaya gagare ni aka koro min sugida. Guda hu]u na saka; kasan akwai tagwaye, Hassanda Husaina, sai kuma Fatimawacce ita ce gambonsu.

Rigimar Fatima daAhmed AbdullahiCi gaba daga shafi na 36

Fim:To su dai jama�a afagen fim ai kallon mataraure suke yi maki.

Fatima: Wannan kuwaai ruwansu. Abin da ya kawohaka don ya je ya raba masutakardu. Don Allah, ina sojama�a su daina saurin zargi,su ri}a bari sai sun tabbatarda gaskiyar lamari.

Fim:Wace rana za a je

kotun?Fatima: Ranar 29 na

wannan August ]in.Fim:To sai mun ha]u a

kotu.Fatima: Za ka je?Fim:{warai kuwa. Me zai

hana? Insha Allahu za ki ganni.

Fatima: To na gode.Sai ka je.

A FIM ta watan gobe...

* Hira da

Alhaji MusaNa Sale,baban dillalankaset damawakanHausa

* Hira da

M. Tijjani BalaKalarawi

Rukayya UmarSanta

Cinnaka

Page 47: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 200146

AN da]e ana rubuto wawannan mujallar wasi}umasu ]auke da }orafin cewame ya sa mujallar Fim batata~a yin hira da HajaraAbubakar ba? To ba wanidalili ne ya kawo haka ba.Idan an tuna, mun ta~a kawohira da ita Dum~aru. Dubishafi na 39 na Fim ta 12 (watota Disamba 2000), za ka ganta. Sai dai kuma cikakkiyarhira da fitacciyar jarumar cekurum ba mu kawo maku ba,sai fa a yau.

A cikin hirar da suka yi tareda ASHAFA MURNAIBARKIYA, za ku ji asalinta,tarihinta, zaman aurenta dakuma yadda aka yi ta zamaruwa biyu.

Wani abin mamaki shi nea daidai lokacin da akerubuta wannan labari wanisaurayi ya shigo cikinofishinmu a Kano, ya kawowasi}a wacce ya ce yayarsace ta aiko shi. Matashin yayi dariya lokacin da ya}yalla ido a kan teburi ya gawata takarda wacce akarubuta wasu daga cikin jerinfinafinan Dum~aru. Ai nan

yi kwantai ba ta sami miji ba.Ibro ya gaji da ganinta a gidasai yake buga cacar tambolada ita a bisa shara]in wandaya ci tambolar to ya dace dawata kyakkyawar budurwaDum~aru.

A duk �yan wasa mata babuwacce yara ke tsokana kamarDum~aru. Kafin su faratsokanarta kuwa can bayatsangwamarta suke yi kanabin da ta yi wa FatiMohammed a cikin Sangaya1, suna cewa, �An da]e anagulma su Dum~aru shegiyarmata!� Sai da yara suka faragane abin shiri ne sai sukuma suka mayar da abintsokana.

Wanda duk ya kalli fim]in Tafarki kuma zai ga cewaHajara a matsayin Inyamirata fito. To ha}i}a kamaryadda muka gaya maku acikin Disamba, ba za�idakuma babu inke Dum~aruInyamira ce, wato �yar }abilarIbo.�Ni ruwa biyu ce.�Wannan furuci ta fara yi wamujallar Fim lokacin da akatambayi asalinta. A ta}aicemahaifinta ]an }abilar Ibo

Mata,muri}emutuncinmu � Dum~aru

take sai ya ce, �Ni ma wannan wasi}ar abin da ke cikintatambaya ce kan dalilin da ya sa ba ku ta~a ba da labarinDum~aru ba.�

Wani abin mamakin kuma shi ne, duk da shaharar da Hajarata yi har yanzu ba ta ta~a fitowa a fim ]in wasu manyankamfanonin shirya fim ba, in ban da �Sarauniya Films�. Saikwanan nan ne ma �Mandawari Enterprises� ya gayyace tainda ta yi fitowa uku a cikin sabon fim ]insa Burin Zuciya.

Dum~aru kenan. {ulla makirci, Dum~aru; algungumanci,Dum~aru; barkwanci, Dum~aru; �yar aikin matan gida,Dum~aru. Kai, babu irin sigar da ba ta fitowa da ita a fim.

Shi ya sa masoyanta ke }alubalantar masoyan wasujarumai mata da cewa ba za su iya yin wasan da Dum~aru tayi a cikin shirin Sana�a Goma ba. A cikin Sana�a Goma neDum~aru ta fito a matsayin mummunar ]iyar Ibro wadda ta

ne, mahaifiyarta kuma Bakanuwa.Dum~aru �ya ce ga marigayi Mista O.C. Ikpo, wanda kafin

ya rasu cikakken akawu ne mai zaman kansa (charteredaccountant). Kai duk ta kame-kame ta }are tunda ga wa}a abakin mai ita. Kuma wa}ar mai da]i, mai tsawo.

Fim: (bayan sallama) Hajara ke wacece?Hajara: (bayan ta ]auki dogon lokaci) To ni ruwa-biyu ce

a ta}aice; mahaifina Ibo ne, sunanshi Mista O.C. Ikpo,mahaifiyata kuma Bahaushiya ce �yar asalin garin Tsakuwacikin {aramar Hukumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano. Anhaife ni a 1976, a compound ]in (tangamemen gida) T.O.Ikpo da ke }auyen Umuokechi Obiohuru na yankin Ohuhuda ke }ar}ashin Umuahia ta Jihar Abiya. Garinmu ]aya daCif Micheal Okpara.

Hajara Abubakar (Dumbaru)

Page 48: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001 47

Fim: To a ina kika yikaratu?

Hajara: Na yi firamare a�Orieameaji Central School�kuma na yi �Afugiri Girls�Secondary School� ta garinAkpahia, duk a Jihar Abiya.

Fim: Me ya sa kika bari harsunan Dum~aru ya bi ki?

Hajara: To ai Dum~arusuna ne na fim, kowa ya sanikuma da aka rubuta labarinfim ]in haka sunan ya zo, nikuma na hau.

Fim: Bayan kin gama yinfim ]in da kika fito da sunanDum~aru ba ki fahimci cewasuna ne na aibi ba?

Hajara: Ko ]aya, an ba nine don in fito in yi suna kumana yi.

Fim: Yaya aka yi kika baroUmuahia kika dawo Kano?

Hajara: Tun lokacin da inamakaranta duk shekaranakan zo hutu Kano in zo inga mahaifiyata, da yakemahaifina ya rasu. Ammayanzu kuwa ina zuwaUmuahia a kai a kai don inga kakannina da }annenkakana da sauran dangi.

Fim: Me ya sa kika fa]oharkar finafinan Hausa?

Hajara: Sha�awa ce, dontun lokacin ina makaranta,nakan yi wasanni idan anawani biki na makaranta,watau dirama. Har ya kai anba ni debate and dramaticprefect (shugabar ]alibaimasu wasannin kwaikwayoda shirya gasar muhawara).

Fim: Wane fim kika farafitowa?

Hajara: Wanda na farafitowa a cikinsa shi ne Zarge.

Fim: Wasu kawo kansusuke yi, wasu kuwa kawo suake. Shin ke wa ya kawo ki?

Hajara: Ni lokacin da nafara ra�ayi sai na samimahaifiyata na ce ina dasha�awa in yi fim ]in Hausa.Ta ce, �To duk da mahaifinkiya rasu ko kin fa]a wa}annensa da kakanninki?�To sai na je na shaida masu.Suka ce �Ba komai ai sana�ace; mu ma ai yarenmu ga sunan suna yin �NigerianFilms.��

Da yake ina da wani yaya,Sani Lamma, wanda a halinyanzu yana daga jami�ancikin Hukumar TaceFinafinai ta Jihar Kano � to]an�uwana ne; kakannimu

na uwa ]aya da shi; damahaifiyar babansa damahaifin babata, uwarsu]aya ubansu ]aya � saibabata ta ce in same shi tundashi yana irin wannan harka.Ba kai tsaye na shiga fim ba.

Fim: To me ya sa kikefitowa a ~angaren ~atanci?

Hajara: Ba komai; ganinake fa]akarwa nake. Ni ban]auki hakan wani abu ba.Kamar yadda malamai za sufito su yi wa�azi, to ni ma hakana ]auki fim. Kai, na fi dukwata �yar wasa ko wani ]anwasa imanin cewa fa]akarwanake yi.

Fim: Mu koma ga ladar daake ba ki idan kin yi wasa.Ko kina da tsada?

Hajara: Wannan sirrina neba zan fa]a ba.

Fim: Tunda ba za ki fa]aba, sai ki fa]a mana abin dakike yi da ku]in idan kintara.

Hajara: Shi ma ba zan fa]aba. Tsakanina da iyayenakawai muka san abin da nake

mutane na cewa wai na yicamama ne. Ni dai kowanefim duk ]aya na ]auke shi.

Fim: Wace sana�a kike yikafin ki fara shiga fim?

Hajara: Da ma can ina dasana�a, ina sana�ar gwanjo.

Fim: Gida-gida kike shigako kuwa kasawa kike a bakinkasuwa kina ka]a masu}ararrawa?

Hajara: Ina shiga gidajetalla, ina kuma sayarwa agida.

Fim: Ko kina jin wani abuidan yara na damunki da �GaDum~aru ga Dum~aru!�?

Hajara: Ai wannan kullumgodiyar Allah nake, ba na jinkomai. Kullum sai addu�a inata gode wa Allah.

Fim: Ko kina jin yaren Ibogangariya?

Hajara: Sosai ma kuwa!Kai, jarabawar WAEC madistinction (yabo) na samu aIgbo Language. Ko yanzuaka gayyace ni zan iya yinfim da Igbo da kumaTuranci.

yi.Fim: Wanne gyara kike

ganin ya dace a yi wafinafinai?

Hajara: Ai ban ga wanigyara ba, tunda wasan fim naHausa namiji ko ta~a hannunmace ba zai yi ba.

Fim: Kin ta~a yin aure;Bahaushe ne ki ka aura?

Hajara: Bahaushe ne naaura. Na haihu, haihuwa]aya namiji.

Fim: [an yana da rai?Hajara: Yana nan, sunansa

Ahmed.Fim: Shekararsa nawa?Hajara: Shekararsa takwas,

yana kuma makaranta.Fim: Yanzu yana ina?Hajara: Yana hannun

mahaifiyata, amma ubansa neke kula da shi.

Fim: Ita mahaifiyar takitana ina?

Hajara: Tana Gwammaja (aKano) tana aure.

Fim: Amma ni ban yardaba a ce ba bambanci tsakaninIbo da Hausawa.

Hajara: Al�ada ko addinikake magana?

Fim: Duka.Hajara: E to, tun can da ma

ni Musulma ce, al�adar cankuma al�adata ce. Ka ga banga wani bambanci da zangani ba.

Fim: Ku �yan wasa kunaburge �yan kallo. To ku kumame ya fi ba ku sha�awa dagamasu kallonku?

Hajara: Yadda mutum nazaune sai a kawo masa ziyarako kuma idan an ha]u agaisa, ko a rubuto wa mutumwasi}a, gaskiya dukwa]annan suna burge ni.

Fim: Yaran da ke bin kigefen titi suna tsokanarki kosuna ~ata maki rai?

Hajara: A�a, ai abin nasu}uruciya ce. Ba wanda baiyi }uruciya ba lokacin dayake yaro.

Fim: Hajara ga shi kinafitowa a manyan finafinaiamma sau da dama ba a bugohotonki a fostar babban fimsai a camama. Ko kina jinhaushin hakan?

Hajara: Ko ]aya ni baburuwana. Tunda dai mutumzai kira ni fim, in yi in gamaya biya ni ku]ina, kuma zanyi masa abin da yake bu}ata,

Ci gaba a shafi na 49

yi da ku]in, sai Allah.Fim: Duk da shaharar da

kika yi har yau ba ki ta~a yinfim a Iyan-Tama,Ibrahimawa da �MandawariEnterprises� ba?

Hajara: Mandawari daiwannan lokaci ya kira ni inyi masa scene uku cikinwani sabon fim ]insa BurinZuciya. Wa]ancan kuma bawani abu ba ne, rabona nebai tsago ba. Idan rabona yaketo duk inda nake sai annemo ni.

Fim: Duk da cewa kinafitowa a manyan finafinai meya sa aka wayi gari sai ga kidumu-dumu cikin finafinancamama (irin na s Ibro)?

Hajara: Ni dai ban ]aukazan wani camama ba. Na]auka duk ]aya ne. saibayan na yi fim wai sai in ji

Fim: Daga lokacin da kikafara fim zuwa yau, an ta~a baki wata kyauta ko kuma anta~a samunki har gida aka yimaki wata kyauta?

Hajara: Gaskiya akwaiwannan, na sami kyaututtukada dama. Don wa]ansu mada suke cewa sun san ni, dukalbarkacina sun sami kyauta.Wani dalilina ya samujarabawa a jami�a da ya cekawai ya san ni.

Fim: [an unguwarku ne?Hajara: Ban san shi ba,

kawai ha]uwa muka yi dashi.

Fim: Wasu mata sun farazama furodusoshi sunashirya fim na }ashin kansu.Ke fa, ko kina da wannanniyyar a zuciya?

Hajara: Ni dai ba zan cekomai ba. Sai yadda Allah Ya

�Kamar yadda malamai za sufito su yi wa�azi, to ni ma haka

na ]auki fim. Kai, na fi dukwata �yar wasa ko wani ]an

wasa imanin cewa fa]akarwanake yi.�

Page 49: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Daga WAKILINMU

BIKIN bayar dakyaututtuka ga finafiaida masu shirya su wanda

za a yi a wannan watan a Kaduna,ga alama lallai zai yi armashi.Dubi dai yadda furodusoshi dadaraktoci daga ko�ina cikinArewacin }asar nan suke taazamar sayen fom da kuma yinrijistar finafinansu. Mujallar Fimta }ara yin wani bincike danganeda wannan gagarumin taro da zaa yi a }arshen wannan wata naSatumba. Kazalika za a jira�ayoyin mutane da damadangane da tsarin bayar dakyaututtukan ga mai rabo.

Jumma�ar da za ta yi kyau, acewar Hausawa, tun daga Larabaake ganewa. Shi ya sanya idanaka dubi tsarin bikin tun a yanzusai a fassara shi da cewa nasarata samu. Madubin da wakilinmuya haska ya nuno masa cewa anakyautata zaton halartar wa]annanmanyan ba}i:

1.SHUGABAN TARO:Tsohon Shugaban {asa JanarYakubu Gowon, wanda kuma shine shugaban }ungiyar tuntu~arjuna ta Arewa, wato ArewaConsultative Forum.

2. MAI MASAUKIN BAKI:Gwamnan Jihar Kaduna, AlhajiAhmed Mohammed Ma}arfi.

3. BABBAN BAKO NAMUSAMMAN: Gwamnan JiharBauchi, Alhaji Ahmed Mu�azu.

4. UBAN TARO: Mai MartabaSarkin Zazzau, Alhaji (Dr.)Shehu Idris.

5. BABBAN MAIMASAUKIN BAKI: Mai MartabaSarkin Birnin Gwari, AlhajiJibrin.

Ba mamakin ganin cewa wasumashahuran mutane za su halarcibikin shi ya sanya a yanzu hakaaka canza wurin bikin daga�Women Multipurpose Centre� dake kan titin Bank Road, aka maida shi zuwa rufaffen filin wasa(Indoor Sport Hall) na DandalinAhmadu Bello. Duk da haka,domin }ara gudanar da

wadataccen shirin kar~ar ba}i,wa]anda suka shirya taron suncanza ranar gudanar da shi zuwa29 ga Satumba, ma�ana sun }aramakonni biyu kenan.

Ganin yadda jama�a ke ta]okin zuwan wannan rana. Fimta tattauna da jama�a da damadomin jin ra�ayinsu. Wa]andaaka tattauna da su kuwa sun ha]ada �yan wasa, furodusoshi,daraktoci da kuma masusha�awar kallon finafinan Hausa.

�Yar wasa Rukayya UmarSanta cewa ta yi wannan tsarina bayar da kyauta yana da kyau,domin �ta wannan hanya ce tarihinan gaba zai tabbatar da cewa bawahalar banza muke yi ba.� Shikuwa babban furodusan fim ]inAlaqa, Alhaji SaniAbdurrashid, cewa ya yi,�Wannan wani yanayin gasa ne,hakan kuwa zai sa a ri}a gyarafinafinai a daina yin su kara-zubemarasa ma�ana.� Sai kuma ya yiro}o da cewa Allah Ya sa wannangasa ta zama ginshi}in ha]in kan�yan fim.

Ita kuwa Aina’u Ade cewa tayi ai ta haka ne kawai za a iyatabbartar da da gwani da kumagwana. �Arewa Films Awardyana da kyau }warai,� inji ta.

Ba su ka]ai ne suka goyi bayanabin ba. Fitaccen ]an wasa AliNuhu nuni ya yi da cewa wannangasa wata shaida ce da za ta nunawa jama�a sun gane shi wannanda aka ba kyautar. Ma�ana, injiAli, wanda ya yi abu har mutane

suka yaba har aka ba shi kyauta,ai abin farin ciki ne.

Kan batun wa]anda suka yi}orafi da gasar shekarar da tagabata, sai Ali ya ce, �Wa]andasuka shirya abin nan fa don ci-gabanmu suke yi, don haka idanan ga kuskure a ri}a nunawa, bawai a ri}a yin }orafi ba.�

Akwai jama�a da dama dasuka nuna cewa ya kamata a ]anri}a saka wa wanda suka ci gasarda wasu ku]i. Wannan ra�ayinasu kuwa ya samu }alubalantadaga jama�a da dama. Fitacciyar�yar wasa Hadiza MohammedSani Kabara cewa ta yi, �Ai suku]i }arewa suke yi idan an baka. Duk da cewa ku]i na dadaraja, ni dai a fahimtata wannankofi ya fi su in dai batun awardne.�

Shi kuwa ]an wasa kumamalamin rawa, Shu’aibu IdrisLilisco , cewa ya yi babbankuskure ne idan aka ce za a ri}aba da ku]i. A fahimtarsa,�Wannan kofi da mutum ko fimzai ci tunda za a rubuta suna ai kobayan shekara talatin sai mutumya ]auko ya nuna wa ba}o kojikansa. Ai ko �Hollywood�(Amerika) da �Bollywood�(Indiya) ba ku]i suke bayarwaba, kofi suke bayarwa.�

Irin wannan ra�ayi kuwa ya yidaidai da na MohammedKabara, wanda shi ma bai goyibayan a ri}a bayar da ku]i ba.Wannan kenan.

Yaro mai tashe Ahmed S.

Nuhu shi addu�a yayi ga wannan gasa,kuma ya }ara dacewa Allah Ya bamai rabo sa�a. Saidai Ahmed ya yimanuniya da cewar,�wanda ya samukada ya yi tunaninwasu aka }i aka bashi. Wanda ya rasakuma kada ya yitunanin cewa waniaka so aka }i shi.�

A Kaduna,furodusa mai tasheYakubu Lere cewa

Bikin zuwa na mai zanen ]aurawa neArewa Films Award:

Ran 29 ga Satumba za a sha kallo a Dandalin Ahmadu Bello da ke Kaduna!

2000: Kasimu Yero yana ba jaruma A’isha Musa kyautar Arewaya yi wannan gasa wani ci-gabane da ya kamata a yi murna dashi. �Mizani ne na aunafinafinai,� inji shi. Duk da cewaya goyi baya, Lere ya yi tuni dacewa yana ro}o kada ya zamaabin da ya kira cinyewa ko waceshekara. Ya kamata duk wandaya ci ko a ina yake a ba shi dominsai an yi haka mutane za su da]ayarda da gasar nan gaba. Ya kumanemi a mai da al}alan shekararda ta gabata, domin a ta bakinsa,�sun nuna su masana ne.�

Yayin da jama�a da dama daaka zanta da su a Kaduna suka yimurna da kai gasar a jiharsu, shikuwa Malam Lawal NaTa’ala, mai sayar da mujallarfinafinai da jarida a bakin tasharmotar Daura, cewa ya yi,�Gaskiya a Kano ne ya fi dacewaa gudanar da wannan gasa.� Anasa ra�ayin kamar yaddaHollywood take cibiya aAmerika, to Kano ce cibiyar fim]in Hausa.

Da muka waiwayi HalimaAdamu Yahaya, wacce ta cinyegwarzowar jaruma (BestActress) a shekarar 2000, cewata yi, �Wannan abu yana nuna ci-gaban Bahaushe ne a ko�ina.�Kan batun wanda ya dace a baiwa kyautar �Posthumous Award�wacce ake bai wa wanda ya bada gudunmawa a harkar fimkuma ya rasu, kashi 70 cikin ]arina wa]anda aka yi hira da su sungoyi bayan a bai wa marigayidarakta Aminu Hassan Yakasai.

48

Page 50: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

kuma abin da zan yi zaiburge �yan kallo, in isar dasa}o, ai shikenan.

Fim: Wasu na ganin cewaba kowa zai iya taka rawarda kika taka a cikin fim ]inSana�a Goma ba,wato fim ]innan wanda kika fito amatsayin �yar Ibro har yaha]a ki ya buga cacartambola da ke.

Hajara: Ba abin da zan ce;ni dai na san fa]akarwa ce.

Fim: Ashe za ki iya yinkowane irin wasa kamar naWasila ko Saliha?

Hajara: {warai sosai kuwa.Fim: A ]aukar wane fim ne

kika ta~a shan ba}ar wahala?Hajara: Babu wani fim da

na ta~a shan wahala wurinshirya shi. Sai dai wurin Gala.

Fim: Gala ta wane gari?Hajara: Galar Bauchi,

Kaduna da Nijar.Fim: Wace wahala kika

sha a Nijar, yunwa ko fatara?Hajara: Muna cikin gidan

sinima za a fara wasa sai akawurgo tear gas (barkonontsohuwa).

Fim: Su wa suka wurgobarkonon tsohuwar?

Hajara: �Yan kallo ba �yansanda ba, wai don ba su samidamar shiga ba. Ai kawai saigudu daga �yan kallon da keciki har mu �yan wasa gaba]aya!

Fim: Wa ya jagorance kuzuwa Nijar?

Hajara: Ahlan Yoko,shugaban �yan camama,muka je yi da {aramar Salla.

Fim: Wasu �yan fim ransuyana ~aci idan darakta yanayawan umartarsu da cewa saian sake scene ]in da suka yi.Shin ke ma ranki yana ~aci?

Hajara: Ni don wannan bana fushi. Idan ma na yi scene]in kuma daga baya na ji ajikina cewa bai yi ba, sai inkira daraktan ko D.O.P. in cegaskiya a sake wani.

Fim: Wace tarangahumakika ta~a shiga a cikin harkarfim?

Hajara: Babu, in dai bawasu mutane biyu da sukari}e ku]i nake bin su bashi

ba. Wannan kuwa na san bawani abu ba ne, halin babune. Ranar da duk suka samusai su biya ni.

Fim: A cikin mutanen ~oye(�yan fim wa]anda basufitowa cikin wasa) an ceakwai wani wanda maganaraure ta shiga tsakaninku.Shin gaskiya ne ko kuwa}adda-}anzon-kurege ne?

Hajara: Allah Shi ka]ai Yasani. Ni dai addu�ata akullum ita ce Allah Ya za~amin abin da ya fi alheri.

Fim: Ai kowa ya yi, kokuwa ke ya tuntu~a damaganar?

Hajara: Ni ya tuntu~a damaganar. Ni kuma na ce idanshi ne mijina Allah Yatabbatar da alheri; idan kumaba shi ne mijina ba, Allah Yafito min da mijina, shi kumaAllah Ya ha]a shi da matartasa tagari.

Fim: Me za ki ce wa �yanfim mata?

Hajara: Abin da zan cemana � don har da ni � dukwanda ya kai munzalinyadda muke a yanzu ai yaisa ya yi wa kansa fa]a.Kowa ya ja mutuncinsa dadarajarsa. Mu mata kullumaddu�armu ita ce mu gamuna cikin gidajenmazajenmu.

Fim: Akwai wani gyaran dakike bu}ata furodusoshi suri}a yi a cikin fim?

Hajara: Ya kamatafurodusoshi su ri}a bai wamalamai }arfi fiye da boka,wato a }arshe a ri}a nunamalami ya rinjayi boka.

Fim: Mu koma kan ]an ki,Ahmed.Ko ana damunsacewa shi ]an Dum~aru ne?

Hajara: Sosai ma kuwa!Shi ma yana samun kyautasosai saboda an san ]ana ne.

Fim: Ko za ki mi}a wanisa}o ga masoyanki,musamman matan aurewa]anda ba su samun damarganinki a fili?

Hajara: Allah Ya sakamasu da alheri. Ina yi masugodiya, kuma Allah Ya }araba su ikon kallon finafinanHausa.

Fim: Hajara mun gode.Hajara: Ni ma na gode.

Ci gaba daga shafi na 47

Hajara Dum~aruArewa FilmsA w a r d :

�Yan kallo ku za~inaku gwanayen!

49

Masu shirya bikin ba da kyaututtuka na Arewasun yi wani tunani, sun ga cewa a bana yakamata a ba mutane masu kallon finafinai dakuma su masu shirya finafinan damar su za~iwa]anda suke ganin sun cancanta a ba sukyauta ta Arewa.

’YAN FIMAna so duk wani mai harkar fim ya fa]i ra�ayinsakan wanda ya ga ya dace ya sami wannankyautar:1. Best Executive Producer of the Year2. Best Cinema Operator of the Year3. Special Film Industry Recognition Award(wannan kyautar ta wanda ake ganin ya fi kowabai wa harkar fim ]in Hausa agaji a bana ce)

’YAN KALLOAna so masu kallon finafinai kuma su cankinasu gwanin, su yanke hukunci da kansu. Gakyaututtukan da ake so su za~a:1. Best actor of the Year (wato Gwarzon [an

Wasa na Bana)2. Best Actress of the Year (Jaruar �Yar Wasa

Mace ta Bana)3. Posthumous Award (wanda za a karrama

bayan rasuwarsa; wannan kyautarwa]anda suka rasu ce)

Tilas ne mutum ya fa]i dalilinsa na za~enwanda yake ganin shi ya fi dacewa. Kuma ahanzarta aikowa, domin a ran 29 ga wannanwatan ne za a yi bikin, don haka ka tabbatartakardarka ta iso hannun mujallar Fim ya zuwaran 24 ga watan Satumba. A ambulan ]inka karubuta:

Arewa Film Awards,c/o Mujallar Fim,P.O. Box 10784, Kano,

ko ka kawo ofis ]in mu da kanka. Mu aikinmushi ne mu ba masu shirya bikin, su za su yial}alancinsu su bayyana wa duniya.

Page 51: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

HIRA DA DARAKTOCI

50

D A R A K T A B E L L O A . B E L L O

IDAN ana maganar shirya fim a Sakkwato, tilas ne a saBello A. Bello a cikin lissafi. Fitacce ne a harkar. Belloya yi suna ne a ~angaren ba da umarni a fim. Shi ne

daraktan finafinai da suka ha]a da ingantaccen fim ]innan mai suna Tuba, wanda ya fito a �yan watannin bayakuma ya ciri tuta a kasuwa. Bello dai shi ne darakta nakamfanin shirya finafinai na �Sakkwata Communications.�

An haifi Bello A. Bello a cikin garin Sakkwato. Ya yikaratun firamare a �Waziri Model Primary,� Sokoto, kumaya yi na sakandare a �Sultan Attahiru Secondary School�inda na yi }aramar sakandare, daga nan ya tafi �NagartaCollege� ya }are. Sai ya tafi �Birnin Kebbi Polytechanic�inda ya yi difiloma a fannin �Agricultural Engineering.�Bayan ya gama wannan, yana gida Sokoto zaune, saiAllah Ya yi masa tafiya zuwa Jamhuriyar Musulunci taIran karatu inda can ma ya yo wata difilomar, amma taharshe (�Diploma in Linguistics�). Da ya dawo sai ya kamaaiki da Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Sokoto. Yanzuhaka shi malamin makaranta ne.

To ya aka yi Bello ya shigo harkar fim, tunda dai ga shibai biyo hanyar ba tun daga farko? Mun tambaye shi. Saiya amsa, �Wato tun fil�azal ina da ra�ayin karance-karance,tun ina sakandare. Daga cikin abubuwan da na lura ina da}wazo a kansu akwai na harshe, musamman na Turanci.Ina karatun novels (littattafan hikaya) da rubutu a kanadabi; (domin yanzu haka akwai wasu littafai na naTuranci (novels) da za su fito). To, tun lokacin banmantawa akwai wata malamarmu, Mrs. Elizabeth Thomas,da ta ta~a ce mani yana da kyau idan na je jami�a inkaranci abin da ya shafi Turanci; akwai kuma wanimalamina ]an Ghana, shi ma takanas ya kira ni yana ba nishawarar in na je jami�a in karanci aikin jarida. To ina jinsha�awata ga finafinai ta samo asali ne tun daga sha�awarda nike da shi ta karance-karancen harshe, to wannan sonadabin Turancin ya sa duk wani abu da ya shafi adabi ina}o}arin in san shi. Shi ya sa ka ga ni ban yin karatunadabi ba amma ko wanda ya yi digiri a kanshi ya shafaman lafiya, amma fa na Turanci, wato literature inEnglish), domin na yi karatuna na daban.�

To, tun daga wannn lokacin ne Bello ya fahimci cewaal�ummar Hausa tana bu}atar ta zama abin da ya kiraideal society, wato al�umma wadda ta ci gaba ko kuma tasan abin da take yi. �A ]an karamin sanina, sai ina ganin acikin hanyoyin da za a iya maida al�umma ta zama tagarishi ne }o}arin isar da sa}wanni masu kyau zuwa gare ta,�inji shi. �To sai nake ganin harkar fim na ]aya daga cikinwa]anda ake bi a nisha]antar da mutane, sannan a lokaciguda a isar da wani sa}o muhimmi wanda zai taimake suda ci gaban al�adunsu da addininsu da kuma tattalinarzi}insu. Wannan shi ya sa na ga cewa ya dace tunda inada haza}a a kan adabi ina iya juya ta in maida ta zuwa gafim, don shi ma wata hanya ce ta isar da sa}o.�

Bello A. Bello ya kuma tuno cewa a can baya wasulokuta da suka wuce, cikin 1994, sun shirya wani fim ��amma dirama zamu kira shi, domin bai cika fim ba,� injishi. �Amma mun tsara shi kamar fim komai da komai,sunan shi Taubatun na Suha. To sai ya salwanta kuma saiduk aka watse, da ma duk ya mu ya mu ne abokai; wasusuka tafi makaranta wasu kuma suka yi wani wurin. Sai acikin 1998 ne muka sake ha]uwa da su Lawalli TukurFaru da wani Aminu Aliyu Bashir injiniya a kamfaninsiminta na Sokoto, muka zauna muka ga cewar ya kamatamu dawo a dama damu a wannan duniyar finafinan. Mukafara rubuta script ]in Tuba, amma sai yanzun muka fiddoshi. Kuma mun fara kenan ba kama hannun yaro dominkwanan nan ma akwai wani muna sa ran fiddo shi.�

Wasu suna yi ma aikin darakta hawan }awara. Sai ka gaba su }ware ba, ba su kuma san yadda aikin yake ba, saikawai su shiga. Mun so mu ji ko Bello yana ]aya dagacikinsu ko kuwa akwai inda ya ta~a yin wannan aikin?

Ya ce, �A gaskiya ban yi aikin darakta a ko�ina ba,amma na san na yi }o}arin na karanci abin da ake ce madarakta da aikin shi a cikin littafai na harkar finafinai alaburare daban-daban, musamman lokacin da nake

Daga BASHIR ABUSABE, a Sokoto

Mun rigaKanawa faradirama

Page 52: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001 51

karatun adabi na sa kai. Saboda sha�awa da nake da shi naadabin shi ya sa ma na karanci wa]anda suka shafifinafinan amma ba tare da na aiwatar da shi ba. Bakatsalandan na yi ma harkar ba, na karance ta, sai daikawai ban ta~a yin ta a aikace ba sai a wannan lokacin.�

To yaya ya fuskanci aikin ba da umurnin a aikace ba akarance ba? �Gaskiya akwai bambanci tsakanin a karatuda kuma a aikace,� inji Bello A. Bello. �Na fuskancimatsala musamman ta mantuwa wajen sassu a aikace saika ga wani lokaci sai bayan na gama darektin sai in tunada wata }a�ida wadda ban bi ba, amma kuma duk da hakalafiya lau. Sannan kuma wannan ne lokacin na farko da nafara yin shi a aikace. Sai matsalar �yan wasa. Duk da yakeni malami ne ina karantarwa; manya sai su tsare mutumgaba a yi da su su gane abu amma su kasa. Sai daga bayana gane rashin rihazal ne ko an kira su ba su zuwa, sannanba su son bin doka.�

Wakilinmu ya lura da cewa matsalar da daraktocinSakkwato suka fi samu ta �yan wasa ce kamar yadda wanidarakta na kamfanin �Faru Films� da ke birnin na Shehu yata~a ce masa. Ko Bello ma ya yarda da haka?

�Ba mu ]aya da daraktan Faru shi yana ganin wayewace ba su yi ba, ni ko ba ni hangen haka saboda aiSakkwatawa sun riga Kanawa fara dirama. Da ma duk maihaza}ar yin dirama zai iya yin fim. To ka ga duk maikwanyar yin dirama to yana iya dawo da wannan fasahartasa zuwa ga sabon yayin da ake yi yanzu. Ni ba ni ganinrashin wayewa ce. Amma akwai matsala wadda nake jinyake kira rashin wayewa, ita ce rashin sanin muhimmancinabu har a yi; rashin sabo ne. Yanzu ba ga shi ba da mukafiddo fim mutane suna zuwa.�

Wa]anne irin nasarori ne su kamfanin �Sakkwata� sukacimmawa a wannan fagen? A cewar Bello, a Sakkwato su

Alhaji A. AbdulrasheedShugaba

Shaguna Masu Lamba 6 da 7, da 8, Babbar Tashar Mota ta Kawo, Kaduna, Tel.: 062-314033

A shagon ALHAJI ABDULRASHEED ne ka]ai za ku samiingantattun finafinan Hausa na da da kuma na yanzu wa]andake fitowa a kowane mako.

Za a kuma samu finafinan Indiya tsofaffi da sababbi; gaChanis, da kuma finafinan Makosa; ga na addini Hausa daTuranci, ga kuma finafinan bidiyo CD iri-iri sai an darje.

Akwai kuma kaset-kaset na rediyo na Hausa da ke fitowa akowane mako, da dai rediyo kaset iri daban daban.Kayayyakinmu suna da sau}in farashi ga masu sari ko sayen]ai ]ai.

Ziyarce mu a shagunanmu da ke Babbar Tashar Motar Kawoinda ake shiga motar Zariya da Kano.

GANI YA KORI JI!!

ne na farko da suka fito da �Sakkwatawa Communication�.�Sannan ga duk finafinan da aka yi a nan Sakkwato ba ayi fim ]in da ya kar~u ba kamar nau Tuba. Muna dalabarin duk finafinan da aka yi da yadda suka samukar~uwa babu kamar namu. Diloli na Kano sun nuna fim]in yana shiga kasuwa }warai da gaske. Muna iya cewanasara ta biyu ita ce kar~uwar fim ]in mu fiye da sauranfinafinan da aka yi a nan Sakkwato.�

A matsayin Bello na wanda ya karanci yadda harkarfinafinai take a litttattafai daban-daban, yaya yake hangenharkar?

�E, to, har yanzu harkar tana a matsayin jaririya, domina irin karnace-karancen da na yi ni fa ina ganin ko Kanawaba na jin sun }ure a harkar fim, domin yawanci akwaikura-kurai da dama a cikin fim ]in su. Amma muna iyacewa wasu kamfanoni na Kano da Kaduna sun wuceyarintaka sun kai matsayin samartaka. Sannan akwaimatsala wurin masu yin dubbing ]in kasa-kasai (wato]aukar fim cikin kasa-kasai) suna saidawa, domin da yawasai ka ga an saida ma mutum kaset amma ya maido shisaboda yana rawa, sa~anin wasu finafinan irin Nigerianfilms da sauransu.�

Bello ya yi kira a kan harkar finafinan Hausa gaba ]aya,kamar haka: �Da farko dai kada gwamnati ta ]aukawannan harkar ta finafinai ba ta da amfani, ta san cewahanya ce ta isar da sa}o masu amfani ga al�umma. Kukuwa �yan kasuwa musamman na finafinai ku ke iyatallafa ma abubuwa har ku yi }arfi kuma ku samo magarinku suna. Kada ku ji ko oho da wagga harka. Daga}arshe furodusoshi don Allah a dinga kula da ha}}in �yanwasa saboda da ma ana zalutar �yan wasa. A lura da cewaduk yanda labari yake da kyau, idan ba �yan wasa to fimba ya yiwuwa; amma kuma sai a zo ana zaluntarsu?�

Page 53: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

MATSAYIN SHIRYA FIM A MUSULUNCI

Malam Ibrahim Zakzaky

A watan jiya ne muka fara gutsuro makujawabin da shahararren malamin nan,MALAM IBRAHIM YA{UB ZAKZAKY,ya yi a wurin }addamar da fim ]in�{azimiyya Productions� mai suna MaceSaliha:Tsiran Al�umma,� a Kano. A yau munkawo }arashen jawabin. Muna godiya gaHassan Muhammad da jaridar Al-mizanwa]anda ta hanyarsu muka sami jawabin.

DOLE KOMAI NAMU YA DACE DASHARI’A

A matsayinmu Musulmi, komai za mu yidole ne ya dace da shari�a. Saboda haka koda al�adunmu ne, al�adunmu da ba su sa~ada shari�a ne ba za mu nuna. Har za ka gamutum yana rera wa}a da Indiyanci bai sanme yake fa]a ba, saboda yana sayen fim]in Indiya. In da za a sayar da na Hausa, saika je Indiya ka ji wani yana rera Hausa, baisan me yake fa]a ba, ai ka ga zai burge ka,daga nan sai ka ga yana sha�awar ma yazonan. To alhamdu lillahi wannan garin yashahara, har ma ya riga ya zama cibiyarwa]annan finafinai. Kuma ya cancanci ya

saye, ba su san abin da suke sayeba, yana shiga }wa}walwarsu ahankali yana maishe su fasi}ai.Yau da kullum kana kallon abu,tun kana kallonsa mummuna, inkana ta kallo, sai ka gan shi ba abakin komai ba, sai ka dainaganin muninsa. Yanzu idan akaaikata mummunan aiki ba mumusanta ba, to da sannu za aaikata shi ba a damu da shi ba. Inkuma ana nan ana ta aikata shi,da sannu zai zama ma�arufi. Saima a ce shi ne ya dace. Har maana iya cewa nan gaba wani yanaba da fatawar me ya sa aka yi fim]in da ba a nuna kaza ba, donyana ganin lazim ne a a yi.Saboda yau da kullum ana yi, harsai ya zama an saba da shi. Daganan sai ya zama ma�arufi, waiyyazu Billah! Kamar yadda yazo a hadisi ma, har sai ya zamawajibi. Ana nan ana nan har saimutane su mayar da abin da yake

52

Daga

J A W A B I

zama ]in, domin kuwa a nan ne duk da yawan ba}in da sukatuttu~o daga wurare daban-daban, musamman dagakudancin }asar nan, ba su fi }arfin �yan asali, suka iya kawosabbabbin al�adunsu, suka yar da na asaliba; wanda in kashigo wannan za ka ga da idonka al�adun Hausa; al�adunHausawan musulmi ~alo-~alo, ko da ko a Sabon Gari ne. Tokamar yadda dai wannan ya zama rinjayen wannan al�ada akan ba}i, haka ya kamat a yi }o}ari a sayar da wa]annanal�adu ]in namu kyawawa a waje. Saboda haka kamata ya yifinafinanmu su ri}a }o}ari suna koyar da tarbiyya irin tamu.

To takaicin, kamar yadda na karanta a wata Al-mizan ]inda ta fito kamar makwanni biyu da suka shige, cewa wannan�Industry� da ya shahara a birnin Kano ya fara }aurin suna amatsayin cewa su ma�abota yin fim ana samunsu da wasumunanan ]abi�u. Har ma idan wannan ya watsu zai sa dukwanda ya ga wani tauraro a cikin fim zai zama ba ya sha�awadon zai ]auka yana ganin lalataccen mutum ne. To zan yikira ga su masu sauran finafinai na nisha]i da su gane cewaa Musulunci ba wai babu nisha]i ba ne, amma ba a nisha]ida haram. Ko da a wajen raha ne, za a yi ne da halas. Amatsayinsu na Musulmi, kamata ya yi su kiyaye mutuncinkansu. Ba mutum daga zama tauraron fim ya zama ya lalaceba. Ya zama ya kiyaye mutuncinsa. Kuma mun ji a wasu mada ke }asashen waje akwai wa]anda suke kiyaye mutuncinsu,ko suna fim. Alal misali, akwai wata Bajapaniya wadda tasha fitowa a finafinai, sai James Bond ya nemi ta fito a fim]insa wanda wani zai bayyana a matsayin James Bond. Saita ce amma da shara]i, ban da tsiraici, ban da jima�i. Sai akace mata ko da za a ba ki miliyoyin daloli? Ta ce komaiyawan miliyoyin dalolin da za a ba ta mutuncinta ya fi ku]i.Ta kare mutuncinta da na �ya�yanta ya fi mata alheri. A }arshefim ]in da ba ta shiga ba kenan. Don galiba a irin wa]annanfinafinan James Bond kamar ado ne ma a nuna tsiraici, kumaa nuna jima�i a bayyane.

Wa]annan munanan abubuwa da ake zuzzubawa a cikinfinafinai da suka maishe su su ne ado a wajen mutane masu

haram ma wajibi. In dai na farko aka aikata haram aka yishiru, to ana nan ana nan, zai zama halas, wato ba a damu dashi ba. Ba fa ya zama halas a wajen Allah ba. Ana nan, ananan, sai su gan shi mustahabbi; ana nan ana nan, sai su cewajibi; wa� iyazu Billahi!

KIRA GA MASU SHIRYA FIMSaboda haka kirana ga wa]annan masu finafinai shi ne su

kiyaye al�adunmu da kuma da dokokin shari�ar Musulunci.Duk wani abin da za a yi, na raha ne ko na nisha]i, ya zamabai sa~a ma }a�idar shari�a ba. Alhamdu lillahi ga shi dagacikinmu an sami wa]anda su ma suka fara tunanin ya kamatasu shiga wannan aiki na yin fim. Na san a cikin tambayoyinnan da masu mujallar Fim suka yi min (har da cewa): �Kokuna da sha�awar nan gaba ku ma za ku shiga wannan fagena yin finafnai?� Na ce, �E to, lallai kam wani abu ne dayake bu}atar ku]i mai yawan gaske. Saboda haka yanzu daiba zan iya ce maka za mu shiga ba, kila sai muna da halin yi,amma dai a}alla nan gaba za mu ci gaba.�

Na san a}alla bayan juyin-juya hali na Musulunci a Iranan sami ci-gaba sosai ta wannan fuska ]in ta yadda har Iranta sami kyaututtuka na }ungiyoyin finafinai na duniya. Harma akwai wani shirin fim ]in su mai suna �Majid Majidi�,wanda ya shiga ajin wa]anda aka nemi a sami �actor� (jarumi)da ya fi kowanne a duniya. Har ya zo a cikin aji na mutumbiyar da suka fi kowanne, a kan wani fim mai suna TarbiyyarYara. To kuma in ka duba jawaban da aka yi bayan�Revolution� ]in za ka gan su tsaftatattu, ba za ka ga waniashsha ba.

To na�am idan muna }o}ari mu nuna al�adunmu ko kumakoyar da mutane, alal misali muna koyar da mutane sanyahijabi mu ce yana da kyau, to tana iya yiwuwa a nuna wataita ba ta da hijabin. A fim ]in da suka (�yan {azimiyya) yi nafarko, sun nuna haka nan. Sai na ce masu a�a bai kamata ba.Saboda ko da an sami wata yanzu (da) ba ta ga muhimmancinsa hijabi ba, to nan gaba in ta ga muhimmancinsa ta sa, ya za

Page 54: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

ta yi da finafinan da ta yi na bayawa]anda ba ta da hijabin ? Kuma in kace a ]auki wata wadda ba Musulma bata fito da shigarta ta al�ada don yahalatta mata, to ya kuma za a yi in tamusulunta ? Ai muna son ta musuluntane. Saboda haka bai kamata a nuna watamace ba hijabi ba.

Don haka in da akwai wasu dabaruda za a yi, sai a yi, domin in aka nunakowa hijabi zai sa, zai zama ba ma�ana,tunda ana }o}arin a nunamuhimmancin hijabin ne. Kila za anuna wata da ba ta sawa, amma yanzuta gano muhimmancinsa tana sawa. Kota yi shiga ba tare da hijabin ba, mazasun nemi su ci zarafinta, daga baya data sa hijabi ta ga ana girmama ta. Anaiya wasu dubarbari wa]anda yake annuna a zahiri wata mata amma mutumba zai ta~a sanin ko wacece ba. To bilhasali ma da dabarun fim an yi mutum-mutumi, ba mutum ba ne, kai amma saika rantse mutum ne, mutum-mutumi ne.

KU KIRKIRO MATAN DA BABUSU

Saboda haka daidai gwargwadonhali kamata ya yi su yi matan da babusu, wato a yi wasu mata da ba za ka ta~aganinsu ba a duniya, babu su! Ba za kata~a ganinsu ba har abada! Wannankamar wani gwaji ne. A hankali abinzai iya ci gaba, domin in muka bi tarihinsalsalar abin da ya ci gaba, za ka gadaga yadda ya fara a hankali ya sami cigaba ]in. Alal misali jirgin }asa; wandaaka yi na farko da ya bi dogon yatarwatsa dogon ne gaba ]aya. Sai daaka sake wani sabon dogon, ya saketafiya, ya zama da tsada, kuma dukwa]anda suka fito sun yi ba}i }irin,saboda sun sha haya}i. Ga shi duk indaya bi, mutanen gari su ce su a gaskiyarugugin ya ishe su haka. To amma ahankali ana ta yi ana ci gaba har yanzuya kai ana yin jirgi mai aiki da lantarki,wanda zai wuce ba ka ma san ya wuceba. Kai da kanka da kake ciki ba za kasan yana tafiya ba, sai ka dubi waje.Saboda haka daga wannan a hankali zaa kai mustawan da zai kai ga za a iyawasu abubuwa da za su dace cikin sau}ikuma.

A cikin wannan fim da �yan{azimiyya suka yi, wanda suka sa wasuna Mace Saliha, sun nuna wani AlhajiMurtala da matarsa Saliha, wanda yashiga cikin halaye na matsalolinrayuwar duniya, wanda har abokansasuka ba shi baya, amma matarsa takasance tare da shi. Kuma aka yi, akayi matar ta rabu da shi, ta fuskanci�yan�uwanta ta }i yarda, ta dage. Sunanan, suna nan har jarabawarsa ta}ar}are, kuma Allah (T) ya sa ya cijarabawarsa. Da ma a da yana da wadata,ya shiga halin rashi, Allah Ya maido

masa da wadatarsa. Sannan kuma suwasu abokan sai ga shi sun shiga halinrashi da shi kuma ya bari a da. To harmatar ta ma ba shi shawarar ya tuna dasu, ya taimake su, bai kamata ya yi irinshi abin da aka yi masa ba.

Kun ga a nan in ma nisha]i kake soka ji, to ka ji nisha]in. A ta}aice kumaana koyar da tarbiyya. Na san dukwanda ya ga fim ]in nan zai so matarsata gani. Ya ce, �To kin gani ko? Kin gamace saliha ko? To haka ake yi.� Dukhalin da ka shiga a kasance tare da kai,ko abin da ya yi kama da haka nan.Daga nan kuma sai }ila a yi tarbiyyakuma irin (ta) mazajen nan masu yi wamatansu }eta. Sai kuma a yi wa mazadarasi, kada su kuma su ga mace salihakawai suna iya yin abin da suka gadama. Matar ta zama ta kirki, shi ma yazama na kirki, da abin da ya yi kama dahaka nan. A hankali sai a yi wannan, ayi wannan.

Amma ba zai yiwu ba sai da goyonbaya, goyon baya ta kowane hali. Alalmisali ta hanyar sayen wa]annanfinafinai ]in a gani. Na san da akatambaye ni dangane da finafinan Hausada ake bayaninsu, ko na san ]aya dagaciki? Na ce ni ko ]aya ban ta~a ganiba, amma ina da labarin ana yi. Da madai ba ni da sha�awar wancan da sukekwaikwayo ballantana su ma makwaikwaya! Amma wannan da yake na�yan {azimiyya ne na kalla. Shi ya sama har na ba su shawarwarin yadda yakamata a gyaggyara wasu abubuwa tayadda za su dace da tarbiyyarMusulunci ba tare da an shiga watamatsala ba.

ANA BUKATARGUDUNMAWARKA A WANNANFAGE

To kuma wannan somin ta~i ne. Koda an yi kuskure, abin da ya kamata bakawai tsaki za ka yi ka ce ai bai yi kyauba. Ba da shawarar yadda za a gyara,sai abin ya ci gaba. To suna bu}atarha]in kai ta wajen kasa-kasai ]in dakuma yadda za su mi}e da }afafunsu.Suna bu}atar wasu gudummuwoyi tawasu hanyoyi. Duk wanda zai ba dagudunmuwa, ta hanyar fasaharsa ne, kaga a cikin wannan fim ]in akwai~angarori da suka shigo. To kumawannan ~angare ya shiga wani ~angarecikin ~angarorin wannan harka daban-daban. Da ma can Al-mizan ta kunnokai, jaridodi sun kunno kai, kai ma damujalloli. Kun ga wani janibi na ya]awannan da�awa. Kuma hurras su ma sunkunno kai, har ma yanzu da ganinsuma Hizbullahi kawai! Ai har waniSakataren Tsaron Amerika a �yanshekarun baya ya ce sun gano akwaiwata }ungiya irin Hizbullahi a Nijeriya.Wani a tafiyata London yake ce min ko

ku ne? Na ce su waye in ba mu ba!Sannan kuma bayan nan ga shu�ara�usu ma sun danno suna ba dagudunmuwa ta fuskacin wa}e, su mayarda da�awa ]in ma, wani lokacin in nazo magana sai in ga cewa masu wa}enma duk sun gama wa�azin gaba ]aya.To ga kuma masu finafinai sun danno.Saboda haka akwai bu}atar kowanejanibi a ba shi ha]in kai daidaigwargwado.

To mun cinye lokaci har muke cewadaidai lokacin da ya kamata a ce nakammala jawabi lokacin ya iso, kumani ina ganin zuwa nan ]in ne ya yi manawahala, saboda inda muka fara yadazango kafin mu zo nan mun samicunkoso a hanya. Kila da muna kusa-kusa ne. Saboda haka ga shi muna somu tara ku]i, abin da za mu so shi ne abubburge mu da irin gudunmuwar daza a ba wa wannan {azimiyya ]in donsu ji }arin }arfin fito da finafinai tahanyar sayen kasa-kasai da bandir-bandir na arzi}iyoyi, ta yadda za a taramana dubbai, yadda nan gaba cikinsau}i, ba da jimawa ba za ka ga wanifim ya fito, wa]ansu sun firfito, inshaAllah.

To kuma zan }ara kira ga �Yan�uwamasu fim su lura da cewa wannan shima wani nau�i ne na da�awarMusulunci. Wani abu ga al�amarinMusulmi shi ne duk abin da yake yi, indai ya yi shi bisa dacewar Shari�a, totamkar ibada ya yi, yana da lada. Sai yazama a lokaci guda ka nisha]antar damutane ka samu ku]i, kuma ka samilada, wanda in ba Musulmi ba ne sai yayi irin wannan kuma ba shi da ladarkomai, saboda shi ya yi don ku]i nekawai. Wannan ko ka yi ne dakyakkyawar manufa. Saboda hakawannan tamkar wani aiki ne na ba dagudummuwa ga tarbiyyar al�ummaMusulma. Saboda haka ko da mutumzai sha maganganu, ko ya ji ba da]i, koya ji da wahala, kada ya ce shikenandaga yanzu an fasa; sai ya daure ya gacewa yana yi don Allah ne.

Kuma da fatan wannan zai zamakyakkyawan samfuri ga sauran masufinafnai, su fara kwafar {azimiyyawajen kyautata tarbiyya. Maimakonraye-rayen nan da kwaikwayon �yanIndiya masu bautar gumaka dakwaikwayon Amerika masu kashe-kashe da harbe-harbe, ya zama anakoyar da mutane kyawawan ]abi�u nena Hausawa Musulmi, ta yadda zai samikar~uwa a wasu wurare, har ma ya zamaya }ara bun}asa martabarmu a idonduniya.

Kuma da yake dai muna bu}atarlokaci ne don tattara ku]i, ba zan cikaku da magana ba. A nan nake sallamada ku.

Wassalamu alaikum warahmatullah.

53

Page 55: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 200154

M U T A N E N | O Y E

YAHAYA Adamu Skito mai ]aukarhoton bidiyo ne na fim. Wato shike ri}e kyamarar bidiyo, darakta

yana gaya masa yadda zai ]auki �yanwasa a lokacin da suke wasa. Idan babuirin su Skito, babu fim kenan, tunda baza mu ga hotunan ba a akwatin talabijin]inmu.

To, ko a cikin masu ]aukar shirin fim,Yahaya Skito ba }ashin yadawa ba ne,domin kuwa shi ne ya ]auki finafinaimanya wa]anda sunayensu suka zamaruwan-dare-game-duniya. Fim ]insa nafarko shi ne Maci Amana. Daga nan saiya yi Dare [aya, Jinin Masoya, Imani,Tsumagiya, Wasila 1,2&3, Tasiri, Fadila,da sauransu. In dai ka kalli wa]annanfinafinan, to ka kalli hotunan da Skitoya ]auka ne da kyamara.

Skito dai haifaffen garin Kaduna ne,a unguwar Kabala Costain. A can ya yikaratun firamare, kuma ya yi �RimiCollege� ta Kaduna. Daga nan kuma yawuce Kwalejin Koyon Fasaha taKaduna (�Kaduna Polytechnic� inda yayi kwas a fannin sadarwa (�mass com-munication�) har ya sami difiloma tafarko (OND). Wato dai, aikin da yakeyi yanzu ya ji~inci abin da ya karantoa kwalejin. To amma ba shirin fim yafa]a ba bayan gama kwalejin, a�a, aikiya fara a hukumar matatar man fetur taKaduna, wato NNPC. �Amma wanidalili ya sa na bari daga baya, kuma nakama harkar fim,� inji Skito, mai mata]aya da �ya�ya hu]u.

Yahaya ya shiga harkar wasankwaikwayo ne a cikin 1983 a matsayin]an dirama a wata }ungiya mai suna�Kabala Youth Dramatic Club� aunguwarsu. A lokacin, wasan da~e(�stage drama�) suke yi.

Bayan finafinan Hausan da mukaambata a sama, Skito ya ]auki irinfinafinan nan na Kudu, wa]anda akanyi a Legas da Anacha, wato �Nigerianfilms�. Guda biyu ya yi, wato Opera-tion Sweep da ya yi a Legas, sai kumawani fim mai suna Abamu na Yarabawa.Shi Abamu har kyauta ya samu ta �BestCameraman� da shi.

Yahaya Skito ya sha gamuwa daabubuwan jin da]i da na ~acin rai afagen shirya fim. [aya daga cikinabubuwan da suka ba}anta masa rai shine rikicin da ya faru tsakanin furodusanWasila da jarumar shirin, Wasila Isma�il,

domin duk a kan idonsa aka yi komai.Ya ji zafin cikas ]in da aka samu alokacin da Wasila ta finjire ta }i fitowaa kashi na 3 na wasan. Skito ya ce,�Gaskiya raina ya ~aci, kuma na yiba}in ciki }warai. Ka san mu a wannanharka tamu ta fim, dole abin ya shafeni.�

A kan ko yakan fuskanci wanibambancin hul]a tsakaninsa da �yanwasan Kano da na Kaduna, tunda yakanyi aiki da kowannensu, Yahaya ya ce,�Shi dai ]an wasa duk inda yake, ko naKano ko na Kaduna, suna da abu biyu:ko dai su da]a]a maka ko kuma a samusa~ani. Ni ko�ina na je harkar fim, �yanwasa da furodusoshi duk muna mutuncida su.�

Shin me ya sa ake yawan samun rikicia cikin }ungiyar masu shirya fim taKaduna? Shin ko wannan rikici ya ta~ashafarsa, musamman ganin yana da }afaguda ]aya a cikin ~angarorin da kehamayya da juna a garin?

Skito ya amsa: �Ni dai ban ta~a yin

lillahi, kullum sai dai in yi matagodiya. Maganar da-na-sani kam banta~a yi ba.�

Yahaya ya sha shan wuya a wurin]aukar fim. Amma ya tuno da guda ]ayaa lokacin zantawarmu: �Lallai kam nasha ba}ar wahala a cikin wani daji aIbadan. Can ne na fa]a maka cewa naje ]aukar wani fim mai suna Abamu naYarabawa. Na farko dai na je ina aiki neda �yan yaren da ba nawa ba. Kuma yarene da ba na ji. Sa�nnan mun shiga cikindazuzzuka masu ha]ari, wanda agaskiya ni na tsorata.�

Ba namun daji suka yi arba da su ba.A�a, }ungurmin dajin da suka shiga, gashi a cikin Yarabawa ne ya razana shi.�Daga ni sai daraktan fim ]in mu ka]aine Hausawa. Shin idan wani abu ya faruda mu, yaya za a yi mu fita?�

To, su Skito dai sun fito lafiya, ga shihar yana ba da labarin. Sa�annan watatsaka-mai-wuya da ya shiga kwanannan, wadda kila ba zai ta~a mantawada ita ba, ita ce harin da �yan fashi da

Y A H A Y A

dakatar da wasu,daga cikinsu har dashi kansa Skito.Da aka tambaye shiyadda abin yake,sai mai ]aukarhoton ya kada bakiya ce, �Ai ba rikiciba ne. Wasuku]a]e ne akanema mu bayar,wasu kuma ba subayar ba. Gaskiyani ma ina cikinwa]anda ba subayar ba. Wannanabu kuwa ya farune kwanan bayalokacin da akes h i r y e - s h i r y e ntaron furodusoshinArewa a Kaduna.�

Shin ko Skito yata~a yin da-na-sanin shigawannan harka,ganin cewa da canbaya ya yi aiki amatatar man feturinda wasu ke ganinwuri ne mai tsoka?

�Ni dai harkarfim alhamdu

rikici da kowane furodusa ba. Harkatashi ne a ]auke ni haya in yi aiki. Idanna gama kuma in ba ka kaset ]in ka kabiya ni ku]ina. Saboda babu ruwanada shiga rikicin manyan furodusoshi,ni ba furodusa ba ne.�

Duk da haka, an ta~a samun sa~anitsakanin su �yan fim na Kaduna, har aka

Yahaya Skito wurin daukar shirin Wasila 3

Sarkin ]auka r hoto

Page 56: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001 55

hasko Wasila har aka san ta, kuma shiya haska wa jama�a Sani Mo]a ya yisuna. Shin ka ta~a yin tunanin riki]ewaya koma ]an wasa? Skito ya ce shi baita~a yin wannan tunanin ba. �Ni daisana�ata ita nake alfahari da ita. Nakanyi farin ciki idan na gan su.�

Mun tsokano Skito da wata tambaya.Shin da gaske ne ana biyan masu ]aukarhoto irinsa ku]i fiye da sauranma�aikatan wasan fim? Sai ya amsa afusace: �Kai rabu da duk mai fa]arwannan maganar! Sai dai zan iya cemaka samun biya mai tsoka ko }alilanya danganta ne ga kamfanin da ka yiwa aiki. Misali, kamfanin �Sarari Ven-tures� na Alhaji Sani Abdurrashid da keKano aikin da yake mani ya fi }arfinaikin da nake masa. Haka nan shi maYakubu Lere ko ban yi masa aiki baabin da nake samu ta hannunsa kamarkyauta ko tallafi ai mai yawa ne, sai daigodiya. Lere fa har gida yake zuwa yaba ni ku]i!

�Ba ni son in ta magana kan YakubuLere don kada a ce na cika yabonsa.Abin da Lere yake yi min sai godiya,Allah ya saka masa da alheri. Ba shika]ai ba, lokacin da na haifi ]anaAbdulmalik, Sani mai �Sarari Ventures�ya ba ni naira dubu ashirin. YakubuLere har gida ya same ni ya ban dubudubu goma lokacin haihuwata ta biyua wurin sunan ]ana Muhammadu Sani.Shi ma Abdullahi Maikano ya ba ninaira dubu biyar.�

To lallai Skito yana amfana da shirinfim bakin gwargwado.

Mun nuna wa Skito cewa �yan wasa,

furodusoshi da ma wasu masu ci daharkar wasan fim suna da }ungiyoyi.Shin ko su ma cameramen suna da}ungiya?

Skito ya ce: �Gaskiya ba mu da

makami suka kaimasu lokacin suna]aukar wani fim acikin dare a Kano.Mun ba ku labarina fim ta watanYuni. Abin ya farune bayan mun yihirar nan da Skito.

To, shin koSkito yana yinwani kishi koganin }yashiganin cewajama�ar gari ba susan da mutaneirinsa ba a harkarfim, tunda sumutanen ~oye ne,ba su fitowa a fim?Babu ma kamar inaka yi la�akari dairin gudunmawarda su masu ]aukarhoto sukebayarwa. �Ni da]ima nake ji da farinciki,� inji shi.

Shi ne fa ya Yahaya tare da yaran da ya dauka a cikin shirin Tsumagiya

Me Skito zai ce a kan haka? Wannan tace tambayar }arshe da muka yi masa.

Sai Skito ya ]an yi tunani. Can yanisa ya ce, �Ni dai babu wadda ban ta~aamfani da ita ba.�

KOLI TRADING COMPANYNo. U.8, Katsina Road by Roundabout, Kaduna

Mu, KOLI TRADING COMPANY, dillalai ne nakowane irin finafinai � na Hausa da na

Kudancin Nijeriya, na }asashen waje dana wasanni kamar }wallon }afa, kokawa

(wato wrestling) � da kuma sababbinkaset-kaset na bidiyo da rediyo, har ma da

na CD.Muna maraba da masu sari da kuma masu

sayen ]ai ]ai.

SAI KUN ZO!A tuntu~e mu aBabban ofishinmu da ke:Lamba U8, Katsina Roadby Roundabout, Kaduna

ko a Reshenmu da ke:Lamba U4, KatsinaRoad, Kaduna

ko kuma ta wayar tarho: 062-241170 ko 062-240228

Sayen nagari, maida ku]i gida!

}ungiya. Mu}ungiyarmu kawaiaikinka ya fito dakai!�

Wannan kenanya nuna cewa ba suda ha]in kai, kumaza a iya saurin cinsu da ya}i idan antunkare su da wani}alubale, ko bahaka ba?

Skito: �E to, bamu sa ran haka. Mudai yanayinaikinmu shi neidan aka kira kaaka ga ba za ka iyaba, sai a ]aukowani ya yi.�

Mun da]e dalurar cewa su Skitosuna amfani ne da}ananan na�uroriwurin ]aukar fim,wato irin su �VHS�da �Super VHS,�wa]anda ake kirada sunan banza na�kyamar gidanbiki,� maimakonsu ri}a yin amfanida kyamara babbakamar �Betacam.�

Page 57: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

tauraruwar fim ]in, wanda (hakan) ba gaskiya ba ne.�A�isha ta ce za ta iya tuno asalin matsalar wadda ta ce ya

faru ne lokacin da kamfanin �Sarauniya� ya kira ta dominyin fin ]in Daskin Da Ri]i, inda aka ba ta matsayin da a}arshe Lubabatu Madawaki ta yi. A lokacin, bisa shawararHindatu sai A�isha ta }i ta yi wasan saboda a ganinta baikamata a ri}a ba ta matsayin uwa ba tun yanzu tana yarinya]anyarta shakaf. Wannan ne dalilin da ya hana ta yin fim]in. Amma duk da haka, �yan �Sarauniyar� ba su ha}ura ba,suka sake kiranta suka ba ta rawar uwa har ila yau a fim]insu na Kainuwa, shi ma kamar wancan karon yayarta tahana ta ta yi.

To menene dalilin da ya sa ake ba ta matsayin uwar duk dacewa }aramar yarinya ce? Sai jarumar ta yi murmushi ta ce,�Wai domin ina da jiki. Amma ai wa]ansu da ake cewa inzama uwarsu da yawansu sun girme ni. Saboda me za a ce infito a matsayin uwarsu?� ta yi tambaya da alamar fushi afuskarta.

Da aka tambaye ta ko wane dalili ke sa ake ya]a ji-ta-ji-taa kanta da kuma manufar yin hakan, sai ta kada baki ta ce,�Ka san mutane, a yanzu wani kana zaune da shi sai ka yitsammani masoyinka ne, nan ko ba }aunar ka yake yi ba, saiya ri}a yi maka zagon }asa yana yi maka kisan mummu}e.�Ta ce ana ya]a ji-ta-ji-tar ne don a sa mata ba}in jini. Tanamamakin masu yin hakan domin ita ba ta damu da harkarkowa ba. �Domin ko fim muka je za ka ga na ware kaina cangefe, domin duk abin da zai ~ata mani rai gudunsa nake yi.Shi ya sa ma ban da }awaye; }awata guda ]aya ce, kuma ba�yar fim ba ce.� Daga nan A�isha Bashir ta yi kira gafurodusoshi da su daina ]aukar ji-ta-ji-ta,ta ce kuma a shiryetake ta yi wa duk wanda ya kira ta fim.

A�isha wadda ta ce ba ta tara ku]in yin fim ba tukuna, tayi fatan alheri ga abin da ta kira �ci-gaban da aka samu nashigar mata harkar fim a matsayin furodusoshi.�

Daga }arshe menene burin Yaya Turai? Sai ta ce, �AllahYa sa fa]akarwar da nike yi ta yi ma mutane amfani. KumaAllah Ya kawo aurena nan ba da da]ewa ba.�

To amin Yaya Turai.

A’isha Bashir (Yaya Turai)

Ina masu cewa Yaya Turai ta daina wasan fim?To ku saurara... Ku tarbe ta a cikin sabon shirinYaya Hindatu Bashir, mai suna Maula

Daga KALLAMU SHU’AIBU

SHAHARARRIYAR jarumar nan A�isha Bashir (YayaTurai) da aka rabu da jin ]uriyarta a �yan watanninda suka gabata saboda ba ta fita a finafinai ta sake

yun}urowa domin a dama da ita a cikin harkar finafinai.Wannan ya biyo bayan muhimmiyar rawar da ta taka acikin sabon fim ]in yayarta Hindatu Bashir, wanda mutaneda dama a fagen shirin fim na Kano (Kallywood) suka zuraido suna sauraren fitowarsa. Ta kuma yi wasu finafinan.

Da muka tambayi A�isha dalilin da ya sa ta yi sanyi a kanharkar fim da aka fi saninta da ita, sai ta ce, �Ka san komai naduniya yana da lokaci. Ni dai ba zan iya cewa ga dalilin daya sa ba. Amma kwanan nan na yi finafinai hu]u.� Finafinansu ne wani mai suna Buri, na kamfanin Iyan-Tama, inda tafito a matsayin }awar Hauwa Ali Dodo, da Tangaran na 2,inda ta fito a }awar Saima, da Judah na �R.K. Studio� inda tafito a sakatariyar Yahanasu Sani. Cikon na hu]un kuwa nagida ne, watau Maula, inda ta fito a matsayin matar SuleimanSa�eed, jarumin fim ]in. Amma a duk finafinan nan gudauku na farko, A�isha ta fito ne a fitowa ta musamman, watauba wata rawar ku-zo-ku-gani ta taka ba, in baya ga Maula,inda ta yi fitowa takwas.

Anya ba wani dalili da ya sa furodusoshi ke gudun jarumarwadda ta ciri tuta a baya a manyan finafinai irin su Ha]arinSoyayya? Da Fim ta matsa tambayarta dalili, sai A�ishar tace, �Ina jin maganganu ta wani gefen wai mutane suna cewaidan aka kira ni fim wai sai in ce ba zan yi ba, sai in ni za a ba

B a s h i rta sake yun}urowa!

56

Page 58: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

’YA’YAN GADO: Salma (a hagu) tare da kawarta Fiddausi

SALAMAT BABA ALIKaratu : Ta gama

makarantar sakandaren �yanmata ta Jogana.

Fim : Ita ce budurwar AliNuhu ta }auye a cikin fim ]inSidiqu. Ta ]an fito jifa-jifa acikin wasu finafinai kamarFargaba, Shuka Ka Girba, dasauransu.

Uba : Baba Ali, wanmahaifiyarta ne wanda yanaharkar fim, musammankwalliya, darakta, dasauransu.

Uwa: Salmat ba ta fuskanciwata matsala ba lokacin da tafara fim.

Inda ta sa gaba: Aure zata yi a ranar 23 ga wannanwatan na Satumba. Za ta aurimai tashen barkwanci ]in nanMika�ilu bin Hassan (Gidigo)wanda yake shekarar }arsheta ]alibta a Jami�ar Bayero.(Mun kawo maku hira da shia wannan watan).

Kawarta: Salmat }awarAbida Mohammed ce dominsun ha]a aji a makarantarSuratul Qur�an da ke Fagge.

Shiga Jama’a: Kafin kaga Salmat a wani ofishinfurodusa sau ]aya, ka gan ta a

SALMAT BABA ALI DA FIDDAUSI TIJJANI IBRAHIM

]anta ya yi rarrafe!

gidan Tijjani Ibrahim sau 30.

FIDDAUSI TIJJANI IBRAHIMKaratu: Ta kammala makarantar sakandaren �yan mata ta

Sani Mainagge.Fim: Fiddausi }anwa ce ga Ali Nuhu a cikin shirin Sidiqu.

Wannan shi ne fim ]in ta na farko.Uba: Mahaifinta ya fi kowa yi wa finafinai darakta.Uwa: Mahaifiyarta ba da son ranta Fiddausi ta shiga fim

ba. Amma da aka ba ta magana, ta ha}ura.Inda ta sa gaba: Ba za ta }ara yin fim ba, domin ta ci

jarabawar sakandare da sakamako mai kyau: 7 credits, 2passes. Jami�a za ta wuce ta karanci fasahar komfuta(Computer Science). Yanzu ma tana karatun ilimin komfutaa makarantar Shemlad da ke kan titin Zoo a Kano.

Kawarta: Ita ma }awar Abida Mohammed ce, watosababba da fararra an gamu.

Shiga Jama’a: Ita ma ba ta zuwa ko�ina daga gida saiShemlad, sai fa gidan Baba Ali wurin Salmat.

SALMAT Baba Ali da Fiddausi Tijjani Ibrahim}awayen juna ne na kut da kut; dare ka]ai keraba su. Baya ga wannan }awance nasu kuwa,

wani abin da ya }ara ha]a dan}on zumuncinsu shine abokantakar da ke tsakanin iyayensu Baba Alida kuma darakta Tijjani Ibrahim.

Da yake iyayen nasu mashahurai ne a harkar fim,a watannin baya Salmat da Fiddausi sun fito cikinwani fim (wanda bai fito ba) mai suna Sidiqu. Fim]in kuwa baban ita Salmat ne ya yi masa darakta,wato fitaccen mai tsara shirin fim ]in nan wandamuka ta~a kawo muku hirarsa, Baba Ali Yakasai(make-up artist). Kwanan baya wakilinmuMUHAMMED NASIR ya sami zantawa da �yanmatan biyu, ga kuma nazarin da ya kasa kan faifaidomin mai karatu ya gane inda tafiyar Salmat daFiddausi ta zama ]aya da kuma inda haryar da sukebiye ta yi masu harshen damo � kowa ya bi tasa:

57

Page 59: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

Daga ALIYU A. GORA II,a Kaduna

ABIN mamaki dai ba ya}arewa. Harkar fim ta shiga

zukatan jama� yadda duk ba atsammani, musamman ma mata;idan da kana kusantar mata kanasauraron kalaman da yawa dagacikin marasa tunanin su, za ka jicewa da mazansu za su yarda, toda sun shiga harkar fim. Wasuma cewa suke yi don dai �yanfim ]in ba za su ]auke su ba,amma maganar aure ba za ta hanasu yin fim ]in ba.

Irin wannan gur~ataccenra�ayin ne ya tsanduma wasumata cikin mugun yanayi, wandaya zama sanadin mutuwaraurensu a wurin bikin kalankuwa(�Gala�) da aka shirya wa FatiMohammed da angonta aKaduna a ranar 28 ga Yuli, 2001.

Wani bawan Allah ne ya zobikin na Gala, kwatsam sai ya yikici~is da matarsa a wajen. Nanda nan kamannunsa suka canza,ransa ya ~aci, hankalinsa ya tashi,idanuwansa suka yi ja zur. Ya yikukan kura zai kai mata bugu,mutane suka ri}e shi. Ita kuwa,maimakon ta yi nadama sai kawaita shige cikin filin da �yan kallosuke. Ganin haka, sai mijin ya bita har inda take, suka yi ido daido sannan ya ce mata ya sake ta,ya juya ya fita.

Shi ma ]aya al�amarin ya farune duk a ranar ta Gala. Yadda yafaru shi ne, wata mata ce ta cero}i mijinta ya bar ta ta je kallonbikin, shi kuma ya nuna matacewa ba za ta sa~u ba, wai bindigaa ruwa. Sai matar nan ta buga kaiga }asa cewa alo tsiya alo danjasai ta je. Mijin, wanda ba ya sona bayyana sunansa, ya ]auki

al}awarin cewa matu}ar matarta je wannan biki, to a bakinaurenta, ya kama hanya ya fita.Ai fa gogan naka yana isa filinGala can ya tarar da matar har tariga shi zuwa. Bai ce mata komaiba, ya kama sabgar gabansa ya}yale ta. Bayan an tashi bikin, damatar nan ta ga cewa zuwa gidanmijinta ba zai yiwu ba, sai kawaita zarce zuwa gidan iyayenta.

Lokacin da shi kuma mijin yasamu labarin tana can, sai ya bi tahar gidan, ya ciro rubutacciyartakarda ya mi}a mata. Bu]ewarda za ta yi, sai ta ga ashe sakintaya yi. Ballagazar kawai sai ta ]orahannu bisa kai tana kururuwa,tana fa]uwa tana tashi, tare daro}on mijin cewa ya rufa mataasiri. Ko kallonta bai yi ba, ya sakai ya fita.

Wannan ishara ce ga sauranmata. Saboda haka, a yi hattara.

Aure biyu sun mutu a filin Gala

A WATAN jiya ne aka cimmawata yarjejeniya tsakanin

furodusoshi da dillalan kaset nabidiyo a Kano, inda aka fito dawani sabon tsari na tilasta wafinafinai bin layi kafin su fitokasuwa. Tsarin ya bambanta dayadda ake yi can baya yaddakowa ke sako nasa yadda ya gadama ba.Wannan sabon tsari ya gindayawasu tsauraran matakai ta yaddaza a sami sau}in yawaitar fitowarfinafinai barkatai. A }ar}ashintsarin, an amince da cewa dukmako za a ri}a fito da fim }wayauku kacal, wato a wata ]aya za asaki finafinai goma sha biyu akasuwa.Kafin haka kuwa tilas ne dukwani wanda ya gama fim sai yabiyo ta hannun {ungiyarFurodusoshi ta Jihar Kano ya kaifim ]insa an rubuta sunansa ansa shi a layi. A can ne za a shaidawa mai fim ]in ranar da fim ]insazai fito.

A sabon tsarin, idan furodusaya kai fim ]insa don ya shigalayi, ba zai sami shiga ba sai faya nuna takardar Hukumar TaceFim ta {asa da kuma ta Kano.Zai kuma je da kwalin kaset ]inhar guda hamsin, inda za a ]auki

An yaba da sabon tsarin sakin finafinai

]aya a bar masa ragowar 49.Ssakataren {ungiyar Dillallan

Kaset, Alhaji AhmedMohammed Amge, ya shaida wamujallar Fim cewa, �An wareamintattun dillalai 18 da ke Kanoda kuma wasu garuruwa kanshara]in cewa su ne za a ri}araba wa kwalayen finafinan dasuka fito.�

Wani sabon tsari da aka ~ulloda shi kuma yanzu shi ne,furodusa zai mi}a ilahirin

kwalayensa ne a hannundillali ]aya, shi kumadillalin shi ne ke daalhakin raba wa saurandillalai �yan�uwansa dakuma }ar~o wafurodusan ku]a]edaga hannunsu.

Tuni dai wannan tsariya fara aiki inda cikinwatan jiya aka sakofinafinai uku a kasuwa:Kada Mage, Garwashida kuma Zulumi . A satina biyu kuma an fito daSamodara 2, Uzuri dakuma Dattijon Biri. An}arshen mako na ukukuma aka fitar da wasuguda uku, Allah gatanKowa (daga Gombe),Alh. Ahmed Moh’d Amge

Kalas, da kuma Garari.Mutane da dama da Fim ta

zanta da su sun yi murna da sabontsarin, suka ce zai ragekwamacalar fitowar finafinanHausa. Wata matar aure a Kaduna,Hajiya Ladi Kabiru, cewa ta yi,�A gaskiya mun ji da]i. Yanzumutum zai tsara yadda zai sayikaset a wata, kuma ko nawa zaikashe.� Wani furodusa kada bakiya yi, ya ce, �Allah dai ya sa abinya ]ore. Ka san abu a Kano!�

An maida ’yanwasan Jos

saniyar ware,inji furodusa

Daga ALIYU A. GORA II,a Kaduna

[AYA daga cikin manyanfurodusoshin Jihar Filato

kuma shugaban kamfanin �FarinWata Films Production� da ke Jos,Alhaji Sani Kanawa, ya koka dairin rashin ]aukar �yan wasanJihar Filato da muhimmanci dawasu furodusoshi ke yi,musamman furodusoshin jihohinKano da Kaduna. Ya ce suna da�yan wasa }wararru wa]andasuka san abin suke yi, suna kumaiya taka kowace irin rawa dafurodusa ke so a fagen shirin fim.

Sani, wanda ya zana kwanannan da wakilinmu a Kaduna yayi tsokaci a kan matsalar da �yanwasan nasu ke fuskanta, inda yace, �Matsala ta farko da �yanwasanmu suke fuskanta, dagafurodusoshi ne. Yawanci za kasamu idan ]an wasa ya taso dabasirarshi, wani ma ya yi karatu,kuma fim ]in ya karanta, ammada zarar ya harzu}o zai yi, in daiaka ce a garin Jos yake, sai a nunamashi cewa tunda ba a Kano yakeba, ba zai saidu a kasuwa ba.�

Furodusan ya ]ora laifinhaddasuwar wannan matsala akan furodusoshin jihar �sabodasu ne suke da ha}}in su fitar da�yan wasa daga Jihar Filato, koin ce daga garin Jos, wanda zaiyi suna shi ma duniya ta san shi.Daga hakan, shi ne nake tabbatarda cewa �yan wasan Jos za susamu damar nuna wa duniya irinbasirar da Allah Ya yi masu.�

Sani ya ce a halin da ake cikisuna nan suna tuntu~arfurodusoshin Kaduna da Kanodon a samar da ingantacciyarhanyar magance matsalar, tare dasa hannun }ungiyar furodusoshita Arewa. Kuma ya ba�yan�uwansa furodusoshishawarar cewa duk furodusan daya san abin da yake yi, to yakamata ya manta da maganarabokantaka ko dangantaka kosoyayya tsakaninsa da wata �yarwasa yayin da maganar shiryafim ta taso. Maimakon haka, yace kamata ya yi a ri}a dubacancanta, matu}ar ana son a samubiyan bu}ata.

58

LABARAI DA [UMI-[UMINSU

Page 60: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001 59

A CIKIN wata sanarwar ba-zata, gwamnatin Jihar Kano

ta soke rawa da kuma wa}e-wa}e a cikin finafinan Hausawa]anda ake shiryawa a cikinjihar. Wannan sanarwa ta biyobayan wani taro wanda jami�anHukumar Tace Finafinai ta jiharta gudanar a ranar 28 ga Agusta.

Taron, wanda ake kira natuntu~ar juna, ana gudanar da shia duk bayan wata ]aya. A wurintaron na kwanan nan, shugabanhukumar daraktocin hukumar,Sheik Yusuf Adamu Gama, yanuna fushinsa kan ha~akar raye-raye da wa}e-wa}en da maza damata ke yi a cikin finafinai. Yakuma nuna rashin jin da]i wajenyin amfani da tashe-tashenhankula (daba) a cikin fim. Kanhaka ne ya bayyana cewahukumarsa ta hana mata rawacikin fim ba tare da wani ~atalokaci ba. Ba wannan ne ka]aiba, an kuma hana �duk wani abuda ya sa~a wa Shari�a,� injisanarwar da hukumar ta bayar.Wannan doka kuwa ta shafi hargidajen sinima da na bidiyo dakuma gidan talbijin mallakargwamnatin jihar.

Sanadiyyar haka kuwa,hukumar za ta }ara matsa }aimiwajen ganin ta yi wa duk wanifim na Hausa kyakkyawan nazarita yadda zai haye sira]in doka da}a�idojin da suka ji~inci wasankwaikwayo da shirin fim kamaryadda tsarin yake shimfi]e cikinkundin dokokin tace fim nashekara ta 2001. A }arshe SheikYusuf ya yi kira ga furodusoshida �yan wasa kan su fahimcicewa an yi wannan doka ce domina tsaftace tsarin shirya finafinai ajihar.

Wannan sanarwa dai ta zo nesakamakon tsarin Shari�arMusulunci wanda aka }addamara Jihr Kano a bara. Bayangwamnati ta hana yin fim awatannin baya, ta kuma ]agedokar bayan t kafa Hukumar TaceFinafinai da Rubuce-rubuce.

Sanarwar ta girgiza jama�a dadama, musamman �yan fim.Yayin da wa]ansu ke maraba daita, wasu ko }orafi suke yi. Ba ada]e da yin sanarwar ba sai wasuda dama suka ri}a zuwa ofishinmujallar Fim domin fa]in

albarkacin bakinsu, wasu kumawakilanmu ne suka tuntu~e sudon jin ra�ayinsu. Mafi yawanwa]anda suka goyi bayan sabontsarin, sun bu}aci mu sakayasunansu.. Amma wani mai sunaMuhammadu cewa ya yi, �An yidaidai, an yi daidai, an yi daidai!�har sau uku, domin shi a ganinsa,�ba su da amfani.�

Musbahu M. Ahmad, wandamarubuci ne kuma mai rerawa}o}i, cewa ya yi, �Don an cean hana wa}a ba za mu ji da]i

ba su fito ba, wasu kuwa ba atace su ba? Ya shawarci hukumarda cewa, �Idan suna ganincondemning nasu (watsar da su)za a yi, to gaskiya da sake; sai subiya mutane ku]insu, illa kawaikowane furodusa ya tafi ya ri}asayar da pure water koso~arodo.�

Ali Nuhu, wanda yawancinfinafinansa duk na soyayya neinda ake cashewa da rawa, cewaya yi in dai an ]auki wannanmataki ne domin a gyara

finafinai ne dokar za ta fara aiki,Alh. Ahmed ya ce a yanzu anfa]a]a dokar ne, amma za a bi tamataki-mataki har zuwa }arshenshekara. �A yanzu ba mu hananamiji shi ka]ai ya yi rawa dawa}a ba. Macen ma za ta iya yidaga zaune, kamar a cikin ]aki,irin wa}ar tunani ko ta bege,kuma ita ka]ai. Amma dai ta fitota ri}a ti}ar rawa ita ka]ai ko dasaurayinta, wannan kuma dagawannan rana gwamnati ta hana,�inji shi.

Sakataren ya ro}i jama�a sugane cewa ba don a ~ata wa kowaaka yi wannan tsari ba, sai donkawo gyara, musamman don }inkauce wa tsarin Shari�a. Ya }arada cewa jami�an hukumar za suzauna da furodusoshi domintattauna yadda za a san irinwa}o}in da ake bu}ata da kumawa]anda aka hana.

Wakilanmu sun ji kalamai iri-iri na martani ga hukumar daga�yan fim da dama. Yawanci sunyi Allah-wadai da sabuwar dokar.A cewar wani, �Mu ba abin dawa]annan mutanen (watojami�an hukuma) za su gaya manamu yarda cewa ba so suke sukashe harkar fim na Hausa ba.Idan za su fito su dawo da dokarhana fim ne irin ta kwanan baya,ai sai su fito kawai su hana, kowaya kama gabansa.�

Wata �yar wasa kuma ta ce,�Shin me zai hana mu kwasheinamu-inamu mu koma wata jiharne, kamar Kaduna ko Jigawa,mu shiryo fim ]in daga can? Aiba dole sai kasuwar fim takasance a Kano ba!�

�A shirya one-million-marchkawai,� cewar wani, wato taronzanga-zangar mutum milyan]aya don nuna }in dokar.

Wani ko cewa ya yi, �Ni zanshirya fim kuma zan sa rawa dawa}a da cashewa irin waddaRu}ayya Umar ta yi cikinDawayya, daga nan sai in cewannan fim ba na sayarwa ba nea Jihar Kano.�

Wani kuma ya ce, �Duk laifin}ungiyar furodusoshinmu ce,domin wallahi ba abin da za su yikan wannan batu. Shi ya sa aketaka mu. In da ni official (jami�i)ne a }ungiyar, sai in ce mu kaiwa]annan mutane kotu kawai. �

LABARAI DA [UMI-[UMINSU

An hana rawa da wa}a a finafinan Hausa

ba? Sai a duba a ga wa]anne irinwa}o}i ne ya kamata a daina. Suma raye-rayen da ba su shafial�adarmu ba ai ba wani abu bane idan gwamnati ta soke su.�Sai dai kuma ya }ara da cewa,�Amma hana wa}a ta gargajiyakuma a cikin fim ]in gargajiyana al�ada, kuskure ne.�

Da shi da za}a}urin mawa}iAlkhamees D. Bature dafurodusa Bala Anas Babinlataduk ra�ayinsu ]aya ne.Alkhamees ya nuna cewa, �Hanawa}a ba zai kashe fim ba idanma har an yi ne da nufin dakushefinafinan Hausa.� Kuma ya ce,�Ai wata wa}a ta fi fim ]in mama�ana. Kada mutane su mantacewa wa}a tana da asali a harshenHausa da kuma tushe mai asali acikin adabin Hausa. To rushe takai tsaye ganganci ne.�

Shi kuwa Bala Anas, wanda afim ]insa mai suna Munkar neaka fara yin wa}a a fim, ya ceidan an hana wa}a, to yaya za ayi da finafinai sama da 250wa]anda aka kashe ku]i akashirya su, wasu an tace su amma

al�umma, to an yi riga-malam-masallaci. �Kamata ya yi a faragyara cikin garin Kano (watoal�ummar Kano),� inji shi. Ali,yaro-mai-tashe, ya ce akwaiwurare barkatai da ya kamata agyara. Ya ba da misali da masuku]i da ke kallon tashoshintalbijin na waje ta hanyarsatalayit, da kuma finafinanAmerika da Canis da Indiya dana Kudanci (Nigerian films)wa]anda ke nuna tsiraici dafa]ace-fa]ace da ake sayarwa ako�ina a Kano. Ya ce idan ba ahana wa]annan ba, to ana ]aukaririn wa]annan matakan a kanfinafinan Hausa ne da watamanufa, ba don gyara harkar fimba.

Wakilinmu ya garzayaHukumar Tace Finafinai ta JiharKano, inda ya sadu da BabbanSakatarenta, Alh. Ahmed [ahiruBeli. Jami�in ya bayyana cewaba kowace irin wa}a ce aka hanaba, sai dai wadda ba ta da ma�anada kuma duk wadda mace za tafito tana yi kuma tana taka rawa.

A kan ko daga wa]anne

Sheik Yusuf A. Gama Alh. Ahmed D. Belly

Page 61: Mujallar FIM - September 2001

FIM, SATUMBA 2001

WANNAN karo daisinima na shiga. Bansan ana yi ba,

kwatsam bayan sallar Isha�i saina ga fostar fim ]in nan mai sunaHali a gidan sinima na Wapa. Saikawai wata zuciya ta ce min inshiga mana. Nan take sai na jebakin kanta na biya N60 cur, nashiga na kama benci na har]e.

Ban yi minti ]aya ba kuwa saina ~arke da dariya. Dalili kuwa,rabona da shiga sinima a Kanotun ranar farko ta shekarar 1988,lokacin da na shiga Eldorado nakalli wani fim na Indiya wai shiDaku Hasina.

A Wapa, tamkar gasar shantaba ake yi. Masu shan tabar kuwaduk yara }anana ne wa]anda abisa dukkan alamu duk ba su iyasha ne a fili ko kuma a gabaniyayensu. To duk ba wannan neya fi ]aukar min hankali ba. Babuabin da ya fi ba ni mamaki saiirin wula}ancin da samari �yankallo ke yi wa wasu �yan wasanda ba su so idan an nunofuskokinsu. Da ma lokacin ba afara fim ]in da na je kallo ba. Saidai kawai ana ta nuno wasufinafinan da za a yi ne wasuranaku can masu zuwa.

Kun san abin da yaran ke yikuwa? Da an nuno fuskar wandaba su so sai kawai ka ji antattakura an rafka masa wani irinzagi mai ]oyi. Wallahi malam duksai na ji kunya ta kama ni kamarni aka yi wa. Idan wata mace cekuwa, sai ka ji an lailayo wataba�a mai ratsa jini da jijiya an ya~amata.

Wai ni ga mai tu�ammali da�yan wasa, sai na kasa ha}ura.Da na tambayi wani yaro sai yace min, �Ai malam duk wandaka ji mun zage shi ko mun yimata ba�a, wallahi wula}anci garesu.� Sai ni kuma na fahimci ai nasami abokin hira. Da yake yaronyana shan sigari, sai na sai masakara biyu, na ba shi kuma na zugashi na ce, �Ja abinka, ai jan taba

ya fi jan dokin uban wani�. Shikuma ya kada baki ya ce, �Wallahitallahi kuwa�. Irin maganar nanda yara wa]anda suka nuske dajibaga ke yi, ana magana anamurgu]a baki kamar taunarcingam.

Da na fahimci ya shanye tasasigarin har ya sha rabin waddana sai masa, sai na saketambayarsa, �Shi wai wane irinwula}anci �yan wasan ke yimaku?� A nan sai wani magidancida ke zaune a layi na gaba da niya juyo ya kada baki ya ce, �Waikai sai ka ce ba ka san �yan wasan

nan ba? Sai fa mutum ya tashi yatafi wurin ]an wasa ko wata �yarwasa amma wai sai ka ga anwula}anta mutum�.

Muna cikin haka sai aka nunowata. Ban ankara ba sai na jiwani ya yi mata ba�a: �Shegiya,sai ka ce an ji}a algarara da ba}inmai!� Kunya ta kama ni, ammatilas na yi dariya don kada a yitunanin cewa yarinyar da aka yiwa ba�a }anwar }awar uwar}awar }awar uwata ce.

Uhnm! Abin dai sai wanda yaji, amma duk wani naman dajinda ka san yaro ya sani, to idan an

Ramuwar gayya sai a sinima!

60

nuno wani wanda suke cewa�yana da wula}anci,� sai ka jisun kira shi da wanna suna. �Yanwasa, wallahi a canza hali tunkafin yaran nan su fara bin ku akan titi suna kiran ku da sunayennamun daji. Kafin dai a gamanuno finafinan, zuciyata ta yisanyi da aka nuno Dum~aru daShu�aibu Kumurci. Ai tamkarNijeriya ta ci }wallo, sai ihu.Wani matashi irin �yanfankashalin nan (ka dai gane!)har wani tsalle yake yana }wartsaihu, wai shi ya ga gwaninsa.

�Yan sinima kenan!

YARA da manya sun yincincirindo, sun yi tururuwa,

suna kallon �yan fim da ke hallaradaga Kano zuwa Jos. Cikinsuakwai Shu�aibu Kumurci,Sinana, da {azaza. Duk sunhallara ne domin shirya wani fimna Ahmed Muhammed Amge maisuna Tarzoma wanda SuleimanSa�eed yake ba da umarni. Akwaikuma Ali Nuhu da Ahmed Salihu,su kuma sun je tace finafinai daAlin ya yi, sannan akwai AminuShariff (Momo), su kuma sun jeneman wurin da za su shirya fim]in su na gaba.

Wa]annan �yan fim su sukafara tara taron jama�a a kusa dagidan sinima na Kwararrafa dake cikin garin Jos. Sun taru nekusa da ofishin shirya finafinanina Mis wa]anda suka shirya fim]in Nazari, daf da shagonshugaban masu saye da sayarwana kaset ]in bidiyo na JiharFilato, wato shagon Ashiraki.Haka dai yara suke cu]anya damanya su wuni ba ci ba sha hardare.

Masu shagunan garin kuwa anhana su shan iska sun ]auki taMa�aiki da dangana. Mutum ]ayana ta zarya da gudu kamarmahaukaci yana tarwatsa yaran

da tsintsiya mai sanda ko kumada ruwa a bokiti yana watsawa,ko kuma ka gan shi da igiya yanayawo kamar saniyarsa ta ~ata;wai tunda dai ba a san shi ba dolene a san shi ta hanyar hakan.Haka dai yara suka gano shi sunata yi masa ihu.

Can sai ga wata yarinya ta rako}awarta Hasana Adam Sani

domin ta ga furodusanta. Saikuwa yara suka ce, �Ga Wasila!�Haba, ai sai wurin ya ru]e dawa}ar Wasila: �Kin ci AmanataWasila!� Ita kuma abin da ba tasaba gani ba ne; sai tsoro ya kamata, ta ]an ja da baya. Yara kuwasuka bi ta rii. Da ta ga abin ba nayi ba ne sai ta ce }afa me na ciban baki ba. Yara ma haka.{arshenta dai sai wani gida tafa]a, aka kulle ta har sai da yaransuka gaji da jira suka tafi sannanaka bu]e mata }ofa ta sulale ta~ace zuwa gida.

Ita dai yarinyar, mai sunaHalima, Allah Ya yi mata sura neda jama�a suke ganin ta yi kamada Wasila Isma�il ta cikin shirinWasila. Ba ma a cikin garin Josba har a duk inda aka san ta anamata la}abi da Wasila. Ni kaina alokacin da Hasana Adam tagabatar mani da ita, da sunanWasilar ne.

Halima da na nemi ra�ayinta akan abin ke faruwa da ita bisadalilin kamannin da ta yi daWasila, sai ta ce ita babu abin daya dame ta. �Kuma idan har akaba ni mataki a cikin wani fim ]inzan kar~a,� inji ta, ta }ara dacewa, �A halin yanzu ma na samufinafinai tun daga hannunwakilinku na Jos kuma har munfara yinsa.�

To Wasila muna murna.

‘La! Ga Wasila a Jos!’

Halima ‘Wasilar Jos’