Upload
others
View
3
Download
0
Embed Size (px)
Citation preview
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
i
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
ii
TASIRIN SOYAYYYA
NA
AMINA YUSUF GWAMNA
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
iii
Juhaifah Ventures
NO. B2 FCE Kano Village,
Kano State.
©Haqqin Mallaka (M), Amina Yusuf Gwamna 2019
Ba’a yarda a juyi wannan littafai ta kowacce hanya, ko
sarrafa shi, ko sake buga shi ba said a izinin
marubuciyarsa.
An fara bugawa a shekarar 2019/1440 A.H.
Kamfanin da ya yi Xab’i Juhaifah Ventures FCE Kano
07037131142, 08063391234
Email: [email protected]
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
iv
Abubuwan da ke ciki
Godiya
Sadaukarwa
Gabatarwa
BABI NA DAYA: SO
1.0 Ma’anar so
1.1 Matsayi mafi Girma
1.2 Soyayyarsa farilla ce gare mu
1.3 Acikin masoya su ne abin koyin mu
BABI NA BIYU: SOYAYYA
2.0 Alamomin soyayya
2.1 Dalilan da kan sabbaba soyayya
2.2 Matakin farko na kafa kyakkyawar
soyayya a rayuwar Aure.
2.3 So ba ya fita daga zuciya
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
v
BABI NA UKU: BEGE
3.0 Ma`anar Bege
3.1 Matakai na bege
3.2 Tarairayar juna cikin soyayya
3.3 Sinadarai dake qara danqon soyayya
SOYAYYA
4.1 Soyayya ruwan zuma
4.2 Labarin Hawayen soyayya
4.3 Labarin Laila da Majanoon
4.4 Labarin Jameel da Buthaina
4.5 Labarin Shayin soyayya
4.6 Labarin Jarumi da Magajiya
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
vi
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah Maxaukakin
sarki da ya hore min rubuta wannan qaramin
littafi. Wato Tasirin soyayya har aka buga.
Godiya ga Babana Alh. Yusuf Isyaku Gwamna.
Da kuma Malamar da ta fara koya min soyayya
dalla-dalla wato mahaifiya ta Hajiya Muhd Voyi.
Godiya ba iyaka ga Mai Gidana, Masoyina
Alh. Abubakar Musa. Godiya ta musamman ga
Bayin Allah da su kai ta xawainiya dani a
vangarori daban-daban na rayuwata. Musamman
wajen bani ilmi, da taimakon rubuce-rubuce na,
Dr. Bala Muhd (Mu`allim), Dr. Usman Shu`aib
Zannuraini sashen a Jamii`ar Bayero. Dr. Nura
Abdullahi (Na madina) sashen koyon addinin
musulunci a Jami`ar Bayero. Mal. Ibrahim
Mu`azzam Mai bushara. Malama Ruqayya (Mrs.
Sheikh Daurawa), Malama Goggo (Mrs. Sheikh
Dr. Hassan Gwarzo), Malama. Hassana (Mrs.
Sheikh Dr. Bashir).
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
vii
Godiya ba iyaka ga dukkanin masoyana,
masoya rubuce-rubuce na. Ina roqon Allah ya
karvi dukkan ibadunmu, ya girmama ladan mu.
Amina Yusuf Gwamna
08037072225
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
viii
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafin ga
dukkanin ma su qaunata. Allah ya sanya su
acikin inuwarsa ranar da babu wata inuwar sai
inuwar al’arshi.
Aminatu `yar Yusuf ne,
Addininki Garkuwa ne,
Iliminki ko ado ne,
Hankalinki abin yabo ne,
Qaunarki ta na faranta rai na.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
ix
GABATARWA
Ita soyayya haxuwar zuciya ce da gamon
jini. Saboda haka manufar buga wannan xan
qaramin littafi shi ne qara fito da muhimmancin
soyayya a fili. Ma`anar So da yin bayani, akan
matakin farko na kafa kyakyawar soyayya.
Wanda hakan zai taimaka wajen rage gurguwar
soyayya. Wacce akan xora ta akan doron
kwaxayi, ko sha`awa. Hakan ke haifar da
matsaloli dayawa ga iyalanmu.
Ya zama tilas mu cika gidajen mu na aure
da Soyayya. Yadda yara za su ta shi cikin yana yi
mai kyau. Su rage qiyayya, su dinga son `yan
uwansu da al-umma. Sai ka ga gidajen mu sun
zama wani dausayi na soyayya.
Wannan littafi na Tasirin soyayya ya
bayyana cewa in dai har soyayya ingantacciya
ce. To, fa, ba ta fita daga zuciya. Da irin
sinadarai da ke qara danqon soyayya. Da yadda
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
x
masoya za su dinga tarairayar juna cikin
soyayya.
Bugu da qari, har ma da labaran sooyayya
ma su tava zuciya. Da mashahurin labarin nan na
Laila da Majnoon. Tare da fito da Darussa da ke
ciki. Da kuma nishaxantar da mai karatu.
Allah ya sanya albarka a cikin wannan
littafi. Ya zama ya anfanar da mu duka. Allah ya
yafe mn dukkan wani kuskure a cikin sa.
Wassalamu Alaikum
Amina Yusuf Gwamna
Shugabar qungiyar Mace ta Musamman Kano
08037072225
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
11
BABI NA DAYA: SO
MA’ANAR SO
So ko qauna shine yarda da amincewar
zuciya game da wani mutum ko wani abu.
Zuciya ita ce inda so ko qauna ke zaune.
Zuciya kuwa babu wani mahalicci daya ke da
iko da ita sai Allah (S.W.T.) da ya halicceta.
Allah shi ya ke kimsa so ko qauna acikin
zukata. Soyayya wani kogine wanda duk ya fada
cikin sa, sai yai ninkaya ya kasa fita.
Son da zukata guda biyu kewa junan su shi
ake kira soyayya. Ta kan zama soyayya mai karfi
ko mai rauni. Ingantacciyar soyayya ko kauna ta
na dawwama a zukata har abada.
Wasu kan faxa kogin soyayya a dalilin son
Allah. Misali kana da ibada a kullum cikin
yawan karatun Qur’ani. Ita kuma in ta saurari
karatun Qur’ani tamkar ta suma. Tabbas so ya
farantawa mutane dayawa, kuma so ya wahalar
da mutane da yawa. Babu wanda ya kuvuta daga
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
12
tasirin sa. Qauna ta gaskiya ba ta Qarewa, sai dai
takan iya sanyi saboda nisa, rashin samun
kulawa, Qiyayya daga xaya vangaren ko rabuwa.
In kuwa kaji ance maka taqare to dama
sha’awace ko kwadayin samun dukiya, mulki da
dai sauran su. Shi so ya na da wahala ka iya cire
shi in har ya shige ka. Masoya na haqiqa sun yi
bayani su na iya haqura da abubuwa dayawa a
rayuwa amma banda son masoyansu.
In muka duba soyayya acikin al’ummar
mu, za ka samu mafi yawan hazuqan mutane sun
so wata mace a rayuwar su. Malamai
Shugabanni, Sarakuna da dai sauransu.
1.1 MATSAYI MAFI GIRMA
Kalmar so (wato hubbi) girma ne da ita.
Allah madaukakin sarki yana soyayya kamar
yadda ya bayyana a wurare dayawa acikin al-
qur’ani mai girma irin wanda ya ke so. Misali:-
Allah yana cewa “Allah yana son masu
kyautatawa.”
(Ma’ida: 93)
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
13
Wurare daban-daban acikin al-qur’ani ya zo da
irin waxanda Allah (S.W.T.) ya ke so.
Alamun cikar imanin mutum shine tsantsar
soyayyar sa ga Allah wato komai za kayi, kayi
don Allah kamar yadda yazo cikin wannan
hadisin.
Annabi (S.A.W.) yace
“ wanda yayi soyayya dan Allah,
kuma ya bayar don Allah, kuma ya
hana don Allah to hakika imanin sa
ya cika” (Turmizi)
Wajibine mu so Allah muqurar soyayya. Alamun
son Allah shine yi masa biyayya, kaucewa sava
masa yawan ibada da yawan ambaton Allah.
Mutum ya dinga samun nishaxi cikin ibada ba
wai ana ibadar kamar ana yin alal-larurati ba.
Idan muka yunqura samun yardar Allah mai
sauki ne ga wanda Allah ya sauqaqawa.
Soyayyar farko da zamu fara nema ita ce ta
ubangijin mu. Sai mu samu albarka acikin
rayuwar mu. Duk mai neman soyayyar ubangijin
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
14
mu to ga bayanin abubuwan yi tare da albishir na
samun soyayyar Allah maxaukakin sarki acikin
wannan hadisin.
Hadisin Qudisi
Allah ya ce “ Bawa na ba zai nemi kusanci izuwa
gareni ba sama da abin da na farlanta masa.
Bawa na ba zai gushe ba yana neman kusanci
izuwa gareni da ayyukan ibada na nafila har sai
na so shi idan na so shi, sai na kasance jikinsa
daya ke ji dashi da ganin sa daya ke gani dashi,
da hannunsa da ya ke damqa dashi, da kafar sa
daya ke tafiya da ita. Wallahi da zai rokeni da na
amsa masa kuma idan ya rantse game da ni sai na
barrantar dashi. (Bukhari)
SubuhanAllahil Azeem!
Yan uwa masu albarka wannan irin matsayi mafi
girma ne abin nema.
1.2 SOYAYYAR SA FARILLACE
GAREMU
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
15
Shine mafi kyawun halitta, kyawawan halaye,
xabi’u kuma mafi cikar su. Shine Bawan Allah
cikamakon annabawa, masoyin mu Muhammad
salAllahu alaihi wasallama. Shine wanda
soyayyar sa farilla ce agare mu. Ya zama lallai yi
masa salati yayin da aka ambace shi.
Annabi (S.A.W.) yace “ Na rantse da wanda
rai na ya ke hannun sa. Imanin xayan ku bazai
cika ba har sai na zamo ni ne mafi soyuwa
agareshi daga iyayensa da yan uwansa da mutane
baki xaya”
( Bukhari da muslim)
1.3 ACIKIN MASOYA SU NE ABUN
KOYIN MU
Ina shaida wa, ina tabbatarwa cewa bayan
Annabi (S.A.W.) babu tamkar sayyadina
Abubakar As-sadiq (R.A.). Sai sayyadina Umar
(R.A.), sai sayyadina Usman (R.A.), sai
sayyadina Ali (R.A.), Da dukkan ragowar
sahabban manzon Allah (S.A.W.).
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
16
Waxannan su ne abin koyin mu da za mu yi
riko.zamanin sahabbai, zamani ne na imani
rayuwar su ta kasance cikin yawaitar Ibada. Su
na da daraja, zamu fahimci irin bambancin
matsayin su acikin wannan hadisin.
Annabi (S.A.W.) ya ce “ kada ku zagi
sahabbai na, domin da xayan ku zai ciyar da
dinare mai girman dutsen uhudu ba zai kai
kwatankwacin su ba”
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
17
BABI NA BIYU: ALAMUN SOYAYYA
2.0 ALAMOMIN SOYAYYA
So ko qauna ana fahimtar su ne ta hanyoyi
dayawa daga cikin su akwai :-
Yawaita ambato
Bin umarni
Sadaukar da kai
Yawaita kyautatawa
Damuwa da halin wanda ake so ya ke
ciki
Qoqarin farantawa wanda ake so
2.1 DALILIN DA KAN SABBABA
SOYAYYA
Akwai dalili dayawa da kan sabbaba soyayya
kaxan daga cikinsu kuwa su ne:-
Dacewar xabi’u da halaye na halitta
Jarumta
Ilimi
Alheri (kyauta)
Gaskiya
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
18
Amana
Kunya
Da sauransu.
2.2 MATAKIN FARKO NA KAFA
KYAKKAWAR SOYAYYA A RAYUWAR
AURE
Matakin farko shine soyayya ta zama soyayya ce
ta gaskiya. Ka da mace ta shigo da yaudara
misali qarin gashi, kirji, qugu, ko launin fatar
jiki. Shima Namijin ban da aron kuxi, takalma,
Riguna, mota, da makaman tansu. A kaucewa
qarya asalin iyaye ko dukiya, alokacin neman
Aure.
Kafin aure lalle ne ya zama soyayya ce
mafi tsarki wato wadda babu tava jikin juna, ko
batsa acikinta, tunanin ko buqatuwar saduwa ta
jiki ba.
Rashin kiyaye wannan matakin shi ke
janyo saurin kiyayya, zubewar mutunci da raini a
mafi yawan aure. Hakan kuma na kaiwa ga sake-
saken aure da ke afkuwa.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
19
Masoya bayan sunyi aure sai su yi tsari na
baiwa juna muhinmanci yin abubuwa tare irin su
hira, aiki, ibada, tafiya, cin abinci, da wanka.
Ma’auratan da ke cikin watanni ko shekarar
farko yakamata ace su na cike da buguwar
soyayya ne. Su na tsakiyar shayar da juna bammi
irin na qauna, soyayya da shaquwa.
Ita amarya ta na cikin bin hanyoyin daban-
daban don yin biyayya da farantawa Ango. Wato
ado, kwaliya, qunshi, gyaran gashi akai-akai da
kammala girki da wuri.
Shi ne ya sa ko budurwa ko bazawara aka
auro. A wannan matakin ake ce mata amarya
komin qarancin shekarunta ko kuma tsufanta.
Shi kuwa ango hankalinsa, lokacinsa na
wajen baiwa amaryarsa kyakkyawar kulawa.
Za’a samu ango da yawan shiga gidan sa. (shine
gudowa daga kasuwa ko ofishin sa). Haka kuma
shine shigowa da duk abinda ake bukata kafin
ma anema. Kai bai tsaya kan abubuwan da su ke
wajibi ba. Harma da irin su tsire, kaza, kayan
marmari don qoqarin sa na farantawa amaryar
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
20
sa. Musamman ma ace ango ya samu amaryar da
ta san yadda za ta tarairayeshi.
Shiyasa galibi gidajen sabon aure a rufe ya
ke sai ka yi ta bugu kafin abude maka qofa.
Wasu ma dai kanyi tafiyar soyayya wato
(honey moon). Wacce masoya ke yi don nu na
soyayya ga juna a kwanakin farko na tarewarsu.
Awannan tafiyar zasu tsara rayuwar auren su
gaba xaya. Wannan tafiya na da matukar
muhinmanci a matakin farko na kafa kyakyawar
soyayya arayuwar auren masoyan.
Amma fa wannan tafiyar ba sai sabon aure
ba. Ko yanzu kuma in ku ka shirya sai axebe
yara akai su gidan kakannin su. Ko agaiyyato
kakarsu ta zo nan gidan ku ta zauna da su. Ku
kuma ku samu damar tafiya ta `yan kwanaki, don
kafa soyayyar ku.
Ga tsofaffin ma’aurata ita ce kevantacciyar
tafiya da waxanda su ka yi auren soyayya ke yi,
don samun kevewa, sakewa, nishadi, da jin daxi.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
21
A irin wannan tafiyar ne za su samu damar
warware duk `yar wata rashin jituwa, ko kura-
kuren da ake yiwa juna. Wato tafiya ce ta
sabunta soyayya.
Idan babu halin yin tafiyar kwanaki, sai ayi
tattalin ranakun hutun mai gida (weekend).
Wajen yini a wuraren shaqatawa ko da kuwa
gidan dabbobi ne (zoo), gidan tarihi (meseum),
wajen tanxe tanxe (Bakery), ko shaqatawa
(minjibir park na kano).
Rashin kafa kyakkyawar soyayya a rayuwar
aure. Shine ya sa irin wannan rayuwa tai mana
karanci ainun. Har akan samu qiyayya, hassada,
rashin shaquwa, rashin amana, tausayi ga
ma’aurata.
Ba shakka hakanne ya ke kawo mana zaman
doya da manja, ko zaman `ya’ya.
A qarshe dai wannan ya zama cikin manyan
dalilan mace-macen aure. Shine aure ke mutuwa
a `yan kwanaki farko ko a `yan shekarun farko
na aure.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
22
2.3 SO BA YA FITA DAGA ZUCIYA
Mutane dayawa sun haqiqance akan so na
ficewa daga zuciya. Sai dai kuma haziqan
masoya dayawa, sun tabbatar da cewa soyayya
bata fita daga zuciya.
Na san wasu za su ce shifa biri ya yi kama
da mutum. Saboda `yan mata da zaurawa kanyi
manema daban-daban. Amma da zarar tafiya ta
yi nisa, sai ka ji an vace bat.
`Yan mata da zaurawa na cikin tashin
hankali sulle vewan masoya. Saboda haka na ga
ya dace yan uwana mu fahimci wanda duk ya
kauce, toh daman Allah bai Qaddara miji ki ba
ne.
Hakan take ma a vangaren samarin, idan
budurwa ta kufcema. To tun chan ba rabon ka ba
ce. Sai ka rungumi qaddara, ka roqi Allah ya
kawo tagari.
Tabbas na gano So ba ya fita da ga zuciya.
In kuwa ya fice, to daman kwaxayin wani abune.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
23
Saboda haka ba’ayiwa masoyi ko
masoyiya biyayya akan abinda ya ke savon Allah
ne.
Anan wani na iya cewa to yaya zan
fahimci wacce take sona da gaske ?
An tambayi wani mai hikima cewa ya
za’ayi mutum ya san mai kaunarsa. Sai yace.
Wanda damuwarka take zama damuwarsa.
Wanda ya ke tambayar halin da ka ke ciki.
Wanda baya qosawa da kai.
Wanda ya ke kau da kai idan ka yi
kuskure.
Wanda ya ke maka addu’a.
BABI NA UKU: BEGE
3.0 MA`ANAR BEGE:
Bege shine nuna matuqar qishirwar ganin
masoyi/masoyiya, son kusanta dashi, qallafe rai
da yawan tunanin sa. Bege da shaquwa ma’urata
na da matuqar muhinmancin gaske.Waxanda ke
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
24
jin daxi galibi cikin aurensu, za ka ga sun shaqu
da juna ne.
Cikin abubuwa da su ke sa begen juna da
shakuwa. Su ne soyayya, ladabi, kyautatawa, yin
abubuwa tare kamar cin abinci, wanka, wasa,
aiki tare da sauran su.
Kyakkaywan misalin masoya su ne Annabi
(S.A.W.) da Aisha (R.A.). Saboda bege da
shaquwa da ke tsakanin Annabi (S.A.W.) da
Aisha (R.A.). Shi yasa da bashi da lafiya ya na
tambaya A`ina na ke ? Gobe fa ? Jibi ? har sai ya
ji ance xakin Aisha (R.A.) tukunna.
3.1 MATAKAI NA BEGE:
Bege nan mataki-mataki ne. Wato
gwargwadon soyayyar ka da matar ka/mijin ki
gwargwadon yadda za ku dinga begen juna.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
25
Abu ne mai asali da muhinmancin gaske
miji ya dinga begen matarsa. Ita ma mata, ta
dinga begen mijin ta.
Anan kyakkyawan misalin da na zaqulo
mana shine na Annabi (S.A.W.) da Nana Khadija
(R.A.), Annabi (S.A.W.) ya na girmama
qawayen ta bayan ta rasu. Idan su ka zo har
mayafin sa ya ke shinfixa musu.
Haka kuma idan ya yi yanka ya na aika
musu da Nama.
SubuhanAllahil azeem! Jama’a ku dubi irin
wannan qauna. Ana begenta alhalin ba ta raye
ma.
AZABTUWA
Mutum yai zugum kullum cikin tunani mai
tsanani. Bai iya walwala har bacci, ci abinci da
dai sauran alamu na rayuwa.
DIMAUCEWA
Mutum kanyi bege har sai hankali ya xan gushe
saboda tsabar bege.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
26
Ana san masoya da ke yanka jikin su, su yi
tawada da jininsu Su rubutawa masoyiyar su
wasiqa da jini .
Sai dai a yanzu begen juna ya fi afkuwa ne
`yan kaxan da ga cikin ma’aurata. Mace za ta yi
tafiya ta jima, kaga mijinta bai jin komai haka
shima in mijinta ya yi tafiya sai ka tarar matar ba
ta da wani damuwa. Ko mene ya jawo haka?
Dalilin shi ne: Muna nesa da juna ne
musamman a rayuwar mu ta yanzu, saboda
abubuwan zamani. Kamar na’ura mai
kwakwalwa, waya, tashoshin talbijin da dai
sauran su.
Za`a zauna cikin xaki guda, miji na latsa
wayarsa, matar na kallo. Ko matar a kan Na`ura
mai qwaqwalwa, miji na kallon qwallo.
3.2 TARAIRAYAR JUNA CIKIN
SOYAYYA
Yakamata mu fahimci kamar yadda ruhi ya ke
al’amarin Allah, haka so ya ke. Da so da ruhi a
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
27
haxe suke. Saboda haka ne yadda tasirin so ya ke
agareshi.
Soyayya ita ce jigon rayuwa ba wanda baya
son aso shi. Ba wanda ba ya son kulawa (care) .
saboda haka dole takan sa mutum ya nemi
hanyar da zai samu soyayya da kulawa.
Ashe kenan abune mai mahinmancin gaske
ma’aurata su dinga tarairayar juna cikin so da
qauna. Mu mata lallai mu zama masu tarairayar
mazajen mu. Su ma maza su zama ma su nu na
mana kulawa. Sai mushaqu har mu dinga begen
juna wato mu dinga misayar soyayya kamar
yadda Annabi (S.A.W.) ke yi da iyalan sa.
Abin tambayar shine, idan ni mijina bai iya
ba. Ko bai damu da soyayyar ba yaya zan masa?
Yar’uwa mai albarka cikin dabaru zaki
lallava. Wato ke ta vangaren ki sai kidinga saka
soyayya a komai na ki. Shi so kamar ciwo ne, za
ki ga watarana ya kamu. Ko da zai xauki tsawon
lokaci kaddai ki gaji.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
28
Idan mun lura da kyau zamu fahimci idan
mace ta bada soyayya. Sai itama a lilliveta da
soyayya.
Wani na iya cewa idan kuma mace ba ta iya
soyayya ba. Mijinta na son ya canjata a soyayya
yaya zai yi ?
Da farko mijinta sai ya fahimci akwai
kevantattun xabi’u ga mata. Wanda dole ne sai
sun siffantu da su kamar jin isa, da jin qai amma
tarbiyar addini ita ce ta ke sai ta ta.
Na biyu kuma xabi’ar mace son yabawa da
zugawa. Ta hanyar haka za’a iya gyara halayenta
dayawa.
Dan uwa mai albarka ka sa ni fa, idan ka na
kyautatawa kai ma za’a soka. Kuma za’a dinga
tarairayar ka da kyautata ma.
3.3 SINADARAI DA KE QARA DANQON
SOYAYYA
Akwai sinadarai da ke da matuqar tasiri
wajen qara danqon soyayya a cikin rayuwar
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
29
ma`aurata. Su na dayawa amma zan zaqulo ma
yan kaxan daga cikinsu.
KALAMAN SOYAYYA: kalmomin soyayya na
cikin sinadaren da ke qara danqon soyayya.
Zuciya ta na jin daxi, kuma ta amince ma wanda
ke mata kalmomin so da qauna.
Kiran masoyi ko masoyiya da suna mai
daxi
Yawan faxawa masoyi/masoyiya “ina
matuqar qaunarki, soyayyarki ta
lulluve ko ina a cikin zuciyata”.
Bayanin yadda ake jin rashin daxi,
yayin da aka yi nesa da juna.
SUMBA
Sumbata na cikin manyan sinadaren da ke
qara danqon soyayya. Yana da kyau ma`aurata
su mayar da shi abin yi akai-akai.
Abu ne mai kyau saboda shugabanmu
Annabi (S.A.W.) ya na sumbatar iyalansa yana
asiwaki kafin ya shiga gida.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
30
Mata da miji ya zama dole kowanne ya
zama mai yawan kula da tsaftar baki, hakanne
zai sa aji daxi tare da nutsuwa. Rashin tsaftace
baki shi ya ke sa, xaya daga cikin ma`aurata ya
dinga qin amincewa.
Sumba duk lokacin maraba, idan an haxu.
Sumba duk lokacin rabuwa, idan za`a fita.
Sumba ta mu kwana lafiya, za`a yi bacci.
Sumba ta godiya, kinyi kyau Sarauniyata,
irin wannan kwalliya.
Sumba ta musamman ta gayattar haxa
shimfixa.
HAXA JIKI
Haxa jiki (wato runguma) ana jin xumin juna
shima na cikin manyan sindarin da ke qara
danqon soyayya.
Haxa jiki ya yin maraba
Haxa jiki kafin fita
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
31
Haxa jiki lokacin hutawa. Cinyarki ta
zamo ita ce matashin kai na mijinki ako da
yaushe.
Kyakyawa misalin da zan kawo mana shine,
Aisha (R.A.) tace “Annabi (S.A.W.) ya na
karanta Qur`ani akan cinyata alhali ina haila”.
Nana Aisha (R.A.) ta nace: ya mutu yana
tsakanin havata da qirgina.
KYAUTA
Xabi`ace ta zuciya ta na son wanda ya ke
kyautata mata. Miji ya dinga yiwa matarsa
kyautar bazata. Musamman Turare, Kayan sawa,
Katin Soyayya, da furanni (flowers). Mace ma ta
kwatanta kyauta ga mijinta dai-dai qarfinta.
Tausayin juna:
Mace ta dinga tausayin miji cefane, bashi
da lafiya ko ya haxu da larura
Miji ya tausayawa mace laulayin ciki
Ta je makaranta ta dawo, aiki,rashin lafiya
da dai sauran su.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
32
SAQONNIN SADARWA
Yana da muhimmanci masoya su zama su na
tafiya da zamani. Miji ya dinga tuntuvar matarsa,
ita ma mata ta dinga tuntuvar mijinta. Wato
tuntuvar juna ta waya don jin lafiyar juna.
Amfani da cibiyoyin sadarwa na zamani
wajen yin hira (chatting) tura saqon soyayya,
hotunan zuciya, filawa da sauran su.
Wadannan abubuwa na taimakawa matuqa
idan anyi amfani da su ta hanyoyi masu kyau.
BABI NA HUXU: LABARAN MASOYA
4.1 Soyayya Ruwan zuma:-
Babu wani abu mai daxi kamar soyayya.
Tabbas gaskiya ne da ake cewa soyayya ruwan
zuma in ka sha, to ka baiwa masoyi.
So abu ne mai tasiri wanda ka iya sa
mutum ya makance alhali gashi da idanuwansa.
Shi ne ciwon da babu likitan da zai iya baka
maganinsa. Sai dai shi masoyi ko masoyiyarka.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
33
Shine abin da kan bugar da masoyi ko
masoyiyarka har ya dinga sambatu. Kamar yadda
wasu masoya su kace.
Mu kan bugu (wato mu yi maye) duk da
kuwa cewar ba mu sha ko da kurva xaya daga
giya ba. Sai dai cewa zantukan soyayya shi ne
giyar. Ga shi kuwa shi mashayin giya ya kan
warware daga buguwarsa. Amma mashayin
soyayya, yana zama cikin mayen soyayya tsawon
rayuwarsa.
4.2 LABARIN HAWAYEN SOYAYYA
Barira: Barira ita ce matar Mugisu, shi bawa ne
na wasu mutanen Madina. Ita baiwa ce ga A`isha
(R.A.) tana zuwa tana yi mata hidima. A nan ma
za mu ga yadda musulunci yake bai wa `ya mace
`yanci.
A musulunci daga an `yanta baiwar a ke auren
bawa, to ita ce ke da zavi na zama da shi ko
rabuwa.
Bayan A`isha ta saye ta, sai ta `yanta ta. Sai
Annabi Alaihissalamu ya ba ta zavin zama da
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
34
mijinta ko rabuwa da shi. Saboda ita ta zama `ya,
shi kuma yana bawa. Sai barira ta zavi rabuwa a
shi. Mugisu yana tsanin son Barira, amma dole
ya haqura.
Abdullahi xan Abbas (R.A.) ya rawaito Hadisi a
cikin Sahihul Bukhari, ya ga Mugisu (mijin
Barira) yana bin ta kwararo-kwararo a Madina
yana kuka. Har gemun sa ya jiqe a hawaye,
domin ta yarda a mayar musu auransu. Amma ta
qi yarda. Har ma Annabi Alaihissalamu yake
cewa baffan sa.
“ Ba ka mamakin son da Mugisu yake yi wa
Barira, da qin da Barira take yi wa Mugisu?” Sai
Annabi (S.A.W.) ya ce mata, “ba kya yarda a
mayar muku da auren ku ba” sai ta ce, “Ya
Ma`aikin Allah, umarni kake ba ni?” sai Annabi
ya ce “ceto nake yi” sai ta ce, “to ba ni da
buqatarsa”.
Kun ga karamci irin na Annabi (S.A.W.) bai
tilasta sai dole ta komawa auren mijinta ba.
Wato hikima irin na Annabi (S.A.W.) bai tilasta
sai dole ta komawa auren mijinta ba.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
35
Wato hikima wajen raba aure idan har mace tana
tsananin qin miji shi ne don tserar da ita daga
halaka. Idan mace tana qin miji, to ba za ta dinga
yin haquri da shi ba, tausaya masa ko faranta
masa rai ba.
Musulunci ya tabbatarwa mace `yancin da take
da shi na neman rabuwa da miji idan ta ji bata
qaunarsa. Ko da kuwa akwai ci da sha. Kamar
yadda za mu ga hakan a wannan qissa mai zuwa.
Jamila Bnt Ubayyu: matar sahabin Annabi
(S.A.W.) Sabitu bn Qais.
Annabi (S.A.W.) ya sami labarin rashin
jituwar da ke tsakanin Jamila da mijinta Sabitu.
Sai ya aika yana tambayarta dalili. Sai ta yi
bayanin cewa ita ba ta da suka game a addinin
mijinta (wato mai kula da addini ne). Ita kawai
son sa ne ta ji ba ta yi. Sai Annabi (S.A.W.) ya
tambayeta ta, ko za ta iya mayar masa da gonarsa
da ya ba ta a matsayin sadaki? Sai ta yarda ta
mayar masa. Kuma suka rabu.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
36
DARUSSA
Ya zama wajibi mace ta ji tsoron Allah.
Mu kaucewa halaka miji, saboda qiyayya
ta shigo. Ba dai-dai ba ne watsawa miji
fetur, yanka shi, balle kashe shi.
Idan sulhu ba zai yuwu ba. To mace ta bi
hanyar da ta dace. Kamar yadda muke ji
a lokacin Annabi (S.A.W.)
Soyayya ake so a cikin rayuwar aure. Ka
da ma`aurata su zama cikin bala`i da
tashin hankali kullum.
4.3 LABARIN LAILA MAJNOON
Akwai wani bawan Allah mai suna Qais ibn
al-mulawwah wanda ya fi shahara da Majnoon
Laila. Anhaife shi ne a wajen qarni na biyar wato
a zamanin daular Umayya. Kuma shi kaxai ne
awajen mahaifiyar sa.
Qais wato Majnoon Laila ya na da kyawun
halitta ga jarumta sosai. kuma ya na da
kyawawan xabi’u. Ya faxa kogin soyayyar wata
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
37
mace da ake kira Laila. Ya so ta soyayya da ba’a
tava yin irin ta ba. Saboda shi haziqine yai
rubuce-rubuce na waqoqi dayawa da ke nuna irin
tsananin son daya ke yiwa Laila. Laila `Yar gata
ce gurin mahaifanta. Ana misali da ita wajen
kyau. Dukkan abinda ya mace za ta mallaka ace
mata kyakyawa, Laila ta na da shi da qari.
Qais da Laila sun kamu da tsananin son junan
su abin har ya wuce hankalin kowa.
Sai dai lokacin da iyayen Qais suka je neman
auren Laila. Sai iyayen Laila suka qi amincewa
su suna ganin `yarsu tafi qarfin ta auri Qais.
Duk daqin amincewar iyayen waxannan
masoya ba su daina soyayyar ba. Sai ma ruruwa
da soyayyar ta dinga yi kai kace ana qarawa
wuta fetur.
Iyayan Laila su ka tirsasa mata ta auri wani
mai dukiya. Sunan sa wardi atha kafi. Shi kuwa
Qais ganin yadda bashi da wani aiki sai begen
masoyiyar sa Laila. Sai akace mahaifinsa ya
kama hannunsa, su ka tafi yin xawafi. Shi
atunanin mahaifin Qais wannnan ne kaxai zai sa
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
38
a samu saukin halin da xansu ya shiga ciki.
Baban Qais yace da xansa idan munje muna
xawafi ka yi ta rokon Allah ya cire maka
soyayyar Laila.
Sai dai kuma ya yin da suke xawafi sai akaji
Qais yana ta addu’a yana cewa “Allah ka qara
min soyayyar Laila”.
Duk da ya ke an auradda Laila ga wardi,
amma zuciyar Laila ta na gurin masoyinta Qais.
Ba ta da aiki sai tunanin wanda zuciyar ta ke so.
Wardi ya rasa yadda zai yi ya ji daxin zaman
auren sa da Laila. Saboda a kullum ta na cikin
kuka da begen Qais. Sai kawai ya yanke shawara
ya koma Iraq tare da matarsa Laila, ko hakan zai
sa ta daina tunanin Qais.
Wane mutum ! Laila ta riga ta kamu da
tsananin qaunar Qais. Shi kuwa so irin wannan
ba shi da magani.
In taqaice muku labari dai ba abinda ya
chanza.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
39
Shi kuwa Qais, alokacin da ya samu labarin
antafi da masoyiyarsa qasar Iraq. Bai yi wata-
wata ba, sai kawai ya bi su.
Mutane sunyi iya yinsu wai mayya ta je
barka ankorota. Akan raba Qais da Laila ba
yadda ba’ai ba, amma abin ya ci tura.
A nan dai qasar ta Iraq Laila ta kamu da
ciwon zuciya ta na tare da mutumin da iyayan ta
suka aura mata ta mutu.
Abin ban mamaki kuwa shi Qais na jin Laila
ta mutu, sai shima zuciyarsa ta buga ya faxi
atake ya mutu.
Ance an bunne masoyan akusa da junnan su
a kusa da wani dutse mai dausayi.
Wannan masoyan Majnoon Laila, Allah bai
nufi sun yi aure ba. Amma dai sun buga soyayya
da sun bar tarihi. Kuma sun nunawa duniya
ma`anar soyayya.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
40
DARUSSA
So ciwone, Ciwon so abune mai
matuqar haxari wanda ka je fa mutum
cikin irin kowani hali. Yana da kyau a
tausayawa irin wanda suka faxa kogin
soyayya.
Iyaye su daina tilastawa `ya`yan su auren
dole
Ba’a siyan soyayya
Masu kuxi su daina tilastawa mace ta
aure su, ko ba soyayya.
Auran da ba soyayya, to ba bu nutsuwa
da tausayi.
4.4 LABARIN JAMEEL DA BUTHAINA
A can cikin qasashen larabawa dai, anyi wani
bawan Allah mai suna Jameel ibn Ma’amar ibn
Abdallah ibn Subah. Sananne mutum ne haziqi
wanda ya shahara da waqoqin soyayya acikin
qasar Masar.
Jameel tun ya na qarami ya faxa kogin son
wata kyakyawar mace da ake kiranta Buthaina
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
41
Ummu-Abdulmalik. Su na matuqar son junnan
su.
Sai dai sun samu cikas acikin soyayyar su.
Saboda a lokacin da iyayen sa su ka je neman
masa aure Buthaina, sai aka hana su.
Iyayan ta su ka nemi wani daban suka aura
mata.
Abin ta’ajibin shine waxannan masoyan sun
cigaba da soyayyar su alhalin ta na gidan wani.
Abu kamar wasa dai, soyayya sosai su ke
zubawa.
In taqaice muku labarin dole ta sa wancan
mijin na buthaina ya gaji ya sake ta. Ita kuwa
takoma gun masoyin ta su ka yi aure.
Acikin waqoqin shi Jameel ya ke cewa “ Ya
wahala a soyayya kamar Qais Laila majoon,
amma Qais bai kai ga cimma burinsa ba amma
shi ya kai.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
42
DARUSSA
1. SALLAMI:-
Misayar soyaya yana da muhimmanci.
Namiji ya tabbata ya samu karvuwa
awajen wacce zai aura. Ya zama ka yi
nasara ka sami soyayyar ta. Ko dai ace da
fari bata kaunar ka, ya zama an jawo
hankalinta acikin kyakkyawar mu’amala
a lokacin zamantakewar aure.
2. HAQURI:-
Rungumar qaddara da baiwa zuciya
haquri, ya na da muhimmanci. Za haifar
da natsuwa, zaman lafiya, biyayya da
samun lada. Wato ga wacce aka
tilastawa, ko kuma qaddara ta jawo ta
auri wanda ba shine zavinta ba. A duk
lokacin da ta yi aure to lalle a rufe shafin
soyayyar wani. Ta yi qoqarin nunawa
zuciyata kyawawan halayen mijin da ta
aura. Har asamu ya samu wani gurbi daga
zuciyata. Irin wannan halin kirki iyayan
mu na da suka yi.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
43
3. TSORON ALLAH:
Iyaye su ji tsoron Allah ka da su dinga
cutar da `ya`yensu. Saboda kwaxayin
abin duniya.
4.5 LABARIN SHAYIN MASOYA
Haneef ya ce na hadu da wata kakkyawar
yarinya `yar gata ce sosai. Da ganinta maza sai
rububinta suke duk inda ta wulga. Mazanma
kasaitattun gaske ne ke iya tunkararta. A wajen
walima na ganta sai bibiyarta samari su ke yi.
Ni kuwa na samu wuri na natsu. Tamkar ni
bata finciki zuciya ta ba. Da alama ma babu
wadda ya damu dani saboda daga ganin shiga ta,
kai ma kasan bani da hali.
Sai dai duk da kauwame kaina da na yi,
na tsaya iya matsayina. Bai hana zuciyata fadawa
kogin son Hanan ba. Kai ba wai a zuciyata ba,
sai da nayi kokari na matsa kusa da ita. Na yi
jarumtar neman izini mu xan zauna tare, mu sha
shayi.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
44
Yadda ta ganni ta yi mamakin wannan
gayyata. Sai dai jarumtata, ya burgeta kwarai.
Tarbiyyar ta kuma ya sa ta ta amsa gayyata.
Ta cika alkawari na bani lokutanta, muka
zauna tare a teburin shan shayi na bada umarni
akawo mana shayi. Sai dai zuciyata ta rikice
sosai ganin cewa gani gata. Soyayyarta ta
baibeyni har ma ban san me na keyi ba. Ina cikin
tunaninta duk da gata a gabana.
Sai kawai na ji ance shayin da me za ka
sha? Ba tare da waige ba, sai nace gishiri. Ban
san me nace ba,sai da na ji ta zubo min
kyawawan idanunta tace ” shayi da gishiri ka ke
sha?
Kunya ta kamani, dana fahimci abun da
nace. Amma sai na dage cikin annushuwa nace
“Ni kuma haka nake shan shayi da gishiri”.
Mamaki duk ya bayyana a fuskarta. Ta ce
“kai kuma ya akai haka? Shayi da gishiri. Sai na
gyara zama don ina son in burgeta. Na fara
zayyano labarina inji Haneef.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
45
A lokacin ina yaro, ina yawan son wasa a
kogi. Saboda gidan mu babu nisa da kogin garin
mu. Wannan yasa idan ina cikin sa, baki na yana
cike da xanxano kogin. Xanxanon sa kuma,
kamar ki sawa shayi gishiri ne. Wannan xanxano
na saba da shi. Haka kuma ya zamar min hanyar
da nake tuno da kuruciya ta. Na ke tuno da iyaye
na da na ke kewarsu. Sai idanuwan Haneef suka
ciko da hawaye.
Bashakka ta ji daxi wannan labarin mai
ban tausayi. Tace lallai kana matuqar qaunar
iyayenka da garin ku. Sai ta yaba da irin yanayin
sa, jarumtar sa, da yadda ya fuskan ce ta. Nan da
nan ita ma ta fara bashi labarin rayuwarta.
Daga wannan rana, muka fara soyayya.
Har ta fahimci Haneef mutumin kirki ne. Ga
kyawawan halaye jarumta da iya soyayya. Hanan
ta gode wa Allah da bai kufce ma ta ba. Ta gode
wa labarin shayin gishiri sa, da ya fizgo hankalin
ta gare shi. Labarin waxanan masoya Hanan da
Haneef bai tsaya a iya zance ba. Sun yi aure sun
ci gaba da soyayya. A kullum tana haxa masa
shayi, sai ta zuba masa gishiri kaxan. Haneef ya
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
46
karva yana sha, yana ta ma ta murmushi har ya
shanye.
Bayan shekara arba`in cikin begen juna da
soyayya, tare da shan shayi mai gishiri.sai
Haneef ya rasu ya bar wa Hanan wata wasiqa.
Wannan wasiqar ta tona sirrin da ya voye tsawon
shekaru.
Yace “masoyiyata kiyi min afuwa. Na
rayu da ke da wata qarya iya rayuwa ta. Wannan
qaryar xaya, ita ce kaxai na san nayi miki. Idon
kin tuna farkon haxuwar mu a ranar na riki ce
ainun. Saboda tsabar son da na ke miki. Shi yasa
maimakon na ce abani sukari, sai nace gishiri.
Yadda ki kayi, sai ya burgeni. Shi ne naka
sa janye maganar gishirin. Na qirqiri wannan
labarin kogi na baki a gaskiya bana jin daxin
shayin gishirin nan. Soyayyar ki ce kawai ta
sani. Nake shan sa kullum don in ciga ba da
birge ki, kamar yadda nace tun farkon haxuwar
mu.
Bayan mun yi aure, na yi qoqarin faxa
miki. Amma sai na tuna mun yi alqawari ba za
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
47
mu yi wa junan mu qarya ba. Sai kawai na ji
tsoron vata miki rai, idan ki ka san gaskiya. Sai
na haqura, nake ta shan shayin gishiri.
Yanzu kuwa tun da lokacin mutuwa ta ya
yi. Shi ne ban jin tsoron ki sani, na rubuta miki
gaskiya. Kai wannan shayin gishiri da rashin
daxi yake.
Babu shakka tun da na haxu da da ke, na
ke azabtar da kaina da wannan shayi. Ina
matuqar son ki zan iya sadaukar da komai
saboda ke. Da za`a qara bani aron wata sabuwar
rayuwa. Da zan cigaba da shan shayin gishirin
nan cikin murmushi. Mu qara zaman soyayya da
begen juna tare da ke.
Hanan tai ta kwarar da zazzafan hawaye.
Qaunarsa ta qara rivanya wa. Kewarsa ta dame
ta. Ga shi ya riga da ya rasu ya barta.
Tun bayan kammala karatun wannan
wasiqar da marigayi Haneef ya bari. Sai Hanan
ta shiga shan shayi da gishiri. Tace “soyayya
abace da bata gushewa, abace mai sa ayi afuwa
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
48
ga juna. Ba`a haqura, sai dai a tabbata cikin
kogin soyayya.
Hanan ta ce yakamata ka so wanda duk
yake yawan tunaka. Wanda ya ke qaunarka ta
gaskiya wanda ya ke alfahari da kai. Zai iya
nunawa abokan sa, ya na ji da kai. Wanda zai
hana idonsa bacci, don ya kula da ke. Wanda zai
iya nuna ki a matsayin ta sa. Ko da kin jiqe da
gumi ga gajiya (ba kwalliya). Wanda zai dinga
kiran ki “Yaa sarauniya ta!” “Yaa kyakkyawa
ta”!
Ba shakka ina alfahari da Haneef yana
raye, kuma ina alfahari da shi bayan mutuwarsa.
DARUSSA:-
Maza aka sani da fara gabatar da abin
bajinta, kyakkyawar kulawa ga mace. Idan
ka nuna wa mace qauna soyayya da
kulawa. To tabbas zaka mallaki zuciyar ta.
Zata lillive ka da ninkin ba ninkin na
soyayya.
Namiji zai iya auren kowacce mace.
Komai kuxinta, sarauta, ko kyau. Kuma su
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
49
zauna lafiya ta lilleveshi da soyayya da
biyayya. Tamkar ta auri wanda ya dace da
ita, don haka yana da muhimmanci maza
su koyi soyayya.
Soyayya tana cigaba koda xaya daga cikin
masoyan ya rasu yabar xayan. Shi ya sa
yake da muhimmanci a kafa aure akan
ingantacciyar soyayya
4.6 LABARIN JARUMI NA MAGAJIYA
A shekarun baya anyi wata baiwa Allah
mai suna Magajiya. Magajiya ta samu karayar
zuciya (broken heart) adalilin mutuwar auren ta.
Saboda aganin ta, zai wahala ta samu mutumin
da zai bata kulawa da soyayya kamar yadda ta
samu a wajen mai gidanta.
Soyayya mai tsanani, kuma da shaquwarta da
mijin na baya. Ya sanya shima mijinta, ba zai iya
jure barinta ba. Saboda haka, ya tarkato ya shiga
layin zaurawanta. Ya na ta lallashi da ban baki ta
koma xakin ta.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
50
Magaji mutum ne mai kirki. Don kuwa ya na
da addini, riqon iyali da gaskiya. Gashi rayuwa
ce ta wanka tare, cin abinci tare, hira tare da
sauran su.
Bashakka da ace babu rigima surukai da
Magajiya ta koma xakin ta. Sai dai haka Allah ya
qaddara rashin komawar nan shi yafi alkhairi.
Domin al-amuran sun yi girma da tsananin da
komawarsu ba kwanciyar hankali.
Magaji ya azabtu sosai kamar yadda alamu
suka bayyana a tattare da shi Na yawan zullumi
da tunani. Sai dai tunani waxanda da suka rura
wutar raba su, su ka nu na masa yai aure shine
zai samu salama. Hakan kuwa akayi, nan da nan
yai auren sa.
Ita kuwa Magajiya bayan yawan tunani da
zullumi. Sai ya zamto ma gaba xaya ta sare da
soyayya da Namiji. Balle kuma ace zancen aure.
Saboda haka ta sa karatun addini, da karatun
boko a gaba. Ta cike lokutanta da yawan
ambaton Allah. Don samar wa kanta nutsuwa. Ta
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
51
cika lokutanta da halartar wa’azi. Da kuma
karance-karance har ma da sana`a.
Akwana a tashi sai ta dinga samun sauyin
tunani, tare da rage tsoron maza daya shiga ranta.
Bayan wani tsawon lokaci sai Magajiya ta
fara fuskantar ta yi daga mutane daban-daban.
Tun ta na janye wa da basarwa har ta haqura
tafara sakin jikin ta. Saboda qorafe-korafen yan
uwa da abokanan arziqi.
Allah Al-musawwiru sai ya fito da wani
jarumi wanda ya yi kukan kura ya dage akan nu
na soyayyarsa ga Magajiya.
Aikuwa dai ya yin da jarumin ya samu izinin
fara nemanta, don su fahimci juna. Ashe Magaji
kamar ya na lave.
Wata rana jarumin ya taho zance wajen
Magajiya sai kuwa wani saurayi ya tare shi yayi
masa gargaxi cewa. An umar ce shi da in ya na
son kanshi da lafiya to ya daina zuwa zancen
nan.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
52
Jarumin bai xauki wannan abakin komai ba
wai an tsikari kakkausa, yaciga ba da zuwa
zancen sa.
A karo na biyu ansake aiko da gargaxi. Aka
shaida masa sharri da qage wani kage da ake wa
Magajiya. Yana tunanin wannan zai sa ya guje
ta. Amma ina! Gogan na ka ya yi nisa. Bai
daddara ba ya ci gaba da zancen sa.
A karo na uku dai aka sake tare Jarumi a
hanyar sa ta zuwa zance wajen sahibar ta sa.
Shine ya ce ma sa idan har ka matsa sai ka auri
Magajiya to ka tabbatar ka na iya rasa rayuwar
ka don kuwa kasan waye tsohon mijin ta ?
Jarumi ya ce wani ne yace ya sake ta?
“ka da ke ni ko ka yanka ni duk xaya ne”
Jarumi ya qara da cewa: Insha Allahu aure
na ni da Magajiya fa tamkar an xaura. Ko zan
rasa numfahshina akanta, to babu fasawa.
Magajiya na ganin irin abubuwan da ke
faruwa sai ta nemi da su canja inda su ke zance
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
53
ita da jarumi. Shi kuma jarumin yai murmushi,
ya ce “me kike voyewa? Ni fa ba na tsoron
komai akanki. Zan iya ba da komai nawa saboda
ke. Ina matuqar qaunar ki. Ban tava jin ina son
wata irin soyayyar da na ke miki ba”.
Bari ma in baki labarin gargaxin da ake ta
yi mini. Wannan tsoratarwaba tai min komai ba
face qara min soyayyarki. Don Allah ki bani
dama azo a kawo sadaki, a xaura mana aure
mana cikin satin nan.
Wallahi da ace ana shafa fatihar xaurin
auren mu. Zan faxi in mutu to Alhamdulillah na
amince. Daga nan ma a wuce da ni maqabarta na
cika burina, na zamanto mijinki. Ballanta na ma
zaman auranmu za mu yi fes. Don kuwa ba
mutuwa zan ba, ke ce ruhina kuma rabin raina..
Ganin hawayen Magajiya ya dakatar da
shi. Menene ? Magajiya ta ce: ban tava zaton zan
samu wani ya nuna min soyayya kamar haka ba.
Ga adireshin waliyyinmu da ke xaura ma na
aure. Ka je ka gaishe shi. Ni kuma a gida zan
shaida musu na amince.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
54
DARUSSA
1. Jarumtaka ta na da muhimmancin gaske a
soyayya ta na sa nan da nan namiji ya
samu martaba a wajen mace. Saboda haka
ne muke ganin yadda maza da yawa ke
koxa kansu ko da kuwa abin da suke faxa
ba gaskiya bane. Su nayin hakanne don
nuna jarumtaka saboda su sami kwarjini a
wajen masoyiyarsu. A cikin waqoqi da
yawa akwai baitoci da masoya ke nuna irin
jarumtarsu.
2. Mane ma daban-daban sun nemi aurenta
sai gashi jarumi daga nuna jarumtarsa sai
yayi nasarar samun amincewarta. Wannan
na nuna mana muhimmancin zama jarumi.
3. Idan aure ya mutu, yana da muhimmanci
musulmi ya rungumi qaddara. Ka da
mutum ya qi haqura har yai ta bin
munanan hanyoyi ya varar da lahirarsa,
saboda neman dawo da wacce ya rasa.
TASIRIN SOYAYYA NA AMINA YUSUF GWAMNA
55
KAMMALAWA
Kowanne mutum na da bukatar soyayya a
rayuwarsa. Ashe ya zama wajibi mu san
yadda za mu inganta soyayyarmu.
Wassalamu alaikum